Showing 114001 words to 117000 words out of 244674 words
wani kayataccen murmushin da ya kara bayyana zalla da kuma tsananin kyawun fuskarsa.
“Always you looking so good bae!
‿
Yafadi hakan cikin matsanancin shaukinta dake matukar addabar zuciarsa.
Idanunsa ya kurawa zan
en fuskartata wanda musamman yasa akayi masa.
“Komae naki me kyaune Laylerh, daga yarintarki har zuwa girmanki, murmushinki, magananki, dariyanki, tafiyanki, komae natsarin halittarki abun burgewane, hakika har yanzu ina bulayi da kuma neman hanyar da zae
sa na iye jure zafin rashinki Laylerh, amma kowacce hanya da nake tunanin bi ta toshe, narasa hanya guda daya, please L.M say something, maybe hakan zaisa zuciyata tayi sanyi, domin haryanzu nakasa gano meyasa, da kuma dalilin da yasa ako da yaushe k’addar
a ke d’awainiya da rayuwata, tabbas nasan cewa ba komae ne idan mutum naso yake samu ba, hakika wannan kaddarace dake sauyawa akowani lokaci!
‿
Dakatawa da maganar tasa yayi tare da lumshe idanunsa.
Cikin matsanancin sanyin zuciyar da ya samu kansa aciki
yace, da wata irin sassanyar murya. “Kaddara ta nesantaki dani, amma har yanzu ina numfashi, tabbas kaddara itace me hadawa kuma me rabawa, ta rabamu akaron farko, Insha Allahu Kuma zata hadamu akaro na biyu, nasani zanrayu dake Laylerh, domin kedin abu bu
yuce awajena, ma' ana bugun zucia da numfashina, tabbas naji ajikina cewar wata sabuwar k'addaran tana nan zuwa, wanda kuma asanadinta zaki rayu dani Insha Allah!!."
Yak’are maganar tasa da wani irin murya dake bayyana asalin abunda ke kwance acikin zuci
yarsa.
Hannayensa ya zura acikin aljihun wandon dake jikinsa, Kallo daya yayiwa zanen hoton nata dake manne ajikin bango, ahankali ya dauke Kansa, tare da matsawa daga jikin hoton, cikin tafiyarsa ta maye kaetsaye ya nufi bathroom dan so yake yadan watsaw
a kansa ruwa ko hakan zaesa yaji sanyi da kuma salama acikin zuciyarsa.
Bud’e k’ofar bathroom din yayi ya shige, anutse ya gama cire kayan jikinsa, tare da karasawa yasakarwa kansa shower, ajiyar zuciya me karfi ya sauke alokacin da yaji saukan ruwan show
er’n ajikinsa, idanunsa ya lumshe yana mejin yanda bugun zuciyarsa ke tafiya ahankali.
Sanin kuma da yayi cewar dare ya raba ne, yasa baiwani tsaya b’ata lokaci acikin toilet d’inba ya kashe shower’n tare da sako bathrobe ya fito, kasancewar kuma tuni bac
ci yacika idanunsa ne yasa ko tsayawa goge jikinsa baiyiba, ya haye saman gado ya kwanta, take kuwa cikin abun da baiwuce 9min ba bacci ya d’aukesa.
B’angaren Abbou Jaheed kuwa bayan wucewan Maleek din cikin gida, akalla ya bata lokaci masu tsawo yana tsa
ye ajikin motar M.Jay din kafun daga bisani ya wuce part dinsa, kasancewar dama karan horn din motar Maleek dinne ya tasheshi daga bacci.
Koda ya koma dakinsa kuwa zugum yayi, acikin rae da zuciyarsa kuwa yake ta sak’a abubuwa kala kala,domin ba kad’anba
halin da yaga Maleek aciki ya d’aga masa hankali.
Saboda yasan hakan alamace dake nuna cewar yana sakaci da rayuwar D’ansa, wanda kuma ya tabbata yau da’ace Mahaefiyar Maleek na raye, sae hakan yafi kona rae da zuciyarta fiye da nasa.
Ajiyar zucia me k’
arfi ya sauk’e sakamakon tunawa da yanda yakaranci abubuwan dake cikin zuciyar Maleek d’in kwance acikin idanunsa, hakika yazame masa dole ya aiwatar da abunda ya kudurta acikin ransa, saboda yasan hakan shi kadaine mafita.
Da wannan tunanin nakawo k’ars
hen matsalan Maleek d’in ya kwanta, Wanda aransa yabarsa amatsayin dole bawae ra’ayi ko tunani ba.
*Washegari*
8:00 am dai-dai alarm d’in dake cikin d’akin ya buga, hakan kuma yayi daidai da fitowar Najeeb daga cikin bathroom, Wanda ke sanye da rigar w
anka ajikinsa, yanayin kuma yanda gaba daya jikinsa ke d’auke da danshin ruwa ne, ke nuna cewar fitowarsa daga wanka kenan.
D’an k’aramin towel d’in dake rik’e ahannunsa ya’ajiye tare da juyowa ya kalli kan gadon.
Har yanzu bacci take, saidai kuma yanayi
n kwanciyar da tayine yasa gaba daya kusan rabin rigar baccin dake jikinta ta d’age sama.
Ajiyar zuciya ya sauk’e tare da k’arasowa jikin gadon, alarm d’in dake saman bedside carbonated wanda gaba daya k’aransa ya cika d’akin ya kashe, ahankali ya d’an ra
nk’wafo da kansa tare da tsurawa kyakkyawar fuskar Laylerh’n idanu, domin yanayin yanda zarazaran eyelashes d’inta suka kwanta ak’asan idanunta ba k’aramin kyau suka k’ara mata ba, sannu ahankali ya shiga yawo da idanunsa akan fuskarta har zuwa kan breast
d’inta da suka d’an bayyana saboda yanayin kwanciyar da tayi.
“Sleeping beauty!
‿
Ya fad’a abayyane adaedae lokacin daya sauk’e idanunsa akan Fararen shining skinny legs d’inta, wanda kwad’ayi da kuma son jin taushinsu yasashi d’aura hannunsa akansu, ahank
ali yad’an matsar da k’afafun nata gefe, wanda hakan ya bashi daman zama akusa da’ita.
Anutse yasa hannunsa ya shafi gefen wuyanta, jin da yayi jikinnata babu zafi ne yasashi sauk’e ajiyar zuciya.
“Laylerh!
‿
Yak’ira sunanta cikin sassanyar murya, duk da
kuwa yasan cewar baccin nata yayi nauyi sosae, tun d’azu yaso tashinta saidai kuma ganin da yayi cewar akwae gajiya atattare da ita ne yasashi k’yaleta, yanzu kuwa idan yabarta baisan sai yaushe ne zata tashi ba, gashi ko sallan asuba batayi ba, kuma k’arf
e takwas hartayi.
“Laylerh!!
‿
Yasake k’iran sunanta akaro na biyu.
Still kuwa ko motsi batayi ba, bare yasa ran farkawanta.
Ahankali ya d’an matso kusa da’ita cikin yanayin sanyi yashiga busa mata iskan bakinsa akan fuskarta.
Acikin baccin nata kuwa ta
kejin sauk’an iska akan fuskarta, hakan yasa tad’an soma motsa jikinta, ahankali ta bud’e idanunta da suka d’an k’ank’ance, ras kuwa idanunnata suka sauk’a akan fuskarsa, ganin fuskar Najeeb d’in da kuma yanda ya sunkuyo kanta ne yasa cikin sauri tatashi z
aune, tare da soma d’an mummurza idanunta.
“Sleeping beauty dama haka kikene ke bakya k’oshi da bacci?
‿
Najeeb da haryanzu bai dauke idanunsa akanta ba ya fad’a.
D’an k’aramin bakinta ta turo masa gaba, ashagwab’e tace. “Ni ae baccin bai isheni ba.
‿
“Uhumm.
‿
Ya fad’a yana me sake matsowa kusa da’ita.
Ganin hakanne kuma yasa ta d’ago da sauri ta kalleshi, ganin yanda idanunsa ke tsaye akan k’irjinta ne, yasa itama tayi saurin kallon k’irjinnata da rabin breast d’inta suka bayyana har yakai ga, ana iya
hango y’an jajayen nipples d’inta, da sauri tasa hannayenta ta b’oye k’irjinnata, cikin hanzari kuma ta diro daga saman gadon, ganin hakane kuma yasa cikin sauri Najeeb yayi yunk’urin rik’o hannunta, saidai kuma batare da ta bari yasamu daman hakan ba ta
gudu toilet.
Idanunsa da suka sanja kala lokaci d’aya ya lumshe tare da sauk’e wani irin ajiyar zuciya, abayyane cikin yin k’asa da murya yace. “I swear nanda someday wannan yarinyar zata kasheni,because feeling d’inta kad’aima barazana yake ga numfashina
, Yah Allah Help me!
‿
Ya k’are maganar yana me dafe saman mararsa dake d’anyi masa zafi,saboda har yanzu jarababben feelings dinnasa bai sauk’aba, mik’ewa tsaye yayi tare da k’arasawa wajen drawer dan Zab’an kayan da zai saka.
Laylerh kuwa koda ta shig
a cikin toilet d’in da sauri ta maida k’ofar ta rufe, tare da sauk’e ajiyar zuciya, anutse ta zare rigar dake jikinta, k’arasawa jikin bathtub tayi, tare da had’awa kanta ruwan wanka me d’an d’umi, shigarta kuwa cikin bathtub dinne yasata lumshe idanu, mus
amman da taji d’umin ruwan na ratsata, anutse kuwa tayi wankanta, koda ta gama wankan d’aya daga cikin bathrobe d’in dake cikin toilet d’in tasaka tare da d’auro alwala, k’arasawa jikin k’ofar bathroom d’in tayi ta tsaya, hakanan takejin kunyan fita ahakan
, duk da cewar ma rigar wankan ya sauk’o har kan guiwowinta, sanin kuma da tayi cewa bata da yanda zatayi ne yasa dole ta bud’e k’ofar bathroom d’in tafito.
Saidai kuma rashin ganin Najeeb d’in da tayi acikin d’akin yasata sauk’e wani ajiyar zuciya, da sa
uri ta k’arasa gaban mirror, k’aramin towel ta d’auka ta goge jikinta dashi, cikin hanzari kuwa batare da ta tsaya shafa Mai ba, ta nufi wajen drawer.
Bud’e drawer‘n tayi cikin yanayin sauri batare da ta tsaya dubawa ba kuwa ta zaro wata doguwar rigar spe
ctrum mai kalan lightpink, tare da wani lightpink bra, and skintight, cikin sauri sauri tasaka kayan domin bataso Najeeb ya shigo d’akin yasamu tana saka kaya.
Sosae kuwa rigar me hawa hawa ta zauna ajikinta tare dayiwa fatarta kyau, wani hijab ta saka ta
re da shumfud’a sallaya ta tada sallah duk dama ta makara sosae.
Koda ta idar da sallan kuwa bata tashi akan sallayan ba, Azkhar ta soma karantawa, tana gama karatun azkhar dinnata kuwa Najeeb na shigowa cikin d’akin.
Sanye yake da shigan jumper da wando
n na wata tsadaddiyar shadda skyblue colour, sosae kuwa shigar tayi masa kyau, musamman yanda ya kafa hula me kalan sky akansa, K’amshin turarensa daya cika mata hancine yasata d’anyi k’asa da kanta.
Ahankali cikin takun nutsuwa ya k’araso inda take, ta
re dasa hannayensa ya d’agota tsaye, sakeyin k’asa da idanunta tayi, dan hakanan tasamu kanta dak’in son kallonsa.
Shikuwa Najeeb gane hakan da yayine yasashi d’ago hab’arta cikin kulawa yace. “G/M madam, hope kintashi lapia.
‿
Wani irin nauyinsa da taji
ne yasata jinjina masa kae alaman “Lapia.
‿
Cire hannunsa akan kafad’unta yayi, fuskarsa d’auke da murmushi yace. “Kishirya Abbou Jaheed yak’iramu yin breakfast.
‿
Again kai ta jinjina masa alaman “To.
‿
“Inajiranki a falo.
‿
Ya fad’a yana me sakinta tare
da juyawa yafita daga cikin d’akin.
Itakuwa Laylerh hakanan taji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, saboda tasan koba komae zataga Yah M.Jay d’inta, da d’an sauri ta k’arasa gaban mirror, body lotion me k’amshi ta shafa ajikinta tare da murza powder aka
n fuskarta, sama sama tashafa lipstick akan lips d’inta, dama ita bagwanar kwalliya bace shiyasa bayan kwalli da mascara ba abun da tasake sawa akan fuskarta, sai turare me dad’in k’amshi da tafesa.
Bud’e drawer tayi ta zaro wani baby vail pink ta yane ka
e zuwa wuyanta dashi, sosae kuwa hakan ya k’arawa shigar nata kyau, wani pink flat shoe tasaka ak’afanta, saboda yanda ta matsu taga Mr.Soldier ne yasa takasa koda duba kanta amadubi, anutse ta murd’a handle d’in k’ofar ta fice.
Najeeb kuwa dake zaune afa
lon k’amshin turarenta da yajine yasashi d’ago kansa ya kae dubansa ga k’ofar bedroom d’in, ganin kuma irin kyaun da Laylerh’n tayi ne yasashi lumshe idanunsa,tare da bud’esu alokaci guda.
“Masha Allah!
‿
Ya fad’a yana me k’are mata kallo from head to toe
, saboda sosae yaga tayi masa kyau.
Harta k’araso kusa dashi kuwa bai d’auke idanunsa daga gareta ba.
Laylerh kuwa ganin irin kallon da yake matane yasa ta sunkuyar da kanta k’asa, had’e da kama y’an yatsun hannunta tashiga murzawa.
Najeeb kuwa badon ya
k’oshi da kallonta ba, haka dolensa ya mik’e tsaye, cikin muryarsa da ta koma chan k’asan mak’oshi yace. “Muje, amma kinyi kyau sosai.
‿
Sarai taji abunda yace, amma tayi muk’us kaman batajisa ba.
Haka suka fito daga cikin falon yana gaba tana biye dashi
abaya.
Koda suka fito compound d’in gidan, kaitsaye part d’in su Abbou Jaheed suka nufa.
Saura kuma baefi taku kad’an su k’arasa part d’inba wayar Najeeb ta soma k’ara alaman shigowan k’ira.
Screen d’in wayartasa ya duba, ganin da yayi k’iran me amfani
ne yasashi juyowa ya kalli Laylerh’n dake bayyana.
“Ummina ne kiyi gaba inazuwa.
‿
Baijira me zatace ba ya d’auki wayar tare da matsawa can gefe.
Laylerh kuwa bata damu ba kaetsaye ta murd’a handle d’in k’ofar babban falon ta shiga bakinta dauke da sall
ama.
Jin sallaman Laylerhn ne yasa Momy dake zaune a dining area ta d’ago kae ta kalleta.
Laylerh kuwa ganin Momy zaune a dining d’inne yasata k’arasowa wajen, cikin girmamawa tace. “Momy good morning.
‿
“Morning, yanaganki ke d’aya, Ina Najeeb d’in?
‿
Momy ta tambaya tana me lek’a bayan Laylerh’n.
“Yana amsa waya awaje.
‿
Tabawa Momyn amsa asanyaye.
Wani irin murmushi me d’auke da ma’anoni daban daban ne ya bayyana akan fuskar Momy.
“Dama ta farko.
‿
Ta fad’a acikin zuciyarta, abayyane kuwa kallon L
aylerh’n tayi cikin salon isar da manufarta tace. “Dama ke nake jira tun d’azu amshi wannan ki kaiwa Captain.
‿
Wani d’an madaidaicin flask Momyn ta miko mata.
Jin an anbaci captain ne kuma yasa zuciyar Laylerh sakeyin sanyi, anutse ta karb’i flask d’in ba
tare da tunanin komae ba kuwa ta nufi dakin Maleek d’in.
Da kallo Momy ta bita, tare da sakin wani killer smile, cikin zuciyarta tace. “Da irin wannan salon duk zan wargaza tunaninku.
‿
Shigewar Laylerh sashin Maleek d’in kuwa yayi daidai da shigowar Naj
eeb cikin falon.
Ganinsa yasa Momy sakin murmushi dan tasan tarkonta ya Kama.
Ganin Momyn ne yasa Najeeb K’arasowa dining area d’in, cikin yanayin girmamawa ya gaisheta fuska asake kuwa ta amsa masa.
D’aya daga cikin Kujerun dake dining table d’in yaja
ya zauna, rashin ganin Laylerh’n kuma da yayi ne, yasashi d’an soma kalle kallen inda zae hangota.
Gane hakan da Momy tayine yasata sakin murmushi cikin kulawa tace. “Amaryarka kake nema ko?.
‿
Jin abunda Momyn tace ne yasashi d’an sunkuyar da kansa k
’asa alaman kunya.
Again murmushin mugunta d’auke akan fuskar Momy tace “Karka damu tanashigowa ta wuce sashin Maleek, da’alama kwana tayi tana mafarkinsa, amma nasan yanzu zata dawo.
‿
Jin abunda Momyn ta fad’a ne yasashi saurin d’ago kansa ya kalleta.
*(
🙏🏻
Nagode matuka da add’u’oinku Allah Yasaka da alkhairi, insha Allah yanzu nadawo zan daura daga inda na tsaya, kuyi hakuri kuma yanzu yanayin typing din ya sanja saboda nadaena amfani da touchpal)*
*13/Jan/2021*
1/19/21, 8:29 PM - Ummi Tandama:
*LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*(Wayyoni
😔
saida nayi typing ya goge, I am so sad wallahi
😭
jinake kamar ma naciji kaina
🥺
)*
*Chapter 37*
Gaba d’aya jin kalaman Momyn yayi wani iri, saboda kwatakwata bai tsammaci jin hakan ba.
“M
eye Laylerh tajeyi wajen Maleek?.
‿
Tambayar da yayiwa kansa kenan wacce kuma bashi da amsarta, idanunsa yadan lumshe tare da jingina bayansa da jikin kujeran da yake kai.
Momy dake kallonsa kuwa ganin irin yanayin da yashiga ne yasata sakin Murmushi, cik
in son nuna abun da ta had’ad’in ba wani babba bane tace.
“Baikamata ka damu akan wannan ba, I think ma kashiryawa irin hakan:
‿
Jin abun da Momyn ta fad’ane yasashi k’ak’alo murmushi ya daura akan fuskarsa, saboda sam bayaso Momyn tafahimci cewa yaji ba
bu dad’i a zuciyarsa.
Kansa ya sunkuyar k'asa tare da d'an lumshe idanunsa.
Ahankali ta d’aura hannunta akan handle d’in k’ofar d’akin tare da murd’a handle d’in ahankali ta tura k’ofar ciki, sassanyan k’amshin turaren daya ratsa hancinta ne yasa ta d’
an lumshe idanunta tare da sauk’e wata siririyar ajiyar zuciya, ahankali ta shiga k’arewa komai na had’add’en falon nasa kallo, kamar kullum kuma kamar koda yaushe komai nasa need yake, dan kuwa ko kad’an baya jurewa k’azanta.
Wani irin k’awataccen murmus
hi ne ya bayyana akan fuskarta alokacin da ta sauk’e idanunta akan d’an madaidaicin hotonsa dake cikin falon, duk dama yanayin yanda aka d’aukesa ya d’an juya baya, hakan baisa hotonnasa k’inyin kyau ba, yayinda faffad’an surar bayansa ta bayyana kasancewa
r yana sanye ne da shirt na uniform d’in soldier irin mai kama jikinnan.
“My beautiful bro
‿
ta fad’a a daidai lokacin da take k’arasowa tsakiyar falon, tare kuma da d’auke idanunta dake kan hoton ta maidashi ga k’ofar bedroom d’insa wanda ke d’an bud’e da
dukkan alama ba’arufe k’ofar da kyau bane.
Ahankali tasoma takawa har zuwa bakin k’ofar tasa sannan ta tsaya, tana me sauraran yanda heart d’inta ke beating, kafun yanzu k’warai idanunta cike suke da so had’i da kwad’ayin ganinsa, ayanzu kuwa da yarage t
sakaninsu baifi wasu y’an taku ba, saitaji k’irjinta na bugawa da sauri, bata kuma san dalilin hakan ba.
Hannunta d’aya dayake empty tasa ta d’an tura k’ofar d’akin nasa kad’an, ba tare kuma da tasaka kanta acikin d’akinba da siririyar muryarta tayi masa
sallama, tare da d’an matsawa gefe saboda tana tunanin zai amsa mata.
Saidai kuma jin shiru ba’a amsa sallaman nata bane yasa take tayi tunanin cewar watak’ila yana wanka shiyasa baijita ba, ahankali ta sake tura k’ofar d’akin tare da d’ansa kanta ta lek’
o kad’an, take kuwa idanunta suka sauk’a akansa.
Ganinsa kwance ak’asa ne yasata saurin bud’e k’ofar d’akin da kyau ta shigo gaba d’aya.
Kwance yake akan wata k’atuwar darduma, yayinda yayi matashin kai da hannunsa na dama, yanayin yanda yayi kwanciyarta
sa ta hanyar takure jikinsa waje d’ayane yasa kallo d’aya zakayi masa kafahimci cewa baishiryawa baccin da yakeyi d’inba, dan da’alama daga idar da sallan asubane baccin ya d’aukesa.
Wani irin matsanancin tausayinsa ne ya dira azuciyarta,take kuwa taji id
anunta sun ciko da hawaye, akan kyakkyawar fuskarta kuwa wani d’an murmushi ne ya bayyana, wanda kuma azahirance yake fitar da asalin abundake cikin zuciyarta.
Maida k’ofar d’akin tayi ta rufe, ahankali tashiga takowa harzuwa inda yake kwance.
Flask d’in
dake hannunta ta ajiye tare da d’an rank’wafowa anutse ta zube guiwowinta k’asa daidai inda yake kwance, idanunta da suke d’auke da danshin hawaye ta sauk’e akansa, tare da tsaida ganinta akan kyakkyawar fuskarsa, dake yalwace da had’adden sajen dake k’ar
a masa kyau akoda yaushe.
Y’an saffa saffan labb’ansa masu yanayi da nata had’e da zara zaran eyelashes d’insa ta kalla, murmushi ne ya sub’uce mata saboda yanda taga ya k’arayi mata kyau, da kwarjini.
Idanunta ta d’an lumshe tare da shak’an wani irin sa
ssanyan numfashi, wanda ya taho da daddad’an k’amshinsa me nutsar da zuciya.
Ahankali taji wani irin feeling d’insa na ratsa duk ilahirin jikinta, wanda hakan yasa tasamu kanta acikin matsanancin shauk’insa, ware idanunta dake alumshe tayi tare da zuba ma
sa narkakkun idanunta akaro na biyu bata ko k’yaftawa, hak’ik’a wani irin abu takeji na musamman adangane dashi, ahankali ta zauna dab’as akan k’afafunta tare da sa tafin hannunta adaidai saitin hancinsa, huci da kuma d’umin numfashinsa