Showing 153001 words to 156000 words out of 244674 words

Chapter 52 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

gate d’in, anutse Fou’ad ya tura hancin motar ciki, tare da neman waje yayi parking.

Kusan atare dukansu suka fito daga cikin mo

tar, ganin yanda Laylerh’n ke layi kaman zata fad’i ne yasa Oum Ayush tayi saurin rik’o hannunta, kana cikin kulawa tace.

“Laylerh ya dai kina lafiya kuwa?.

‿

Kanta tad’an girgiza tare dasa hannu ta dafe daidai saitin kanta dake masifar ciwo har wani sara

wa yake kaman zai rabe gida biyu haka takeji.

“Kaina ne yake ciwo sosae.

‿

Tafad’i hakan cikin muryarta dake shaking.

“Ayya sannu to kije kisha magani sai ki kwanta kinji, dole dama da irin wannan kukan da kikayi sai kanki yayi ciwo.

‿

Cewar Oum Ayush ta

na me k’ok’arin sake hannun Laylerh’n.

Ahankali ta soma d’an taka k’afafunta, saidai bai wuce taku uku tayi ba ta tsaya tare da juyowa ta kalli Oum Ayush d’in, cikin wata irin sassanyar muryar dake bayyana rauni tace.

“Dan Allah Oum Ayush kada ki koma ki

barni idan zaki koma ki gayamin!

‿

Yanayin yanda ta k’are maganar cikin karyar da wuya ne yasa Oum Ayush ta sake jin matsanancin tausayinta, asanyaye tace.

“Insha Allah Zan gaya miki, kuma kema ki tabbatar da cewar kinsha magani.

‿

“To.

‿



Tace tare da ju

yawa cikin tafiyarta na rarrabe hanya ta nufi sashin su.

Ajiyar zuciya Oum Ayush ta sauk’e tare da kallon Fou’ad daya kafe Laylerh’n da idanu baya ko k’yaftawa, yayinda idanunsa kuwa suka zama jajur dasu.

“Fou’ad.

‿

Oum Ayush ta k’ira sunansa cikin tau

sasa murya.

Jin K’iran da Oum d’in tayi masa ne kuma ya sashi d’auke idanunsa daga kan Laylerh wanda harma ta isa sashinsu, dawo da kallonsa ga Oum Ayush d’in yayi, cikin yanayin bayyana damuwar dake cin zuciyarsa yace.

“Yanzu shikenan Oum Ayush haka ray

uwar Laylerh da Maleek zata ci gaba da tafiya? sai yaushe ne zasu samu farinciki arayuwarsu? sai yaushe abunda dukkanin su ke b’oyewa zai zama kammalalle? Tabbas Ina matuk’ar jin tausayinsu, musamman Laylerh da ta kasance yarinya k’arama dudu du ko 20years

bata cika ba, amma k’addara nata wasa da rayuwarta, dama duk wani burinta, lallai na gamsu cewa akwae abunda Allah Ya b’oye atsakanin Laylerh da Maleek, domin kuwa abune me girman gaske soyayyar da Laylerh keyiwa Maleek, domin na fahimci cewa bawai da iya

ka zuciyarta take son shiba, harma da gaba d’aya rayuwarta, wata soyayyace ta daban atsakaninsu bawai kuma irin normal soyayya da kowa ya sani ba, soyayyace ta musamman wanda Ina da tabbacin cewa har abada bazata tab’ayin

k’arshe ba.

‿



Ajiyar zuciya me

k’arfi Oum Ayush ta sauk’e tare dasa hannu tad’an sharce hawayen dake idanunta, lallai tabbas ta gamsu da duk kalaman Fou’ad, domin kuwa babu kuskure acikinsa komai ya fad’a gaskiya ne.

Ita kanta ayanzu tsoron soyayyar Laylerh Maleek takeyi, saboda ta fu

skanci cewa, ba soyayya bace irin ta kowa, wata sabuwar halittace da bata tab’a ganin irinta ba, duk da kuwa cewa daga Laylerh har Maleek d’in Miskilai ne amma hakan bai hana Soyayyar tasu tumbatsa har ta bayyana kanta a idanun mutane ba, hak’ik’a da ace L

aylerh bata da auren Najeeb akanta, to da babu wata k’addara da ta isa hanata aurawa Maleek Laylerh, koda kuwa su Abbou Jaheed basa so, amma kuma saidai k’addara ta riga fata, Auren Najeeb dake kanta ya zama shamak’i.

Numfashi taja tare da soma k’ok’arin

daidaita nutsuwarta, kallon Fou’ad tayi kana cikin nutsuwa tace.

“Baka kaini jin tausayinsu ba Fou’ad saboda dukansu yara ne da suka taso cikin maraici, Laylerh tataso babu Uwa da Uba, Maleek kuwa ya taso babu Uwa, tabbas maraicin Uba akwai wahala, amma

Maraicin Uwa yafi komai ta gayyara da k’unci saboda Uwa itace gaba d’aya duniyar duk wani bawa, ba komai Amma akwae Allah, muje ciki kaci abinci.

‿

(Yah Allah Kabarmin Mamana Araye, cikin koshin lafiya da farinciki, saboda itace komaina itace Haskena, kum

a farincikina

🙏🏻

dama duk wasu mutanen duniya, wanda kuma nasu suka rasu Allah Yajik’ansu da rahama Ameen.)

Asanyaye Fou’ad ya bi bayan Oum Ayush kaitsaye suka nufi sashinta.

Laylerh.

Ahankali ta tura k’ofar falon nata ta shiga bakinta d’auke da sas

sanyar sallama.

Shiru haka falon yake ba abunda yake tashi acikinsa sai k’amshin turare da kuma sanyin A/C, harta k’atuwar tv plasma d’in dake aje akan wani had’add’en glass table dake d’an manne da jikin bango wanda girmansa yakai 65inch shima akashe yak

e, Banda k’aran A/C ba abunda ke tashi acikin falon.

Dama ita ba gwanar son zama afalo bane wannan yasa kai tsaye ta nufi bedroom d’inta.

Sam ko da wasa bata tab’a kawo cewar Najeeb na d’akin ba, shiyasa anutse ta tura k’ofar d’akin ta shiga, sanin da t

ayi cewar ba kowa acikin d’akinne yasa tana shiga ta cire hijab d’in dake jikinta, tare dasa hannunta abayanta ta zuge zip d’in rigarta, batare kuma da ta juya bayanta ba, ta zauna abaki bakin had’add’en original royal bed d’inta.

Tafukan hannayenta duka

biyu tasa ta rufe fuskarta dasu, haka takejin zuciyarta na wani irin bugawa, yayinda wani sabon kuka ke shirin zuwar mata, duk da kuwa cewar kanta na mata ciwo sosai amma babu yanda ta iya da wannan kukan dake cinta, lallai tabbas tana buk’atar tayisa ko

hakan zaisa taji zuciyarta ta d’anyi sanyi.

Take kuwa ita kanta batasan ya akayi ba kawai sai jin kanta tayi ta fashe da kuka mai sauti.

Najeeb kuwa dake zaune a gefen gadon kan sofa yana wasu rubuce rubuce ganin shigowarta ne yasashi saurin b’oye paper’

n dake gabansa, tare da k’ura mata ido domin da’alama ya fahimci cewar idanu da hankalinta basu gane mata shiba.

Ganin kuma da yayi ta fara kuka ne yasa shi sake k’ura mata ido tare dasa hannu ya zare AirPod d’in dake kunnensa, ahankali ya mik’e tsaye da

ga zaunen da yake, cikin nutsuwa ya zauna adaidai bayanta, batare kuma da ya k’ira sunanta ba yasa hannunsa ya dafa kafad’anta.

Cak kuwa kukan da takeyi d’in ya tsaya, a matuk’ar tsorace ta juyo dan ganin ko waye.

Ido hud’u da sukayi dashi ne ya sa ta

k’walalo idanunta waje, tare dasa hannu ta dafe k’irjinta dake tsalle saboda tsoro.

Hawayen dake kwance akan kyakkyawar fuskartata ya kalla, tare dasa harshensa ahankali ya d’an lashi pink lips d’insa.

Ita kuwa Laylerh ganin irin kallon da yake matane y

asa tayi saurin sanya hannu ta shiga share hawayennata.

Murmushin daya bayyana kyawun fuskarsa yayi, ahankali ya kamo hannayenta, Jin yanda hannayen nata keda zafi ne yasashi d’an zaro idanunsa waje, ahankali ya d’an matso kusa da ita, cikin yanayin damu

wa yace.

“Kinyi kuka sosae gashi har jikinki yayi zafi, still kuma kinzo kina sakeyin wani kukan, sai yaushe ne zaki daina ta kura kanki da yawan kuka? kin manta cewar Dr. yace kina da hypertension? ko so kike kullum ya zama baki da lafiya?.

‿

Ya k’are ma

ganan nasa cikin sanyin murya, had’e kuma dasa hannu ya jawo Laylerh’n jikinsa.

Tabbas awannan lokacin tana da buk’atar rarrashi da kuma nutsuwa, hakan yasa ta kwantar da kanta akan chest d’insa, tare dasa hannayenta ta zagaye cikinsa zuwa bayansa.

Jinta

acikin jikinsa ne yasa shi sakin sassanyar ajiyar zuciya, hannunsa d’aya ya d’aura akan naked skin d’in bayanta, tare da soma shafa bayannata ahankali, bakinsa ya kawo daidai saitin kunnenta cikin murya me kama da rad’a asanyaye yace.

“Ya jikin Maleek?.

‿

Yanayin yanda yayi mata maganan acikin kunnenta ne yasa ta shagwab’e fuska, tare dajin wani irin motsawan tsikar jiki, kamar kuwa dama jira take ya tambayeta jikin Maleek d’in saiga hawaye sun sake cika idanunta, hakan yasa tayi raurau da idanunta tare

da karyar da wuyanta gefe, araunace tace.

“Har yanzu baya motsi, kuma bai bud’e idanunsa ba, abu d’aya ne kawai me motsi ajikinsa, itace zuciyarsa.

‿

D’an tsagaitawa da maganan nata tayi tare da d’agowa daga jikinsa, hannayensa ta kamo ta rik’e acikin nas

a.

Cike kuma da tsananin damuwa taci gaba da cewa.

“Inason naga ya bud’e idanunsa, Inaso naga yana motsi kaman yanda kowa keyi, banason nagansa acikin k’unci, sannan kuma banason duk wani abu da zai cutar dashi, saboda shi kad’aine Yayah nah, shi kad’ain

e acikin duniyar nan, bana tantamar basa rayuwata Idan har hakan zaisa ya zamo kamar kowa!!!

‿

Lumshe idanunta tayi wanda hakan ya bawa hawayen dake cikinsu daman sauk’a akan k’uncinta.

Najeeb kuwa idanu ya zuba mata baya ko k’yaftawa, yayinda yakejin wan

i irin soyayyarta na ratsa duk ilahirin jikinsa, daga wani b’angaren na zuciyarsa kuwa tausayinta ne yayi masa k’awanya wanda har hakan ya sashi kasa jurewa, har saida ya sake jawota ya rungumeta k’am, labb’ansa ya d’aura adaidai saitin forehead d’inta, ta

re da sakar mata wani irin kiss, take kuwa idanunsa sukayi jajur dasu.

Abundake yawo acikin k’irjinsa ya soma k’ok’arin dannewa, ta hanyar saita nutsuwarsa, d’an d’ago Laylerh’n yayi cikin kulawa yace.

“Jikinki yana k’ara zafi sosae bari na d’auko miki m

agani kisha.

‿

Baijira me zata ce masa ba kuwa ya mik’e tsaye.

Direct gaban bedside drawer d’insu ya nufa, murfin drawer’n ya bud’e ya ciro sachet d’in paracetamol, k’waya k’wayan paracetamol d’in guda biyu ya b’alla, tare da fita falo ya d’auko goran ru

wa marar sanyi sosai.

Dawowa yayi ya zauna akusa da ita, had’e da mik’o mata k’wayan magananin.

Ba musu kuwa ta amsa Tasha.

Murmushin dake bayyana damuwar da yakeji acikin zuciyarsa yayi, ahankali ya kama kafad’un Laylerh’n ya kwantar da ita akan gadon,

tare dajan blanket ya rufa mata, Dan ran k’wafowa yayi ya sake kissing goshinta, cike da kulawa yace.

“Zanje wani waje, bazan jima ba zan dawo ki d’anyi bacci ki huta kinji.

‿

Kai ta girgiza masa cikin muryarta da ta disashe tace.

“Anjima zamu sake ko

mawa asibiti nida Oum Ayush.

‿

Jin ta ambaci asibiti ya sashi d’an lumshe idanunsa, kansa kawae ya jinjina mata alaman “To.

‿

Baatare kuma da ya iya cewa komai ba ya d’au wayarsa tare da juyawa ya fice daga cikin d’akin.

Ganin kuma ya fita ne yasa ta lums

he idanunta, duk da cewar kuwa sam sam batajin bacci amma lallai tana buk’atar nutsuwa.

Asibiti.

Akaro na barkatai kenan da Abbou Khareem ke d’ago kai ya kalli d’an Uwa kuma Yayan sa, da duk yanayinsa ke baiyana matsananciyar damuwa.

Gyara zamansa ya

yi tare da fuskantar d’an uwannasa kana cikin sanyin murya yace.

“Tabbas Kallo d’aya kawai za’ayi maka asan cewa kana cikin damuwa, amma ko kusa ban tab’a kawowa araina cewar akwai wata damuwa da zata dameka wanda har zaka iya kasa fad’amin ba, musamman

damuwar da ta shafi Maleek domin koba komae shid’in matsayin d’ana yake.

‿

Jin maganan Abbou Khareem d’inne yasa Abbou Jaheed sauk’e ajiyar zuciya.

Hak’ik’a ko zai jinkirta fad’an damuwarsa to baga d’an uwannasa ba, sannan kuma matsalar da Maleek d’in

ya gamu da ita ba irin wacce za’a b’oye bane, saboda haka ya zame masa dole ya gayawa k’aninnasa abundake faruwa.

Kansa ya d’an sunkuyar k’asa, tare da tattaro nutsuwarsa, duk dama baya da kuzari amma dole zai nemo jarumta, barayin da Maleek d’in ke kwa

nce ya kalla, cikin muryarsa me d’auke da sanyi yace.

“Tabbas Maleek ya had’u da jarabawar Ubangiji, wanda kuma ya d’aura masa itane bawae don baya sonsa ba, ba kuma yayi hakanne wai don Maleek d’in ya aikata masa zunubi ba, domin kuwa jarrabawa ce da kow

ani bawa na duniya zai iya fuskanta, domin kuwa shafin dake cikin littafin k’addara yawane da su, bayan ka gama da wannan sai wata sabuwa ta sake bud’ewa, Dr. Mouhammad ya fad’amin cewa asanadiyar accident d’in da Maleek yayi, ya samu matsala acikin marar

sa, wanda hakan yasa, k’waya k’wayan haihuwarsa ba zasu iya rikid’ewa su zama k’wayar halittan da zasu samar da d’a ko y’a ba, bi ma’ana Maleek bazae tab’a haihuwa ba saidai wani ikon Allah.

‿

Idanu Abbou Khareem ya zaro waje cikin matsanancin tashin ha

nkali, Jin cewar wai Maleek bazai sake haihuwa ba.

Domin kuwa maganan ya zo masa amatuk’ar ba zata, wanda har saida yasa idanunsa suka ciko da k’walla, masu d’auke da matsanancin tausayin Maleek d’in.

Asanyaye ya shiga ambaton sunan Allah dan kuwa al’ama

rin ya sakashi a shock sosae.

Magana yakeson yi amma duk sai yaji ya kasa.

Daidai lokacin kuwa k’iran Alhaji Farouk wato Baban Munnira ya shigo wayarsa.

Take Abbou Jaheed yaji k’irjinsa ya buga, domin yasan cewa lallai acikin biyu za’ayi d’aya, abu me y

iwuwar ce kuwa bazaiyyi dad’i ba.

*16February/2021

*4:13 pm*

2/18/21, 8:33 AM - Ummi Tandama: *L.M*

*Not Edit*

*Chapter 53*

Ci gaba da ruri wayan Abbou Jaheed d’in tayi, yayinda ya k’urawa screen d’in wayar idanu, zuciyarsa cike da fargaba

n abunda zai biyo baya nan da y’an kwanaki kad’an.

Ganin kuma da yayi wayar tasa ta kusa tsinkewa ne yasashi d’aga wayar tare da karata akan kunnensa, gudun kuma kada yawan maganansa yayi yawa acikin wayarne yasashi tashi tsaye ya fice daga cikin d’aki

n, don amsa wayar tasa awaje.

Abbou Khareem kuwa da har yanzu tausayi, da kuma aljabin daya shigesa najin matsalan Maleek da yayi baisake saba, maida kallonsa yayi ga Maleek d’in, tare dasa hannu ya tallafi hab’arsa.

Tausayin Maleek d’inne tsantsa ya cik

a masa zuciya, domin kuwa shi kansa yasan ya zafi da rad’ad’i had’i da ciwon rashin haihuwa yake, yasan abune me tsananin ciwo da k’unci, abune dake sa zuciyar mutum koda yaushe ta zamana cikin rauni, saidai kuma babu wanda ya isa gujewa k’addararsa, domin

kuwa abunda Allah Ya tsara tabbataccene sai ya faru ko min jimawa.

Y’an guntun k’wallan da suka zuba masa yasa hannu ya share, tare da maida kansa jikin kujera, ahankali kuma cikin sanyin murya yace.

“Yah Allah Ina rok’onka da kabawa Maleek ikon cin wan

nan jarrabawa mai tsananin k’una da ciwo daya sameshi, Allah kasa ya d’auki k’addararsa da hannu bibbiyu, domin kuwa kafi kowa sanin abunda ka shirya.

‿

D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi tare da soma ambaton sunan Allah dan samawa kai nutsuwa.

Baiwani

jima ahaka ba kuwa Abbou Jaheed ya dawo cikin d’akin bayan ya gama amsa wayar.

Kallon d’an uwansa yayi kana cikin sanyin murya yace.

“Alhaji Farouk ne ya k’ira nakuma shaida masa cewa Maleek ya samu accident, yanzu haka Insha Allah yace suna zuwa shida i

yalansa.

‿

Kai Abbou Khareem ya jinjina tare da cewa.

“Allah Ya kawosu lafiya.

‿

Daganan kuwa shiru sukayi babu wanda ya sake cewa d’an uwansa wani abu.

Acan gida kuwa duk yanda Laylerh taso samarwa kanta nutsuwa ta kasa, abubuwa da yawane ke faman ci

da azalzalan zuciyarta wanda hakan yasa taji bazata iya jurewa kwanciyar da takeyi d’in ba.

Ahankali ta yaye blanket d’in da Najeeb d’in ya rufa mata, tare da zuro da k’afafunta k’asa, yanzun kam Alhamdulillahi domin kuwa ciwon kan da takeji d’in ya d’an

lafa mata, duk da kuwa cewar kannata baidaina ciwo duka ba, amma baya mata ciwo sosai kaman na d’azu da takejinsa kaman zai rabe biyu.

Hannunta tasa abayanta ta k’arasa zuge zip d’in rigar dake jikin nata, tare kuma da zare rigar gaba d’aya daga jikinta.

Hakanan taji tanason yin wanka, saboda tana da yak’inin cewa yin wankan zai taimaka mata ta d’anji kuzari ajikinta.

Doguwar rigar da ta cire d’in ta d’auka tare da jefata acikin dustbin d’in wanki, cikin tafiyarta me d’auke da sanyi ta k’arasa gaban make

ken drawer’n dake cikin d’akin, anutse ta bud’e murfin drawer’n inda ta ciro wani mini pink towel sabo k’al ta d’aura ajikinta.

Brush da kuma Maclean d’inta dake aje akan mirror ta d’auka, kai tsaye kuwa ta wuce toilet.

Kasancewar kuma akwai komai da kom

ai na kayan wanka acikin toilet d’inne yasa tana shiga ta zare towel d’in dake jikinta, d’aya daga cikin showercap d’in dake jere akan wani abu na glass dake cikin toilet d’in ta d’auka tare da suturce gashin kanta dashi, tayi hakanne kuma saboda sam bat

aso yau d’in ruwa ya tab’a kanta, saboda ana busa sanyi sosae.

Ruwa me d’an d’umi ta had’awa kanta acikin had’add’en bathtub d’in wankan nasu me yanayi da jikin kakkauran glass.

Ahankali ta shiga cikin babban bathtub d’in ta kwanta, tare da nutsa duk ji

kinta acikin ruwan, wanda dad’i da kuma d’uminsa yasa ta lumshe idanunta ahankali.

Take kuwa kaman jira idanunnata suke ta rufesu, kyakkyawar fuskarsa ce ta soma yi mata gizo, wanda hakan yasa bisa dole ta karyar da wuyanta gefe, cikin muryarta da tayi sa

nyi kana take fidda rauni sosae tace.

“Banason ka tafi ka barni, domin kai bawai iya duniyata bane kawae, gaba d’aya rayuwata ce kai, bana fatan ciwo da kuma k’unci su d’ore acikin rayuwarka Yah Maleek!!!

‿



Ahankali wasu irin hawaye masu zafi suka gangar

o kan kumatunta, yayinda kuma lokaci d’aya ta sakejin matsanancin tausayin kanta da kuma na Maleek d’in ya cika mata zuciya.

Asanyaye cikin rashin kuzari tayi wankan, koda ta fito daga cikin bathtub d’in kuwa alwala tayi domin taga yamma ya d’an soma rufa

wa sosai.

Fitowarta daga cikin toilet d’in kuwa yayi daidai da bugawan agogon dake nuna cewa daidai lokacin k’arfe biyar tayi.

K’arasawa gaban dressing mirror d’inta tayi tare da d’aukan wani towel ta tsane ruwan jikinta.

Body lotion na Nevea me dad’in

k’amshi ta shafa ajikinta, batare kuma da tunanin shafa powder ko kuma yin kwalliya ba ta k’arasa gaban sif d’in kayanta.

Wani riga da sket d’in Australia’n lace me kalan blue da golden ya ciro, wanda akayi masa simple style d’in pencil sket da kuma riga

fitted wanda iyakanta cinyarta.

Koda ta sanya kayan kuwa sosae sukayi mata kyau, musamman ma rigar da ta zauna ajikinta, tamkar ma ajikinta aka d’inka rigan.

Dogon gashinta ta nannad’e da ribbom, tare da d’auko wani siririn Australia’n vail

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login