Showing 198001 words to 201000 words out of 216641 words
tabbata idan aka shiga tiktok za'aci karo da abubuwa masu amfani kamar yanda za'a samu na banza marasa amfani. Kawai dai shima bamai ra'ayin yawan biye-biyen shafuka bane kowanne iri. idan ma ya kama sai yabi abinda ya kaisa kawai yake zuwa
yayi saboda aikinsa na cimasa kaso mafi yawa na lokacinsa. Da sauri yabar inda su Mubeen suke ya nufi Shareff daya shiga mota da alamar barin wajen zaiyi. Bu
ɗ
ewa yay ya shiga gefensa.
“Please yaya k.....”
Hannu ya
ɗ
aga masa alamar kar yace komai.
“Ka gafarceni Yaya, ka bani to na tuƙaka”. Bai sauraresa ba ya tada motar ya fice dasu da gudu. Duk magiyar da Khaleel ke masa bai nuna yaji ko daya ba har suka iso gidansa cikin ƙanƙanin lokaci. Tun a gate mai gadi ya sanar masa Fadwa ta fita ai tare da
wata mata. Reverse yayi, nanma Khaleel nata roƙonsa amma ya sharesa. Kai tsaye gidansu Fadwan ya nufa, dan baiyi tunanin taje gidan bikin ba. Sai dai anan
ɗ
in ma dai maigadi ya sanar musu bataje ba, sai dai sunga hajiya ta fita zuwa gidan biki. Khaleel da
yasan ba saurarenaa zaiyiba yace, “Bara mu bincika ko tana can gidanmu din”. Bai tankaba nan ma. Khaleel kuma bai fasa kiranba. Cikin sa'a ya samu Amrah, ita ya tambaya ko Fadwa na gidan ta sanar masa eh tazo gashi ma ana rigima tsakanin Gwaggo Halima da w
asu dangin Mommy. Amma ga su Abba sun dawo gida yanzun nan....
Gudun da yay a yanzu yamafi na farko, dan cikin ƙanƙanin lokaci suka iso nan gidansu, sai dai sun sami rigima ta
ɓ
arke sosai tsakanin Mommy da danginta, da kuma Gwaggo Halima. Har Fad
wa ta mari aunty Sakina saboda itama tace zata mari Gwaggo Halima. Gida ya caku
ɗ
e harda dambe, Mommy na fa
ɗ
in Shareff yazo sai ya saki Fadwa a yau, Gwaggo Halima na iƙirarin itama sai Daddy ya saki Mommy a yau. Ran Daddy yakai ƙololuwar
ɓ
aci a yau shi da M
ahaifin Fadwa daya biyosu gidan domin yima su Mommy murnar an
ɗ
aura aure. Hajiya Luba mahaifiyar Bibah itace ta fara ganin Shareff. Ta nufesa tana kuka bayan ta gwargwa
ɗ
a ma Mommy cewar ga Shareff nan. Isowar Mommy inda Shareff
ɗ
in yake tana rantsuwar in b
ai saki Fadwa ba zata tsine masa Daddy ya dakatar da ita, sai dai kafin ya fa
ɗ
i abinda yay niyar fa
ɗ
a Abie ya dakatar da shi.
“Please yaya karka ce komai dan ALLAH, inaga ya kamata a zauna dasu ko yaya asan dalilin wannan tashin hankali. Ba'a gyara
ɓ
arna da
ɓ
arna na roƙeka”.
Da ƙyar Daddy ya saurari Abie a wannan ga
ɓ
ar, Gwaggo da dama haka takeso tai murmushi, sai kuma tai saurin nufosu tana matsar ƙwalla. “Ni wannan fitina ta wannan yara ta isheni Muhammadu, gaskiya an shiga tsakanin Nafi da H
alima dan da dai ba haka sukeba. Yara kansu ha
ɗ
e kamar uwa
ɗ
aya uba
ɗ
aya ta haifesu amma yanzu komai ya canja.....”
“Kinga Gwaggo kiyi haƙuri komai zai daidaita insha ALLAHU, inaga ku mu shiga can tunda nan da mutane.”
Gwaggo ce da
kanta ta tattara su Gwaggo Halima zuwa gidan Abie, shi kuma Abie ya saka su Shareff da gaba
ɗ
aya yama rasa abinyi gaba. Sai da kowa ya hallara har mahaifin Fadwa da su Baba Ibrahim dana duk wani mai fa
ɗ
a aji a falon kasancewar duk dangi na gidan, maza sun
taso a wajen
ɗ
aurin aure, matan kuma duk suna a cikin gida. Ran baba Ibrahim a
ɓ
ace ya dinga zagin su Mommy a yau dan shikam halinsu ya fara kaishi maƙoshi. Fitina daga wannan sai wannan kamar sune ka
ɗ
ai mata a cikin family
ɗ
in.
Hayaniya na neman
ɓ
arkewa ya daka musu tsawa, amma sukaƙi saurarensa. Daddy da dama a wuya yake kai tsaye ya buga musu tsawar da tafi ta baba Ibrahim. “Tabbas a wannan ga
ɓ
ar na gaji da halinki Nafisa. Kije na sakeki saki
ɗ
aya”. (biyu kenan
😲😱
).
Lokaci
ɗ
aya falon yay t
sitt tamkar ruwa ya cinye kowa. Gwaggo da tafi kowa firgita dan ita Gwaggo Halima take burin ganin an saka ta waro idanu, “A'a Muhammadu bakai gaskiya ba, yo ai ba Nafi ta cancanci saki ba Halima ce, ko kuwa dan ita ƴar uwarkace shiyyasa. To wlhy yanda ka
saki Nafi kaima Sadiqu sai ka saki Halima in har na isa da kai matsayin ƙanwar uwarka”.
Hajiya Luba ta fashe da kuka. “Gaskiyafa Gwaggo, Halima ita ta cancanci saki kodan baƙin halinta ita da ƴarta.....”
Saukar mari Hajiya luba taji a kuncinta
tauu, kafin ta dawo hayyacinta Gwaggo Halima ta sake sauke mata wani. “Babbar magana kenan”. Cewar Gwaggo tana miƙewa. “Halima shine zaki mareta dan ta fa
ɗ
i gaskiya, to idan Mustapha da Sadiqu sun sakeku ba dan an saki Nafi ai dole su sakeku dan zubarda c
iki da Fadwa taima Mustapha...........
✍
😆😆
Kai jama'a ALLAH ka rabamu dayin amai ka lashe kayanka dai.
[11/23, 5:14 PM] Marsy
😘
: BABU SO
Chapter 77
77
........Ka
ɗ
an ya rage zuciyar Fadwa yin tsale ta fito, jikinta na rawa tace, “Wlhy
ƙ
aryane, munafukar tsohuwa da bazataga MANZON ALLAH ba”.
Saukar mari taji lafiyayye daga Mahaifinta. Gwaggo ta jinjina kanta cike da jin da
ɗ
i, “Nagode Sadiqu. Ba laifinta bane uwace bata moraba. Yo dama yaushe Halima taga wata tarbiyya balle ta bata.
Ai bakai dace da mata ba wlhy”.
Cikin matuƙar mamaki su Daddy suke kallo da sauraran Gwaggo da alamu suka nuna akwai su
ɓ
utar baki a kalamanta. Gwaggo Halima zatai magana Alhaji Sadiq ya dakatar da ita. “Wlhy kikace tak sai kinyi nadama Halima...”
“Barta tace in ma tanada abin cewar mana. Dan kuwa inada ƙwaƙwaran hujjar ita ta zubar da cikinta da kanta, saboda karya hanata wa
ɗ
an nan raye-rayeda sukeyi na zamani a wannan abubuwan da kuke kira yanar gizo-gizo ko uwar mima. K Luba kiramin Bibah ta sh
igo da likitan da ta saka yaymata aikin. Amma kafin sannan fara latso min ita a wayarki su gani”.
Cikin rawar
ɓ
utiya Hajiya Luba ta latso Fadwa a tiktok ta miƙama Baba Ibrahim dake a tsakkiyar Daddy da Abie, sai Baban Fadwa a gefen Daddy, Abba kuma n
a gefen Abie. Wani video ne na rashin mutunci da aka
ɗ
auka a ranar kamun Fadwa. Ana gobe
ɗ
aurin aurenta da Shareff kenan. Kayan barcine jikinta riga fingila iyakarta cinyarta amma ta kusa gwiwa, sai gashinta dake a bu
ɗ
e tama warwaresa akan kafada. A yanda
taketa komanta kai tsaye da farko na rawar wata wakar turanci zaka san bata san ana dauka ba. Sai a kusan ƙarshe-karshe take kare jikinta da filo data
ɗ
auka tana masifar miyasa zatai mata video, sai dai anyi cutting sunan wadda ta ambata na mata video
ɗ
in.
Bayan shi akwai wasu daban-daban na rashin mutunci, abindama zai baka mamaki kamar an tsinto iya wanda tayi abin ALLAH wadai
ɗ
inne kawai an
ɗ
ora a shafin. Hatta wayarsu ta ranar daurin aure da Shareff duk akwai a wajen, duk wani fa
ɗ
a datai da wani a tikto
k ko rawar banza cikin shigar wofi duk sune aka tato aka
ɗ
aura. Harda ma wanda bata kai tiktok
ɗ
in ba
Komai ya ƙara tsayama Shareff cak, bama shi ka
ɗ
aiba hatta sauran jama'ar falon gaba
ɗ
aya. Kafin wani ya samu damar tofa tasa sai ga Bibah da likita
n daya zubdama Fadwa ciki. Harga ALLAH tayi matuƙar firgita. Zuciyarta ta dinga tsitstsinkewa lokacin da Gwaggo ke fa
ɗ
a masa ya fa
ɗ
i miye alaƙarsa da Fadwa. Kansa tsaye babu fargabar komai saboda an toshe bakinsa da ku
ɗ
i ya fara bayani tiryan-tiryan tun zu
wan su Fadwa da ƙawayenta Sima da Amal. Baice akwai Bibah da Siyyah ba. Sai yanzu ne Fadwa ta samu damar fashewa da kuka.
“Wlhy wlhy ba haka akaiba. Bibah kiji tsoron ALLAH, dan kina son auren mijina basai kin ƙullamin sharri ba.....”
“Sharri k
uma. Idan sharri nake miki aiga wayarki a hanunki a amsa a duba agani”.
Duk da Fadwa tasan duk wa
ɗ
ancan videos
ɗ
in tayisu amma ta goge mafi yawa a ciki saita bada wayar tata, saboda sanin masu dama-damar ne kawai a shafin nata na yanzun. Baba Ibrahim
ne ya amshi wayar, sai dai koda aka duba babu wani accaunt akai sai irin wanda Bibah ta nuna.
“To'ai babu banbanci tsakanin wannan da wanda ke anan ciki”.
Ba karamin ru
ɗ
ewa Fadwa tai ba. Harta fisgi wayar a hanun Baba Ibrahim batare da tasan t
ayi ba. Koda ta duba itama sai taci karo da abinda suke maganarne kawai babuma accaunt
ɗ
inta data sani akan wayarta kwata-kwata. Mamaki da tsoro suka risketa. Takai dubanta ga Bibah sai ta samu tana murmushi, hakan ya bata tabbacin itace tai komai. Wata ir
in wawuyar mikewa tai ta shaƙi Bibah, nan take kokawa ta kacame Bibah ta fara kakarin mutuwa. Da ƙyar Maheer ya rabasu shi da su Aunty Bintu.
“Shareff idan baka saki Fadwa ba wlhy wlhy wlhy har abada babu ni babu kai. Yanzu nan ka saketa, dan baka t
a
ɓ
a rayuwa da wadda ta zubar maka ciki ba dan son zuciyarta, sannan ballagaza.”
Shareff da gaba
ɗ
aya brain da Heartbeat
ɗ
insa sun tsaya cak daga aiki, ya dago yana kallon Mommy.” “Ba kallona nace kayiba saketa nace, idan kuma bazaka saketaba to wlhy
zan......”
“Haba Nafisa kinada hankali kuwa, ki tsaya abi komai a sannu mana”.
“Yaya daina wani maganar a sannu, ai tunda Ubansa ya sakeni wlhy shima sai ya saki Fadwa. Dan na tabbatar abinda na aikata bai kama kafar abinda taiba. Itafa ciki ta
zubar masa”. Kafin ma Baba Ibrahim yace wani Shareff da dake cikin matsanancin fushi ya furta “Na saketa saki biyu”.
Tamkar saukar aradu Fadwa taji saukar wannan kalma. Tai baya ta zube ƙasa, ihu take son yi amma ta kasa yi tsabar yanda falon ke juya
mata tana ganib bibbiyu, da sauri ta rarrafa gaban Shareff.
“Soulmate dan girman ALLAH ka saurareni, wlhy ba.....”
Wani irin hanka
ɗ
ata yay tai baya ta zube har kanta na buguwa da kujera sai da Abba ya tareta. “Wlhy idan kika sake koda matsoni z
an iya shaƙeki ki mutu, ballagaza. ALLAH ya isa ban yafe miki zubarmin da ciki ba, na tsaneki, na tsaneki, bana buƙatar sake ganin mummunar fuskarki a rayuwata har abada. Idan har zaki iya salwantar da ƙyautar da ALLAH ya bamu, abinda ke amsa suna gudan ji
ninki to zaki iya halakani nima, na tabbata zaki iya kasheni saboda cikar burinki. Kin wulaƙanta aure na, kin nunama duniya ke
ɗ
in baki da tarbiya, har wasu banzaye najin wani abu akanki saboda kin nuna musu ke ballagaza ce. Anya Fadwa kinada ilimin addini
kuwa? Anya kin san darajar kanki kuwa? Anya kina tuna zaki mutu kuwa?, na godema ALLAH ma da ban haihu da ke ba, dan bana fatan ƴaƴana su taso su kalleki matsayin mahaifiya balle har halayenki su zama naso ga tasu rayuwar. ALLAH ya wadaran mace irinki mai
tara ƙawaye da bata da ra'ayin kanta sai nasu, kije ƙawayen naki su cigaba da baki rayuwar da kike buƙata, kije, kije bana son ganinki wlhy”. Idanunsa har tara ƙwalla suke na tsananin
ɓ
acin rai, Shareff nada kishi matuƙa akan duk abinda yakeji ya killace
matsayin nashi. Yanzu haka yanajin kamar zuciyarsa zata tsage, babu abinda ke masa amsa kuwwa sai zantukan samarin
ɗ
azun a kanta. Wata muguwar shaƙa ya kai mata jijiyoyin kansa na matuƙar tashi. “Fadwa na tsaneki, bazan yafe miki ba.....” da ƙyar su Abie s
uka ƙwace Fadwa a hanunsa, sai numfashi take fiddawa da ƙyar na wahala ga Gwaggo Halima na ihu da kururuwar kuka zai kashe mata yarinya. Kansa ya kife a jikin Abie dake kusa da shi, yana mai ƙoƙarin danne hawayensa. Abie ya shiga shafa kan nasa cikin lalla
shi tausayinsa na ratsashi. Ba Abie ka
ɗ
ai ba kowama yaji tausayin Shareff
ɗ
in dan abune mai matuƙar ciwo ga duk namijin daya san ciwon kasa. Su kansu sunajin ra
ɗ
a
ɗ
i a zukatansu matsayin iyaye, mahaifinta kam ma ai ya kasa ko motsi dan gaba
ɗ
aya ya tattara
laifin a kansa shima, zuciyarsa suka take matuƙa a ƙirjinsa...........”
*_“Tabbs da ace kayi haƙuri saki bashi bane mafita Yaya MM”._*
Kusan gaba
ɗ
aya suka waiwaya a inda sautin maganar ta fito. Anaam ce sanye da hijjab har ƙasa. a kallo
ɗ
aya za
ka fahimci a barci ta tashi ma. Kuma yanayinta yana nuni da batajin da
ɗ
i....
“Ke kuma a wa, kajimin ƴar iskar yarinya. To ko ubanki Usman da uwarku basu isaba balle ke haihuwar yau”.
“Badan na isa bane na fa
ɗ
a Mommy, ba kuma dan iyayena nada wa
ni kusanci da zama masu isa a wannan Family
ɗ
in ba. Sai dan kusan gaskiya ku daina dukan jaki kuna barin taiki (ALLAH yasa na fa
ɗ
i hausar tawa dai-dai). Tabbas Fadwa bata ta
ɓ
a ƙaunataba. Kamar yanda Gwaggo Halima bata ta
ɓ
a ƙaunar iyayena guda uku ba. Haka
kema baki ta
ɓ
a ƙaunarsu ba. Kafin wata rana ina ganin laifinku matuƙa ina kuma jin zafinku mai tsanani, sai dai lokaci ya saukaƙamun hakan sakamakon fahimtar kuma a haka aka raini zukatanku. Zan fa
ɗ
i gaskiyane a yanzu ma badan ku soni ni da iyayena ba, sai
dan ku sani wadda ta raineku ku kanku ba ƙaunarku take ba bawai iyayena ne kawai take ƙi
ɗ
inba. Lallai da sanin Fadwa aka zubar da cikin jikinta, sai dai kuma Gwaggo itace ta tsara komai da taimakon momyn Bibah, su Bibah ƙawayenta su hu
ɗ
u suka
ɗ
arata a ha
nya har komai ya faru.....”
Wani irin harziƙowa Hajiya Luba tayi, amma sai Baba Ibrahim ya dakata mata wata irin razananniyar tsawa. Komawa tai ta zauna da
ɓ
ar. Anaam tai murmushi mai ciwo da dafe karfen benen takai zaune saboda jiri da take gani. Sai
da ta
ɗ
an dafe kanta na wasu sakkani sannan ta
ɗ
ago tana
ɗ
an murmushi. “Kuyi haƙuri.” Batare data jira cewar wani ba ta cigaba da fa
ɗ
in, “Ban fa
ɗ
a muku wannan maganarba sai dana riƙe hujja, kuma dama irin wannan ranar nake jira dan nasa duk yanda Maman Bi
bah da Bibah zasuyi da Gwaggo sai sunyi domin Yaya MM ya auri Bibah, kuma Fadwa itace kawai makaminsu da Mommy”. Ta ƙara maganar da miƙa wayarta dan bazata iya tasowa ba saboda jiri. “Gashi komai na'a cikin nan. Ku kira Amrah ma kuji dan tasan abubuwa da y
awa itama”.
Aunty Bintu ce ta amso wayar, ta kaima Baba Ibrahim. Gwaggo ta miƙe a fusace sai dai jikinta rawa yake. Amma sai Gwaggo Halima tasa ƙafa ta ta
ɗ
ota ta koma zaune da
ɓ
ar har tana sakin ƙarar azaba data ratsa
ɗ
uwawunta. Sosai da mamaki mai ci
ke da
ɗ
unbin razani suka bayyana a fuskokinsu Baba Ibrahim. Dan kuwa dai ga muryar Gwaggo gata Hajiya Luba da Bibah. Su Mommy zasu fara hayaniya Baba Ibrahim ya hanasu, cikin matuƙar razanarwa Baba Ibrahim yace Hajiya Luba ta fa
ɗ
a kokuma ya
ɗ
auka mataki a
kanta. Jikinta tsuma yakeyi, musamman da taga irin mugun kallon da Shareff ke jifanta da dashi, wanda ba ita ka
ɗ
ai ba, hatta Gwaggo ha
ɗ
iyar yawu take da ƙyar...
“Wlhy Yaya mu ba laifinmu bane, kawai dai Bibah ce ke tsananin son Shareff, nayi-nayi Na
fi ta fahimci abinda nake buƙata na mu ha
ɗ
a aurensu taƙi, sai nunawa takeyi da Fadwa za'a ha
ɗ
a. Har nayi zuciya da hakan sai dai Bibah ta shiga damuwa, shine nazoma Gwaggo da batun ko akwai yanda za'ayi, amma saita nunamin itama bata san zancenba. Ban gaji
ba muka cigaba da binta har akai auren Fadwa da Shareff, sai lokacinne ta fara saurarena, ta kuma tabbatar min idan har muka taimaka mata cikin Fadwa ya zube zatai duk yanda zatai dan auren Shareff da Bibah ya yuwu”.
Salati falon ya
ɗ
auka baki
ɗ
aya,
yayinda a lokaci guda Gwaggo Halima da Mommy suka kaima Gwaggo shaƙa, da ƙyar aka
ɓ
an
ɓ
areta a hanunsu idanunta har sun firfito waje kamar na tsohon kwarto. Nan fa sabuwar hayaniya ta kaure har wani baijin zancen wani, dan Fadwa kam tuni ta turmushe Bibah t
ana jibga, itama uwarta Hajiya Luba ta turmushe Fadwan. Ƙurace sosai ta tashi a falon, wadda ta saka Anaam ji kamar duniyar na juya mata. Cikin sa'a Shareff ya hangota tana jujjuya kanta. Da sauri ya miƙe yay inda take, cak ya dauketa ya koma saman da ita
tana faman jujjuya masa kanta, Mamie da itama ta hangosu tai saurin bin bayansa dan ita kam ma ba komai take fahimtaba a abinda ke faruwa a falon.
Fa
ɗ
a sosai ya kaure, duk yanda su Abba sukaso kwantar da abun ya gagara, dan tun anayi a falo har aka k
oma tsakar gida, kafin kice mi ƴan biki sun fara tururuwar shigowa bama idonsu abinci tunda dama akwai ƙofar dake a tsakanin gidajen wadda basai kaje gate ba. Cirko-cirko mutane sukai sunajin fallasa da tonon asirin da su Mommy sukema juna, yayinda Gwaggo
ke neman na
ɗ
e tabarmar kunya da hauka. Sai