Showing 108001 words to 111000 words out of 216641 words
kanta yake ta maida ta sake duƙarwa.
“Mamana!”.
Abba ya kirata cike da kulawa.
Cikin rawar murya ta amsa masa. Yay
ɗ
an murm
ushi da sake gyara zamansa. “Kin yarda mu
ɗ
in iyayenki ne bazamu ta
ɓ
a cutar da ke ba?”.
Kanta ta jinjina masa tana ha
ɗ
iye hawayenta. Ya cigaba da fa
ɗ
in, “Alhmdllhi naji da
ɗ
i da kika fahimci haka, ina kuma fatan ki kasance mai biyayya tamkar yanda shima
ɗ
an uwanki ya kasance amatsayinsa na namiji. Duk da nasan abinda mukayi munyisane akan ga
ɓ
ar data dace akaran kanku bawai zumincinmu kawai ba. Ki ƙara daurewa ki zama mai haƙuri da biyayya,
domin aure dai an riga an
ɗ
aura, ba kuma yanzu aka
ɗ
aurasaba ko j
iya, an
ɗ
aurashi rana
ɗ
aya dana ƴar uwarki kamar yanda Yaya ya fa
ɗ
a ranar a gaban kowa, sai da aka
ɗ
aura naki da safe sannan aka
ɗ
aura nata da azhur, hakan yasa ko shi Shareff bai sani ba, mun kuma
ɓ
oye ne saboda wasu dalilai, hakama a yanzu mun bayyana a
gareku da kowa ma saboda wasu dalilai. Dan haka zaki tare ranar juma'ar nan insha ALLAHU a
ɗ
akin mijinki. ALLAH yay miku albarka, ya baku zaman lafiya da zuria masu albarka da MANZON ALLAH zai alfahari da su kamar yanda muke fatan yay alfahari da ku da mu
baki
ɗ
aya.”
Kuka takeyi sosai. Sai tausayinta ya kamasu, kiranta Daddy yay ta rarrafa zuwa gabansa. Hanunsa ya
ɗ
aura saman kanta ya shiga saka mata albarka da mata nasiha mai ratsa jiki tamkar yanda Abbah yay mata. Shi dai Abie bai ce komai ba yana d
ai kallonta ne kawai. Hakama Mamie da aunty Mimi. Sai da suka tabbatar ta tsagaita da kukan da takeyi sannan suka fice su duka, Aunty Mimi ce ta dawo kusa da ita, jikinta ta jawota ta rungume tana lallashinta, a haka su Mom suka shigo suka samesu ita da au
nty Amarya. Suma dai nasihar sukai mata da lallashi. Daga ƙarshe Mom tace hajiyar sudan zata zo ta ƙarasa aikinta tunda wancan yabi iska.
Ɗakinta ta koma ta cigaba da kuka har barci ya kwasheta, bata kuma farka ba sai kusan azhar da hayaniya ta i
sheta. Wanka tai cikin rashin ƙarfin jiki sannan ta fito, ganin akwatuna barbaje a tsakkiyar falonsu ga mutane cike anata kallo ya sata komawa da sauri tana faman tura baki. Amrah ta kira cikin roƙo tace ta kawo mata tea, babu jimawa kuwa ta kawo mata tana
tsokanarta da fara bata labarin kayan lefen da aka kawo mata. Duk da bata da ƙarfin jiki haka ta kora Amrah waje ta sakama
ɗ
akinta key dan bata buƙatar jin komai. Saboda ma ta kauda abun a ranta sai ta
ɗ
auki lap-top ta kunna film abinta, tana shan tea tan
ayi, data gama shan tea
ɗ
in sai ta kwanta ta cigaba da kallon a haka tana jiyo hayaniyar gidan har lokacin sama-sama.
A falo kam ƴan uwa da abokan arziƙi da makota kowa ya yaba da wannan lefe na girma. Babu fariyya a cikinsa kuma babu ƙaranta,
ango Shareff ya taka rawar gani duk da ya ha
ɗ
a lefen ne a ƙurarren lokaci dan Daddy ne ya bashi umarnin yinsa a cikin kwanaki hu
ɗ
u kacal. Jiya da dare kuwa sai gashi da akwatina set biyu kamar yanda akayi na Fadwa. Sai dai wa
ɗ
annan shi da Aunty Amarya suka
ha
ɗ
osu ba kamar na Fadwa ba da Mom ce ta ha
ɗ
a Mommy ma ta ha
ɗ
a set
ɗ
aya.
Bayan watsewar gidan Mamie ta samu zama da Anam. Nasiha tai mata mai ratsa jiki da
ɓ
argo, wadda ta ƙara sanyaya ranta da sake sakata karaya. Ta fahimci kowa son wannan *_Auren
ƙadda ko biyayyar?_* nasu yake a gidan, bata da wani mai goya mata baya akan ƙinsa sai Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima. Duk yanda Mamie taso daurewa itama kasawa tai saida tai hawaye, dama dauriya kawai take na rabuwa da tilon ƴarta. Sai dai idan ta ke
ɓ
e
tana kukanta ko kuma agaban Abie da shima dai dauriyar kawai yake sai dai yana lallashinta.
Washe gari alhamis akaje aka tsantsarama Anam jeren daya girgiza zukatan su Mommy, dan kuwa akwai ƴan rahotonsu a wajen a cikin dangin mahaifiyar su Dadd
y da suke manne da Gwaggo Halima. Ranar ma dai ƙaramin hauka aunty Halima tazo sukayi da su Mommy a gidan, anan ne ma su Daddy suka san Fadwa na gida bata koma gidan mijinta ba kamar yanda mahaifinta ya shar
ɗ
anta. Rai
ɓ
ace Daddy ya nema ba'asi, dan shima b
irkice musu yayi fiye da yanda suke zato da tsammaninsa. Ai fa babu shiri Fadwa ta fadi cewar Mommy da Mahma (Gwaggo Halima) sukace bazata koma ba. Ran Daddy ya
ƙ
ara
ɓ
aci, a take yanke yayma Mommy saki
ɗ
aya. Tsitt gidan yayi na wucin gadi dan zuciyar kowa
sai da ta girgiza musamman Mommy
ɗ
in dake cika bakin idan ya saketa sai mi daga farko, dan ita a tunaninta fa Daddy cika baki kawai yake babu wani sakinta da zai iyayi. Zai ƙara na biyu Abie ya shiga roƙonsa da magiyar dan ALLAH kar yayi. Yana matukar jin
nauyin Abie, dan haka yay shiru batare daya ƙarasa na biyun ba ya bar wajen yana huci. Itama dai Gwaggo jan Mommy tayi sashenta tana faman yimata fa
ɗ
an kato
ɓ
arar tata.
Ranar dai haka aka kwana gidan rai
ɓ
ace, yayinda Abba da kansa ya
ɗ
auka Fadwa ya m
aida gidan Shareff. Duk abinda ke faruwa a gidan Maheer ya kira Shareff ya sanar masa dan yaje gidan gaishesu ya tadda ƙura ta tashi. Amma sai Shareff
ɗ
in baije ba dan yasan zuwansa
ɗ
in sabon masifane, kuma har yanzu tsoron ha
ɗ
uwarsa yake da Mommy. Abbah b
ai baro gidan ba sai da ya ha
ɗ
asu yay musu nasiha mai ratsa jiki, daga ƙarshe ya sa musu albarka da garga
ɗ
in sake barin wata
ɓ
araka ta shigo musu da har zasu dinga kawota gabansu matsayinsu na iyaye, ya kamata su dinga juriyar sasanta kansu kamar sauran ma
'aurata su riƙe sirrin gidansu.
Washe gari aka tashi da hidimar sabon shagalin biki, dan kuwa dai Abie ya shirya gagarumar walima dama tunda ALLAH bai cika masa burinsa na gayyatar tarin mutane
ɗ
aura auren tilon ƴar tasa ba kasancewar a
n
ɗ
aurashi a sirrance ne. Abin zai baka mamaki idan kaga yanda mutane ke
ɓ
ullowa tako ina, da wanda invitation ya sama a ranar
ɗ
aurin auren Maheer da wanda ma ba'a gayyata ba. Dan danan fa gidajen suka cika taf.
Mommy da Abie yay tsaye tun a daren j
iyan Daddy ya maidata
ɗ
akinta abin duniya ya gama isarta ita da gwaggo, sai dai Gwaggo ta hanata cewa komai sai danginta da suka iso gidan keta kananun magana akan
ɓ
oye musu auren da akai tun farko, dan zuwa yanzu dai kowa ya shaida Anam itace Uwargida duk
da ba addini ne ya wajabta hakan ba, amma ga al'ada irin ta bahaushe mukance wadda aka riga
ɗ
aurama aure itace Uwargida musamman ma wannan da akai rana
ɗ
aya.
Gwaggo Halima dai bata leƙo gidan ba ma, tana can itama tana zuba tata tijarar a gidan ta
sai dai mijinta ya tabbatar mata ko sawun inuwarta ne ya fita gate a bakin aurenta kuma saki uku yake nufi, wannan shine ya hanata fitowa. Sai daita bada umarnin canja komai na Fadwa a gidan Shareff. Dan tun sassafe akaje aka kwashe kayanta tas na furnitur
es da labulale da wasu a kayan kicin aka zuba mata sabbi ƙal ƙirar waje wai duk dan dai kar Anam ta fita wani abu dan dukiyar da Abie da Mamie suka zubawa
ɗ
iyarsu harma da Aunty Mimi sai yama
ɗ
i
ɗ
i ake da shi a dangi. Wasu ma a waya suka gani sai kuma yau da
aketa zuwa ganin amarya da masu zuwa gulma wai dannar ƙirjin Fadwa. (
😂
Basai an dannemu ba ma ku kwantar da hankalinku mu bama kishi
😜
).
Amarya Anam data ci kukanta tun daga daren jiya har safiyar yau tayi ƙyau cikin kwalliyar ha
ɗ
a
ɗɗ
en l
esirin da Abie ya mata, aka kuma na
ɗ
eta cikin alƙyabba kai kace daga gidan sarauta aka
ɗ
akkota. Kuka dai da hawaye na ƙarewa da na Anam amarya sun ƙare, musamman lokacin da walima ke gudana dan manyan malaman addini aka
ɗ
akko suka rugurguza wa'azi akan zam
antakewar aure a musulunci da al'adar malam bahaushe. Duk da tasan haƙƙoƙin miji kan matar tasa, dana mata akan mijinta hakan bai hana hankalinta sake tashi ba da sake jinsu a yau a bakunan malamai. Anci an sha kowa ya godema ALLAH. Yanda amarya tai ƙyau h
akama ango Shareffuddeen yay matuƙar ƙyau cikin
ɗ
anyar shadda daketa maiƙo ga wani ƙamshi na musamman da kwarjinin da ALLAH ke sama duk wasu ma'aurata a
ranar aurensu. Anam dai bata san da zamansa ba sai lokacin da za'ai hoto, bata yarda kuma ta kallesa ba
fuskarta na rufe da hular alƙyabba, sai dai kamshinsa ya cika mata hanci matuƙa. Koda aunty Amarya ta bu
ɗ
e mata fuska ma ƙin kallon sashen da yake tai har aka gama zuba hotuna datai matuƙar gajiya taro ya tashi lafiya gab da magrib. Baƙi sun fara bajewa,
yayinda akaima Amarya Anam sabon shirin miƙata gidan angonta.
Gaba
ɗ
aya iyayenta zagayeta sukai harda Gwaggo a falo, sabuwar nasiha akai mata mai ratsa jiki, tuni kuka ma ya kama gabansa a idonta, dan zuciyar tata ta bushe ta kasa hawaye sam. Sai d
ai tana saurarensu daki-daki. Mommy dai babu wanda zaice yaga idonta yau a gidan, amma duk da haka an fita hakkinta an kai mata amarya Anam har sashenta domin yin bankwana da ita a matsayinta na uwa. Sai dai kuma suna shiga ta tashi tai shigewarta ta barsu
da danginta da basu da alamar niyyar barin gidan.
Yanda tai
ɗ
in ya ƙona ran Hajiyar sudan, dan haka batako tsaya tofa wani abuba ta kamo hanun Anam suka fito. Sauran sassan aka zagaya da ita harna Gwaggo data bama kowa mamaki da al'ajab, dan kuwa
takarƙarewa tai tanama amarya nasiha. Babu dai wanda yace komai amma ta ciki na ciki.
Lokacin da akai gurfanar da Amarya Anam gaban Abie da Mamie a matsayin sallama dolene ka tausayama wa
ɗ
an nan iyaye da tilon ƴarsu. Dan kuwa dai duk dauriya da Ma
mie keyi daga ita har Abie
ɗ
in sai gasu suna kuka har bakunansu suka gagara furta komai sai addu'a a gajarce, dole dai aka haƙura aka
ɓ
an
ɓ
areta jikin Abie da ƙyar aka fiddota ƙofar gida inda motocin abokan ango su Fharhan ke jiransu...........
✍
_ZAF
AFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi
hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS
👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA
👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏🏻
_*
[11/4, 12:38 PM] Marsy
😘
: *_Typing
📲
_*
*_
❤
🔥
BABU SO....!!
❤
🔥
_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_BABU SO
👉🏻
AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_39_*
.........Alhmdllhi amarya ta iso gidanta lafiya, ta kuma samu tarba daga wajen dangin mahaifiyar su Daddy da suma sukazo suka taru anan domin nuna gata gasu daddy
ɗ
in, duk da tun zuwan nasu ƙawayen aunty Halima dake gidan zagaye da Fadwa suka
kirata suka sanar mata. Babu ko kara na tuna cewa dangin mahaifiyarta ne ta kirasu tai musu tas a waya da tabbatar musu zata iya da makircin kowa daya nuna goyon bayansa akan aima ƴarta Fadwa kishiya, kishiyarma
ɗ
iyar ƴar uba. Inna Suwaiba! Wadda ta kasanc
e
ɗ
iyar wan maman su daddyn ce ta amshi waya tai mata tas itama dan in masifa ce ta fita iyawa, ai ko babu shiri ta yanke wayar tana zage-zage.
Kowa ya yaba sashen amarya tare da jinjinama ƙoƙarin iyayenta, dan tabbas kam sun nunama duniya ita
ɗ
in
ɗ
aya ce tilo a garesu kuma ƴar gata. Cikin ra
ɗ
a Mom da Hajiyar sudan suka sake yima Anam da keta sauke ajiyar zuciya nasiha. Rungume Mom tayi, muryarta a
ɗ
ashe alamar taci kuka mai yawan gaske tace, “Mom ni bana son sa dan ALLAH, Mom karku barni anan za
n iya mutuwa”. Mom dake rungume da ita tana shafa kanta tai murmushi. “To kiyi haƙuri, zan samu Abbanku nai masa bayani yanda zai fahimceni, yanzu dai ki kwantarmin da hankalinki kinji”.
Da sauri ta fiddo fuskarta dake cikin mayafi tana kallon Mom da
jajayen idanunta da suka kumbura matuƙa saboda kuka. “Mom dan ALLAH da gaske?”. Hajiyar Sudan Da Mom suka ha
ɗ
a ido, murmushi sukayi, kafin Mom ta jinjina mata kanta “Da gaske mana. ba Baba ibrahim ma yace nanda wata uku indai da wata matsala zai
ɗ
auki mat
aki ba”. Sake rungumeta tai tana
jinjina kanta fuskarta na bayyanar da murmushin da tunda aka fara badaƙalar auren nan ba'aga irinsaba a fuskarta. Cikin dabara hajiyar Sudan ta fita a
ɗ
akin, dan dama su ka
ɗ
aine suka rage mutane duk sun fice kowa na tsoron
ya rasa mota. Lallashinta Mom ta ƙarayi, kafin itama ta miƙe cikin dabara da plan
ɗ
in da suka ha
ɗ
a da hajiyar sudan.
Hajiyar Sudan
ɗ
in ce ta leƙo tai kiranta wai tazo taga wani abu, miƙewa Mom
ɗ
in tai tana gyarama Anam zama. “Kinga zauna ina zuwa”.
Ji Anam tai kamar dabara zasu mata, sai dai kafin tai wani yunƙuri Mom
ɗ
in har ta fice a
ɗ
akin, tun tana irga seconds harta koma minutes, ganinfa alamar mintuna kusan goma sun cika babu alamar motsi ma ya sakata miƙewa da sauri hawaye na ciko mata ido. Tab
bas babu kowa a falon, hakama sauran
ɗ
akunan zuwa kitchen, wasu irin zafafan hawaye ne suka silalo mata, ta dafe kujera saboda jiri dake neman
ɗ
ibarta, da ƙyar ta iya maida kanta bedroom
ɗ
in da suka barta, ta zube a kan gadon hawayen na cigaba da sauka a g
uje dan bata da ƙarfin yin kuka mai sauti.....
Gida ya koma tsitt, duk da sashen Fadwa har yanzu akwai wasu ƴan uwan babanta uku na hanun damar Gwaggo halima da su Mommy basu da alamar barin gidan, sun zagaye Fadwa dake kuka suna ƙara mata
fanfo dan ba'ace nasiha ba. A kallo
ɗ
aya zaka tabbatar da taci kuka itama har ta godema ALLAH, dan hatta da muryarta ma ta dishe. Gaba
ɗ
aya ji take Shareff
ɗ
in ma ta gama tsanarsa, ko ganinsa bata sonyi shi da duk wanda ya shafesa. Tsoron mahaifintane kawa
i ya taka mata birki akan ƙudirinta na barin gidan, amma batajin zata iya cigaba da rayuwa da Shareff ƙarƙashin inuwa guda da maƙiyarta, yarinyar datai matuƙar tsana a rayuwarta ace a yau itace kishiyarta, kishiyarta da zata iya shearing da mijinta abin so
nta. Kai ina wannan ma maganar tatsuniyace, za kuma ta tabbatarma duniya cewar tatsuniyar ce...
Duk wannan hidima da akeyi ango Shareff na can gidansu gurfane gaban su Daddy suna sake masa nasiha da jaddada amanar matan nasa a hanunsa domin a yanzu
matsayi guda suke amsawa a wajensa. Kuma su dukansu ƴan uwansa ne na jini da basa fatan zuminci ya samu wani nakasu ko rauni a dalilin aurensu. Basu barsa ya baro gidan ba sai da ƴan rakiyar amarya suka koma. Yay musu sallama ya fito. Babu sashen daya shi
ga, dan shima yasan baida wannan damar a yanzu. Ga kuma kansa na masa matuƙar ciwo ma na hayaniyar da aka sha ga kuma jikinsa da bawai ya gama dawowa dai-dai bane shima dama. Dauriyace kawai da ƙarfin zuciya irin ta maza.
Duk yanda abokansa suka so
masa rakkiya kamar auren Fadwa ƙi yay, dole suka haƙura suka gudu sai Fharhan ne kawai dazai jasa