Showing 201001 words to 204000 words out of 216641 words
dai fa ganin lamarin yafi ƙarfinta dan hatta Mommy yau la'antarta take ga ƴan biki sai ta nema fita a gidan tana kuka wai su Daddy sun shirya wulaƙantata. Nanfa wasu a munafukai masu son jin ba'asi suka take mata
baya, sai dai taƙi sauraren kowa, tana gab da barin layin nasu wani mai mota ya shawo kwana, duk da horn da yakeyi sam Gwaggo daketa faman sambatu da surutai batajisa ba, shi kuma ALLAH ya hanashi damar taka birki, ya kwasheta sama ya direma kasa, yana son
riƙe kan motar ina saida taya
ɗ
aya ta dirza ƙafar Gwaggo har ana iya jin karar farfashewar ƙashi. Tun ƙarar azaba ta farko data saki bata sake fahimtar ina take ba ta suma. Dan danan aka rufu kanta, har su Daddy labari yazo musu sun fito, nan fa layin ya
cika dankam. Matasa zasu rufu kan mai mota da ƴan biki yazo dauka baba Ibrahim ya dakatar da su. Kamalarsa da dattakon kasancewarsa tsohon arziƙi ya sakasu bin umarni, sai dai an kama Gwaggo da babu alamar numfashi a jikinta an saka a motar mutumin aka nuf
i asibiti.
Babu ko tausayi a fuskar Gwaggo Halima, sai ma faffa
ɗ
ar magana take wai ai ƙarshen Gwaggo kenan. ALLAH ma ya kara sakata a masifa fiye da hakan. Mafi yawan mutane maganganun Gwaggo haliman basu
ɓ
ata ransu ba, sai dai duk da mugun halinta
baban Fadwa ya kasa haƙuri shima a wajen ya yanke igiyar auren Gwaggo halima biyu. Ai sai lokacin Fadwa da Mommy suka sake tunawa da mutuwar nasu auren fa suma. Nan guri ya kara daukar zafi fa
ɗ
a ya dawo sabo fil da ƴar koke-koke abin zakkunya da takaici...
........
✍
*_Typing
📲
_*
*_
❤
🔥
BABU SO....!!
❤
🔥
_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_BABU SO
👉🏻
AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_78_*
..
.......Wannan harmutsi da dangin mijin Aysha suka tarar yasa suka dakatar da
ɗ
aukar amarya, acewarsu ai basu san haka uwar amaryar da danginta suke ba. Ƙololuwar tashin hankali Mommy ta sake shiga, har takai ta yanke jiki ta fa
ɗ
i itama dai sai da aka kaita
asibitin. Gwaggo halima dake dariyar mugunta ta tafi gida ranta fes Mommy da Gwaggo a bala'i, sai dai kuma mahaifin Fadwa ya hana mata koda shiga gate, yace Fadwa ka
ɗ
ai ce ƴarsa, itama zai bata mafakane har tai idda saboda karya salwantar da rayuwarta a c
igaba da samun bara gurbi a cikin al'ummar musulmai. Amma ta sani bazata ta
ɓ
a jin da
ɗ
i ko
ɗ
igon farin ciki a gidansa ba. Rikicewa Gwaggo Halima tayi, kamar yanda Fadwa dake kuka rirus dama dan da ƙyar Gwaggo Halima ta jawota suka tahonan saboda ido rufe ta
ke neman Shareff amma taƙi ganinsa. Masu aiki yasa suka shigo da ita, Gwaggo Halima kuma ya tabbatarma masu gadi ko hanunta ya ta
ɓ
a masa gate abakin aikinsu. A karan farko itama ta fara kuka, dan a zatonta koda yay sakin guda biyu zai haƙura ya barta ta ci
gaba da zama cikin ƴaƴanta har a sasanta. Sanin da yay mata zata iya ƙin nufar gida ya sakashi turata a mota da kansa yaja motar ya maidata gidan su Daddy da tuni ƴan biki sun fara watsewa, ba kowa na
ɓ
angaren Mommy. Na
ɓ
angaren Mom kuwa da dangin su Daddy
zama daram wasuma shirin tafiya dinner
ɗ
in Khaleel da amaryarsa suke. Dan su Hajiyar Sudan sun shiryama wannan biki kwarai da gaske....
Komai ya hargitse, komai ya rikice. Burin Gwaggo na watsa biki wani yankinsa ya tabbata. Domin kuwa akan bigi
re na duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka ake. Ita dake amsa matsayin suna uwar daba tana can asibiti ƙafa a ragargaje batama san inda kanta yake ba likitoci sun rufu akanta. Manyan dodannin fadarta su Mommy sun masifar tsanarta fiye da rayukansu a
yanzu. Dan kuwa Mommyn da kowa kema kallo matsayin ƴarta da zata iya zama magajiya a gareta na kwance bisa gadon asibiti jininta yay ƙololuwar hawa har yana son zarce abinda ba'a fata. Tana da saki guda biyu a kanta, igiya daya ce kacal ta rage mata a yan
zu, kuma Daddy ya tabbatar musu daga asibiti su wuce da ita karta sake dawo masa gida. A daren daga gidan angon Aysha takardar saki ta iso a cewar iyayen ango
ɗ
ansu bazai rayu da ƴar mace ba. Wannan al'amari yayi matuƙar ƙona zuciyar su Daddy har Abie na t
abbatarwa sai ya kaisu kotu, da ƙyar su Abba suka lallashesa. Gwaggo halima data
ɗ
auki Gwaggo tamkar uwarta mahaifiya a yanzu babu wanda tafi tsana a duniya sama da Gwaggo, a sanadinta
ɗ
iyarta mafi soyuwa a gareta ta rasa ciki ta rasa aurenta, ita a karan
kanta ta rabu da ƴan uwanta shekara aru-aru a dalilin hu
ɗ
uba ko muce tarbiyyar Gwaggo. Ta rasa igiyoyin aurenta da ƴaƴanta a cikin abinda bai gaza awa shidda da barinta gidan mijinta cike da fatin ciki ba.
Yayinda Aysha itama ke can tana rusar kuka t
amkar ranta zai fita, dan kuwa ta tabbatar alhakin mahaifiyarta da kakartane ke bibiyar ƙaddararta, a ranar da aka
ɗ
aura mata aure a ranar miji ya saketa ko gidansa ba'a kaita ba. mijin data
ɓ
ata tsahon shekaru tana mutuwar so da ƙauna.
Haka zali
ka Fadwa celeb.... Wadda ke ganin ko ta tashi a rayuwar da ita a karan kanta bata ta
ɓ
a gundurartaba balle kallonta a juye. Shareff shine dukkanin farin cikin duniyarta, da sonsa ta rayu da shi ta horu, a rana
ɗ
aya dalilin makircin ƙawayen data
ɗ
auka babu y
asu a duniyarta da cigabanta ta rasashi. Auren mahaifiyarta da aka ƙulla tsahon shekara talatin yau ya girgiza shima a dalilin wadda suke kallo gunkiyarsu da bayan horon tarbiyya ga uwarsu suma akan zaren tarbiyyar tata suka horu.....
Shareff da kom
ai ya ƙwace masa a wannan ga
ɓ
ar tunaninsa yama rasa ina zai kama ko samun mafaka, sai dai ya jure, ya danne wajen tattare hankalinsa kan matarsa da jikinta yay ru
ɗ
ewar da daren sai da Dr Jamal yazo ya sanya mata ruwa...., ya kuma saka Fharhan a daren kaim
a su Sima, Siyyah, Amal, Bibah ƴan sanda suka cafkesu, tare da doctor
ɗ
in dayay aikin.
Abba, Daddy, Abie, aunty Mimi. Mamakin Gwaggo da
ɗ
unbin al'ajabinta ya hana zukatansu bugawar gaggawa a ƙirazansu. Sun rasa wane aji na duniya ya kamata sunan Gwag
go ya fita, dan a iya hasashensu sun gagara kama minene dalilinta na duk aikata wa
ɗ
annan abubuwan?. Kenan akwai abubuwan da suka shu
ɗ
e da yawa a baya dake buƙatar nazari mai fa
ɗ
i da neman ba'asin dalilin aikatashi ko ganinsa a aikace. Sunyi ta mazan bin su
Baba Ibrahim asibiti, inda har dare ya raba suka dawo gida babu wani bayani akan jikin Gwaggon likitoci dai sun rufu a kanta sunata faman kaikawo....
*_WASHE GARI_*.
Sai a yau asabar zuri'ar MD Shareff suka sami ganin Gwaggo, sun fara
shiga
ɗ
akin da aka kwantar da Mommy itama bisa matsawar Abie suka dubata, inda acan suka sami Shareff da Maheer tare da ita. Basu jimaba suka fito, Mommy da abubuwa da yawa ke cin ranta musamman sakinta da Daddy yayi ta taso ta biyosu, duk yanda su Sharef
f sukaso dakatar da ita taƙi yarda da hakan. Hankalinsu ya tashi da ganin jikin Gwaggo, dan ƙafarta tayi wani irin mahaukacin kumbura daya ninka jikinta biyu, gashi an yanketa daga gwiwa zuwa ƙasa dan can
ɗ
in yayi ragargajewar da bazai ƙara aiki ba. Sai ka
nanun ciwuka da ba'a rasa ba. Da ƙyar take iya amsa musu, sai dai abin mamaki idonta a soye babu ko alamar hawaye. Bayan sun jajanta da
ɗ
aukar kusan mintuna goma sha biyar a
ɗ
akin sukai haramar tafiya. Muryarta a
ɗ
ashe, amma hakan bai hanata fita da kaushi
ba ta dakatar da su...
“Na rikeku na muku gata fiye da uwar data haifeku, amma a dalilin kanƙanin abu kuke nuna alamun juyamin baya Muhammadu. Bazan hanaku ba, sai dai ku sani bazan yafe muku wahalar dana sha a kanku ba”.
“Bakece zaki ƙi yaf
e mana ba, mune bazamu ta
ɓ
a yafe miki ba Hindatu...”
Muryar Gwaggo Halima ta ratsa kunnuwansu a bazata. Su dukansu suka juya suna kallonta da mamaki, dan kuwa babu lallashin da basu mata ba danta biyosu tace bazata ba. Ta cigaba da takowa firingau-fir
ingau dan a kwana
ɗ
aya duk ta sususce ta fita a hayyacinta tamkar ba halima ƴar gata ba. Ta ƙaraso gaban Gwaggo tana mai share hawayenta. “Hindatu kamar yanda na fa
ɗ
a mune bazamu yafe mikiba annamimiya azzaluma. Musamman ni nan Halima. Hakama iyayenmu dake
kwance a cikin kabari, da sunada damar da zasuyi magana sautin yaje cikin kunnuwanki da sun nanata miki kalmar ALLAH ya isa fiye da sau dubu. Kinga wannan ƙafar taki da aka yanke, ba itace ka
ɗ
ai ƙarshen azabar da zakisha a duniya ba. Yanzu kika fara gani,
bayan
ɗ
an
ɗ
anar
ɗ
acin rashin haihuwa na shekaru sama da sittin da kikai a duniya, yanzu zaki cigaba da fuskantar ra
ɗ
a
ɗ
in azaba ne mai muni tsinanniyar tsohuwa mai zubin ƴan wuta.......”
“Ke ce dai mai zubin ƴan wuta...”
Cewar Mommy a hasale. Dariya
Gwaggo Halima ta sanya. “Ke kumafa? Maza je kiji da kanki shasha kawai. Hawan jini da zawarci ma sun ishi rayuwarki ƴar wahala, sannan kema a gurinta baki tsira ba”.
“Hahaha garama ni, kuma koba komai zuwa yanzu na tabbatar miki Shareff jinina ne tun
da gaki a zawarci ƴarki a zawarci. Kuma yanda ya saki Fadwa itama Anaam sai ya saketa dan bazai zauna da zuri'ar wa
ɗ
anda basu san hallaciba. Ƴar dukiyar da akaga ya tara akemawa to babu mai cinta har kai uban nasa”.
A karan farko Daddy ya
ɗ
ago y
ana kallon Mommy, amma sai kafin yace wani abu Abba ya cafe murya a kausashe.
“Mu bamu kasance marasa halacciba Nafisa. Wannan tsohuwar dake da kika rayu a gidanmu matsayin agola kune marasa halacci, kuma dukiya da kike takama Shareff ya tara bara na
bu
ɗ
e muku zancen yau, kaso biyu bisa ukun abinda kuke ganin Shareff ya tara na Usman ne.......”
“Please Yaya Abubakar ba wannan ga
ɓ
ar mukeba...”
Abie yay niyyar katse Abba. Amma sai Abban ya fisge jikinsa. “Barni Usman, gara wannan mahaukaciyar
tasan ANNABI ya faku. Duk da ƙulle-ƙulle datai domin ganin ta raba tsakaninku da Usman hakan bai hana ka cigaba da tallafa rayuwarsa ba, har take iƙirari da fariyyar dukiyar
ɗ
anta. ki shiga hankalinki kuma kisan mikikeyi, daga ke har uwar taki, sakamako ku
ma yanzu kuka fara girba, dan wlhy Gwaggo alhakin iyayenmu ka
ɗ
ai bazai barki sake jin da
ɗ
i ko farin cikin rayuwa ba. Tur da masu irin halinki na annamimanci da hana zaman lafiya a cikin zuri'a. ALLAH zai saka mana matuƙar sakayya a ranar da ga
ɓ
o
ɓ
i zasuyi m
agana madadin bakuna”.
Tuni Mommy da kanta ke bada wani yuuuu na haurawar jininta sama ta dafe gadon da Gwaggo ke kwance. Kallon Shareff take cike da son ƙarin bayani. Lips
ɗ
inta na rawa. Kansa ya jinjina mata tun kafin tace komai. “Mommy abinda Abb
a ya fa
ɗ
a shine gaskiyar magana. Dukiyar Abie ce ni nawa basu wice kudin siyan ruwa ba a cikin taron biki”.
Wata irin ƙara Mommy ta saki da faduwa ƙasa da
ɓ
ar, Gwaggo ma tuni gadon da take a kai ya fara jijjigar shiga a tashin hankali. A halin da tak
e ciki da dukkan ƙarfin halin nata Shareff
ɗ
in shine kawai gadararta a yanzu, dan ko maganar aikin da ake fa
ɗ
ar za'ai mata na ƙafarta ta gama sawa a ranta ko kowa ya gujeta suna da Shareff ai. Ashe-ashe abinda sukema gadarar ma ba nasu bane. Da tasan haka
bazata ta
ɓ
a yarda taima su Abba hakaba. Da ta cigaba da musu fuskarta ta tun ƙuruciya. Amma yanzu ta tabbatar bakin alƙalami ya rigada ya bushe kuma....
Cikin ƙanƙanin lokaci duk sukai waje, hatta Shareff da Maheer ji sukai bazasu iya zama ba, dan da
ma tsananin kunyar su Daddy sukeji saboda abin kunyar da kakarsu ta jima tana tafkawa da mahaifiyarsu duk da kuwa akwai Gwaggo Halima tare da su......
_________
★
Kwanaki sun cigaba da shu
ɗ
awa, ta tabbata dai Gwaggo Halima ta dawo gida da zama, d
ole ta share sashen Baba Umar da babu wanda yasan a duniyar da yake yanzu ta zauna. Mommy kuma ta koma gidan Baba Ibrahim kamar yanda ya shardanta mata, dan ya hana su Shareff bata wajen zaman da sukai niyya. Yayinda Gwaggo ke cigaba da jiyya mai wahalarwa
a asibiti. Dan kuwa babu wani mai jiyyarta sai Nurse's dake kula da ita. Mommy din ma data raina da kanta tace bazata iya jiyyarta ba dan ƙafar tata duk da likitanci na kula da ita wari takeyi matuƙa. Su Daddy basuyi butulci ba tare da su Baba Ibrahim da
mahaifin Fadwa ke biyan ku
ɗ
in zamanta a asibitin. Hakama Fadwa na gidansu, mahaifinta ya amshe wayarta, ya kuma kwashe dukan ƴan aikin gidan yanzu itace ke komai ga ƙan
enta, girki, gyaran gida, ya baza camaras tako ina, inma bataiba ko baya gidan zai gani,
hakama waya kota ƴan uwanta ta
ɗ
auka da nufin kiran wani itama tasan sauran. Duk ta fige ta fita a hayyacinta saboda kuka da tsananin ƙulafucin mijinta da takeyi, ga Gwaggo Halima ta mata nisa yanzu, ƙanenta kuwa sai zuba mata rashin kunya sukeyi tunda da
ma a haka suka taso na ƙasa baya girmama na sama da shi. Satinsa uku a gidan maganar auren Babansu ya tashi da wata hamshaƙiyar mace ƴar boko mai babban mukamin gwamnati a jihar ta kano...........
✍
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBI
N IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAK
U BIYA KUDIN BOOKS
👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA
👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏🏻
_**_Typing
📲
_*
*_
❤
🔥
BABU SO....!!
❤
🔥
_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_BABU SO
👉🏻
AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_79_*
..........Yanda Fadwa ke jigatuwa a gidansu haka Mommy ke ji
gatuwa a gidan Baba Ibrahim, dan kuwa matansa babu kanwar lasa a ciki. Basa raga mata koda da wasa. Abinci kuwa iya abinda suka bata shine zataci, bata isa cewa tak ba Baba Ibrahim zai silleta tass. Kaf ƴaƴanta an hanasu ra
ɓ
arta har su Shareff kuwa. Itama
duk ta fige ta ru
ɗ
e da damuwa mai tsanani, ga rashin aure, ga rashin ƴaƴa, ga dukiyar
ɗ
an da take taƙama dashi ashe ta maƙiyintace. Kai ina itako zata saka kanta taji sanyi wannan rayuwa haka.
Gwaggo Halima kam ai zamu iya cewa ta susuce a wannan
ga
ɓ
ar. Dan kuwa maganar auren mijin nata ya risketa dan abune da aketa faman watsasa a gidajen talabijin da rediyoyi. Bikine ake shiryawa na hamshaƙai biyu masu daidaiton ƙwarya tabi ƙwarya. Ga rashin ƴayanta tare da ita, dan kuwa itama dai su Abba sun ƙw
ace wayoyinta, sun kuma kafa mata sharadin inhar tana buƙatar zama da su sai ta nutsu, inba hakaba zata bar musu gida, dan yanda sukayi haƙuri da ita a baya a yanzu kam bazasuyi ba.
Kwanan su Sima takwas a police station aka shiga kotu, dan duk m
agiya da roƙo da iyayensu ke ma Shareff ya rantse sai sunyi shari'a. Kasancewar laifinsu a bayyane yake ba'awani wahalar da shari'a ba a zama biyu kacal aka yanke musu hukuncin zama gidan yari na watanni goma sha
ɗ
a. Tare da tara mai tsoka. Kafin kace mi me
dia ta
ɗ
auka, babu abinda ke trending kamar labarinsu. Manyan yaran da akeji dasu a tiktok da istagram dama mafi yawan kafafen yanar ta gizo sunsha
ɗ
auri a dalilin shugabarsu. Ga labarin mutuwar auren Fadwa ya zama kamar wani abin izgili a bakunan wanda su
ke jin haushinta. Sai dai wasu hakan ya sanyaya musu jiki matuka. Dan inhar haka zata kasance ga Fadwa suma
ɗ
in basu tsiraba kenan tunda duk iri aiki guda sukeyi, wasu ma nasu yafi nata
muni matuƙa. A take wasu suka fara goge wasu videos na rashin tarbiyya
dake a shafukansu, wanda kuwa ke kai musu ji suke yanzu aka fara wasan ma. (Ya rabbi ka shirya mana zuriya damu baki
ɗ
aya
😭🙏🏻
)
Kwanan Anaam goma sha biyar a gidan Shareff ya dauka matarsa suka