Showing 147001 words to 150000 words out of 186858 words
yana tura hancin motar tasa ciki.
Cike da
ɗ
oki wasu jami'an samari biyu suma suka iso garesa dai-dai yana bu
ɗ
e motar ya fito. Wellcome sir!”. Suka ha
ɗ
a baki wajen fa
ɗ
a. Murmushi yay musu tare da m
iƙa masu hannu alamar suyi musabaha. Ɗabi'arsa ce hakan tunkan yay balaguron da babu wanda yasan ina yaje, sudai sun bar ganinsa ne kawai. Hannun suka bashi suma suka gaisa. Kafinyay musu nuni da Kayayyakinsa da ke cikin motar alamar su
ɗ
ebo.
Ya
yinda shi kuma yake bin ko'ina na station
ɗ
in da kallo cike da kewa, duk da dai yakan shigo dama a sace cikin
ɓ
adda kama.
Duk da dare ne akwai jami'ai sosai a ciki ta kowanne department, kuma mafi yawancinsu sun duƙufa ne akan batun Master
ɗ
in, dan
shine aikin da gaba daya ya birkita kowacce hukuma daga jiya zuwa yau.
Duk ta inda ya gitta sannu da zuwa ake masa bisa balaguron da yay na kusan shekaru biyu da rabi da girmamasa tamkar yanda shima yake bama kowa girma a rayuwarsa. A gefe kuma abo
kansa da manyansa na nuna jin da
ɗ
in dawowar tasa a dai-dai ga
ɓ
ar daya dace. Masu kuma jin haushinsa najin takaicinsa dan mutum ne jajirtacce akan duk abinda yasa gaba tun ma yana ƙaramin
ɗ
an sanda.
Katafaren office
ɗ
in da yafi kowanne girma da al
farma a headquarter
ɗ
in ya nufa kai tsaye su Rayyan biye da shi. Tun kan ma suyi knocking aka bu
ɗ
e musu ƙofar alamar ansan da zuwansa. I.G da ke zaune shi da wasu manyan ginshiƙai na hukumar ƴan sandan EFCC da General na sojoji suka maida hankalinsu ga ƙof
ar fuskokinsu cike da fara'ar tarbar gwarzonsu, wanda ya yarda zai sadaukar domin ƙasarsa da yankinsa bisa aikin sirri na ha
ɗ
in kai da suka shirya a tsakaninsu kawai saboda tashin hankali da rikicin da kowa ya kasa gane bakin zarensa a yankunansu..........
✍
_________________________
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI......_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHA
DI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA
SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA
'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUC
IYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017
082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*
🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BI
YAR
🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏🏻
_*
*_Chapter Forty_*
..........A kallo
ɗ
aya da sukai masa suka fahimci lallai bashi da wadataccen lafiya, dauriya da jarumtace kawai irin tasa ya sashi amsa kiran nasu. I.G
da gaba
ɗ
aya dama burinsa yaga halin da Master
ɗ
in ke ciki dan bashi da nutsuwar zuciya akan harbin da akai masa tun jiya ya mike da sauri ya nufesa.
Dai-dai master na karasowa garesa ya dan kame jikinsa alamar girmamawa. “Shuraim wannan ganganci
ne ai. Shiyyasa nace maka basai kazo ba a wannan halin da kake ciki ka aiko Habib kawai”.
Murmushi Master yay mai ciwo, cike da girmamawa a garesa ya ce. “Karka damu Uncle ina lafiya. Idan mun biyema ciwon da kawai mukeji a jiki su kuma masu ji a
cikin zuciyoyinsu fa?. Tabbas inajin ciwo a jikina, dan shigar bullets a cikin jiki ba wasan yara bane, amma idan ina kwatantashi da ciwon da su wa
ɗ
anda babu inda zasu kai kukansu sukeji sai naga ban cancanci raki ba”.
I.G da ke murmushi mai ciwo
ya
ɗ
an bubbuga kafa
ɗ
ar Master. Tabbas shima yanajin irin ciwon da Master
ɗ
in keji a cikin ransa. Dan shine ma ya horesa akan wannan tsarin duk da dama shima yanada irin wannan zuciyar ta damuwa da halin da al'umma ke ciki fiye da kansa. Bin master
ɗ
in dak
e ƙoƙarin isa gaban Efcc Chairman da General yay da kallo, yana jin ƙaunar yaron matuƙa a cikin ransa tun kafin randa ya gansa a wajen taron bikin gama secondary school. Kwazonsa ya sashi jin kwa
ɗ
ayin biya masa ku
ɗ
in karatu.
Master da ya juya ga
General da efcc chairman duk da kuwa ha
ɗ
akace ta aiki ta ha
ɗ
asu dalilin I.G duk yana basu girma suma, kodan shekarunsu da ƙyaƙyƙyawar zuciyarsu. Ƙame jikinsa ya sakeyi da risinar da kansa ya ce. “Good Everning Sirs”.
Sosai ƙwazonsa da ƙoƙarin
mutunta na gaba da shi ke sake saka musu ƙaunar yaron a zuciya. Efcc Chairman ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha. Babu musu Master ya bashi dan shima yafi bukatar hakan. Shima General musabahan sukai.
Cikin nuna kulawa suka tambayesa jiki
nsa? Akan harbin da ya sha. Ya tabbatar musu babu wani damuwa yaji sauƙi. Karkuma su damu tsautsayi ne kawai.
Dukansu murmushi sukai, dan sun san dai Master
ɗ
insu ya fa
ɗ
a soyayya da gaske. Dukansu sun san Hibbah, tun harin farko data kai masa batare
da wani niyya ba I.G ya bashi shawaran aurenta, a cewarsa ba'a sakaci da irin wa
ɗ
an nan yaran masu ƙwazo. Ko basu fito duniya ta sansu ba zasu taimakama mazajensu da ƙasa a gidajen aurensu. Da farko Master yaso zillewa. Sai dai kuma shiga cikin ahalinta da
yay ya fahimci matsalar da suke ciki a hannun Halilu ya sashi amincewa. I.G
ɗ
in ma da kansa suka nema masa auren nata.
“Madam dai ta rantse sai da kasha bullets”.
Efcc Chairman ne mai maganar cikin ƴar tsokana. Dariya sukayi gaba
ɗ
aya, y
ayinda Master ya
ɗ
an kai hannu ya shafi ƙeyarsa yana murmushi shima. A zuciyarsa kam aiyanawa yake (ai itama yau tasha nata bullets
ɗ
in).
Sai da suka
ɗ
an gama barkwancinsu Master dai na tayasu da murmushi kafin su fara abinda ya tarasu. Cikin
nutsuwarsa da bama aikinsa dukkan hankalinsa ya fara musu bayani akan abinda suka buƙata. Harma da wanda basu san da shi ba.
Mamakin yanda Master ke tafida aikin da har wanda bai shafesaba ya basu. Shi dai
ɗ
an sanda ne,
ɗ
an sandan ma normal
ɗ
an s
anda. Sai dai a dalilin faruwar wani abu da ya shafi I.G yake
ɗ
aurasa akan wasu ayyuka na sirri da yake yi domin hidimtama ƙasa batare da wani mahaluki ya sani ba. General abokinsa ne, hakama Efcc Chairman. Kamanceceniyar halinsu na kirki yasa akoda yaushe
suke zaman tattaunawa akan abinda ya shafi yankinsu dama ƙasar baki
ɗ
aya. Wanda suna iya bakin ƙoƙarinsu sai dai sukan rasa a ina matsalar take akoda yaushe suna tufƙawa ana warwarewa?.
Akoda yaushe sai dai suyi zaman kawai su tashi, dan duk da ka
sancewarsu manya masu fa
ɗ
a aji a hukumomin tsaro basu iya yin komai dake dai-dai da burikansu. Aikin da I.G ya fara
ɗ
aura master a sirance yayi nasarane yaja ra'ayinsu gareshi har sukai kwa
ɗ
ayin dinga sakashi ayyuka na musamman, duk da kuwa shi baida alaƙa
r aiki da su ta wani fanin. Ba yau kawai bane Master ya fara musu aiki. Yasha zaƙulo musu bara gurbi a cikin jami'ansu da manyan mutanen dake akan karagun mulki, kuma idan sukabi diddiginsu sukan samu abinda suke buƙatar.
Bai wani jimaba tare da su sa
boda halin da yake ciki, sun tabbatar ƙarfin haline kawai yakeyi badan lafiya ta ishesa ba. Sallama yay musu akan zai ƙarasa sauran ayyukan da suka rage masa na tattare dukkanin bayanai na kowanne fanni nan da kwanaki biyu insha ALLAH da zasu kasa komai a
fai-fai dangane dasu A.G da ire-irensa. Daga haka yay musu sallama ya fito cike da dakewa kamar yanda ya shigo. dan baya buƙatar wani ya fahimci halin da yake ciki musamman akan ciwukan harbin dake tare da shi.
★★★★
Gudu yayi sosai akan t
itin, hakan yasashi isowa gidan cikin ƙanƙanin lokaci duk da kuwa ya
ɗ
an tsaya a wani waje. Ledojin dake bayan motarsa na tsarabar su Habib ya
ɗ
iba zuwa sashensu. Koda ya shigo suna baje a falo suna aikin da ya sasu, sai dai hakan bai hanasu shan shaftarsu
ta hira ba kamar ko yaushe. Ko sallamarsa basuji ba sai da Sharifat ta nufosa da gudu tana kiran “Uncle oyoyo”.
Tattausan murmushi ya saki a karon farko yana ajiye ledojin hanun nasa ya kai duƙe dai-dai da tsahonta yana bu
ɗ
e mata hannayensa. Jikins
a ta haye tana dariya, ya lakaci hancinta shima yana murmushi da fa
ɗ
in, “Beauty
ɗ
in gidanmu batai barci ba”.
Sharifat data makale masa kafa
ɗ
a tai yar dariyarta da kwantar da kanta kan kafa
ɗ
arsa. “Uncle ina game ne a wayan Yaya Idris”.
“L
allai ƴar gatan Yaya Idris”.
Ya fa
ɗ
a yana kaiwa zaune batare da ya kula su Habib da sukai tsitt ba tun kiran da Sharifat tai masa. Ledojin daya ajiye ma Adam ne ya miƙe ya kwasosu. Leda
ɗ
aya ya amsa a ciki ya bama Sharifat. “Tom ga wannan maza ki cinyesa
duka ki kara ƙatuwa. Kina gamawa kuma ayi brush da alwalan barci ai addu'a. Ki gaidamin baba sai da safe”.
Cike da
ɗ
oki ta amsa sheƙa da gudu tana fa
ɗ
in, “Yeee thanks you Uncle ”.
Hannayensa ya har
ɗ
e akan ƙirjinsa yana binta da kallo da m
urmushi harta shige. Yana son yara matuƙa tun shima yana yaron, shiyyasa a yanzu bashi da babban burin daya wuce yaga jininsa a rayuwa. Numfashi ya
ɗ
an ja da gyara fuskarsa ya gimtse yana maido dubansa gasu Habib. A kusan tare suka ha
ɗ
a baki wajen gaishesa
da tambayarsa jikinsa. Cike da nazartar yanayinsu ya amsa musu dai-dai idonsa na sauka kan Habib da yaƙi yarda ya kallesa.
Dukansu tarbiyarsa ce, dan haka ko laifi sukai masa a ƙanƙanin lokaci yake gano wanda ya aikata
ɗ
in. Komai baice ba game da
abinda ke a bakinsa ya miƙe, kai tsaye ƙofar fita ya nufa, sai da yaje gab fitar batare da ya juyo ba yace, “Habib ka sameni”. Daga haka yay ficewarsa.
Dama tun kallon da yake binsu da shi suka sha jinin jikinsu akan an masa laifi, kowa fatansa
kar yazam shine ya aikata. Jin ya ambaci Habib ya sasu maida kallonsu kansa. “Yaron nan wane ruwa ka
ɓ
allo mana ne?”.
Cewar Musbahu cikin
ɗ
an tsoro. Harararsa Habib
ɗ
in yayi yana miƙewa yabi bayan Master
ɗ
in dan gudun sake wani laifin. Yana fita Adam y
ace, “Ni wlhy tun shigi da ficin danaga yanayi jiya akan waya nai tunanin hegen mai jajayen kunne wata tsiyar yake shiryawa. Sai dai banyi tunanin bahagon zaki zai
ɓ
allo ba”.
Salis yace, “Ni nasan laifin daya aikata, amma ku jira dai ya dawo muj
i a bakinsa”.
Kansu duk suka jinjina alamar gamsuwa. Kafin su ajiye aikin gaban nasu a koma bu
ɗ
e ledojin tsaraba cike da jin da
ɗ
i da farin ciki.
Habib kam koda ya fito can ya hango master ya
ɗ
ebo sauran ledan daya bari a motan. Nufarsa y
ay ya amsa suka sufi sashen nasa tare. Kamar yanda yabar falon a haka ya samesa. Ya kai zaune bisa kujerar 1seater yana
ɗ
an dafe kansa da ke masa ciwo har yanzun. Yasan akwai issue
ɗ
in jini tattare da shi, shiyyasa ciwon kan yaƙi barinsa sam. Bayansa ya kw
antar jikin kujerar da zare mask
ɗ
in fuskarsa ya ajiye, yana daura ƙafarsa
ɗ
aya kan
ɗ
aya, razanannun idanunsa ya zuba akan Habib dake tsaye kai a ƙasa.
“Miyasa ka aikata?”.
Yay maganar yana dauke idonsa a kansa ya maida ga takardun dake a sam
an centre table ya
ɗ
ebo su yana dubawa.
Habib da kansa ke ƙasa saboda girman laifin da ya aikata. Sanin halin yayan nasa akan buƙatar yin magana kai tsaye koda ta laifi ce, yace, “Itama taji irin ra
ɗ
a
ɗ
in da kaji”.
Master da bai
ɗ
ago ba
ya sake tamke fuska da cizar lip yana cigaba da aykin gabansa
“Yaushe na fara wasan banzan nan da kai?”.
Shiru Habib yay yana faman ha
ɗ
iyar zuciya.
Master da yaji shiru ya
ɗ
ago ido ya dubesa fuska a tamke. “Ince da kai nake magana ko
?”.
Yanda yay maganar a
ɗ
an zafafe yasa Habib
ɗ
in girgiza masa kai. “Yaya hakan dazan mata ne kawai zaisa na huce da ga abinda ya faru, itama kuma zata kiyaye sake yin wani yunƙuri makamancin hakan.”
Idanu kawai Master ya zuba masa saboda ma
makin Habib
ɗ
in matuƙa. Shiko yaki yarda ya kallesa dan yasan yayi ba dai-dai ba.
Kansa ya sake maidawa ga takardun, “Hum aure kake buƙata kenan? Ko ka fara neman mata ne?”.
Da sauri Habib
ɗ
in ya
ɗ
ago ya dubesa yana girgiza masa kai. “Wlh
y Yaya ni ko
ɗ
aya babu a raina. Kawai dai.....” sai kuma yay shiru bai ƙarasa ba
Takardun hannunsa ya ajiye ya maida hankalinsa gaba
ɗ
aya garesa yana sake tsuke fuska irin yanda bai ta
ɓ
a gani ba. “Ƙawai dai me?. ƙarya kakeyi, idan har baka neman m
ata taya kasan ka sakamin pills nasha dan naje ga mace koda babu niyyar haka a gareni.”
Habib da idanunsa suka ka
ɗ
a sukai jajur ya kai tsugunne gabansa. “Wlhy yaya ban ta
ɓ
a aikata zina ba ka yarda dani, kamar yanda na fa
ɗ
a maka kawai nayine dan kar
ta sake tunanin kwatanta abinda ta aikata, sannan inason ku rayu har abada”.
“Kai da wa kukai shawarar aikata hakan a cikinsu?”.
“Ni ka
ɗ
ai ne, dukansu babu wanda yasan abinda ya faru sai Yaya Abdull da ya bani”.
Idanu kawai master ya
zubama Habib
ɗ
in batare da ya sake cewa komai ba. Dama ya zargi babu wanda zaiyi wannan aikin garesa sai Abdull
ɗ
in. Tunda aka
ɗ
aura aurensa da Hibbah kullum cikin masa tsegumi yake su baby suke so da wuri. Habib da yaji yay shiru ya
ɗ
ago ya dubesa, shi k
a
ɗ
ai ne ya san ainahin fuskarnan a cikinsu, dan haka bai wani damu da ganinta a yanzu ba. “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri. Nasan nayi kuskure tunma kan na aikata hakan. Inason naga kunyi zama irin na kowa
ɗ
anne ma'aurata da ita. Bana son ka rabu da ita saboda ƙ
yawawan halayyarta. Duk da ƙarancin shekarunta tasan kanta matuƙa kuma tanada tarbiyyar da kowanne irin nagartaccen namiji zaiso ta kasance uwar ƴaƴansa. Mu
ɗ
in nan marayune, daga mace tagari kawai muke saran samun zuri'a mai albarka da zamu sake ginawa. W
adda zaka fara ginawa kuma itace ginshiƙin da zata riƙe tamu mu duka bakwai
ɗ
in”.