Showing 39001 words to 42000 words out of 216641 words
tsohuwarnan kedai bakinki bai iya shiru, kawai dan mutum yayi wadataccen waje a gidansa sai yazam na aure? Nayine saboda ke in kinzo kwa
ɗ
ayin jar miya”.
Dariya su Aunty Amarya s
uka sanya. Mommy ma ta
ɗ
an saki fuska tana murmushi dan tun farkon fara ginin gidan da tazo ta gani ta masa irin wannan maganar ganin sashe biyu da nasa na uku, amma sai yace yayine kawai saboda baƙi. Haka kawai zuciyarta taƙi aminta da shi taita masa bin.
....
“To shikenan muje ka kaimu naka sashen muga namai gida”.
Gwaggo ta katse mata tunani. Gabansane ya fa
ɗ
i, zaiyi magana Gwaggo ta nufi ƙofar sashen da basu shiganba wanda tabbacin nasan ne, itama Mommy saita take mata baya. Hakan yasa dole s
u Mom ma binsu. Da ƙarfi ya rumtse hanunsa da cije lip
ɗ
insa. Ganin har Gwaggo ta shige yay saurin bin bayansu shima dan ya tabbata target
ɗ
inta na biyu shine bedroom
ɗ
insa. Kamar yanda yay hasashen kuwa hakane. Dan ko falo bama tagama nutsuwa ta ganiba ta
nufi ƙofar bedroom acewarta da nan zata fara a sashen. Shigowarsa tayi dai-dai da
ɗ
aura hanunta a handle
ɗ
in ƙofar.............
✍
*_
🙆🏻
Yau munga idi wagga tsohuwa babu man kai zata
ɓ
aro aiki. Dangin Anam kuna ruwa, maganin masu bin mazan mutane ken
an
🚶🏻😂🤭
_*
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Li
ttafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS
👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA
👇
09134848107
*_ALLAH ka g
afartama iyayenmu_*
😭🙏🏻
[10/14, 6:15 PM] Marsy
😘
: *_Typing
📲
_*
*_
❤
🔥
BABU SO....!!
❤
🔥
_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_11_*
.......Ɗin! Ɗinn!! Horn dake nuna alamar iso
war dangin amarya Fadwa ya saka Gwaggo juyowa baki a washe tana fa
ɗ
in, “A to ga masu ganin gidan nan ma sun iso ai? Kai Alhaji ƙarami muje ka bu
ɗ
e musu ƙofa
ɗ
in saina tarbesu ai ko”.
A hankali ya lumshe idanunsa da sauke
ɓ
oyayyar ajiyar zuciya. Momm
y ma bin bayan Gwaggo tayi, suma su Mom sai suka bisu kawai dan abu ka
ɗ
an zai iya jawo Gwaggo taita surutu. Har zai bisu ya dawo da baya,
zuciyarsace ta bashi shawaran ya sakama ƙofar key, dan haka ya kulle da sauri ya fidda key
ɗ
in
ɗ
akin a cikin keys ya s
aka aljihu sannan yabi bayansu...
Mota uku ce a jere kai kace jeren kayan sukazo. Motar farko Fadwa ce ta fara fitowa a ciki, sai ƙawayenta uku. Ta biyu kuma ƙannen babanta ne su biyu da cousin
ɗ
inta biyu suma dai duk masu aure ne. Sai am
iniyar Gwaggo Haliman. Motar ƙarshe babban yayan Fadwa sauran kuma ƴan kamfanin da zasuyi aikinne dan motarma akwai tambarin kamfanin. Cikin mutunta juna aka gaisa tunda dama akwai alaƙa, kafin su
ɗ
unguma gaba
ɗ
aya zuwa can. Fadwa sai satar kallon Shareff
take amma yayi kicin-kicin kamar ma bai ganta ba. Dama tun waccan ranar ko kiransa tai baya
ɗ
agawa, idan tai masa magana koda yana a online kuwa ko bu
ɗ
ewama bayayi. Tabi duk hanyar daya dace su sasanta amma yaƙi kulata dan yayi alwashin koya mata hankali a
wannan karon.
Ko'ina sai da suka shiga kowa na yabawa dan gida kam yayi sai dai maƙiyi. Ma'aikatan kamfanin da zasu saka kayan kuwa nata faman gwaje-gwajensu tunda dama amarya ta gama za
ɓ
ar wanda take buƙata tun a gida. Zare jikinsa yay ya koma sash
ensa batare daya amsa tambaya ko
ɗ
aya ba akan
ɗ
ayan sashen dasu Gwaggo sukai magana suma. Shi dariya ma suke bashi da mamaki, ina ruwansu da sashen to tunda basu suka basa ku
ɗ
in ginin ba, sashen dama ko ƙarasa masa ayyuka ƙananu ba'aiba ya tsolema kowa ido
.
Baifi mintuna biyar da shigowa ba Fadwa ta biyo bayansa. Bai nuna alamar yasan da shigowar tata ba. Duk da shariyar tasa ta sosa ranta sai ta shanye ta shiga yaba yanda sashen nasa yay matuƙar ƙyau shima. Yanda tsarin ya kasance na black and milk da
ratsin ash ya matuƙar ƙayatarwa.
“Soulmate!”.
Ta kira sunansa a hankali tana kaiwa zaune kusa da shi. Bai amsa ba, bai kuma
ɗ
ago ya dubeta ba yanata aikinsa kamar yanda ta samesa. Murmushin takaici ta
ɗ
anyi tana kallonsa, ta lumshe ido ta bu
ɗ
e ak
ansa zuciyarta na raya mata abubuwa masu yawa dan ba ƙaramin ha
ɗ
in kayan mata tasha ba. Sake matsawa tai jikinsa a kasalance ta
ɗ
aura kanta a shoulder
ɗ
insa ta saki kuka.
Cak ya tsaya da aikin da yakeyi, yaja numfashi ya fesar yana mai rufe idonsa d
a bu
ɗ
ewa a lokaci guda.....
“Dan ALLAH kayi haƙuri ka daina fushi dani haka nan Yaya Al-Mustapha. Karka manta kwanaki takwas kacal ya rage mu zama abu guda, ina buƙatar ganin murmushi a fuskokinmu yayinda jama'a zasu fara taruwa dominmu daga gob
e. Naji nayi laifi kuma na amsa na kuma bada haƙuri bazan sake ba mijina”.
Kalamanta sun
ɗ
an saka masa sassauci, sai dai baida alamar cewa wani abu a zahiri. Kanta ta
ɗ
ago daga kafa
ɗ
arsa tana kallonsa idanunta na rige-rigen matso hawaye, ta riƙo han
unsa dake dafe da lap-top har yanzu sai dai ba aikin yake ba. “Baka haƙuraba ko My Soulmate? Shike nan na baka damar kaimin kowane irin hukunci amma dan ALLAH banda naƙin kulani na tuba”.
Karon farko ya
ɗ
ago idanu ya dubeta, kafin ya maida ga hanun
su dake cikin na juna. Nasa ya janye tare da
ɗ
an bada tazara daga kusancinsu. “Naji ya wuce, sai dai ki tabbata kika sake hukuncin dazan
ɗ
auka bazakiji da da
ɗ
i ba. Ni da ke zamu zauna bada iyayenmu ba, dan haka matsalarmu mune ya kamata mu fuskanceta basai
wasu sunyi alƙalanci a ciki ba”.
“Insha ALLAHU zan kiyaye mijina”. Tai maganar tana fa
ɗ
awa jikinsa ta rungumesa. Hannu yasa ya janyeta. “Nasha fa
ɗ
a miki bana son
ɗ
abi'ar nan sam. Domin babu wani hallaci daya halatta hakan garemu”.
“To k
ayi haƙuri, amma karka manta kwana takwas ya rage kacal mu zama ma'auratan ai ko, kaga kenan akwai banbanci da da yanzun”.
“Sai ki bari sai mun zama
ɗ
in, a yanzu dai haramunne”.
“Hummm” kawai ta fa
ɗ
a dan bata bukatar su sake wani rikicin kuma sa
boda kar yay amfani da damar yaƙi halartar duk events da suka shirya gara ta lalla
ɓ
asa ayi a tashi lafiya karya kunyatata ga ƙawayenta. “My Soulmate bara na
ɗ
anyi using toilet Please”.
Ɗagowa yay ya
ɗ
an dubeta dan harya sake maida kansa ga aikin gaba
nsa. “Yanzu a barowanki gida har sai kinzo wani waje kin shiga toilet?”.
Murmushi tayi daya sake ƙawata ƙyawun fuskarta. “Oh My Soulmate nan
ɗ
in aiba wani waje bane na daban, shine fa gidana nanda kwanaki ka
ɗ
an zan dawo rayuwar cikinsa. Bawani
abu zanyiba part zan canja dan bana iya wuce awa
ɗ
aya da shi a jikina”.
Idanunsa ya
ɗ
auke daga kallonta, haka kawai yaji wani iri a ransa ganin babu ko ƴar kunya tattare da ita take fa
ɗ
in part zata canja. Da hannu ya nuna mata toilet na falon.
“Ah-ah my Soulmate bara dai na shiga bedroom mana. Nan kuma idan cikin su Mommy wani ya shigo fa”. Komai baice mata ba, harta nufi hanyar bedroom
ɗ
in Anam dake barci a ciki ta fa
ɗ
o masa. Dakatar da ita yayi. “No ki shiga wannan
ɗ
in can ƙofan nada ma
tsala ne, sai angyarasa a rufe yake”.
“Okay! To bara naje naga bedroom
ɗ
in namu ko?”. A
ɗ
an kausashe yace, “Shi nake nufi”. Ɗan jimm tai tana kallonsa. Sai kuma tayi murmushi cikin rausaya kai ta nufi na falon kawai. Shima aikinsa ya cigaba dayi, a zu
ciyarsa yana ALLAH-ALLAH su kammala su tattara subar gidan.
Addu'arsa kam ta karbu, dan koda ta fito bata zauna ba kasancewar ƙanwar abbanta nata faman kiranta a waya akan ta fito zasu wuce.. Tare da shi suka fita, yaji da
ɗ
i sosai da su Mommy sukac
e suma zasu wuce ne magrib na gabatowa.
Bayan duk wucewarsu ya dawo ciki, kai tsaye bedroom
ɗ
insa ya nufa, key
ɗ
in daya cire yasa ya bu
ɗ
e babu zato ko tunanin ta tashi a ransa.... Kusan a tare ƙofofin guda biyu suka bu
ɗ
e. Shi yana shigowa ita tana
fitowa daga bathroom. Wata irin ƙara ta fasa da ƙanƙame guntun towel
ɗ
in data
ɗ
auro a jikinta dake
ɗ
igar ruwa tareda fa
ɗ
awa saman gado ta cukuykuye zanin gado da duvet
ɗ
in gaba
ɗ
aya a jikinta....
“you are vary stupid!!”.
Ya daka mata tsawa jin t
ana barazanar fasa masa dodon kunne.
“Na shiga uku ni dai ka fita, dan ALLAH ka fita, Yaya wlhy babu ƙyau ganin tsiraicin wani. Wayyo ALLAH Mamie banji maganarkiba nashiga halaka.......
“Shut up! Stupid!”.
Ya sake fa
ɗ
a da matuƙar takaicinta.
Bedsheet
ɗ
in ta tusa cikin baki tana gya
ɗ
a masa kai ga hawaye na faman mata gudu a fuska kai kace wani abu yace zai mata. Shiko gaba
ɗ
aya idanunsa sun birkice dan takaici, ya ƙarasa takowa gaban gadon yana watsa mata mugun kallo. “Ubanwa ya saki yin wanka
anan
ɗ
in? Ko an fa
ɗ
a miki nan gidan wanka ne?”. Kanta take girgiza masa tana ƙara maƙurewa waje guda, dan ita a yanzu ba fa
ɗ
an nasa take tsoro ba a yanda ya ganta da a yanda take. “Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya. ALLAH zafine ya dameni kamar fatana zai
ɗ
aye zu
fa ya jiƙani ina
ƙ
yanƙyami shiyyasa nayi”. Rasama mizai ce mata yay, ga jikinta sai rawa yake matuƙa. Tsaki yaja ya juya ya fita kawai. “Mintuna biyar na baki”. Ya fa
ɗ
a dai-dai yana jan ƙofar har saida ta zabura saboda bugata da yay.
Kanta ta cusa t
sakanin ƙafafunta ta ta sake sakin wani kukan na baƙin cikin ya ganar mata jiki abinda wani mahaluki bai ta
ɓ
ayiba bayan Aunty Mimi da Mamie. Duk da bawai tsirara ya ganta ba a ganinta ƙanƙantar towel
ɗ
in baida maraba da hakan ita kam. Tuna abinda ya fa
ɗ
a n
a karshe da yay yasata zabura. Durowa tai a gadon ta nufi ƙofar ta saka sakata, da sauri ta kwashi kayanta duk da
ɗ
unbin ƙyanƙyamin da take musu ta shiga maidawa a jikinta da sauri-sauri. Bata kammala
ɗ
aure igiyar abayar jikinta ba ta fito. A falo ta sames
a tsaye sai faman kai da kawo yake tamkar mai safa da marwa. Tai ƙasa da kai dan a yanzu kam babu abinda take gudu kamar su ha
ɗ
a ido, wani irin matsanancin kunyarsa takeji har ƙarƙashin zuciyarta. Shima bai dubi inda takenba ya nufi bedroom
ɗ
in nasa, bai k
oyi mintuna biyu ba ya fito da kayansa da sukazo gidan suna jikinsa. Magungunanta da lap-top
ɗ
insa ya
ɗ
auka yay waje. Da sauri tabi bayansa dan dama kamar jira take ace ar ta kwasa ana kare.
A motar ma hankalinta ta maida gaba
ɗ
aya waje badan tana
fahimtar abinda take kallo ba, sai dan bata buƙatar koda kallonsa. Shima
ɗ
in dai aikin tuƙinsa yake kawai lokaci-lokaci yakan amsa waya har suka iso gida. Yana gama parking ta fice. “Waye zai biki da wannan?!”. Baya ta dawo kanta a ƙasa ta
ɗ
auka ledar mag
ungunanta daya
ɗ
aura saman mota ta wuce har tana har
ɗ
ewa saboda yanda take tafiya da sassarfa.
★★★★
Shirye-shiryen biki ya ƙara kankama, yayinda Anam ke faman wasan
ɓ
uya da Shareff. Sam ta daina yarda su fita aiki tare, kafin ya fito ta
shirya tabi bus
ɗ
in su Fawwaz da ake kaisu school. Data tashi aiki kuma zata saka wani abokan aikinta ya tare mata Napep ta dawo gida. Bata yarda dai ta fa
ɗ
ama kowa abinda ya faru ba, sai dai tun ranar har yanzu bata sake ganin Yaseer ba. Ya daina shigowa
aiki ta daina samun number
ɗ
insa kuma. Ta tambaya iya wanda suke mu'amula a wajen aikin nasu duk sun sanar mata suma basu san miya hanashi zuwa aiki ba. Amma dai ance ya kawo reason nashi wajen oga. Haƙura tai tabar bin kowa, sai ma haushinsa ya kamata. A
yanda suke tana ganin ya dace ace ya sanar mata idan zaiyi tafiyane kokuma wani abu ya samesa ai.
Ranar laraba gidan aka tashi da shirin isowar su Abie. Wannan ne ya
ɗ
auke mata dukkan hankali ta manta da batun Yaseer. Taso ace da ita za'aje tarbo
iyayenta airport sai dai batasan waye zaije
ɗ
akkosu ba, dan haka ta haƙura kawai tai zaman jiransu a gida. Aiko ƙarfe hu
ɗ
u da rabi na yammaci sai ga Shareff da Dr Jamal abokinsa
ɗ
auke dasu a motocinsu ashe sune sukaje tarbosu. Cikin ƙanƙanin lokaci gida y
a hautsine da murna dan harda aunty Mimi da yaranta itama. Duk da an share musu nasu gida an gyara komai tsaf anan suka fara sauka. Anam ta rungume iyayenta harda kukan da
ɗ
i su Mubarak na mata dariyar ta girma batasan ta girma ba. Duk wannan kaikawo da ihu
n yara da hayaniya Mommy da Gwaggo ko leƙe basu leƙo ba duk da kuwa sun san su Mamie sunzo ne domin bikin
ɗ
ansu. Hasalima duk wani
ɗ
awainiyar biki Abie da Mami suka
ɗ
auka. Acewarsu Shareff
ɗ
ansu ne, sune suka cancanci yimasa aure ba kowa ba. Hatta lefe da
duk abinda aka kai gidansu Fadwa sai da Abie ya dawowa Daddy da Abba abunsu. Mommy taita masifa amma Daddy ya taka mata burki tun wancan lokacin dan a sanda Abie ya rako Anam ne. Sai da sukaci suka sha sannan suka shiga suka gaida Gwaggo. Mommy kuwa basu n
una sun san da zamanta a gidan ba Gwaggon ma dan
uwa ce shiyyasa suka bata girmanta. Ai tuni Anam tabi su Mamie can gidan, dan taci alwashin bazatai zaman gidan nan ba dan bata ra'ayin ayi bikin nan da ita, duk da kuwa katanga
ɗ
ayace tasan wasuma zasu shig
o gidansu a ƴan bikin, amma dai ko yayane bazai kai nan gidan ba ai. Sai dai kuma batasan tayi gudun
gara bane ta fa
ɗ
a gidan zago
😚
.
★★★
Acan gidan su amarya Fadwa kam wannan rana itace ranar ƙunshi, suna can ita da taren ƙawayenta waya
yyu da gayyar media an ware musu part guda sunata shagalinsu harda su shisha. Ga hotunan amarya sun baje media musamman tiktok da istagram da amaryar ta tara
ɗ
unbin followers da suka sakata yin ƙaurin suna cikin jerin celebrities da akeji dasu. Amarya tash
a ƙyau da gyara harta gaji, sai dai ba'ai mata nata ƙunshin bama sai gobe idan ALLAH ya kaimu alhamis.
★★★
Bayan sallar isha'i Mom ta aiko kiran Anam data maƙale taƙi bin su Aysha can gidan yin ƙunshi. Amma hatta da Amrah
ɗ
iyar Aunty Mimi d
ake kusan sa'anni dasu Anam
ɗ
in tana can itama za'ai mata. Cewa tai bataso itakam, dan ko wankin kai da sukaje yau ita ƙin zuwa tayi. Sai da Mamie tamata jan ido ta biyo ƴar aikin Mom. Amma da ta langa
ɓ
e wai kanta ke ciwo. Koda tazo anan
ɗ
in ma fa
ɗ
a Mom ta
i mata akan batun ƙunshin. Amma saita hau hawaye wai ita bata da lafiya. Kowa kallonta kawai yake da mamaki a falon, dan kuwa dai ko awanni hu
ɗ
u bata cikaba da gama murnar isowar su Mamie ai. Ganin yanda take kuka Mom tace mata taje ta kwanta ayi mata gobe
idan ALLAH ya kaimu. Ai kafinma ta rufe baki tayo waje. Maimakon taje ta kwanta
ɗ
in can ta samu inda babu wadataccen haske ta zauna taci kukanta da batasan daliliba itama sannan ta koma gidansu tai kwanciyarta.
Washe gari wajen sha biyu yaran gida
n kowa da ƙunshi abin sha'awa amma banda Anam dako wanke kai bataiba balle maganar kitso. Tana gani suka