Showing 177001 words to 180000 words out of 244674 words
take, still kuma idanunsa wanda suke cike da ruwan hawaye na kanta, ya k’arasa da ita kan gado, tare da shumfud’eta atsakiyar gadon.
Sauk’e ganinsa kuma da yayi akan kyakkyawar fuskarsa ne yasashi kasa d’auke idanunsa daga gareta,
tayayama zai iya jurewa? tayaya zai iya fasalta rad’ad’i da kuma k’unan da zuciyarsa keyi? kafun yanzu takasance wani b’arine na rayuwarsa, amma yanzun fa? shikenan ya rasata? yarasa Laylerh yarinyar da kowanni kwanan duniya sake jin sonta yake acikin zuci
yarsa, tayaya zata d’auki abunda yayi mata? yasan dolene zataji zafi, saboda hakan da yayi tamkar bud’e mata sabon shafine dake cikin babban littafin k’addararta.
“I’m sorry Laylerh! I’m very sorry...!!
‿
Ya fad’i hakan abayyane, cikin kuma muryarsa dak
e shaking take kuma bayyana tsananin damuwar da yake ciki.
Batare kuma da yayi aune ba yaji wani abu mai d’umi nabin fuskarsa, wanda ko tantama babu yasan cewa hawayene ke fita daga idanunsa, kasancewar kuma yayi kusa da Laylerh’n ne yasa hawayennasa ke d
’iga akan fuskarta, ganin hakan da yayine kuma yasashi sake matsowa ahankali ya kawo fuskarsa gab da nata, cikin sanyi da damuwa ya d’aura bakinsa adaidai saitin forehead d’inta, batare da tunanin komae ba kuwa ya sauk’e mata wani irin hot kiss, dake bayya
na condition d’in da mutum ke ciki.
Bayan yayi kissing forehead d’innata ne kuma, ahankali yad’an gangaro da kansa, wanda hakan yasa fuskarsu daidaita dana juna, har takai ga hancinsu ya had’e awaje d’aya.
Amatuk’ar sanyaye ya d’aura labb’an sa akan nata
jajayen l’abban, atake kuma yayiwa lips d’innata wani irin kiss,wanda sanyi da kuma k’arfinsa yasa ta sauk’e k’akk’arfan ajiyar zuciya, saidai kuma kasancewar bacci take yasa bata bud’e idanunta ba.
Shikuwa Najeeb idanunsa ya k’ura mata yanajin sabon so
yayyarta na sake shiga zuciyarsa.
Hak’ik’a ayanzu bazae tab’a iya misalta yanayin da yakejin kansa aciki ba, domin da ace yau shid’in ya kasance ajinsin mata ne ba maza ba, to da babu abunda zae masa shamaki da zama dirshan ya rera kuka har sai yaji zuc
iyarsa ta samu salama, amma kasantuwarsa Namiji ya zame masa tilas ya shanye hawayensa, duk da zaiyi kukan zuci amma dole ya tausashi kansa.
Janye jikinsa yayi tare da nesanta kansa daga gareta, ahankali ya soma jan jikinsa baya, saidai kuma har yanzu ya
kasa d’auke idanunsa daga gareta, ahaka har ya k’arasa bakin k’ofar fita daga d’akin.
envelope d’in dake hannunsa ya yiwa wani irin rik’o tare da juyawa cikin sauri ya fice daga cikin d’akin.
*M.JAY*
Zabgegiyar kwalban wine d’in dake hannunsa yake ta
faman jujjuyawa, kusan sama da mintuna 10 kenan yanzun da yake ta faman abu d’aya.
Asanyaye kuma akaro na barkatai ya sake sauk’e idanunsa akan kyakkyawan hoton da gaba d’ayansa ya cika gaban screen na laptop d’in companyn Apple dake gabansa, sosae ya k’
urawa hoton idanu wanda akullum kuma akoda yaushe baya tab’a gajiya da kallonsa, sam koda da second d’ayane kuwa idanunsa basu tab’a jin gajiya da kallon kyakkyawar fuskar wanda ke jikin hoton ba, haka kuma ko wani bugun zuciyarsa da tunaninta yake tafiya.
Idanunsa masu kala da jin bacci ya lumshe tare da kai hannunsa ahankali ya shafa gefen cikinsa dake d’auke da k’awaraccen rubutu da akayisa kaman zanen tattoo.
Ci gaba da shafa gefen cikin nasa yayi yayinda kuma ahankali idanunsa keyi masa gizo da kyakk
yawar fuskarta, yanayin hakanne kuma yasashi shagala dajin wani irin kasalalllen bacci.
Bisa dole haka ya kwanta flat akan had’add’en carpet d’in dake malale agaban makeken gadonsa, still kuma idanuna alumshe yana me sake shafa gefen stomach d’insa dake d
auke da zanen rubutun sunanta.
Fitowarsa daga cikin part d’in nasune yasashi soma tafiya ahankali, tare kuma da aro jarumta ya sakawa kansa, gudun kada wani ya fahimci zallar yanayin damuwar dake kwance akan fuskarsa.
Isowarsa bakin k’ofar sashin Oum
Ayush da yayine kuma yasashi tsayawa, tare dasa hannunsa ahankali yayi knocking k’ofar, shirun da yaji babu amsa ne kuma yasashi ci gaba da knocking door d’in.
Oum Ayush kuwa dake cikin kitchine jin ana knocking k’ofar falonne ya sata fitowa daga ciki
n kitchine d’in, cikin yanayi na d’an d’aga murya ta yanda za’a jiyota, ta bawa mai knocking door d’in daman shigowa.
Najeeb dake atsaye kuwa jin anbashi daman shigowa ne, yasa ahankali ya murd’a handle d’in k’ofar ya shigo.
Ganin Najeeb d’inne kuma
yasa Oum Ayush dake tsaye ta fad’ad’a fari’arta, cikin sakin fuska tace.
“Najeeb sannu da zuwa, ae da ma shigowa kayi kai tsaye basai kayita knocking ba.
‿
Murmushin daya k’ak’alo da k’yarne ta d’an bayyana, cikin yanayin sanyi yace.
“Bansan bakya
kusaba Oum Ayush shiyasa.
‿
Kai Oum Ayush d’in ta d’an jinjina, still fuskarta d’auke da murmushi tace.
“Badamuwa Ina kabaro Sarauniyar kuka da kuma shagwab’ar taka?
‿
Kansa ya sunkuyar k’asa tare kuma da kasa k’arasowa cikin falon, domin tambyar d
a Oum Ayush d’in tayi masa ba k’aramin karyar masa da zuciya tayi ba.
Oum Ayush kuwa jin Najeeb d’in bai amsa mata bane yasa ta d’ago kai ta kalleshi.
Lokaci d’aya kuma taji k’irjinta yayi wani irin bugawa, domin kuwa tsananin damuwa ta hango kwance ak
an fuskarsa dama duk wani yanayinsa.
“Najeeb lafiya kuwa? Mai yake faruwa naga duk yanayin ka ya sanja?
‿
Tayi masa tambayar tana meyi masa kallon tsab, yayinda kuma wani sashi na zuciyarta ke wani irin bugawa.
Najeeb da gaba d’aya gabb’an jiki
nsa ke rawa, asanyaye ya k’arasa shigowa cikin falon tare da neman waje ya zauna, saidai ya kasa koda d’aga ido ya kalli Oum Ayush d’in, saima shiru da yayi tare dasa tafukan hannayensa duka biyu ya rufe fuskarsa.
Hakanne kuwa yasa zuciyar Oum Ayush ts
ananta bugawa, hankalinta tashe tace.
“Please Najeeb ka fad’amin meyake faruwa? Ko wani abune ya samu Laylerh? dan Allah Ka fad’amin, domin yanayinka ya d’agamin hankali!
‿
Yanayin yanda ta k’are maganar cikin matsanancin damuwane yasa Najeeb d’an numf
asawa, tare da zame hannayensa dake kan fuskarsa, araunace ya kalli Oum Ayush d’in, cikin kuma son bawa kansa k’warin guiwa da iya jure damuwa, murya asanyaye yace.
“Bansan tayaya zan iya jure k’alubalen da zae fuskanceni anan gaba ba Oum Ayush, akullum
a kuma koda yaushe nasan cewa Laylerh tana da damuwa, duk da kasancewarta k’aramar yarinya kuma, amma kullum cikin kuka take, da yawan lokuta nakan gane cewar akwae abunda ke damunta, yakan hanata sukuni, sannan koda yaushe tunani take, sometimes murmushi
nta yakan zamo na dole ne, sannan tana da matsanancin rauni sosae, Bansan tayaya zata kalli abunda na aikata agareta ba, saidai nasan nan aikata hakan dan wata manufa ba, ahak’ik’anin gaskiya kawae nayi abunda nake ganin shine daidai!
‿
D’an tsagaitawa d
a maganganun nasa yayi ta hanyar Jan wani irin doguwar ajiyar zuciya.
Idanunsa wanda suka jajur ya rumtse tare dasa hannu ya kama chest d’insa, still asanyaye yace.
“Ina Son Laylerh sosae, saidai kuma amma yafini sonta, duk yanda nakai ga jin soyayyart
a azuciyata shi fiye da haka yakeji, babu wani irin son da yake mata, domin ba wae sone na haka kawae ba, ba irin sone da kowa ya sani ba, Tabbas ni zan iya rayuwa babu Laylerh, domin ko ada daban santa ba nayi rayuwa cikin farinciki, shi kuma fa? bazae ta
b’a iya rayuwa babu itaba Bawae don soyayya kawae ba, no itace numfashinsa,rayuwarsa, dama zuciyarsa, duk yanda wani zai sota aduniya bayan son da yake matane, soyayyarta halittace acikin jikinsa da akayi wanda har abada bazae gushe ko goge ba, sannan hali
ttace dake girma tana hab’aka akowanni rana bayan kuma kowani minutes, kullum zafi yakeji azuciyarsa haka itama, because zuciyoyin nasu abu d’ayane basu da banbanci da juna, mafarkinsa itace haka itama mafarkinta shine, ita cefa duniyarsa Oum Ayush, itace
komae nasa, ban tab’a ganin irin wannan soyayyar ba, wanda komae zai faru da junansu sai d’aya daga cikinsu ya sani, Tabbas na yarda cewa Laylerh zanen k’addarar muce muduka biyun, amma nasa k’addarar tafi k’arfin nawa, hasalima Ba za’a tab’a had’awa ba, d
omin ni soyayyar Laylerh azuciyata kawae take, shi kuma soyayyartata rayuwarsace gaba d’aya, acikin jijiya da jini b’argo dama duk gangar jikinsa take, bazan iya jurewa hakanba Oum Ayush, domin sabodani kawae koda yaushe zunubi ake rubuta musu, aduk lo
kacin da sukayi tunanin juna, ko sukayi imagine junansu, k’warai nayarda cewa k’addara babu yanda bata juyawa rayuwar d’an adam, sannan na kuma yarda cewa komae rubutac
cene kuma tsararrre, Dan haka ina fatan abunda na aikata ya zamo silar farinciki arayuw
arsu!
‿
Ya k’are maganar cikin dauriya da kuma tsananin cijewa, asanyaye kuma ya d’an durk’usa agaban Oum Ayush wanda tunda ya fara maganganun nasa ta zuba masa ido.
“Kiyi hak’uri Oum Ayush bani da wani zab’i ne wanda ya wuce hakan, Dan Allah Na mik’a
komae ahannunki kiyi k’ok’ari wajen ganin Laylerh bata sake shiga k’unci ba, Sam bansan tayaya ne zan fara fuskantarta da wannan maganan ba, Brain d’inta k’aramane saboda haka sam bai kamata na hautsuna tunaninta ba, sannan ban barta dan banasonta ba, Ina
sonta sosae wallahi, koda yaushe da soyayyarta acikin zuciyata, yafini buk’atar ta sosae, domin akan fatar jikinsa ma sunantane arubuce, please Oum Ayush idan tayi kuka ki rarrasheta, domin ayanzu ita d’in batawa bace!!!
‿
Wasu irin hawaye masu ts
ananin zafin gaskene suka silalo daga kan kumatunsa, wanda kuma hakan ya tilasta masa rumtse idanunsa, asanyaye ya mik’awa Oum Ayush envelope na takardar dake hannunsa.
Sosae jikin Oum Ayush ya d’auki rawa alokacin da ta sa hannu ta karb’i envelope d’i
n da Najeeb d’in ke mik’o mata, wanda kuma tun fara maganarsa zuciyarta ke tsinkewa, ga kuma kirjinta dake bugu da k’arfi, tuni kuwa hawaye sun cika idanunta, domin tunkafun ya ida maganganun nasa ta fahimci komae.
Da hannayenta dake matsanancin rawa t
a bud’e envelope d’in tare da zaro y’ar white paper’n dake ciki.
Duk da tafahimci takardar ta meyene amma kuma tun kafun ta bud’e ta taji wani irin bugawan zuciyar dayasa tayi saurin ambaton sunan Allah.
Ahankali kana jiki amace ta warware takardar
.
Abunda idanunta suka gane matane kuma yasa tayi saurin rumtsesu, take kuwa hawayen dake cikinsu suka shiga fitowa wasu na Koran wasu kamar an kunna famfo, cikin wani irin matsanancin tashin hankali, tsoro, fargaba, da kuma wani yanayi na daban wanda b
atasan dame zata k’irasa ba ta ambaci kalmar.
“Innalillahi Wa Inna Ilaihirraju’un!!
‿
*3/3/2021*
*8:12 pm*
3/5/21, 5:50 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*Not editing*
*Chapter 62*
Idanu Oum Ayus
h ta rumtse tare kuma da cigaba da ambatan kalmar “Innalillahi wa inna Ilaihirraju’un!!
‿
Domin kuwa ba kad’anba abunda idanuwanta suka gane mata ajikin farar takardar da Najeeb d’in ya bata suka d’aga mata hankali.
Sake k’urawa rubutun dake cikin takarda
r idanu tayi, aranta tana mejin wani irin k’unci da ciwo.
Cikin muryarta kuma dake d’an carkewa kana kuma yake bayyana alaman tsananin damuwar da ta samu kanta aciki tace.
“Yah Subahanallah Najeeb ka saki Laylerh? meyasa zaka aikata haka batare da nema
n shawara ba? Meyasa Najeeb, shin bakasan cewa Allah Bayason saki ba, duk da kasancewarsa halak, Why Najeeb why kayi gaban kanka? Menene fa ida da kuma ribar aikata hakan? sannan da wacce irin hujja ka aikata hakan? shin ma kasan ya ciwo da kuma d’acin mai
da y’a mace bazawara yake? Musamman ga Laylerh yarinya k’arama?
‿
Idanunsa wanda suke zubar da k’walla ya bud’e, tare da d’ago kansa ya kalli Oum Ayush d’in, cikin wata irin sassanyar murya yace.
“Ko kad’an banyi niyar tozarta Laylerh ba Oum Ayush, sab
oda Ina sonta, inasonta sosae, amma ya zanyi da soyayyar da takewa Maleek? yaya zanyi? soyayyar Maleek dake zuciyarta ya wuce duk wani gaban kwatance Oum Ayush kuma kema kinsan hakan, a iya soyayyarta kad’ae ya kamata na saudakar, balle kuma idan akaje ga
zuciyar Maleek, wallahi nayi rantsuwa Oum Ayush bazan kumayi kaffaraba akan soyayyar da Maleek da Laylerh keyiwa juna, Bawae soyayyace da kowa yasani ba, wata irin halittace dake sake ginuwa akowacce rana, k’arfinta da kuma zafinta ya wuce duk yanda kowa k
e zato, tayaya zan zama silar katse fara da burinsu? tayaya zan zamo maison kae haka? Tayaya? Bazan iyaba Oum Ayush domin Maleek ne kwance acikin zuciyar Laylerh bani ba, nayarda zan jure rashinta dom
in kuwa haka Allah Ya tsaramin, sannan inason dan Allah
Ki fahimci cewar ban aikata hakan dan banasonta ba, Inason Laylerh wallahi Inasonta sosae!!!
‿
Kasa k’arasa maganan nasa yayi asakamakon wani irin yanayin da yaji ya samu kansa aciki, hakanan yaji kamar ya fashe da kuka, saidai kuma amma yasan yin hakan t
amkar maida kansa rago ne.
Kansa ya d’an shiga girgizawa ahankali batare kuma daya sake cewa komae ba ya juya ya nufi hanyar fita daga falon gaba d’aya.
Tsura masa idanu Oum Ayush tayi har ya gama ficewa daga cikin falon.
Still wasu irin hawaye masu
zafine suka silalo daga cikin idanunta, yayinda acikin zuciyarta takejin wani irin matsanancin tausayin Laylerh’n na k’ara shiga jiki da jininta, Tabbas bazatace Najeeb baiyi Namijin k’ok’ari ba, domin ba kowane zaiyi irin abunda yayi ba, saidai kuma har a
cikin zuciyarta bataso ya gano matsananciyar soyayyar dake tsakanin Laylerh da Maleek d’in ba.
Jikinta amatuk’ar sanyaye ta maida paper’n cikin envelope d’in tare dasa hannayenta duka biyu ta tallafi hab’arta, Allah Yasani har acikin zuciyarta bataji d
ad’in sakin da Najeeb d’in yayiwa Laylerh’n ba, domin saki ko yaya yake bashi da dad’i, duk dama tasan cewar hakan mafarin k’arshen wata matsalace, amma koba komae ayanzun Laylerh’n ta zama wata k’aramar bazawara, tunda auren nasu ko wata d’aya bai wuce b
a, tasan kuma zuwa yanzu baza’ace wani abu na auratayya bai tab’a shiga tsakanin Laylerh da Najeeb d’inba.
Acan b’angaren Najeeb kuwa lokacin daya fito daga falon Oum Ayush d’in direct sashinsu ya nufa, yayinda gaba d’aya jikinsa ke asanyaye, Sam bayaj
in dad’in zuciyarsa, abubuwa tare da damuwa duk sun masa yawa.
Ahankali ya murd’a handle d’in k’ofar d’akin, cikin kuma muryarsa wanda bata fita da kyau yayi sallama, tare da kutsa kansa ciki.
Yana sa kansa acikin d’akin kuwa idanunsa suka sauk’a akan
ta, har yanzun dae kwance take kamar yanda ya tafi ya barta.
Idanunsa masu d’auke da rauni ya lumshe, tare kuma da jingina bayansa ajikin k’ofar shigowa d’akin.
Wani irin sabon sonta da k’aunarta yakeji na ratsa zuciyarsa, hak’ik’a baesan cewa yanason La
ylerh’n ba saida ya rabu da ita.
Inama da ace k’addara zata barshi ya rayu da ita rayuwa tahar abada, Inama da ace babu Maleek acikin rayuwar ta, lallai tabbas da yasan watarana zata soshi, domin zaiyi iya k’ok’ari wajen ganin ya koya mata sonsa, saidai a
mma kuma Ina, k’addara ta riga fata.
Ahankali ta d’an soma bud’e idanunta, wanda suka d’an k’ank’ance saboda kukan da tayi, bud’e idanun nata da tayi kuwa, yayi daidai da soma sarawa’n kanta, wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta sauk’e, tare dakai hannu
nta ahankali ta rik’e kannata, cikin kuma son samawa kanta kuzari ta tashi zaune.
D’an soma k’arewa d’akin nasu kallo tayi, batare kuma da tayi zato ko tsammaniba ta sauk’e idanunta akansa, saboda har yanzu tsaye yake ajikin k’ofar still kuma idanunsa alu
mshe suke, wanda kuma hakan alamane dake nuna cewar yayi nisa acikin duniyar tunaninsa.
Cikin yanayin mamaki take kallonsa domin bata tab’a ganinsa acikin irin wannan yanayin ba, saidai kuma yanayin yanda taga yayi tsayuwar nasane ya d’auki hankalinta,
domin yayi kyau sosai, sai yanzunne kuma ta lura da shigar maroon jumper’n dake jikinsa, da kalanta ya bayyana kyau da kuma hasken fatarsa,
Ji kuma da tayi ajikinta cewar yana cikin damuwa ne, yasa taji zuciyarta ta karye.
“Yah Najeeb!!
‿
Ta k’ira sun
ansa murya amatuk’ar sanyaye.
Jin amo da kuma sautin muryarta da yaji acikin kunnuwansane ya sashi dawowa daga duniyar tunanin daya fad’a, ahankali kuma ya bud’e idanunsa ya sauk’esu akanta.
Sanadiyar hakan kuwa yasa idanunsu suka fad’a cikin na juna.
Wani irin murmushin daya bayyana asalin kyawun fuskarta tayi, cikin kuma murya mai d’auke da sakalci tace.
“Tunanin mekakeyi? yanda zaka d’auko Dr yamin injection ko?
‿
Idanunsa da suka ciko da k’walla ya sunkuyar k’asa tare da d’an jinjina mata ka
i, cikin son b’oye matsanancin damuwarsa akanta yace.
“Eh saboda naji har yanzu jikinki da zafi, bansan sai yaushe ne zakiyi lafiya ba Laylerh!
‿
Ya k’are maganan yana me kokarin maida k’wallan dake cikin idanunsa.
D’an k’aramin bakinta ta turo gaba
, tare da sake shagwab’e fuska, asanyaye tace.
“Yanzu ma fa kaena ciwo yakeyi Yah Najeeb, please kabani ruwa nasha.
‿
Jin abunda ta fad’ane ya sashi sake d’ago kae ya kalleta, ganin ita d’inma kallonsa takeyi ne yasashi sakar mata wani murmushi mai kam
a dana k’arfin hali, anutse ya k’arasa gaban maidaidaicin fridge d’in dake cikin d’akin, bud’e murfin fridge d’in yayi tare da dauko bottle water marar sanyi ya nufo gareta.
Koda ya iso jikin gadon kuwa mik’a mata goran ruwan yayi, tare da matsawa can gef
e ya tsaya.
Itakuwa kafa goran ruwan tayi abakinta har saida tasha fiye da rabin ruwan kafun ta janye bottle d’in daga bakinta.
K’afafunta ta zuro k’asa tare da mik’ewa tsaye.
Najeeb kuwa ta gefen idanunsa yake kallonta, harta gama zura bedroom slippers
ak’afanta.
Kaitsaye ta nufi hanyar toilet, hakanne kuma ya bashi daman d’ago kansa ya bita da kallo, har saida ta shige cikin toilet d’in kuma kafun ya d’auke idanunsa daga kanta.
Wani irin sassanyar murmushi mai d’auke da ma’anoni daban daban yayi, sa
boda har acikin ransa yana buri da kuma fatan da cewa da auren wata macen kamarta.
Laylerh kuwa tana shiga toilet d’in fuskarta kawae ta wanke, tare da juyowa