Showing 126001 words to 129000 words out of 244674 words

Chapter 43 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

abu na farko kuma shine dole ne ya koyawa Laylerh’n zama tare dashi, son kasancewa dashi

da kuma son yin magana dashi.

Ahankali yakai bakinsa daidai saitin kunnenta,cikin yanayin sanyi had’i da karkarwar da muryarsa keyi yace.

“Is okay Laylerh, i promised you bazan miki komae ba, ki daina kuka please, kawai dai nakasa control d’in kaina ne,

amma Laylerh kimin alk’awarin cewa watarana zaki bani kanki cikin amincewa da kuma yarda, please Laylerh kimin wannan alk’awarin...

‿

yakai k’arshen maganartasa yana me rumtse idanunsa da k’arfi saboda yanda yaji mararsa na murd’awa.

Tabbas maganganun nas

a sunsa jikinta matuk’ar yin sanyi, take kuma tausayin kanta dana Najeeb d’in ya kamata, domin tasan cewa K’addara ce kawae ke bibiyan rayuwarsu, shi yana sonta ita da zuciyarta kuma suna son wani, tasani cewa Maleek bugun zuciya da numfashinta ne, amma ku

ma Najeeb Mijinta ne, kuma yana iko da komae najikinta.

Tambaya d’aya kawae take ta nanatawa azuciyarta shine ya zatayi?

Najeeb kuwa jin tayi shirune yasa ahankali ya janye jikinsa daga nata, tare da mirginawa gefe ya kwanta irin kwanciyar nan ta rubda c

iki, hannunsa yasa ya dafe kan maransa dake masa wani irin ciwo, har wani zugi yakeji awajen.

Wasu irin hawaye ne suka silalo daga cikin idanunta, wanda kuma ita kanta batasan hawayen nata na meye bane, haryanzu tana neman hanyar da zaisa ta juri d’aukan

duka way’annan nauyin akanta, ahankali ta sulale ta kwanta akan gadon tare da jawo rigarta da Najeeb din ya soma cire mata sama, dunk’ule jikinta waje d’aya tayi tare dajan tattausan wadataccen blanket d’in dake kan gadon ta rufe gaba d’aya jikinta dashi,

ahankali take sakin wani irin numfashi, wanda yake fita da sautin sheshshek’an kuka.

Kasancewar kuma bata cikin mood me dad’ine yasa ko mintuna 15 batayi ba bacci ya d’auketa.

Duk da cewar baya cikin bargon amma yana iya jiyo sautin fitan numfashinta m

e had’e da sheshshek’a, yanayin yanda yaji fitan numfashinnata ne kuma yasa shi gane cewar bacci takeyi.

Ahankali ya bud’e idanunsa dake alumshe, tare da juyowa ya k’urawa Bayan Laylerhn idanu, haka yakejin wani irin abu na yawo acikin zuciyarsa.

Duk da

cewar kuwa yanajin ciwon Mara me tsanani, amma haka dan dolensa ya daure, da Allah Yatashi taimakonsa kuwa baiwani jima ba bacci ya d’aukesa.

*Washegari*

9:30 am daidai k’aran alarm d’in dake gefen had’add’en gadon ya karad’e cikin d’akin, bugawan al

arm din kuwa yayi daidai da shigowar k’iran wayan dake aje gefen alarm clock d’in.

K’aran daya karad’e kunnuwansanne yasa ahankali ya soma bud’e kyawawan idanunsa masu kalan maye wanda ke cike da bacci.

Cikin yanayin k’osawa da k’aran yakai hannunsa ya k

ashe alarm d’in, akasalance ya jawo wayartasa dake ta faman tsuwa, k’ok’arin kasheta gaba d’aya yasoma yi saidai kuma ganin sunan Abbou Jaheed da yayi rubuce akan screen din wayar ne yasashi fasa kashe wayar, swiping na wajen picking call d’in yayi tare da

kara wayar akan kunnensa.

Abbou Jaheed kuwa jin Maleek d’in ya d’aga wayar batare da yatsaya yaji ta bakinsa ba yace.

“Mekake jira da har zuwa yanzu baka fito ba?.

‿

Jin tambayan da Abbou Jaheed d’in yayi masa ne yasashi d’an rumtse idanunsa, cikin mury

arsa da ke d’auke da yanayin bacci yace.

“Bantashi abacci ba.

‿

“Badamuwata bane hakan, nabaka nan da 30 minute kazo kasameni afalona, dannayi alk’awari ba kuma zan zama mai sab’a alk’awari ba.

‿

Cewar Abbou Jaheed ransa amatuk’ar b’ace, wanda jin yanayin

yanda muryar Maleek d’in ya sanja, yasashi yin Tunanin ko wani abun mayen Maleek d’in ya sake sha, kashe wayartasa yayi tare da maida ita cikin aljihu, ya zauna zaman jiran zuwan Maleek d’in.

Jin Abbou Jaheed ya kasha k’iranne yasashi zare wayar akunnensa

, Allah Yasani maganar auren da Abbou’n yace zaiyi masa ya matuk’ar d’aga masa hankali, wanda har yake fatan ace mafarki yake bawai gaske bane.

Ahankali ya yaye blanket d’in dake jikinsa tare da tashi zaune ya zuro da k’afafunsa k’asa daga kan gadon.

Han

nayensa yasa ya d’an murza idanunsa, kana kuma cikin yanayin kasalan da yakejin kansa aciki ya mik’e tsaye.

Kamar kullum kuma kamar koda yaushe hotonta yasaba kallo Aduk sanda ya tashi daga bacci, to yanzun ma hakanne takasance, domin saida ya sauk’e ida

nunsa akan d’an k’aramin hotonta dake aje bisa bedside d’insa.

Idanunsa ya d’an lumshe tare da sauk’e sassanyar ajiyar zuciya, tabbas ya aminta cewa kallon kyakkyawar cute face d’inta yana sama masa nutsuwa, saidai kuma akoda yaushe idan ya tuna cewar aya

nzu matsayin mata take ga waninsa sai yaji gaba d’aya komae na duniyar ya daena yi masa dad’i.

Cikin son kawar da duk wani tunani daga cikin zuciyarsa kaitsaye ya nufi toilet, yana shiga kuwa ya sakarwa kansa ruwa, wanka yayi tare da d’auro towel akan wai

st d’insa ya fito.

Sanin halin Abbou Jaheed ne yasashi goge jikinsa cikin hanzari ya shags mai ajikinsa, k’arasawa gaban drawer’nsa yayi tare da ciro kayan da zai saka.

Wani riga da wandon jeans masu d’an kauri yasanya ajikinsa, kasancewar ana d’an yana

yin sanyi, sosae kuwa kayan suka amshi murd’add’iyar surar jikinsa, yayinda suka k’ara bayyana kyawunsa, kasancewar kuma kayannasa nada kalan dark blue ne yasashi saka wasu dark blue d’in takalma masu yanayi da sneakers shoe, dark blue d’in hulan facing ca

p ya saka akansa, tare da d’aura agogon Gucci ahannunsa.

Sassanyan perfumed d’insa ya fesa, tare da d’aukan wayarsa yasa acikin aljihunsa, duk da cewar kuwa bayajin dadi acikin ransa, amma dole haka ya daure tare da kokarin samawa kansa nutsuwa.

Yayinda

acikin zuciyarsa kuwa yake mamakin cewar wae kamanshi Maleek za’ayiwa auren dole.

Wani murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa daidai lokacin da yake ficewa daga cikin dakin nasa, badan komae yayi murmushinba kuwa face ji da yayi ajikinsa cewar auren da Abbo

u Jaheed d’in keson d’aura masa bazae tab’a yiwuwa ba.

Locking k’ofar d’akinnasa yayi, tare dasa kansa direct b’angaren Abbou Jaheed ya wuce.

Yana zuwa kuwa ya samu Abbou Jaheed tsaye yana jiransa.

Ganinsa yasa Abbou Jaheed soma k’are masa kallo kamar

zaice wani abu kuma saiya fasa, cikin had’e fuska yace.

“Muje.

‿

Haka suka fito daga sashin Abbou Jaheed d’in Maleek na biye dashi abaya.

Kaitsaye wajen da motar Abbou Jaheed d’in ke fake k’iran tundra suka nufa, gidan baya suka shiga dukansu, take kuwa

driver’n Abbou Jaheed d’in yaja motar suka bar cikin gidan.

*(Am sorry Nagajine Wllhy

😰

)*

1/25/21, 9:16 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Note edit*

*Chapter 42*

Sassanyar iskan dake hura jikinta ne yasa ta

soma bud’e idanunta ahankali, samun kanta da tayi kuma cikin sabon yanayi ne yasa ahankali tasa hannunta ta shafa saman mararta da takejin na d’anyi mata ciwo kad’an, wanda kuma tun asuba da ta tashi yin sallah takejin hakan, saidai kuma yanda taji abun ya

tsananta mata yanzunne yasa ta d’an rumtse idanunta tare da cizon labb’anta.

D’an yunk’urawa tayi ta tashi zaune, tare da juyawa ta kalli gefenta.

Rashin ganin Najeeb kwance awajenne yasata d’an soma k’arewa d’akin kallo, tare da kasa kunnuwanta ko zata

ji k’aran ruwa acikin toilet.

Saidai kuma jin shiru babu alaman motsi wani bayan ita da take cikin d’akinne yasa ahankali ta zuro da k’afafunta k’asa daga kan gadon, tare da mik’ewa tsaye, anutse take taka k’afafunta harta k’arasa bakin kofar toilet d’in

dake cikin d’akin, ahankali ta tura k’ofar toile d’in ciki tare dasa kai ta shige, kayan dake jikinta ta rage, cikin kuma yanayin sanyin da ta samu kanta aciki ta k’arasa gaban babban bathtub d’in wankan dake cikin toilet d’in.

Kasancewar kuma Ana sanyi s

osae ne yasa ta surka ruwan dake cikin bathtub d’in dana zafi, ganin hasken ranan da tayi ta cikin windown toilet d’inne yasa ta gane cewar safiya tayi sosae, kasancewar tun da tayi sallan asuba ta koma bacci, bata sake tashi ba kuma sae yanzu.

Duk da kuw

a cewar tanajin marar nata naci gaba da murd’awa, amma haka ta daure tayi wankan nata cikin nutsuwa, tana fitowa daga cikin bathtub d’in wankan kuwa taji wani irin abu me d’umi na fitowa daga jikinta, wanda ko tantama batayi cewar period d’inta ne yazo.

Wanda kuma akoda yaushe idan taga period d’inta saitaji duk ba dad’i, saboda ba kad’anba yake takurata musamman ma menstrual pain d’in da takeyi wanda yake matuk’ar wahalar da’ita amma wani abun mamaki hakanan yau ganin period d’in yasa ta d’anji wani sany

i acikin zuciyarta.

Bathrobe tasa ajikinta, sanin kuma bakowa adakinne yasa kaitsaye ta bud’e k’ofar bathroom d’in ta fice, direct wajen da hand bag d’inta ke ajiye ta nufa, zuge zip d’in handbag din tayi, cikin sa’a kuwa taga d’an jakan pad d’inta aciki,

d’aukan pad d’innata tayi tare da komawa toilet ta kimtsa kanta, still harta sake fitowa daga toilet d’in kuwa Najeeb bai shigo cikin d’akinba.

Hakan kuwa bak’aramin dad’i ya mata ba, domin matuk’ar yana cikin d’akin bazata tab’a sakewa ba.

Agaban dress

ing mirror ta zauna, tare da bud’e body lotion d’inta me dad’in k’amshi ta shafa ajikinta, duk da cewar kuwa bata wani damuwa da kwalliya sosae ba, amma hakanan taji yau tanaso ta d’anyi light meckup akan fuskarta, cikin mintuna kad’an kuwa ta kammala kwal

liyan da yayiwa fuskarta kyau sosae.

Yanayin kuma yanda weather’n garin yake ne, yasa ta saka wani dogon wandon jeans da kuma baby top me d’an kauri wanda ya lafe ajikinta, ya kuma bayyana shafaffen surar cikinta.

Kana ta d’aura wata denim jacket me kala

n bak’i akan shigar nata, duk da cewar jacket d’in bashi da girma sosae, amma kuma zai hana mata Jin sanyi sosae.

Kasancewar kuma ita d’aya ne ad’akin yasa bata wani damu da saita sanya d’ankwali ba, komawa kan gado tayi ta kwanta, tare da jan blanket ta

rufe jikinta, saboda har yanzu tanajin mararta na d’an murd’awa hakan, wannan dalilin yasa ko breakfast bata nema ba tana kwanciya kuwa wani sabon bacci ya d’auketa.

Tunda suka kama hanyan unguwan na Wuse Zone 3, idanunsa ke kan titunan da suke ta wucew

a, tabbas azahirance kuwa idan ka kallesa zakayi tunanin cewa gaba d’aya hankali da nutsuwarsa naga titin ne, saidai kuma sam bahaka abun yake ba, tabbas idanunsa titunan suke kallo, amma tunaninsa da kuma zuciyarsa ba’anan suke ba, domin tun fitowansu dag

a gida abu d’aya ne ke yawo acikin tunaninsa, shine maganar Auren da Abbou Jaheed d’in yace zai masa.

Sam zuciyarsa bata gaya masa gaskiya akan auren, yayinda ajikinsa kuwa yakejin kamar wata sabuwar k’addara ne ke shirin tunkarosa, k’addaran da zata sauy

a masa gaba d’aya rayuwa.

Babban abunda yake tambayar kansa kuwa shine. “Agaba d’aya rayuwarsa tayaya zai fara zama da wata mace amatsayin matarsa? tayaya zai iya had’a shumfud’a da wata ta daban?

‿

Sam bayajin yiwuwar hakan, saboda yasan so ana ginasa ne

azuciya, idan kuma yayi k’arfi sai ya mamaye dukkan sassan jiki, tabbas auna mizanin abunda ka taso kanaso daban yake da wanda zakazo agaba ko kuma ayanzu, sannan kuma kowani irin soyayya takan iyayin tsuntsuwa tatashi amma Banda soyayyar da aka halittata

acikin jini da tsoka, wannan so d’in baya tab’a fita har abada.

Auna mizanin son da yakeyiwa Laylerh kuwa abune, me matuk’ar wahala, saboda ya gina gaba d’aya rayuwarsa ne akan soyayyarta, Hak’ik’a ya raini sonta acikin zuciyarsa tun tana k’arama, tsari

yanayi dama body structure d’inta yayi masa yanda yakeso, saboda haka bayajin cewa akwae wata mace aduniyarnan da zaigani ya kwad’aitu da ita ko kuma tashiga ransa idan ba Ayshnoor d’insa ba.

Idanunsa ya lumshe adaidai lokacin da yaji driver’n na danna ho

rn d’in motar, wanda kuma hakan alamane dake nuna cewar sun iso inda zasu je.

Ko minti 1 ba ayiba kuwa aka wangale musu babban gate d’in gidan dayaji had’uwa, wanda dagani kasan cewar gidan attajirin maikud’i ne.

Anutse driver’n ya kutsa hancin motar cik

in gidan.

Jin tsayuwar motar ne kuma yasa shi bud’e idanunsa wanda suka d’an sanja kala.

Daidai lokacin kuwa Alhaji Farouk wato abokin Abbou Jaheed ya k’araso wajen motar tasu da gaggawa, fuskarsa d’auke da murmushi kana kuma cikin mutuntawa ya bud’ewa A

bbou Jaheed murfin motar ya fito, mik’a masa hannu Abbou Jaheed yayi sukayi musabaha.

Ganin hakanne kuma yasa Maleek d’inma bud’e murfin motar ta b’angaren da yake ya fito.

Kallonsa Alhaji Farouk yayi cikin sakin fuska da walwala yace.

“Captain Maleek G

wani sannu da zuwa.

‿

Sanin cewa Alhaji Farouk d’in abokin babansa ne, kuma mutum me mahimmanci ne awajen Abboun sa yasashi d’an bayyana murmushi akan fuskarsa, cikin muryarsa da ako yaushe take tafiya da aji yace.

“Yauwa barka da gida.

‿

Murmushin fuskar

Alhaji Farouk d’inne ya fad’ad’a, cikin halinsu na y’an boko bawani surukunta ya mik’owa Maleek d’in hannu suka gaisa.

Cikin son nuna zallan farincikin dake ransa, da kuma murnar ganinsu agidan nasa yace.

“Masha Allah Bismillah mu isa daga ciki.

‿

Babu

musu kuwa suka rufa masa baya, saidai kuma Maleek kam ko kad’an baiso hakanba, sanin da yayi cewa idan sun shiga ciki d’in surutu su Abboun zasu tayi, shikuma Sam Ko kad’an bayason damuwa, amma gudun kada ya b’ata ran Abbou Jaheed yasashi rufa musu baya.

Kaitsaye babban falon Alhaji Farouk inda yake sauk’e bakinsa na musamman suka nufa.

Koda suka k’arasa cikin falon kuwa sake gaisawa sukayi, inda kuma Buzuwa wato matar Alhaji Farouk d’inkenan ta shigo suka gaisa, tun shigowarta kuwa ganin Maleek d’in yasa

take ta sakin murmushi, domin dama Alhaji Farouk ya fad’a mata komai agame da had’a auren Maleek d’in da tilon Y’arsu, wanda kuma hakan bak’aramin nasara da d’aukaka zai jawo musu ba, domin sun san had’a zuri’a da Alhaji Jaheed Gwani ba k’aramin girma da

k’ima zai k’ara musu awajen mutane ba.

Bata kuma sake yarda da hakan ba sai ayanzu da tayi ido hud’u da Maleek d’in, wanda ta tabbatar cewa idan y’arta tasamu daman aurensa to bak’aramin sa’a tayi ba, ko shakka babu kuwa sai y’arta tazama autar mata, sann

an kuma lokacin arzikin yarinyar nata ya soma, dan musamman tasa akayi mata bincike akan Maleek d’in da kuma irin tarin dukiyar da ya mallaka wanda shi kansa baisan iya adadinta ba, tabbas ya had’a komae na more rayuwar duniya, ga kyau ga to kud’i.

Shikum

a Maleek ganin matar da take matsayin wai uwar wacce zai aura, yasa lokaci d’aya yagano wani irin zab’ine Abbou Jaheed d’in yayi masa.

Fuskarsa ya kwab’e tare da tab’e bakinsa, acikin zuciyarsa yace.

“Banji ajikina cewar zan rayu da wani tsatso na gidann

an ba, because a irin gidannan ba asamun choice d’ina.

‿

B’angaren Buzuwa kuwa jikinta yana b’ari tasa aka cika gaban su Captain Maleek d’in da kayan sha dana ciye ciye.

Saidai Maleek ko ruwa bai shaba bare ma yace zaikai wani abu bakinsa.

Abbou Jaheed k

uwa sanin abunda suka shirya shida abokinnasa ne yasa su mik’ewa tsaye suka fice daga cikin falon.

Inda suka bar Maleek d’in zaune, M.Jay kuwa ganin sun barsa shi kad’aine yasashi zaro wayarsa k’iran iPhone12pro dake cikin aljihunsa ya soma dannawa.

Afte

r 10 minutes.

Ahankali aka turo k’ofar falon aka shigo, wata matashiyar budurwace wanda bazata wuce 23 years bane ta shigo, sanye take cikin wani tsadadden atamfa wanda yaji d’inkin riga da sket, ak’afanta kuwa wani uban takalmi ne me tsini, duk da cewar

kuma tana da tsayi amma takalmin ya k’ara mata tsayi, yanayin yanda kayan jikinnata suka kamata ne kuma yasa d’an k’aramin surar jikinta bayyana, kaitsaye za’a iya k’iranta da fara amma ba irin farinnan na turawa ko larabawa ba farin buzaye, akan fuskarta

kuwa meckup ne kwance wanda dagani kasan anb’ata lokaci ana zana shi, bata da wasu manyan ido, sannan kuma bata da tsayin hanci sosae, haka kuma bata da babban baki, tabbas ga wanda baisan kyauba idan ya ganta zai iya k’iranta da kyakkyawa, amma kuma abad’

inance ba haka abun yake ba, domin kyaun nata bawani kyau bane, saidai kawae tana da yanga.

Munnira kenan y’a d’aya tilo awajen Alhaji Farouk, yarinya mejin kanta da wayewa kasancewar a k’asar syprus tayi karatunta na degree.

Tabbas ayangance ta shigo

cikin falon tana me taunar chewing gum abakinta, yayinda take ta faman baza k’amshi, saidai kuma sam babu wani mayafin kirki ajikinta.

Shigowarta cikin falon da kuma sauk’e idanunta akansa da tayi ne, yasa ta tsayawa cak yayinda taji wani irin abu mekama

da shock ya shiga jikinta.

Sallaman da take k’ok’arin yine ya mak’ale abakinta adaidai lokacin daya d’ago kansa, Dan ganin ko waye ya shigo cikin falon.

Kusan fad’uwa Munnira tayi saboda tozali da tayi da kyakkyawar fuskar da aduniya take mafarkin ganint

a face to face, fuskar da sau d’aya ta tab’a ganinta ajikina jaridar Daily Trust, fuska mafi tsadan gani da kyau, tabbas zata iya cewa tunda take aduniya bata tab’a ganin Namiji me kyau da had’uwarsa ba.

“Handsome

‿

Tafad’a acikin zuciyarta saidai kuma bat

asan cewa maganar nata ya fito fili ba.

Kallo d’aya kawai yayiwa tsigau fiyau d’in da yagani agabansa ya kau da kai, tare da cigaba da latsa wayarsa, cikin zuciyarsa yace.

“Allah kasa ba wannan tsigau fiyau’n Abbou Jaheed ya kawoni na aura ba.

‿



Munnira kuwa ganin da tayi ya d’auke kansa daga kallonta ne yasa, ta k’arasowa cikin falon, cike da d’okin ganin had’add’en Namijin dake gabanta, da k’yar ta had’o kalaman bakinta wajen fad’in

“Sannu da zuwa.

‿

Shiru yayi tare da shareta yayi kamar baij

i abunda ta fad’a d’inba.

Ganin haka kuwa yasa duk saitaji guiwowinta sunyi sanyi, saidai kuma amatsayinta na gwanar rawan kai kasa yin shiru tayi cikin son jin muryarsa tace.

“Ina wuni

‿

Again shareta yayi bai d’ago kansa bama bare ya amsa mata

.

Still kuwa Munira bata daddara ba, zama tayi akan kujeran dake facing nasa, cike dason

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login