Showing 51001 words to 54000 words out of 216641 words
wani haushi na ƙara turniketa, cikin ta
ɓ
e baki take bin ko'ina na kitchen
ɗ
in da kallo. Tabbas yayi ƙyau, sai dai hakan ba yana nufin wani abu na cikinsa ya burgeta ba. Abinda y
a aikota ta nufa ta
ɗ
auka, sai dai ta nufi sink dan ta
ɗ
auraye, sai ƙunƙuni takeyi da bazaka iya sanin mitake fa
ɗ
a ba. Juyowa tai tana jan tsaki, da sauri taja baya har plate
ɗ
in na neman su
ɓ
uce mata. Duk ta daburce dan sam bata san ya biyo bayanta ba, ga
idanunsa masu kaifi daya kafeta da su. A hankali ya tako gabanta duk hannayensa cikin aljihun jallabiyar jikinsa, ya tsaya dab da ita har tana iya jin hucin numfashinsa. Sai taji gaba
ɗ
aya kwarjininsa ya cika wajen har bata shaƙar numfashi a wadace...
“Ya jikin ki?”.
Yay maganar cikin taushin muryar da bata ta
ɓ
a ji daga garesa ba. Kasa jurewa tai sai da ta
ɗ
ago ta kallesa. Har yanzu idanunsa a kanta suke, tai saurin janye nata tana girgiza kanta. Muryarta da
ɗ
an rawa tace, “Alhamdulillahi”.
“Kin tabbatar?”.
“Nifa zazza
ɓ
i ne dama kawai Yaya MM”.
Jin baice komaiba ta
ɗ
ago ta dubesa, still dai har yanzu idonsa a kanta. (Ya ALLAH! lafiyarsa kuwa?) ta ayyana a ranta tana ƙoƙarin son barin wajen. Amma sai furucinsa ya sakata dakatawa
babu shiri.
“I'm sorry”.
Kasa yarda tayi daga bakinsa furucin ya fito, musamman da babu alamar shi
ɗ
in ya fa
ɗ
a a yanayinsa. Sannan bata san dalilinsa na fa
ɗ
arba. Kamar ya fahimci ƙarin bayani take buƙata sai ya bar wajen cike da basarwa. “Z
oki dafamin lipton”. Shiru bata motsa ba, da alama bata tare da tunaninta ma. Ya juyo ya dubeta fuska a tsuke. “Badake nake magana ba!”. Itama fuska ta ha
ɗ
e, sai dai cikin sanyin murya tace, “Yaya matarka fa?”. Ido ya tsura mata na wasu sakanni, sai kuma
ya janye. “Nasan da
ita ai na sakaki. Sannan ganin amarya a kicin irin wannan ranar kema kin san bamai yuwuwa bane”.
Da hausa yay maganar, dan haka ba komai ta fahimta da ƙyau ba. Amma sunan amarya kawai daya shigo ciki ya saka yanayinta ƙara canjaw
a. Sai dai bata sake cewa komai ba, ta
ɗ
auka tunkuyar daya fiddo mata domin dafa shayin ta
ɗ
auraye, ruwa ta zuba dai-dai shan mutum
ɗ
aya, tana ƙoƙarin rufewa taji tsaiwarsa a bayanta, kafin tayi wani yunƙuri ya janye hanunta da sake bu
ɗ
e murfin ya bu
ɗ
e fan
fo ya ƙara ruwan.
“Nadai bazan dafama wata ƙatuwa shayi tana kwance tana barci ba”.
Karon farko ya saki murmushi, sai dai komai baice ba ya rufe mata tukunyar. Zata sake magana ya dakatar da ita. “Zakimin abinda na saki ko tsiwa? Trouble maker!”
.
“Ga babbar Trouble maker can ka bari a
ɗ
aki”. Tai maganar ƙasa-ƙasa yanda bazaiji ba. Da kansa ya kunna mata gas
ɗ
in, ta
ɗ
aura tukunyar sannan ta
ɗ
iba kayan ƙamshi da lipton da duk ya fiddo da kansa ta zuba. Flask daya fiddo a kwali shima ta
ɗ
auka
ta
ɗ
auraye tare da kofi duk yana tsaye yana kallonta. Baiyi mamakin yanda take komai a tsaftace da kuma tsari ba, dan sai dai ya bama wani labarin Mamie badai a bashi ba, yasan kuma hakan duk tarbiyyar data samune daga gareta. Yana kitchen
ɗ
in harta kamma
la komai, ya sake
ɗ
aukar kofuna uku ya
ɗ
auraye da kansa ya ha
ɗ
a da wanda ta wanke. Bata tanka masa ba, ta
ɗ
auka flask
ɗ
in kawai ta fita. Shine ya
ɗ
auka sauran kayan ya fito da su, samunta yay tanama Ikram masifa akan ta tashi su wuce gida, ashe da wayarsa
ya ha
ɗ
ata shi ya tafi neman magana kitchen..
“Sai kun karya, tunda tace bakuyi breakfast ba kuka fito”.
Ranƙwashi takaima Ikram
ɗ
in, amma sai ta kauce tana dariya da fa
ɗ
in, “Wlhy Yaya ita a barci ma aka tasota gara ni nasha tea”. Wani ranƙwashi
n zata sake kaimata ya zuba mata hararar data sata dakatawa, sai dai tayi gefe da kanta tana ƙunƙuni.
“Oya zauna ki ha
ɗ
amin yunwa nakeji”. Ya fa
ɗ
a yana ajiye ledar dake
ɗ
auke da kayan tea da abokansa suka rako shi da su a daren jiya tare da kaza.
Batai magana ba, shima kuma bai sake maganar ba ya nufi ƙofar fita yasa key sannan ya wuce kitchen. Harara ta dinga zubama Ikram tana ha
ɗ
a tea
ɗ
in, tsabar mugunta ta zabga masa sugar. Ikram ta mikama nata tana fa
ɗ
in, “Makwa
ɗ
aiciya kawai, daga zuwa gidan mu
tane”.
Ikram tace, “Ni banyi kwa
ɗ
ayiba tunda gidan Yaya ne”. Fitowarsa ta hanata bama Ikram
ɗ
in amsa, ya dire babban plate dake
ɗ
auke da kaza sai turiri take alamar
ɗ
umamata yay. Zata miƙe yace, “Koma ki zauna.” babu wasa a lamarinsa dole tabi umarni
, sai dai idonta harya fara tara ƙwallar takaici. Hanyar corridor
ɗ
in da take ƙyautata zaton bedrooms ne ya nufa, cikin jin haushin da babu dalili ta raka bayansa da harara. Wayarta ta
ɗ
auka ta cigaba da daƙila, kusan mintuna uku sai gashi ya fito, zama ya
y a ƙasan carpet
ɗ
in shima kamar yanda take zaune. Yace, “Bani tea”.
Batai magana ba, ta
ɗ
auka flask ta zuba masa ruwan zafin akan kayan tea
ɗ
in data ha
ɗ
a a kofin. Sai da ta juya ta tabbatar sugar
ɗ
in ya ha
ɗ
e sannan ta miƙa masa. Duk da yaga bata ha
ɗ
a
nata ba sai baice komai ba yaja nasan gabansa da ƙyau, ka
ɗ
an ya
ɗ
iba a cokali yakai baki dan yaji yaya test
ɗ
in. “Ya ALLAH!”. Ya ambata da sauri. Tasan tsiyar da tai dan haka taƙi
ɗ
agowa. “Kina hankalinki ƙuwa zaki saka min wannan sugarn?”.
“Toni Ya
ya nasan yanda kake so ne?”.
Idanu ya zuba mata kawai tsahon wasu sakanni. “Idan ma mugunta ce harda kanki zaki mawa, ba wadda take cikin gidan kawai ba, dan duk dodo
ɗ
aya zaku yima tsafi”. Komai bata fahimta a zancensa ba. Wani kofin ya
ɗ
auka ya raba
shayin biyu, ya ƙara kayan tea
ɗ
in banda sugar ya sake zuba
ruwan zafi. Ikram dake ta faman latsa waya tana shan nata tea
ɗ
in yace ta sakko.
Duk yanda Anam ta so nuna ta ƙoshi bai saurareta ba. Haka ya tilasta mata karyawa tare da shi da breakfast
ɗ
in da suka kawo da kazar daya
ɗ
umama. Sai dai ita taƙi cin kazar ko sau
ɗ
aya. Ikram kam komai sai da taji yakai mata sannan tai hamdala. Tayi niyyar suna gamawa su wuce, amma sai taga babu dacewar barin kwanikan, ita ta kwashe komai zuwa kitchen, ta
ɗ
auray
e kwanikan da suka
ɓ
ata. Koda ta fito bata samesa a falon ba, tacema Ikram ta tashi su wuce gida.
“Lah aunty Anam Yaya yace mu jirashi zai fito muje tare”.
Harara ta zuba mata, “Shi kuma driver daya kawomu fa yake zaman jiranmu?”.
Fit
owarsa ta hana Ikram bada amsa. babu abinda ya canja a jikinsa sai key
ɗ
in mota daya
ɗ
akko, ta
ɗ
auke kanta gefe harya ƙaraso ya amsa wayarsa a hanun Ikram. Suna gaba tana binsu a baya har wajen mota, bataga driver ba, ba kuma ta tambaya ba. Ganin Ikram ta
shige baya itama tai yunƙurin shiga....
“Waye driver
ɗ
inku?”.
Fuska ta tsuke tana hararar Ikram kamar itace tai maganar. “Malama koma gaba”.
“Ni dai aunty ki barni anan nafi son baya cikina ya cika da yawa zan kwanta”. A fusace ta ƙara y
unƙirin yin magana ya dakatar da ita. “Bana son shirme fa kina
ɓ
atamin lokaci nabar matata tana barci kowane lokaci zata iya tashi, ganina kusa da itane kuma abinda tafi buƙata a yanzun”.
Tamkar saukar aradu haka furucinsa ya daki ƙirjin Anam saboda
da yaren malay yay maganar yanda zata jisa ta fahimta da ƙyau. Idanunta ta rumtse ta bu
ɗ
e motar ta shiga batare datace masa komai ba. Shima bai sake cewarba ya harbar motar zuwa waje dan maigadi dama ya wangale masa gate tuni........
✍
*_
🚶🏻🤕😣
ask
iya kuyima ƴar mitsilarnan taku kashedi ta fita sabargar angonmu.
😚
_*
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn A
bdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS
👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDA
N KUMA KATI NE SEKU TURAWA
👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi
biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS
👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA
👇
0913484810
7 ko
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏🏽
_**_Typing
📲
_*
*_
❤
🔥
BABU SO....!!
❤
🔥
_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_14_*
..........Ko parking bai gamayi ba da ƙyau a ƙof
ar gida ta bu
ɗ
e motar ta fice. Ya bita da kallo harta shige gida. Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya saki tare da murmushi. Ikram ta fito tana masa bye-bye. Hanun shima ya
ɗ
aga mata har lokacin da murmushin a fuskarsa. Motarsa ya tada tare dayin reverse yabar an
guwar dan baizo da niyyar shiga ko'ina ba tunda ko wanka baiyiba. Ga Fadwa dake buƙatar taimakonsa ya baro tana barcin gajiyar daya tara mata a daren jiya wadda shi kansa barcin bawai ya ishesa bane ba, kawai dai sawun giwa ne ya take na raƙumi.
Anam batai magana da kowa ba ta haye sama, tasan
ɗ
akinta zai yuwu su Amrah na ciki yanzu, na Mamie ma tana jiyo maganar mutane a ciki. Dan haka tai wucewarta falon Abie. Nan kam kowa bata samuba, hakan ya bata damar kwanciyarta ta saki kuka mara sauti. Kuk
a tayi sosai bana wasa ba har barci
ɓ
arawo yay awan gaba da ita batare data sani ba. Wajen sha biyu Abie daya shigo ya ganta ya shiga ta
ɓ
a goshinta da tunanin ko zazza
ɓ
in nata ne ya dawo. Amma sai yaji babu zafi jikinta. Idanu ta bu
ɗ
e da suka maita nauyi d
an kukan data sha. Ta dubi Abie
ɗ
in dake mata murmushi. “Sleeping beauty na ta tashi”.
Murmushi tai da tashi zaune. “My Abie good morning”. Ta fa
ɗ
a a marairaice. “Morning Darling duk gajiyar bikince ta saki zuwa nan
ɓ
uyan barci?”. Fuska ta
ɗ
an
ɓ
ata
. “Abie su Amrah basa barina nai barci mai ƙyau dan surutunsu. Gashi ƙasa nake kwana dan bana son kwana da kowa
ɗ
akin ma ya mana ka
ɗ
an”.
Murmushi kawai yay da shafa kanta. Sai kuma ya dubi idanunta da suka sake fitowa da ƙyau. “Mamana idanun nan kamar
anyi kuka da su?”. Da sauri ta girgiza masa kanta. “Abie rashin barcine fa”. Bai gamsu ba. Sai dai baice komai ba. Itama mikewa tai da fa
ɗ
in, “Bara naje nayi wanka”. Tai maganar da zuwa ta kama hanunsa ta sumbata. Da kallo kawai ya bita, dan yasan tayi ha
kane dan karya cigaba da tuhumarta akan kumburin idonta daya tabbatar kukane ya sakasu komawa hakan tunda ba yau ya santa ba.
Ta fito wanka tana shafa mai Amrah ta shigo ta sanar mata tayi baƙo. Da mamaki take kallonta sai dai batace komai ba. A
mrah ma ta juya ta fita abinta. A nutse ta ƙarasa shirinta ranta fal tunanin wanene?. Ba ta da mai bata amsa dan haka ta fesa turare da
ɗ
aukar wayarta ta fito.
Tayi ƙyau sosai cikin wando da rigar jikinta, sai siririn mayafi data yana a kanta. A wajenta wa
nnan shigace normal saboda a inda ta tashi, sannan rigar bata kama jikinta ba ta kuma sakko har kan mazaunanta. A falo ta samu su aunty Mimi, har zata zauna Mamie ta harareta. “Bake naji ance anzo nema ba?”. Cikin
ɓ
ata fuska tace, “Ni banyi da kowaba fa za
i zo Mamie”.
Aunty Hamida tai dariya. “To
ɗ
iyata kika sani ko a ƴan biki ne wani yay sau da baya?. Tashi kije dan da alama mun kusa dawowa wani shagalin insha ALLAHU”.
“Hu'um aunty ALLAH ya kiyaye ni karatu ma zan koma”.
Daƙuwa aunty Ham
ida tai mata. “Karatun gidan ku, a wannan shekarun naki ai aure ne ya dace ko dan kina ganinki ƴar ficika da ƙaramin jiki? Maza tashi kije ana
ɓ
ata masa lokaci”.
Badan taso ba ta fito, Mamie na kiranta tazo tasa hijjab bama taji ba dan a fusace take
da taikaicin koma wanene.
Dr Jamal dake daƙilar waya ya
ɗ
ago fuskarsa
ɗ
auke da murmushi yana kallonta. Itako kallo guda tai masa ta kauda idonta. Kujerar dake gefensa ya gyara mata, ta ƙaraso fuska babu walwala tana masa sallama. Amsawa yay
murmushinsa na sake fa
ɗ
a
ɗ
a. “Barka da fitowa gimbiyar mata”.
“Ina yini”.
Ta fa
ɗ
a a takaice.
“Lafiya lau. Bismillah ki zauna mana”.
Kamar zatace a'a sai kuma ta zauna.
“Kiyi haƙuri nazo babu izini. Sai dai karki manta dama nac
e zan zo dubiya”.
Ɗan murmushin yaƙe tayi, a taƙaice tace, “Babu damuwa”.
Idanu ya
ɗ
an kafeta da shi, a ƙasan ransa yana tattaro abinda ya dace ya fa
ɗ
a. Ɗagowa tai ta dubesa itama fuska a murtike. Ya kauda nasa idon. Cikin zolaya yace, “ALLAH
ni sai ma naji ina jin tsoronki kamar”.
Haka kawai yanda yay maganar ya bata dariya, ta shiga ƙyalƙyalawa shiko ya kafeta da idanu yana murmushi. A dai-dai nan aka bu
ɗ
e gate
ɗ
in gidan mota ta shigo. Su duka sukabi motar da kallo har lokacin kowanne
da dariyar kan fuskarsa. Dr Jamal ya fa
ɗ
a
ɗ
a tasa ganin Shareff, itako haka kawai sai da gabanta ya
ɗ
an fa
ɗ
i.
Ya kai kusan mintuna hu
ɗ
u bai fitoba idonsa kafe a kansu, sai dai shi basa ganinsa kasancewar tinted glass ne da motar. Murfin motar ya bu
ɗ
e
ya fito da nufin shigewarsa ya nuna bai gansu ba kawai. Sai dai Dr Jamal daya taso fuska
ɗ
auke da murmushi ya hana hakan. Fara'ar dole ya ƙaƙaro yana mika masa hannu kamar yanda shima ya miƙamasa. “Ango! Ango!! Ƙyallinka dabanne”.
“Haka dai kace”.
Shareff ya bashi amsa hankalinsa nakan Anam data
ɗ
auke kai kamar bata gansa ba.
“Haka
ɗ
inne ma abokina. Dan ko kamshinka yau ya sake bunƙasa fiye da kullum. Muma dai gamu nan fara kafa foundation mukai matsayin nan naku haka nan”.
Gabansa n
e ya fadi, amma sai ya dake ya saki gajeren murmushi. “ALLAH yasa haka to.”
“Insha ALLAH wannan karon da gaske nake abokina”.
Nan
ɗ
in ma murmushin yayi kawai da fa
ɗ
in, “Bara na shiga na gaida su Mamie”.
“Okay to a fito lafiya”.
Ido suka
ha
ɗ
a da Anam ya wulla mata wani mugun kallo data jima bata gani daga garesa ba ya wuce. Dr Jamal daba lura yay ba ya dawo ya zauna yana dariya. “Kinga Yayan nan naki da gaske angwancin nan fa ya amshesa. Kwana daya kacal harya canja kamar bashi ba”.
Ƙin cewa komai tayi, sai dai tayi ƙaramin murmushi. Shima murmushin yayi yanaji kamar ya ha
ɗ
iyeta. Sallamar Amrah ta katsesa daga kallon da yake mata. Duk suka dubeta. Gaishe da Dr Jamal tai, ya amsa cike da fara'a da tambayarta gajiyar biki. Tace masa A
lhmdllhi tana maida kallonta ga Anam. “Anam Yaya Shareff yace yana jiranki zai amshi ajiyar daya baki”.
Kallon Amrah take cike da mamaki da rashin fahimta, sai dai ta rasa abin cewa. Sai Dr jamal dake kallonsu ne ya katse shirun da fa
ɗ
in, “Inaga jek
i kawai ki basa saƙon sai na jiraki. Dan da muhimmiyar magana nazo”.
Kamar zatace ita babu wani saƙonsa a wajenta sai