Showing 81001 words to 84000 words out of 186858 words
Da gudu Ammar ya taho ya rungume Isma'il ta baya yana dariya da hawaye a l
okaci
ɗ
aya. Hakan yasa Ummi ma da tai mutuwar zaune tana kallon
Isma'il
ɗ
in ta miƙe zuwa garesu. Hannun Isma'il ta riƙo cikin nata hawaye na sakko mata saman kumatu. Jawo hannun nasa tai ta zaunar da shi akan kujera tare da
ɗ
aukar goran ruwa da ke a saman
centre table da aka ajiyema baƙi ta
ɓ
alle murfin ta
ɗ
ora masa a baki tana shafa kansa.
Babu musu ya hau sha yana jan ajiyar zuciya. Sai da ya shanye shi tas ta janye goran tana cigaba da shafa kan nasa.
A hankali ya lumshe idanunsa da komawa b
aya ya jingina jikinsa da kujerar, numfashinsa tun yana sauka da zafi-zafi har ya koma sauka a hankali alamar zuciyarsa nayin sanyi.
Ummi ta share hawayen fuskarta tanayin murmushi da duban su Yaya Usman da har yanzu ru
ɗ
ani da al'ajabin mamakin Isma'
il
ɗ
in ya gaza barinsu. Matsowa sukai gareta. Yaya Umar da yaya Usman suka rungume Isma'il
ɗ
in. Yayinda Ammar yazo ya zauna gabansa ya
ɗ
aura kansa a saman cinyarsa fuskarsa washe da dariya tamkar gonar audiga.
Hannu ya kai a hankali bisa kan Ammar yan
a shafawa. A karon farko ya saki murmushi da
ɗ
ago kansa ya na kallon Ummi da su Yaya Muhammad.
“Kiyu haƙuri Ummi, lamarin mutanen nan sai da over acting. Na fahimci wannan ce kawai mafita a garemu. Inba haka ba sai wata fitinar ta kaure har akai ga
jima wani ciwo”.
Yanda yay maganar cikin sanyin murya tamkar yanda suka sanshi ne ya saka su Yaya Usman sakin ajiyar zuciyoyi.
“Amma Isma'il ka bani tsoro matuƙa wlhy, har mun fara tunanin ko baka da lafiya ne”. Cewar Yaya Muhammad yana mu
rmushi.
Ɗagowa Isma'il yayi zaune sosai yana saki ƴar dariya. “Yayanmu lamarin tsohuwar nan ne sai da haka. Sai dai fa nasan wlhy ba haƙura sukai ba, dan da alama na jima wancan wawan yaron Junaid ciwo a haƙarƙari. Ummi inhar shirinku na barin gidan
nan na nan to lallai dole ne ki tafi kema a yau
ɗ
in nan. Kamata yay ma ace yanzu kawai. Kinga sai ki tarbi amare da kanki”.
Yaya Abubakar da har yanzu shi dai yake kallon Isma'il
ɗ
in cike da nazari da wasiwasi ya gya
ɗ
a kansa cikin gamsuwa. “Wannan
mafita ce mai ƙyau. Dan Abba kam ba kanwar da za'a lasa bace aji kaifi kawai. Ummi kamar yanda Isma'il
ɗ
in ya fa
ɗ
a barin gidan nan yanzu shine mafita kawai”.
Sosai itama Ummi ta gamsu da zancen. Dan duk abinda zai
ɓ
ata mata taron auren yaranta bat
a fatansa. Sarai kuma ta fahimci abinda su Hajiya mama ke burin yi kenan. Sai dai kuma cikin damuwa da rauni ta ce, “Tanee
ɗ
in fa an ganta?”.
Da sauri Yaya Umar ya gya
ɗ
a mata kai. “Eh karki damu tana tare da ƙawayenta ashe. Zuwa anjima nasan zata
bi masu kai su can kawai”.
Duk da zuciyarta a raunane take hakan bai hanata gamsuwa ba. Ta mike tana warware mayafinta da dama tana tare da shi tun
ɗ
azun ta sake yafawa. Dama ba wani muaten bane sosai a sashen. Makwafta da suka shishshigo sukai ma
ta ALLAH sanya alkairi duk sun fita saboda yamma tayi sosai. Sai ƙawayenta na kusa sosai irinsu Hajiya Mardiyya. Suko sunsan da shirin barin gidan. Dan dama sune zasuje amsar amare acan. Jin hukuncin da su Yaya Muhammad
ɗ
in suka yanke ne ya sakasu mimmiƙew
a suma suka hau kimtsawa.
Su Ummi basu da matsala da komai na sashen dan sun tsince masu muhimmancin sun killace sauran. Su hajiya mama nacan akan Junaid cike da ru
ɗ
ani suka samu suka fice dan dama gari ya fara duhun magrib da ake ta faman kira a ma
sallatan anguwar. Mutanen da ke a tsakar gida kuwa gulma da tsugudidin da suka ha
ɗ
a kai sunayi group-group yasa basu hankaltu da su Ummin ba. A tunaninsu kawai ƴan biki ne zasu wuce gida.
★★★★★
A can L.E street k
uwa cike da farin ciki da ƙaunar yaran har cikin rai baba Saude ta mike domin gabatar da sallar la'asar
ɗ
in itama. Tana idarwa ta fito ta hau shirya musu abincinsu na rana da basu ci ba.
Kasancewar yunwar kuwa na ƙwaƙular cikinsu ana idar da s
allar la'asar
ɗ
in suka dawo gidan. Sai dai su ka
ɗ
ai suka shigo falon banda Master da yay zamansa a ƴar runfar bunun da ke a gefen swimming pool
ɗ
in gidan. Dan yasan tunda suka dawo gidan shegen surutinsu ba zai barshi ya huta yanda yake bukata ba.
Suko da ga can cikin zalamar kayan da
ɗ
in da baba Sauden ta baje musu a babban dining
ɗ
in suka baje da fara
ɗ
urama cikinsu. Yayinda kowa ya fara kai lauma sai sabon surutu ya
ɓ
alle, baba Saude na gefe na musu dariya kamar yanda ta saba har suka kammala. Su
ne suka za
ɓ
ar mata
ɗ
akin da zata zauna anan downstairs
ɗ
in. Hundred percent kuwa ta gamsu da
ɗ
akin, dan yana
ɗ
an nesa da
ɗ
akunansu ga shi kuma gab da kitchen.
Sune suka shiga gyara mata komai duk da bama wani datti bane da
ɗ
akin. Bayan sun kammala
Salis yay list
ɗ
in abubuwan da yasan Baba Sauden zata buƙata na amfani musamman a toilet. Da ga haka suka dawo falo kowa ya kama hidimar gabansa. Lokaci-lokaci suka sakko zancen Zaidu da ke can gidan su Hibbah yana gano duk cakwakiyar da ke faruwa batare d
a kowa ya fahimci shi
ɗ
in wanene ba.
*_8:16pm_* ya shigo gidan. Lokacin su Idris da dawowarsu da ga sallar isha'i babu jimawa na baje a falo suna kallon ƙwallo. Duk sun cika falon da hayaniyar gaddamarsu.
Khalid da ya fito da ga kitchen riƙe d
a drik ne ya fara farga da Master da ko sallamarsa basu ji ba. Cikin
ɗ
an daga murya yanda zasu fahimta ya ce, “Barka da dawowa Master”.
A take falon kuwa yay tsit duk suka juyo ga ƙofa. Cikin
ɗ
an hararsu ya ajiye ledojin da ya shigo musu da shi ya h
aura sama da
ɗ
aya batare da ya amsa sannu da zuwan da suka ha
ɗ
a baki wajen masa ba. Suna ganin ya gama hayewa har rige-rige tasowa Zaidu da bai jima da dawowa gidan ba suke shi da Salis wajen zuwa su
ɗ
auka ledojin da ya jiye. Suma sauran tasowa sukai akan
ledojin cike da farin ciki da ƙaunar Mastern nasu.
“Dalla malamai karkuyi mana hayaniya anan kuja a samu barcin dole”. Cewar Adam yana harar su Zaidu da suka ƙanƙame ledojin.
Cikin ƴar dariyar shaƙiyanci Musbahu yace, “Wanann ka
ɗ
an da ga ai
kin Master. Balle fa yau ango yake a gidan nan kuna ganin harda kazar tarbar amarya”.
A tare suka wage bakuna zasu ƙyalƙyale da dariya Idris yay musu nuni da sama. Saurin saka hannayensu sukai suka dafe bakunan kowa na ƙoƙarin danne ta shi. Da ga
haka suka koma tsakkiyar falon zaune Salis na ƙoƙarin bu
ɗ
e ledojin dake
ɗ
auke da kwalayen pizza da shawarma.
Sosai suka shiga farin ciki kowa yaja shawarma
ɗ
aya dan dama a lissafe suke. Pizza kuwa kwali hu
ɗ
u ce itama.
Da ga
ɓ
angaren og
a Master kuwa koda ya haura sama a falo ya ajiye ledar ya nufi bedroom
ɗ
insa. Kusan mintuna goma sha biyar sai gashi ya fito. Ya sake
ɗ
aukar ledar ya nufi
ɗ
akin da ya kai Hibbah
ɗ
azun. A yanda suka barta a haka ya isketa. Ya ajiye ledan a saman mirror fusk
arsa na sake tsuƙewa. Ledar da Habib ya ajiye
ɗ
azun ya
ɗ
auka. Ya zaro handkerchief
ɗ
in cikinta yana nufar gadon. Wata ƴar ƙwafa yayi dai-dai yana ranƙwafowa akan Hibbah da batasanma ya nai ba. Kansa tsaye ya
ɗ
ora handky
ɗ
in saman hancinta. Tsahon minti
ɗ
ay
a taja wani irin dogon numfashin da zai iya razanar da mai tsoro. Bai
ɗ
aga handkerchief
ɗ
in ba sai ma sake danna mata shi da yay akan hanci.
Numfashin ta kuma ja da ƙarfi tare da sakin tari lokaci guda. Ya janye hannunsa da jikinsa yana mikewa da ƙ
yau. Ganin yanda take jujjuya kanta da cigaba da tarin ya sashi
ɗ
aukar goran ruwan da ya ajiye a bedsite tare da
ɗ
ora kafarsa
ɗ
aya akan gadon ya sake ranƙwafowa kanta. Murfin gorar ruwan mai
ɗ
an sanyi ya
ɓ
alle ya shiga tsiyaya mata a saitin wuyanta duk da
akwai hijjab a jikinta har yanzu dan basu cire mata ba. Yanda yake kwarara ruwanne ya sashi tsalle har saman fuskarta zuwa ƙirjinta da kan gadon.
Tai wata irin zabura da jawo numfashinta da ƙarfi ya iso har cikin hancinta. Duk da wani irin nauyi da
jikinta yay mata hakan bai hanata
ɗ
ago hannunta ba ta shiga ƙoƙarin sharce ruwan da har yanzu yake kwarara matan.
Ɗayan hannunta ta kai cikin lalube da rashin ƙarfin jikinta da nufin ture ruwan da ke sakko matan. Sai dai hannun nata bai kai ba, s
ai kafarsa data
ɗ
an shafo ka
ɗ
an ta ajiyesa yaraf tana ƙoƙarin son bu
ɗ
e idanunta da sukai matuƙar nauyi.
Dakatawa yay da tsiyaya mata ruwan jin ta fara magana a fisge. “Y... y... ya... ya... Mu.... ham.... mad... kar... Kar...ku
ɗ
aura zasu kashe ku
”. Ta shiga fa
ɗ
a a rarrabe cikin ƙoƙarin fisgar numfashi da yunƙurin son tashi. Sai dai kuma luuu ta koma yaraf bisa gadon dan sam babu wani ƙarfi tare da ita. Hasalima abin bai gama sakinta ba baki
ɗ
aya.
Fahimtar hakan da yayi ne ya sakashi jan t
saki da cillar da goran ruwan yana sauke kafarsa ya miƙe tsaye sosai. Kallonsa ya kai ga agogon hannunsa yana sake tsuƙe fuska.
Tunanin mi yayi oho masa, sai kawai ya ja bargo a
ɗ
an fusace ya lullu
ɓ
a mata, tare da sake ranƙwafowa ya kama hijjab
ɗ
in jikinta yaja da ƙarfi ya farkesa. jansa yay baya ya fita da ga wuyanta. Da ga haka ya
ɗ
auka ledan da ya shigo da ita ya fice ransa fal takaici.
Bedroom
ɗ
insa ya wuce, duk da yana jiyo hayaniyar yaran nasa da ke cigaba da kallon ball da ciye-ciyen ab
inda ya kawo musun suna zabga gardamar da sukafi ƙwarewa akai.
★★★★
Su Ummi sun isa katafaren sabon gidan da su Yaya Muhammad sukai matukar ƙoƙari wajen ginasa. Dan babu abinda su Hajiya Mardiyya ke ambato sai masha ALLAH. Ƙwarai da gaske
matasan samarin na Ummi sun nuna ƙwazon da za'a yaba musu ƙwarai da gaske. Dan komai yayi cif a talauce ba'a sarauce ba. Sashen Ammar ne kawai ba'a karasa ba daga linta aka barsa.
Kai tsaye sashen Ummi da ke a farko suka shiga. Inda nanma dai su H
ajiya Nafisa keta sakama yaran albarka dan komai yayi a asashen tamkar bana dattijuwa Ummi ba. Akwai
ɗ
akin Ammar da na Hibbah a sashen Ummin.
Sai bedroom
ɗ
inta dana baƙi guda biyu. Ga babban falukanta biyu da kitchen da dining babba da ke
ɗ
auke da dogon di
ning table na family baki
ɗ
aya. A kallo ma zaka san sashen Ummin yafi kowanne sashe girma a gidan, sai dai nasu kawai upstairs ne su kuma. Itama kuma catai bataso shiyyasa akai mata nata flat da ya kayatu da zamani.
Suna shirin fara gabatar da sal
loli dan mazan sun fice sai ga kuloli ana shigowa da su. Cikin mamaki Ummi ke tambayar da ga ina?. Matasan samari biyu da ke shigo da kulolin suka bata amsa kai tsaye da fa
ɗ
in. Isma'il ne ya turosu.
Rasama mi Ummi zatace akan wannan yaro
ɗ
an albarka
tayi, sai kawai ta saki murmushi zuciyarta na ƙara jin matukar ƙaunarsa har cikin jini............
✍
*_Amin afuwa da jina shiru. Ciwo me ya kadani a bazata._*
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*
ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI......_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA
SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARU
BUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan la
mbobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*
🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR
🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏🏻
_*
*_Typing
📲
_*
*_Za
fafa biyar na ku
ɗ
i ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna ha
ɗ
aki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika sa
ɓ
a mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
*
_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK
👇🏾
_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr
66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK
👇🏾
_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
_________________________
*_Chapter Twenty Four_*
............Kusan karfe
tara na dare amare suka fara isowa. Sheikh Aliyu Abdul-Ra'uff Maina ne ya fara isowa da tawagarsa. A bisa al'adarsa na kai duk ƴaƴansa gidan aurensu kuma. Ba wani gayya bace yayo. Mota uku ce kawai ta ƴan uwansa mata sai
ɗ
aya mazan ƴan uwansa sai
ɗ
aya shi
da Amarya Maimunatu da ke jikinsa tana faman kukan rabuwa da gida tamkar kowacce amaryar ƙwarai.
Ya fara damƙata a hannun Ummi matsayin uwa kafin ya damkama Yaya Muhammad da musu addu'ar zaman lafiya da zuri'a
ɗ
ayyiba, harma da sauran angunan da
amarensu. Da ga haka yay musu sallama ya taho ransa fal kewar
ɗ
iyarsa data kasance ta ƙarshe a cikin ƴaƴansa da ya aurar.
Tamkar jira suna barin ƙofar gidan gayyar abokan su yaya Umar ƴan
ɗ
aukar sauran amaren uku suka iso anguwar suma. Dama su su
Yaya Umar
ɗ
in duk suna nan gida basuje ba. Suna can gefe sun kulle kansu suna tattauna batun Hibbah dan sam hankalinsu baya a kwance. Yaya Abubakar ma tun
ɗ
azun baya gidan da alama shima dai duk akan Hibbah
ɗ
inne.
Sosai gidan ya kacame da hayaniya.
Suma sauran amare duk sai da aka kawosu sashen Ummi aka damƙasu gareta kafin a mimmiƙasu sashen su. Wa
ɗ
anda bazasu kwana ba suka firfito domin a maidasu. Aka bar masu kwanan nan da ƙawayen amare.
Hayaniyar mutane yasa Ummi bata maida hankali akan r
ashin ganin Hibbah da akace tana tare da su Zahidah ba. Gaba
ɗ
aya hankalinta ya
ɗ
auke. Har takai gidan ya koma tsit batasan kai kawo da ƙulle-ƙullen da ƴaƴanta keta faman yiba akan autar tasu.
★★★★
A can gidan
ɓ
angaren su Abba kam