Showing 174001 words to 177000 words out of 244674 words
da Munniran bane, taji
zuciyarta tayi mata babu dad’i domin hakan alamace dake nuna ko anan gaba Maleek zai fuskanci k’alubale sosae kafun ya samu wacce zata aureshi, kuma kamar yanda Abbou Jaheed d’in ya fad’ane ba lallaine duk wata macen da zata auresa ya zama da zuciya d’aya
zata zauna dashi ba.
“Kayi hak’uri Maleek akan duk wata k’addarar da ta sameka arayuwa, Insha Allah Watarana komae zae wuce kamar bai faru ba!
‿
Abbou Khareem ya fad’i hakan asanyaye tare dasa hannunsa ya kamo hannun Maleek d’in wanda har yanzu bai f
urta komae ba.
Shirun da Maleek d’in yayine kuma yasa gaba d’aya dining area d’in ma ya d’auki shiru, babu wani mai motsi acikinsu, saboda ba kad’an ba maganan fasuwar auren Maleek d’in ya wujijjiga tunaninsu, kasancewar abune da sam basu tsammacesa ba.
Ahankali ta lumshe Idanunta wanda suka cika tab da k’walla, akaro na biyu kenan da ta sakejin wata mummunar magana akansa ta doshi kunnuwanta, still kuma akaro na biyu kenan da taji zuciyarta ta tsananta rauni akansa, yayinda kuma wani irin matsanancin
tausayinsa ya lullub’e duk ilahirin jikinta, har hakan yayi sanadiyar zubowan wasu siraran hawaye daga cikin lumsassun idanunta.
Sosae hawayen nate ke d’auke da yanayin damuwa, wanda da ace wani daga cikinsu zai kali fuskarta ayanzun to fa lallai daya fus
kanci hali da kuma irin ciwon da takeji acikin zuciyarta, wanda kuma ahak’ik’anin gaskiya Bawae tana kukane saboda fasa aurensa da Munniran da akayi ba, no tana kukane saboda matsanancin tausayinsa da takeji, da kuma irin k’alubalen da ta fahimci cewa yana
dab da fuskanta arayuwa.
Lallai tasan dolene zaiji babu dad’i, ga kuma alama abayyane domin har yanzu baice komae ba.
Ahankali ya zame hannunsa dake cikin na Abbou Kareem, kujerar da yake kai yad’anja baya tare da mik’ewa tsaye, still ko k’ala baic
ewa kowannensu ba ya juya cikin takunsa dake amsa amo ya nufi hanyar barin falon ma baki d’aya.
Ganin hakanne kuwa yasa duk suka zuba masa idanu, ciki kuwa harda Laylerh wanda tabi bayansa da idanu, yayinda acikin zuciyarta takejin kaman taje da gudu ta
fad’a jikinsa, ko hakan zaisa zuciyoyinsu dake matuk’ar azabtuwa kowanni seconds da minutes su samu rangwame da salama.
Ganin ya fice daga cikin falonne kuma yasa ahankali duk suka janye kansu daga kallonsa, zuciyar kowannensu cike da tunani da kuma abu
buwan da suke sak’awa acikinta kala kala.
Abbou Jaheed da gaba d’aya jikinsa yake asanyaye mik’ewa tsaye yayi shima, kai tsaye ya nufi sama wanda ananne kuma asalin bedroom d’insa yake.
Ganin Abbou Jaheed yayi tafiyarsane kuma yasa Oum Ayush da Abbou Kh
areem ma mik’ewa zuciyoyinsu duk babu dad’i haka suka fice daga falon.
Hakan yasa dining table d’in ya rage daga Najeeb sai kuma Laylerh’n wanda ta kasa iya controlling nutsuwarta.
Sanadiyar hakanne kuma yasa duk hankalin Najeeb ya dawo kanta, ganin ta
sunkuyar da kanta ne kuma yasasahi sa hannunsa ahankali ya d’ago hab’arta, bisa dole ya zama sun fuskanci juna.
Kyakkyawar fuskarta ya zubawa idanu, tare kuma da tsaida ganinsa akan zararan eye lashes d’inta wanda suke d’auke da danshin hawaye.
“Kuka
?.
‿
Ya fad’a cikin yin k’asa da murya.
Ahankali ta d’an girgiza kanta, Alaman “A’a.
‿
Murmushin daya bayyana kyawun fuskarsa yayi, duk da cewa kuwa yasan silar yin kukan nata, amma saiya share, cikin yanayin bada umarni yace.
“Ya isa haka kici abinci
!
‿
“Nak’oshi.
‿
Ta fad’i hakan asanyaye batare kuma da ta jira wani abu da zaice ba ta mik’e tsaye, cikin yanayin rashin kuzarin da takejin kanta aciki ta nufi hanyar barin falon, yayinda shikuwa yarakata da idanunsa harta fice.
Sauk’ak’akk’iyar ajiyar
zuciya yayi, kana shima ahankali ya mik’e tsaye tare dabin bayanta.
Laylerh kuwa koda ta fito daga cikin babban falon gidan, kaitsaye sashinsu ta wuce, bata kuma tsaya a falo ba direct bedroom d’insu ta wuce.
Yanayin yanda takejin rauni sosai azuciy
arta ne kuma yasa tana shiga cikin bedroom d’in, asanyaye ta k’arasa wajen wani had’add’en sofa dake cikin d’akin ta zauna.
Tafukan Hannayenta duka biyu tasa ta rufe fuskarta, tare kuma da sauk’e wani irin k’akk’arfar ajiyar zuciya, kwata kwata duniyar ba
tayi mata dad’i, k’unci da damuwa kawai takeji acikin zuciyarta wanda ita kanta batasan sai yaushene zata samu sassauci da kuma salama akan abunda takeji acikin zuciyarta ba.
Hawayen da suka gangaro kan fuskarta ta share tare da d’an cije labb’anta kana a
bayyane cikin kuma muryar dake bayyana damuwarta k’arara tace.
“Bansan sai yaushe ne zamu samu farinciki ba, a kullum damuwa da ciwo suke tasiri acikin rayuwarmu, kana kuma su sukecin k’arfinmu, bayan wannan k’addarar sai kuma wannan jarrabawar, kullum
dae abu d’ayane babu canji, shin tayaya zuciyoyinmu masu rauni zasu jure irin way’annan abubuwan? Tayaya zamu iya fuskantar k’alubalen da zasu zo rayuwarmu anan gaba? Mezai faru? Meyakeji? Wani irin ciwo yakeji duk babu wanda zai fahimta, shi ne kawae shik
ad’aine yasan meyakeji azuciyarsa, nayi imani cewa zafi da ciwo bazasu tab’a barinsa ya huta ba!!
‿
Ta k’arishe maganan alokacin da take zamowa daga kan sofan ta zubar da guiwowinta ak’asa.
“Tabbas zai huta Laylerh, sannan kuma zafi da ciwo zasu ba
r cikin rayuwarsa bari kuma nahar abada!!.
‿
Muryar Najeeb ta karad’e gaba d’aya d’akin wanda hakan yasa da sauri ta dawo da kallonta ga Inda taji amo da kuma sautin muryartasa.
Ganinsa tsaye abayanta ne kuma yasa tayi saurin sunkuyar da kanta k’asa.
Shikuwa Najeeb asanyaye ya k’arasa shigowa cikin d’akin tare da zama akan sofan dake kusa da ita.
Hannayensa duka biyu yasanya ya rufe fuskarsa kamar yanda tayi d’azun, cikin wata irin murya da ko kad’an batasan cewar yana da ita ba, ya jefo mata t
ambaya tahanyar cewa.
“Me kikeji azuciyarki dangane da Maleek? Meyasa akoda yaushe kike kuka akansa? Meyasa duk wani ciwo nasa kikejinsa har acikin jiki da zuciyarki?.... kada kimin k’arya Laylerh domin ayau bana buk’atar k’arya saboda gaskiyar abunda k
e zuciyarki na bayyane acikin idanunki, meyasa Laylerh meyasa???
‿
Ya k’are maganar tasa cikin wata irin raunanniyar muryar da tasa bisa dole Laylerh ta d’ago idanunta ta kalleshi.
Lallai ne kuma Tabbas koda ace bai yi mata wannan tambayar ba dole
ne yau ta fad’a masa yanda takejin fargaba, tsoro, da kuma tsananin tausayawa akan d’an uwannata.
Zafafan hawayen da suka gangaro daga cikin idanunta ta sharce kana asanyaye cikin wata murya mai d’auke da matsanancin damuwa tace.
“Tausayinsa nakeji
Yah Najeeb, tausayin yah Maleek nakeyi, baisan farinciki ba, haka kuma baisan jin dad’i ba, gaba d’aya mummunar k’addara ta kewaye rayuwarmu, ko yaushe k’unci da kuma muradine marar cika, nasan cewa bayajin dad’i , kuma nasan da cewar akoda yaushe yanajin
k’unci acikin rayuwarsa!.
‿
D’an tsagaitawa da maganan nata tayi tare da matsowa kusa da Najeeb d’in, d’aya daga cikin hannayensa ta kamo ta d’aura akan k’irjinta daidai saitin zuciyarta.
Cikin wata irin raunanniyar murya tace.
“Yah Najeeb please koda
sau d’ayane ka tab’a zuciyata, na tabbata zakaji yanda take harbawa akan kowani damuwar sa, duk wani ciwonsa azuciyata nakejin zafin, domin shine mutum na farko aduniya da tun Ina k’arama ya fara shayar dani da yawun bakinsa, kana kuma shine mutum na fark
o aduniya da idanuna ke yawan yimin gizo dashi, komai zai samesa sai naji hakan ajikina, ko kuma nagani amafarkina, banason wani abu ya sameshi, banason koda d’igon abu na cutarwa ne ya sauk’a akansa,
Domin saboda shine kawae nake rayuwa, Tabbas inajin
ciwo sosai acikin zuciyata, amma kuma nasan nasa ciwon da yakeji ya zarce nawa zafi da rad’ad’i, ance bazae tab’a haihuwa ba, yanzu kuma ance ba za’a bashi aure ba saboda yana da lalura, nasani kwarai nasan cewar wannan masomin k’alubalen da zai ci gaba
da fuskanta ne agaba d’aya rayuwarsa, Saboda wannan kawai bazai samu farinciki ba? bazai samu mai kulawa dashi koda sau d’ayane ba? shin menene laifinsa aciki dan k’addarar rashin haihuwa ta fad’a masa? kenan wannan shike nuna saboda hakan Yarasa duk wat
a dama nasa kenan? Bazai samu mai kulawa dashi da bashi abinci ba, bazai samu me nuna masa soyayya ba, kullum zai zauna acikin damuwar da baya iya fad’anta ga kowa, haka zaiyita jin ciwo azuciyarsa, sh
ikenan shi bazaiyi farinciki ba, ko yaushe zuciyarsa
k’uncine!!
‿
Idanunta ta rumtse da k’arfi, wanda kuma hakan ke bayyana abunda takeji acikin zuciyarta mai tsananin ciwo ne,
Asanyaye da kuma muryarta me rauni sosai tace.
“Please Yah Najeeb ko da sau d’aya ne ka saurari bugun da zuciyata keyi, domin a
cikintane kawae zaka fahimci abunda Yah Maleek yakeji acikin tasa zuciyar, wanda baki bazai tab’a iya furtawa ba, wanda kuma yake kassara masa duk wani burinsa na kowacce rana, tabbas yau naji dama ina da iko, to da na d’aukewa Yah M.Jay gaba d’aya duk wat
a mummunar damuwarsa, tayanda shima zaiyi farinciki kaman kowa, domin ko kad’an banason gani kojin ciwonsa, saboda nayi imani ni mai matsanancin raunine akansa!!!!
Ta k’are maganar nata tana me girgiza kanta tare kuma da kama hannayen Najeeb din duka biy
u ta had’e su waje d’aya, lokaci d’aya kuma ta fashe da wani irin fitinannen kuka mai tsananin tab’a zuciyar mai sauraro, kukan dake zayyane duk wani abunda ke cikin zuciyarta, haka kuma kukan dake nuna cewar ta gaza, sannan kuma tazo last hope d’inta.
Manyan idanunsa wanda suka kad’a sukayi jajur ya lumshe tare da kamo hannunta dake kan nasa ya matse gam, wani irin ciwo mai tsanani yakeji acikin zuciyarsa, yayinda kuma gaba d’aya gangar jikinsa ya d’auki rawa, daga gefe guda kuwa gargasan dake kwance a
jikinsane suka mimmik’e, yayinda idanunsa suka cigaba da runewa zuwa kalan ja.
Wani irin tsalle da zuciyartasa keyine kuma yasashi bud’e idanunsa, tare da sauk’e ganinsa akan Laylerh’n wanda take kuka sosae.
Akaron farko na tarihin rayuwarsa kenan da yaj
i wasu irin hawaye masu d’umi sun zubo daga cikin idanunsa, yayinda zuciyarsa kuma tayi wani irin mummunan karyewa, matsanancin tausayin kansa da kuma na Laylerh’n ne ya lullub’esa, wanda har hakan ya sashi kasa iya jurewa.
Saidai kuma gudun kada Laylerh’
n ta d’ago kai taga hawayensa ne yasashi saurin kawar da kansa gefe tare da mik’ewa tsaye, cikin yanayin sauri da kuma son daidaita nutsuwarsa ya fad’a cikin bathroom.
Laylerh kuwa da zuwa yanzu kukan da take ya soma cin k’arfinta, ahankali ta zame jiki
nta ta kwanta akan lallausan carpet d’in dake malale asaman tiles d’in wajen, haka takejin numfashinta na fusga kaman zai bar gangar jikinta.
Najeeb kuwa yana shiga cikin toilet d’in sassanyan ruwan dake kwance acikin had’add’en jakuzzie ya d’ebo ya wat
sa akan fuskarsa, yayi hakanne kuma wae ko zaiji sanyi da salama na daga wutar dake cin zuciyarsa, saidai kuma sam hakan baisa yaji wani sanyi acikin zuciyarsa ba.
Ahankali ya jingina bayansa da jikin bango tare kuma da sake rumtse idanunsa.
Abayyane ka
na cikin wata irin murya mai dauke da rauni sosae yace.
“Tabbas zan aikata hakan koda zan kasance acikin k’unci, saboda ayanzu dolene na samawa zuciyoyin da aka ginasu akan muradi d’aya haske da kuma farinciki, ko da ace badon komae ba, idanuwana sungan
emin abunda ya zama tilas d’ina!!!
‿
D’agowa daga jinginen da yake yayi tare da daukan towel ya goge fuskarsa.
Cikin k’arfin hali da kuma bugun zuciyar daya samu kansa aciki ya murd’a handle d’in kof’ar bathroom d’in ya fito.
Idanunsa ya sauk’e ak
an Laylerh da keta sakin sheshshek’an kuka, ga kuma wani wahalallen bacci daya d’auketa, wanda da’alama bata shiryawa yinsa ba sam.
Wani irin matsanancin tausayintane yaji ya k’ara narkar da zuciyarsa, tare kuma da wani sabon shauk’in sonta,
Saidai k
uma amma ayau sam bashi da zab’i domin yayi imani cewa har abada ba kowani so bane yake iya zama tsuntsu.
Asanyaye ya k’arasa gaban d’aya daga cikin bedside drawer’n dake gefen gadon su, duk da yanda kirji da kuma zuciyarsa ke tsananin bugawa amma hakan
bai hanashi daurewa ba, ahankali ya jawo murfin drawer’n tare kuma dasa hannunsa aciki ya d’auko wani littafi wanda samansa ke d’auke da biro.
Idanu ya tsurawa littafin dake hannun nasa kusan na mintuna 10 kafun ya dawo da kallonsa ga Laylerh wacce ke kw
ance ak’asa tana bacci.
Wani irin kallo yake mata wanda ke bayyana sabuwar soyayyarta dake ratsa kowani kofa na jikinsa, Tabbas yanayiwa Laylerh so mai tsanani, irin wanda a kullum yake fatan yin rayuwa da ita.
Yaya zaiyi? Tayaya zai bari saboda shi kawa
e komai ya lalace? Tabbas abunda yake shirin aikatawa yanzu cutarwane amma bashi da wani zab’i wanda ya wuce hakan.
Asanyeye ya janye kansa daga kallonta.
Wani irin rumtsewa yayiwa idanunsa adaidai lokacin daya d’aura hannunsa dake rik’e da abun rubuta
akan farar takardan dake gabansa, ahankali ya shiga sarrafa hannunsa dake rawa wajen rubuta abundake zuciyarsa akan takardan.
Adaidai lokacin daya kammala rubutun nasane kuma wasu irin hawaye masu tsananin zafi suka fito daga cikin idanunsa tare da d’ig
a akan takardan.
*(Wayyo Allah Na Najeeb
😭😭
kome ya aikata haka oho gaskiya I’m so sad
😞
son Najeeb yasa bazan iya karasa page d’innan yau ba. 1/3/2021 Najeeb first March abunda zaka mana kenan
😭😭
)*
*8:23 pm*
3/3/21, 9:07 PM - Ummi Tandama: *L
AYLERH MALEEK*
*Written By*
fatymasardauna
#hearttouching
*Chapter 61*
Rubutun da yayi akan farar takardar ya tsurawa idanunsa wanda suka kad’a sukayi wani irin ja tamkar wanda aka watsawa garin barkono acikinsu, yayinda yakejin wani irin z
afi da kuma k’una acikin zuciyarsa, lallai Tabbas yasan yayi abunda zae damesa, saidai kuma bashi da wani zab’in daya wuce hakan, k’warai yasani daga yanzun har zuwa wasu lokuta masu tsawo zai cigaba da ruskar kansa acikin bak’inciki, hak’ik’a zuciya da ku
ma gangar jikinsa suna matuk’ar son Laylerh so kuma ba nawasa ba, saidai akwae wani abu daya tabbatar da cewa rashin kammaluwansa babban matsalane sannan zai iya haifar da kowani irin matsala.
Janye idanunsa daga kan takardar yayi tare dasa hannunsa ya n
annad’e ta, cikin wani irin rashin kuzari da kuma alhinin dake cike azuciyarsa, ahankali ya zame tare da zama abakin had’add’en gadon su, idanunsa wanda sukayi matuk’ar ja ya d’aura akan Laylerh’n wanda har yanzu ke kwance ak’asa, duk da cewar kuma bacci t
ake, amma time to time take sakin sheshshek’an kuka, wani irin kallo mai d’auke da tsananin shauk’i ya shiga yi mata, yayinda yakejin matsanancin tausayinta na ratsa duk kowani gaba da sashi na jikinsa, zuciyarsa tayi matuk’ar karyewa, kana rauninsa ya bay
yana afili, shikansa baisan cewa son da yake yiwa Laylerh’n ya girma azuciyarsa har haka ba, ya sani kuma k’warai cewa yayi babban asara, domin abune dayake abayyane cewar bazae tab’a samun mace kamarta ba, koda ma ace zai samu to da matuk’ar wahala, ba ku
ma sak irinta ba saidai maiyanayinta, saboda yayi imani cewa Laylerh’n ta dabance acikin sauran mata, komae nata mai kyau da tsari ne, k’warai yasan cewa zaiyi missing abubuwa da dama, musamman kallon kyakkyawan fuskarta, da kuma had’add’iyar surar jikinta
, uwa uba shagwab’a da kuma yanayin yarintarta.
Hawayen da suka sauk’a akan fuskarsa batare daya san da sauk’owarsu ba yayi saurin sa hannu ya share.
Jin kuma yanda zuciyarsa ke bugawa kaman zata faso k’irjinsa ta fitone yasashi janye idanunsa daga kan L
aylerh’n, asanyaye ya shiga jujjuya ninkakkiyar farar takardar dake hannunsa, wanda awajensa abunda ke rubuce ajikin takardar yafi komae d’acin ji da gani, badon kuma yakai zuciyarsa nesa ba, to fa da har abada bazae tab’a iya rubuta hakan da hannuwansa ba
.
Tayaya zai fuskanci Laylerh da wannan abun daya aikata mata? baisan ayaya zata d’auki maganar tasa ba, baisan ma zata fahimta ko bazata fahimta ba.
Abu d’aya kawae yasani shine yayi iya abunda zae iya, sannan baya kuma jin zai iya fuskantar ta fuska d
a fuska ya gayamata abunda ke rubuce acikin takardar, saboda ita yarinyace k’arama da sam baikamata ace ta fara fuskantar k’alubalen rayuwa tun daga yanzu ba, shekarunta kad’anne hakan yasa ba komae ne zata iya jurewa ba, batasan ya abun yake ba, sannan ba
ta kuma san ya girmansa yake ba.
Labb’an bakinsa masu kalan pink da suka bushe ya d’an taune, tare da had’iyan wani yawu mai d’acin gaske daya tsaya masa amak’oshinsa.
Cikin yanayin dauriya da kuma son k’arfafawa kansa guiwa akan abunda yayi d’in ya mik
’e tsaye, tare da d’aukan wani envelope dake ajiye asaman bedside drawer’n ya zura farar takardar aciki.
Ahankali kuma cikin yanayin son kawar da damuwar dake shirin duk’ar dashi k’asa ya shiga taka k’afafunsa zuwa inda Laylerh’n ke kwance.
Hak’ik’a da
ace ayau kuma ayanzu zai bayyana zuciyarsa ga kowa to da dayawan mutane sai sun tausaya masa, amma kuma yasan cewa babu daman yin hakan, domin shi kansa shaidane duk yanda zuciyarsa kejin k’una, to abayan wata zuciyar take, wata zuciyar wanda ta share ts
awon shekaru tana jiran cikar burinta, ta kuma samu rauni mai ciwo asanadin watsewan duk wani muradinta, zuciyar da tun asali aka halicceta da wani irin k’akk’arfan SO, wanda yake neman gusar da hankali da kuma tunanin maiyinsa.
Tabbas abunda idanunsa suk
a gane masa kad’ai sun isa tabbatar masa da cewa aduniya bayan wannan soyayyar babu wata, haka kuma bayan wannan muradin babu wani sauran muradi daya rage, kana idan wannan burin bai cikaba to Tabbas har abada babu wani buri aduniya nasu da zae tab’a cika.
Amatuk’ar sanyaye ya d’an ran k’wafo da kansa zuwa gareta, bayan ya tsayar da duk wani zancen zuci da zuciyartasa keyi.
Haka yakejin tausayinta tamkar zai fasa zuciya da k’irjinsa.
Hannayensa duka biyu yasa asanyaye ya d’agota cad’ak, tamakar wata y’
ar baby daga kwancen da