Showing 156001 words to 159000 words out of 186858 words

Chapter 53 - TAKUN SAKA COMPLETE

10 Sep 2026

26

/>
e tana kallon fuskarsa har batasan ta shagala ba. Sosai yaji idanu na yawo masa a j

iki, amma ya dake harda sauya saukar numfashinsa tamkar mai barci. Tunaninta barcin gaskiyarne ya

ɗ

aukesan. A hankali takai hannu bisa girar idonsa ta

ɗ

an gyara, sai kuma ta murza goshinsa ka

ɗ

an duk dan son ta tabbatar ba facemask ya saka ba. Sake kumawa t

ai kan la

ɓɓ

ansa nan ma dai taji, ta cigaba da shafa kumatunsa da siririn gashi na saje ke kwance har zuwa kunnensa ta

ɗ

an murza nan ma zuwa bayan kunnen da ƙeyarsa. Yanda take masa gaba

ɗ

aya tsigar jikinsa miƙewa take, ganinfa da gaske neman firgita masa j

iki takeyi sai da ya shammaceta ya bu

ɗ

e idanunsa da suka fara sauya kala. Aiko karaf suka fa

ɗ

a cikin nata. Saurin janye hannunta tai a fiskarsa amma ya riƙe ya dannesa da nasa. Gaba

ɗ

aya ta daburce, baya ta juya masa murmushi na kufce mata dan taji kunya h

arga ALLAH.

Shima murmushin ya saki da kwantowa bayanta yana son leƙa fuskarta. “Ki kalli mijinki nakine auta, yanda kike auta a gidanku insha ALLAH kece ta fari kece auta a zuciyar Shuraim

ɗ

inki. Karkiji komai, kiyi komai ba komai baby luv”.

Fuskar ta cusa a cikin filon, duk yanda yaso ya janye taƙi. Dole ya haƙura ya miƙe yana dariya da take mamaki. Tanaji ya shiga toilet ta sauke nannauyan ajiyar zuciya. Jin motsin ruwa ya sata tabbatar da wanka yake dan haka ta miƙe ta fara gyara ga

don, fatanta ta fice kafin ya fito. Tana cikin gyaran takardun daya ajiye idanunta ya sauka akan wadda ke sama da tsautsayi yasa file

ɗ

in ya

ɗ

an goce suka zubo. Tsugunnawa tai tana tattarosu sai taga tamkar sunan Abbansu a jiki. Duk yanda taso hana kanta d

ubawa ta kasa,

ɗ

aya bayan

ɗ

aya ta dinga dubasu sai taga duk takardun kaddarorinsu ne da ta ta

ɓ

a jin su Yaya Muhammad na maganar suna hannun Halilu. Mamaki ya kamata ta cigaba da dubawa har zuwa na ƙarshe da ke rubuce da dogon bayani. Ƙofar bayin ta

ɗ

an kal

l

a jin har yanzu akwai motsin ruwa yasata zaman dirshan ta fara karantawa a nutse..........



TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI......_*

*KINA DA BUQATAR TSA

FTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUW

AN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*

*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura

shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DAN

A SANI*

🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR

🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu

😭🙏🏻

_*



*_Chapter Forty Three_*

...........Bayanine tiryan-tiryan daya shafi takardun da harƙallarsu, harda ku

ɗ

a

ɗ

en daya k

washe na Halilun da yanda akai ya amshesu, da masu mallakin dukiyar da alaƙar dake tsakaninsa da su A.G. A yanzu kam Hibbah ta sake tabbatar da Master baya tare da su A.G

ɗ

in, duk da ya mata bayanin komai ta yanda ya shiga jikin nasu da tunanin shai

ɗ

aninsu

ne shi. Wasu irin irin hawaye suka gangaro mata saman fuska zuciyarta na tunano mata randa Isma'ill ya karyama Abba ƙafa akan abinda yay ma Ummi.....

Zare takardar da akai ta bayanta da

ɗ

isowar ruwan wankan jikinsa ne ya sata juyowa da sauri. Mast

er daya tamke fuskarsa matuƙa kamar bashine ya gama tarairayarta yanzun ba, ya

ɗ

an harareta yana

ɗ

aukar sauran takardun ya maida cikin file

ɗ

in. Ya ajiye ya juyo kawai yaji ta fa

ɗ

a masa jiki a bazata ta rungumesa da sakin wani marayan kuka. Babu shiri ya d

afe towel

ɗ

in daya

ɗ

auro a ƙugunsa dake neman fa

ɗ

uwa. Dama ba wani rigan arziƙi bane a jikin nata, hakan sai ya bashi damar jinta bisa fatarsa dake ta faman ra

ɓ

ar ruwa yanda ya kamata. Ya lumshe idanunsa yana riƙota da ƙyau shima da sakin nannauyar ajiyar

zuciya.

Baice komai ba sai yatsun

ɗ

ayan hanunsa daya tura cikin gashinta,

ɗ

aya kuma yana shafa bayanta a hankali, zuciyarsa sai wani irin zallo take da tsalle-tsalle kamar zata fito waje. Ganin kukan nata bana ƙare bane yajata suka zauna a bakin

gadon tana jikinsa. Fuskarta ya

ɗ

ago dasa babban yatsansa yana share mata hawayen.

“Miya faru kuma?”.

“Ka yafe min”.

Wani ƙasaitaccen murmushi ya saki yana

ɗ

an

ɗ

age gira sama, idanunsa na yawo akan fuskarta. “Ni baki min laifin komai ba”. Yay

maganar yana

ɗ

an sumbatar la

ɓɓ

anta.

Kanta ta girgiza masa hawayen na sake rige-rigen sakkowa. “Nasan na maka laifi, na fahimceka a bai-bai, amma wlhy karkaga laifina nima inada hujjata. Nagode, ALLAH ya saka maka da alkairi, ya cigaba da baka kari

ya a dukkan motsinka da al'amuranka. Abinda naji wajen su Abba da shegen jami'in nan yasa nake maka kallon bai-bai. Kuma koba niba duk wanda yaji tunda baisan gaskiya ba zaiyi komai kamar nine”.

“Na sani Muhibbat, shiyyasa naita miki uziri. Duk da

kin hasalamin zuciya a ranar, dan ka

ɗ

an ya rage ki bu

ɗ

emin dukanin aikina da zai iya sa harsu Ummi su rasa ransu ma. A hakanma ka

ɗ

an ya rage ki jefa rayuwarsu a ha

ɗ

ari, ALLAH ya taƙaita. Ina ƙaunar Ummi Muhhibat, hakama su yaya Muhammad. Bayan yaran nan da

kike ganina da su a yanzu ahalinki sune ahali na biyu da nake kallo mafi kusanci dani a duniya. Tun bayan rasa mahaifiyata Ummi ce ta fara dafa kaina taimin addu'a cike da soyayya. Taya kike tunanin bazanyi yaƙi a kan zuri'arta ba. Taya bazanso ha

ɗ

a jini

da ita ba.” ya

ɗ

aura hannunsa saman cikinta “Ina fata da addu'ar ALLAH yasa wannan cikin nayi ajiyar jinina da zai miki rakkiya zuwa wajen Ummina”.

“Nidai ba yanzu ba”.

Ta fa

ɗ

a tana tura baki da kwantar da kanta a kafa

ɗ

arsa.

“Haba baby lu

v kiji tausayina mana, Su uncle Habib mafa shi suke jiran gani”.

“Wa

ɗ

an nan na daina kulasu a gidan nan ai, dan suma haushina sukeji”.

Ƴar dariya yayi mara sauti da kamo hannunta ya

ɗ

aura bisa fuskarsa. “Kefa kikai musu laifi, kika sa aka h

arbar musu Yayansu. Ba dole suyi fushi da ke ba. Amma nasan da sunga kin

ɗ

an fara amai sun samu

ɗ

a zasu daina ai”.

Baki ta tura tana ƙara cusa kanta a wuyansa. “Ni dai nace ba yanzu ba”.

“To ai ya riga ya shiga insha ALLAH, dan ban bug

a ƙwallona da wasaba tun a farkon fari”.

Tashi tai zata bar jikinsa da fa

ɗ

in, “Nidai babu ruwana wlhy inada kunya”.

“Nima ai inada ita. Bakiga tun shekaran jiya kunyarki nake ji ba”. Yay maganar yana binta da kallo.

Juyowa tai t

a kallesa da

ɗ

an waro idanu tana riƙe ha

ɓ

a “Kai

ɗ

inne kake wani jin kunyata?”.

A yanda tai maganar da waro idanun da bage bakin ya bashi dariya, amma sai ya gimtse baiyiba, yay

ɗ

an murmushi kawai da

ɗ

age gira

ɗ

aya. “Baki yarda kin kalleni ba yazaki

gani. Idan kina son tabbatarwa zoki gani”.

Kafinma ya rufe baki

ɓ

urum ta fa

ɗ

a toilet da sauri. Murmushin fuskarsa ne ya sake fa

ɗ

a

ɗ

a. Ya miƙe domin shiryawa yana godema ALLAH da wannan farin ciki daya bashi a lokacin da bai zata ba. Harya kammala shi

rinsa tsaf cikin ƙananun kayan nasa na fama Hibbah bata fito ba. Yasan inhar tanajin motsinsa a

ɗ

akin kota gama bazata fito ba. Dan haka ya tattara wayoyinsa da lap-top yayo falo.

Tun a ƙofar fitowa yaja ya tsaya saboda cin karo da baƙon dak

e zaune a falon ƙafa

ɗ

aya kan

ɗ

aya yana kallo. Abdull da ya

ɗ

an

ɗ

ago ya kallesa ya

ɗ

auke kansa yana wani shaƙiyin murmushi. Hararsa Master yayi da cigaba da takowa cikin falon. Ya zube kayan hannunsa saman centre table

ɗ

in da fisge remote

ɗ

in hanun Abdull

ɗ

in ya rage ƙarar tvn.

“Banza

ɗ

an nanaye ko ina ake sai an nuna hali”.

Murmushi Abdull

ɗ

in ya sake saki har da ƴar dariya. “Ni da kai a tantance

ɗ

an nanaye ai ayanzun. Mutumina kafa samu lafiya da alama. Na wani tada hankalina a banza harda

baro canada babu shiri”.

“To ubanwa yace kazo mai kan gwanda kawai.”

“Zakako cika baki yanzun tunda harbi yayi sauƙi, tsabar zalama ma ga ciwo sai da ka tafi kwa

ɗ

ayi filin ball”.

Murmushi master yayi dan Abdull ba ƙaramin tasa

rayuwarsa yake gaba ba. Shima mutum ne mara son hayaniya da yawan magana, dan harma yafisa miskilanci. Amma inhar suna tare to bakin Abdull cau-cau akansa.

“Wai yaushe ka shigo haka dan ALLAH?”.

“Tun randa aka harbeka. Daddy (I.G) ya sanar

min naji bazan iya kwana a canada banzo naga rabin jiki ba.”

Dariya Master yay yana gyara zama. “Shine sai yau nake ganinka, kazo kuma kanamin iskanci anan. ”

“Tun randa kasha harbi ina gidan nan, kai ne dai kai wahalar gani saboda ka

na daga lungu kana tsinkar fure.”

“ALLAH ya shiryeka to”.

Master ya fa

ɗ

a yana murmushi.

“Amin ya rabbi tunda addu'a kaimin. Ina madam

ɗ

in tazo na ganta, dan na huce zuwa yanzu tunda nasa an rama mana harbinmu”.

“Mara kirki, ALLAH

zai saka mata ai”. Master ya fa

ɗ

a yana miƙewa. Dariya Abdull yayi yana binsa da kallo, “Eh lallai ka shiga hannu

ɗ

an gimbiya. Da alama dai ƴar shilar nan taka tauraruwa ce cikin taurari”.

Master da ke ha

ɗ

o musu coffee yay murmushi kawai batare da

ya bashi amsa ba. Sai da ya kammala ya dawo falon ya ajiye a centre table ya zuba musu sannan ya zauna bayan ya mikama Abdull

ɗ

in nasa.

“Bestie ya yarana da madam?”.

Abdull ya

ɗ

an

ɗ

age kafa

ɗ

a da fa

ɗ

in, “Lafiya lau suke, sunata gaisheka.”



“Ina amsawa, nayi kewarsu da yawa gaskiya”.

“Karka damu suna gab da dawowa kusa da kai insha ALLAH. Ya gwagwarmaya? Daddy nata bani labarin ayyukanka da jajircewarka. ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara girma”.

Master dake murmushi ya kai ko

fin coffee

ɗ

in bakinsa ya

ɗ

an kur

ɓ

a. “Uncle baya gajiya da yabona, shi baya tsoron kar wataran naci amanarsa”.

Harararsa Abdull

ɗ

in yayi ya

ɗ

auke kansa. Zaiyi magana Hibbah da batasan da zaman Abdull

ɗ

in ba ta fito cikin shirin son zuwa gaida baba Sau

de yau. Ganin Abdull

ɗ

in na kallon hanyar bedroom

ɗ

inne yasa Master juyawa ya kalla wajen shima. Numfashi ya

ɗ

an ja a hankali ganin yanda kayan sukai mata ƙyau, baiyi zatonma zasu mata ba a lokacin daya sayesu. Ganin ta

ɗ

an daburce kamar zata juya yay mata

alama da idanu tazo. Babu musu ta gyara ƙaramin gyalen data yafo saman wando da rigan parkistan

ɗ

in ta nufosu cike da nutsuwa tamkar ba ita ba. Abdull da tuni ya

ɗ

auke kansa da ga kallonta ya maida ga tv yace, “Amarya baƙya laifi ko kin kashe

ɗ

an masu gid

a”.

Murmushi Hibbah tai da kaiwa zaune a kujerar da ke kusa da ita. Cikin girmamawa ta shiga gaida shi. Shima amsa mata yay da kulawa yana kallon Master da ya cigaba da shan coffee

ɗ

insa yana saurarensu.

“Amarya yaya kina kulamin da bestie

na sosai ko?”.

Murmushi tayi, dan gaba

ɗ

aya jitai kunya ta dabaibayeta. Sai take ganin kamar kowa zai iya fahimtar halin da take ciki tsakaninta da Master yanzun. Shi dai Abdull ya cigaba da tsokanarta ne. Yayinda ita kuma ta kasa amsawa dan kunya.

Sai da ya gaji dan kansa ya barta. Master dai bai tanka musu ba har sai da Abdull

ɗ

in yay shiru sannan ya duba Hibbahn, saboda nutsuwar tata yay masa da

ɗ

i.

“Muhibbah!”.

Ya kira sunanta a hankali. Ɗan

ɗ

agowa tai ta dubesa da amsa masa. Ganin ita y

ake kallo ya sata sake maida kanta ƙasan.

Ya

ɗ

an sake kwantar da bayansa jikin kujera yana kallon nata. “Wannan sunansa Abdul-Hakim. Aminina ne kuma

ɗ

an uwana. Likita ne a yanzu haka yana zaune a canada tare da iyalinsa da yaransa biyu”.

Jin

yayi shiru ne yasa Hibbah jinjina masa kanta. Tace, “Masha ALLAH Yaya sannu da zuwa. Ka baro su lafiya?”.

Abdull da Hibbahr ta birge ba kamar yanda yake tunanin ganintaba yay murmushi, “A lallai na samu ƙanwa kenan. To ina godiya sosai Muhibbat

. Suna lafiya, suna kuma gaisheki”.

“Nagode ina amsawa”.

“Nima nagode sosai da samun tarba daga gareki”.

Kanta kawai ta jinjina masa tana miƙewa. Rasa madafar ina zata dosa ya sakata nufar kitchen, a yanda ta samu kitchen

ɗ

in sai kawai y

a birgeta taji sha'awar yin abinci a ciki. Ƙofar baya ta fita ta kitchen

ɗ

in, wadda daga nan babu nisa da sashen su Habib. Babu wani tunani ta nufi can. Sai dai bata samu kowa ba sai baba Saude da taji da

ɗ

in ganinta. Dan sai tambayoyi take mata akan yaya t

ake? Ina ta shiga? Yaya jikinta?.

Hibbah da itama tai kewarta harsu Habib

ɗ

in ma da Sharifat ta amsa mata cike da girmamawa. Daga nanne suka

ɗ

an ta

ɓ

a hira har Hibbah ta sakko zancen sonyin girkin amma ta duba a can sashen babu kayan abinci.

Kar

an farko da baba Saude taji aranta kodai akwai alaƙa ta aure tsakanin Master da Hibbah ne? Kamar zata tambaya dai sai tai shiru. Sai ma sanar mata da tai cewar gama breakfast

ɗ

insu nan tun

ɗ

azun take jiran shigowar su Salis sukai amma babu wanda ya shigo t

un fitar safe da sukayi.

A nutse Hibbah ta amsa mata har baba Saude na mamakin yanda ta canja mata a ƙanƙanin lokaci. Sai dai ta danne a ranta ta bita da kallo harta fice.

Koda ta dawo sashen nasu a yanda ta fito ta kitchen da babban tray



ɗ

in sai Abdull yay tunanin ita ta ha

ɗ

o musu abincin, Master dai da kallon mamaki ya bita amma sai baiyi magana ba harta kai trayn ajiye saman centre table.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login