Showing 138001 words to 141000 words out of 216641 words
ja
ɗ
aya yay mata ta warware dam
a
ɗ
aurin zarge tai mata. Rigar ta bu
ɗ
e, ƙara ta fasa masa, babu shiri ya kai hannu ya rufe bakin. Muƙutt ta ha
ɗ
iye abinda ya rage bai fito a bakin nata ba, idanunsa da suka ƙara canja launi ya watsa mata, “Ba haka kike so ba na bu
ɗ
e na gani”.
“ALLA
H ya kiyaye wlhy”. Ta fa
ɗ
a da sauri tana son motsa jikinta ko yaya amma yayi mata riƙo na gaske.
“Idan wannan bakin naki ya sake cewa (tak!) saina yage
ɗ
ayar ma silly girl”. Ya ƙare maganar hannunsa na sauka saman wuyan rigar da gaba
ɗ
aya ya bayyana
ƙ
irjinta saboda girmansa, rabin jikin nata ma duk a waje suke gashi ta kamata tsam kasancewar roba ce sannan copy lass mara nauyi.
Fashewa tai da kuka na tsananin borin kunyar daya jefa rayuwarta a ciki, dan ita harga ALLAH bada tunanin komai tai tam
bayar ba. Sai da ya tabbatar ya firgita ta sannan ya saketa, wani irin kwakusa ta kaima duvet ta ƙudundune har kanta...
Ƙara danne abinda ke hargitso masa brain yay da ƙyar ya koma ya zauna. Robar ruwan data kawo masa ya
ɗ
auka, batare da yabi tak
an kofin ba ya
ɓ
alle murfin ya dasa a baki. Tass ya shanye ruwan yay wurgi da robar yana rumtse idonsa da jijjiga kai tamkar mai girgije ruwan cikin suma. Ture stool
ɗ
in da laptol
ɗ
insa ke kai yayi yana jan wani bahagon tsaki, toilet ya nufa cikin sassarfa
kai kace ingizashi ake da remote.
Anaam da bata san yanai ba na maƙure cikin bargo tayi luff takaicin kanta da kanta ya gama dabaibayeta. Ji take tamkar ta ciji kanta dan haushi. A gaba
ɗ
aya abinda ya faru sai yanzu take iya lissafa rashin wayonta
, mima ya kaita masa tambayar? Ta cije lip da ƙarfi tana kaiwa gado mugun mintsini tamkar shine ya mata laifin.. Jin shirun
ɗ
akin yayi yawa ta
ɗ
an leƙo kanta ka
ɗ
an, wayam babu shi a
ɗ
akin, jitai wani farin ciki ya ratsata, ta miƙe da sauri ta dire a gadon,
ƙofa taje ta sakama key duk a tunaninta fita yay a
ɗ
akin. Ranta fess ta juyo tana karka
ɗ
a keys
ɗ
in da fa
ɗ
in, “ALLAH na gode maka daya fita azababbe, sai iya fassara mutum akan abinda ba haka yake ba, kuma ban yafe ba ganinmun jiki da akai da way......”
Numfashinta ya tafi zuuu ta ha
ɗ
iyeshi tare da yawu, da ƙyar ta iya
ɗ
ago ido ka
ɗ
an ta kalla abinda taci karo da shi. Shine
ɗ
in dai ba wani ba, zirr! Zirrr! Zirrr!! Haka jininta ke gudu a cikin jijiyoyinta yana kaima zuciyarta da ƙwaƙwalwa rikitattun sa
ƙ
wanni masu tabbatar da firgicin mutum a cikin idanu. Miya rage? Kawai ta kwasa da gudu tabar
ɗ
akin nan. Zuciyarta ta ayyana mata cikin ƙarfafawa domin ta tabbatar babu makawa yaji abinda take fa
ɗ
a
ɗ
in.
Hannu ya miƙa masa alamar ta bashi keys
ɗ
in. Ci
kin langa
ɓ
e kai da girgiza shi, hannunta
ɗ
aya na tattare da rigarta da taketa faman kare ƙirji. “ALLAH bafa da kai nake ba, kayi haƙuri zan maka bayani yanda zaka fahimta...”
“Nazo na amsa da kaina kenan?”.
“A'a wlhy, ni dai ba sai kazo ba,
daga nan ma zan maka bayani”.
Yunƙurin matsota yay, da sauri ta jefa masa keys
ɗ
in ya cafe. Cikin aljihun wandonsa ya zurasu da nuna mata gado. “Wuce ki kwanta”.
Hankali tashe ta bu
ɗ
e baki zatai magana....
“Idan kika furta (A) sai na miki f
ata-fata a
ɗ
akin nan. Idan kuma kinji ƙarya bismillah”.
Summ summ ta wuce hankalinta a matuƙar tashe. Ya raka bayanta da wani shegen kallo tamkar idanun nasa zasu wantsalo waje........
✍
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN ID
O_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BI
YA KUDIN BOOKS
👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA
👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏🏻
_*[11/11, 7:37 PM] Marsy
😘
: *_Typing
📲
_*
*_
❤
🔥
BABU SO....!!
❤
🔥
_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_BABU SO
👉🏻
AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_51_*
.........Kwance ta kai tana faman tu
ttura lips gaba, a zuciyarya kam babu abinda take sai masifa, sai dai babu damar yi a fili. Tashi tai zaune zaram kamar wadda aka tsikara tana kallonsa, ganin ya koma ya zauna gaban laptop
ɗ
insa.
“Yaya MM?”.
Shiru ya mata yaƙi ya amsawa, amma tsabar
bazata iya haƙuri ba saita cigaba da maganarta kamar sharetan da yay bai zafeta ba.
“Amma dai can
ɗ
akin zaka koma ka kwana kamar ranar idan ka kammala aikin ko?”.
Banza yay mata nanma, takaicinta ya bayyana har tana jin tuƙuƙimsa a maƙo
shi, harara ta dallama bayansa, cikin jin zafi ta fara
ɗ
aukar pillows
ɗ
in gadon
ɗ
aya bayan
ɗ
aya ta jera a tsakkiyar gadon tun daga farko har ƙarshe tana muy-muy da baki alamar magana take. Ƙarshen gadon ta koma da salon kwanciyar kai da ƙafa ta kwanta bada
n zuciyarta ta bata nutsuwar haƙurin sake kwanciya
ɗ
aki
ɗ
aya, gado
ɗ
aya da shi ba. Dan tayi alƙawarin kafin cikar wata ukunnan bazata ta
ɓ
a bari ya samu nasara a kanta ba.
Duk abinda take yana jin motse-motsenta sai dai bai juyi ba, aikinsa kawai yake
badan yana fahimtar wasu abubuwan ba. Bayan shu
ɗ
ewar kusan mintuna arba'in da biyar yaji shiru ta daina sukur-sukur da motse-motsen da takeyi, ka
ɗ
an ya juyo ya kalleta, a can ƙarshen gado take ƙudindine da bargo ta juya masa baya. Ya maida kallonsa akan pi
llows
ɗ
in data jera, kansa ya girgiza ka
ɗ
an wani
ɗ
an guntun murmushi na su
ɓ
uce masa. Hankalimsa ya maida ga aikinsa, wanda ya sake jansa kusan awa guda, ganin two ta kusa ya ga hamma yanata jerawa ya sashi tattara komai ya ajiye. Alwala yayo, ya shimfi
ɗ
a a
bin salla, sallar nafila ya gabatar raka'a biyu, yay addu'oi dan barci sai faman rinjayar idonsa yakeyi. Bai cire shingen datai musu ba yay kwanciyarsa bayan yayi addu'oi. Babu jimawa barci yay awan gaba da shi shima.
Duk da ta rigashi kwanciya shine
ya rigata farkawa, ya yunƙura da ƙyar ya tashi bayan karanta addu'ar barci, shanyayyun idanunsa da har yanzu barci ke cike a cikinsu ya zuba mata ta
ɗ
an hasken lamp dake a
ɗ
akin ka
ɗ
ai. Yanzu kam ta juyo fuskarta, sai dai tana a inda take kwance tun jiya.
Sai da yayo alwala sannan ya tasheta, a ranta ALLAH-ALLAH take ya fice ta sama ƙofarta key, sai da yaga ta shiga toilet sannan ya fice zuwa sashen Fadwa itama ya tashesu. Koda ta fito kai tsaye ƙofar ta nufa, amma wayam babu keys
ɗ
in alamar ya zare. Ta dal
lama ƙofar harara da murgu
ɗ
a baki.
Sai da gari ya
ɗ
anyi sha ya shigo, har sannan tana zaune tana azkar. Batare da ta yarda ta kallesa ba tace masa ina kwana. A taƙaice ya amsa yana kaiwa kwance dan barci ne fal idanunsa. Jin ya fara sauke numfashi
ta
ɗ
an juya ta kallesa, ya juya mata baya, amma ta fahimci barci ne ya
ɗ
auke sa. Itama dai ƙarasa azkar
ɗ
in tai ta koma ta kwanta tunda ba wani aikine da ita ba.....
★★★★
Tsabar yanda ta kwana da abubuwa masu yawan gaske a ranta tana idar da
salla sashen Gwaggo ta nufa. Burinta kafin su Daddy daga massallaci su shigo ta shige, dan ita yanzu ko
ɗ
akinsa bata zuwa, shi kuma yaƙi ce mata komai akan hakan. Gwaggo na zaune tana lazimi Mommy ta shigo, kallonta kawai take baki a sage, sai dai kuma ba
tai mamaki ba musamman akan sanin halin rashin haƙuri irin nata. Mommy ta gaisheta kamar yanda ta saba, damuwa ƙarara akan fuskarta.
“Wai Nafisa kuwa anya hankalinki na jikinki? Wace irin rayuwace wannan duk kin firgita kanki akan abinda bai taka
kara ya karya ba. Da alama yau ko barcin kirki ma bakiyi ba ko?”.
“Humm Gwaggo ina naga ta barci nikam, kema kin san babu wani barci dazan iya a wannan halin. Ki duba fa kiga Shareff ya
ɗ
auke ƙafa gaba
ɗ
aya a gidan nan tamkar ya manta dani a raye, ko'
a waya baya kirana tumma yanzu kenan za'a rabani da yarona. Maheer ma yaƙi zuwa duk da shi nasa bai cika damuna ba nasan fushin banza da wofi ya sakama ransa bayan ni gata naima rayuwarsa. Gwaggo taya zanyi barci a wannan yanayin to? Na kasa gane kan Share
ff sam. Son yarinyar nan yake da yake gudun ha
ɗ
uwarmu ko yaya ne?”.
Ƴar dariya Gwaggo tai. “Banda abin Nafisa halin namiji kuma kika manta! Shi yanzu Mustapha a wannan ga
ɓ
ar bake ka
ɗ
ai ba kowama zai iya rasa gane kansa ai.....”
“Gwaggo to sab
oda mi? Ni wlhy kaina duk ya kulle”.
“Uhhm haka dai, tunda kin ru
ɗ
a kanki ba dole kanki ya kulle ba. Kina tunanin duk ƙin da yakema yarinyar zai kawo ido ya saka mata ne a gidansa”.
Ka
ɗ
an ya rage Mommy ta ha
ɗ
iye harshenta. Cikin in ina da shig
a ru
ɗ
ani take magana. “Gwaggo wai kina nufin ya kwanta da yarinyar nan?”.
“Har kuwa ki ganta da ciki nan da watanni ka
ɗ
an”.
“Aiki dana tsine masa”.
“Ki tsine masa! Kinga Usman da Ai'sha sunci riba a kammu kenan. Ki kiyayi harshenki da amba
ton tsinuwa ya ƴaƴanki saboda kawai ranki ya
ɓ
aci. Ki koyi nutsuwa a duk lokacin da kikaci karo da abinda bai miki ba. Nafisa idan kikai sakaci k da kanki zaki tabbatar da nasarar maƙiyanki akan ƴaƴanki. Yanzu dakin kwantar da hankalinki tun bayan da akai
rikicin farko akan auren nan da yanzu mun kai ga mafita. Mustapha da kike gani hatsabibin yaro ne mai shegen zurfin cikin tsiya da wayo. Gaggawa a al'amarinsa ba shi bane mafita, kuma tsananinki ba shi bane zaisa muci nasarar rabashi da yarinyar cikin sauƙ
i, musamman da matarsa dama ta kasance shashasha, dan nikam sai yanzu nake dana sanin yin wannan ha
ɗ
in nasu”.
Da mamaki Mommy tace, “Wani abun ya faru ne Gwaggo?”.
“Nafisa ai shiyyasa nace ke
ɗ
in ru
ɗ
a
ɗɗ
iyar mutum ce, yo banda haka halin Fadwa
har wani
ɓ
oyayye ne da zaki kasa ganewa. Duk wani baƙin halin Halima shine tare da ƴarta, kodan shi Mustaphan bamai yawan magana bane da kullum zai zauna fa
ɗ
a miki matsalarta shiyyasa kike kasa fahimtar halinta?”
“Gwaggo bawai ban fahimci wasu
abubuwa bane, dan ni kaina yawan kirana da takeyi kullum tana kawomin ƙararsa ya mata kaza ya mata kaza yana cimun rai, sannan Aysha ta fa
ɗ
a min ko abinci sai ta gadama takeyi a gidan sai dai mai-aiki, Shareff da ko'a gidan nan baicin abincin masu aiki”.
“Humm zatayi abinda yafi haka ni na sani. Amma karki damu zamu fara gyara mata zama. Yanzu abinda nake so da ke ki sassautama zuciyarki komai, ki nunama su Muhammadu komai ya wuce kin ajiye makamanki, shima
ɗ
in Mustapha ki kirashi a waya ya sameki ki
nuna masa komai ya wuce. Mu kuma daga nan zamu fara namu yaƙin, badai wata uku shi Ibrahim ya bata ba, to duk yanda zamuyi sai munyi nanda wata ukun tabar gidan, babban fata na dai ace bai ta
ɓ
ata ba. Kai koda ya ta
ɓ
atan ma ba komai”.
“Gara dai karya
ta
ɓ
atan Gwaggo, danni bana fatan ha
ɗ
a kowace sabga da Usman balle shegiyar matarsa”.
Ƴar dariya kawai Gwaggo tayi da fa
ɗ
in, “To ALLAH yasa haka. Yanzu dai inaga kima Sakina magana yau taje mana gidan taga yaya zaman nasu yake”.
“Wannan shawar
an yayi gwaggo, bara na sanar mata yanzun nan kuwa”.
Daga haka suka cigaba da tattaunawa kuma har gari yay haske sannan Mommy ta koma sashenta zuciyarta na
ɗ
an sassauta nauyin da tai kwana biyu. Masu aikinta ta bama umarnin ha
ɗ
a abincin Daddy. Duk da
sun
ɗ
anji mamaki babu wanda yace komai tunda ba huruminsu bane, itako ta shige domin shiryawa tunda dama girkin tane.....
★★
Kusan ƙarfe takwas ta farka. Ganin har yanzu shi barcinsa yake hankali kwance sai ta koma
ɗ
ayan
ɗ
akin tai wanka
ta shirya a can. Ganin har lokacin baida alamar tashi saita nufi falo ta gyara duk da ba wani datti bane ba. Yunwa takeji matuƙa, dan haka ta ha
ɗ
a tea ta dawo falon tai zaman sha tana buga game a waya. Koda ta kammala a falon ta cigaba da zama tana game
ɗ
i
n har kusan ƙarfe tara.
“Wai mutumin nan bazai tashi bane? Koya manta yau monday akwai office?”.
Ta fa
ɗ
a tana kallon agogon dake falon, miƙewa tai kanta tsaye ta nufi bedroom
ɗ
in. Mamaki ya ƙara kamata ganin har yanzu dai a kwance yake, (Lallai
babu lafiya) ta ayyana a ranta tana ƙarasawa gaban gadon, dan ita dai a sanin datai masa na rashin wasa da aiki inda ƙalau yake babu yanda za'ai yakai yanzun yana barci. Fuskarsa ta
ɗ
an tsurama ido dan kwance yake a rigingine. Lumshe idanu tai da sake bu
ɗ
e
wa a kansa, ita shaida ce Shareff ƙyaƙyƙyawa ne, ƙyawu irin na masu kwarjini da cikar haiba bawai na fitar hankali ba. ALLAH ya bashi dukkan kamala ta cikakken mutum tamkar wani babba. Baida yawan hayaniya, sannan bai da yawan fara'a. Mutane da yawa kance
mata yanada sauƙin kai da da
ɗ
in zama, sai dai ita har yanzu bata ganinsu tattare da shi, dan zata iya bugar ƙirji tace babu wadda yatsana a rayuwarsa ƙila sama da ita, ta rasa minene laifinta a gareshi. Ta ta
ɓ
e baki da juya idonta, a fili ta furta “Yo kary
a soni
ɗ
in nima ai ba son sa nake ba humhh”. Ta ƙare maganar da murgu
ɗ
a baki ta juya zata bar wajen a bazata taji an riƙota. A firgice ta juyo dan ta tsorata, sosai idanunta suka firfito waje dan batai zato ko tsammanin shi
ɗ
in bane tunda taga barci yake.
Idanunsa ya
ɗ
an rufe ya sake bu
ɗ
ewa a kanta tare da fisgota ta fa
ɗ
o kansa.....
“Wayyo Yaya zaka karyani ne?”.
Komai baice mata ba, sai dai kafeta da idanunsa dake a yanayin wanda ya tashi barci. Ƙoƙarin son zame jikinta take a nasa amma ya hana hak
an ta hanyar
ɗ
ora hanunsa a bayanta ya tallafeta da ƙyar a saman jikinsa, fuskarta dake a gab da tashi ta kautar gefe saboda yanda yake kallonta tsigar jikinta har tashi take. Ɗayan hanunsa yasa ya maido fuskar tata a saitin tasa har yana jin saukar numfas
hinta.
“Kina yin miye tsaye a kaina?”.
Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta tura baki da ƙara ƙoƙarin janye fuskarta dan bazata iya jurar kallonsa ba. “Ni to mizanyi? Kawai nazo tadaka ne dan naga lokacin office yana wucewa”.
Agogon dake
ɗ
akin ya
ɗ
an kalla tare da maido idanunsa a kanta lokaci guda. “Dama ango na zuwa office ne?”.
Sosai ta yatsine fuska tamkar wadda aka fa
ɗ
ama wani mugun abu. sai kuma ta ta
ɓ
e baki da sake yunƙurin barin jikin nasa........
✍
_ZAFAFA BIYAR_
*_
INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Li
ttafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS
👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA
👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏🏻
_*
[11/11, 7:37 P
M] Marsy
😘
: *_Typing
📲
_*
*_
❤
🔥
BABU SO....!!
❤
🔥
_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce