Showing 117001 words to 120000 words out of 244674 words
da ya bugi hannun n
atane yasata lumshe idanunta tare dajan wani dogon numfashi me kama da nishi, bakomae yaja hakan ba kuwa face dad’in da taji ya ratsata, wanda har yasa takasa d’auke hannunta daga kan fuskarsa, cikin wata irin sassanyar muryar da itakanta batasan tana dash
i ba ta k’ira sunansa, duk da kuwa tasan cewar ba amsawa zaiyi ba, dan baccin nasa yayi nisa sosae.
Sardae Kuma azuciyarta cike take da mamakin abun da zai rabasa da gado, da har sae dawo k’asa ya kwanta, kwanciyar ma kuma irin na takura kai.
“Kodai yana
da wata damuwa ne?.
‿
Wani yanki na zuciyarta yayi mata tambayar dayasa taji take jikinta yayi sanyi, lokaci d’aya Kuma ta marairace fuska, cikin salon maganarta tace. “No namasan baya cikin wata damuwa, Ya M.Jay dagaske baka cikin damuwa ko?
‿
Yanayin yan
da tayi maganar tana me sake matsowa kusa dashi ne, ya bayyana cewar lallai amsarsa takeso, saidai kuma tayaya shi da yake bacci zai bata amsa?.
Shirun nasa kuwa baisa tawani damuba, ita kad’ai kuwa tabawa kanta amsa ta hanyar cewa. “Dama nasan baka cik
in damuwa, amma Katashi ak’asa kaji, kaga wajen akwae sanyi sosai, please kahau gado kaji Ya M.Jay, kadaina kwanciya ak’asa saboda jikinka zaiyi ciwo, kuma zakaji ba dad’i, dan Allah Nidae Yah M.Jay kadaina bacci ak’asa pleaseeeee!!!
‿
Ta k’are maganar ama
tuk’ar shagwab’e, tare da sa hannunta ta shafa gefen fuskarsa.
Gaba d’aya ta shagala, yayinda tamanta asalin abun daya kawota d’akin nasa.
Acan falo kuwa yanzu sama da 15 minute kenan da Najeeb ke zaune akan dining table d’in yana tunanin dawowan Layle
rh daga sashin Maleek, zuwansu Abbou Jaheed dining table d’inne yasashi d’an sakin fuskarsa, saidai kuma har suka fara cin abinci zuciyarsa bata samu nutsuwa ba, tunaninsa d’aya shine me Laylerh keyi awajen Maleek da haryanzu bata dawo ba?
Agogon dake d’a
ure a tsintsiyar hannunsa ya duba, almost 20min kenan yanzu da tafiyanta, idanunsa ya rumtse da k’arfi domin duk yanda yaso tsaida zuciyarsa waje d’aya ya kasa, wasu irin tunani na dabanne ke yawo acikin k’wak’walwarsa, wanda kuma ko kad’an bayaso suyi tas
iri.
Momy kuwa tun d’azu tana ankare da komai,domin komai da ta tsara yazo mata ayanda takeso.
D’ago kanta tayi ta kalli dukansu, Inda Abbou Jaheed da kuma Abbou Kareem ke zaune akujerar dake facing na juna, gefen Abbou Kareem kuwa Oum Ayush ce zaune, ci
kin nutsuwa da kwanciyar hankali dukansu sukecin abincinsu, idan kacire Najeeb dake tsakuran abincin da kad’an kad’an.
Murmushi tayi again kana cikin daidaita nutsuwarta tace.
“Inamamakin abunda zai zaunar da Laylerh ad’akin Maleek harzuwa wannan lokaci
n basu fito sunyi breakfast ba.
‿
Jin abunda Momyn ta fad’ane yasa Abbou Jaheed d’ago kai ya kalleta, cikin yanayin mamaki yace. “What Laylerh da Maleek kuma suna tare ne.
‿
Murmushin samun nasara Momy tayi cikin nuna halin ko inkula tace. “Eh, tunkafun
shigowarku suke tare.
‿
Spoon d’in dake hannunsa ya ajiye, lokaci d’aya fuskarsa ta sanja, cike dason nuna rashin dacewar hakan yace. “For how reason zasu kasance atare har tsawon wannan lokacin?.
‿
Cewar Abbou Jaheed da fushin da yakeyi da Maleek d’in y
a dawo sabo, har acikin ransa bawae yana k’in kusancin Laylerh da Maleek bane, aa yana gudun faruwar wani abune, duk da cewar akodayaushe zatawa kai alkhairi yafi komai, amma kuma duniya tariga da ta sanja, shaid’an yana yawo ajikin mutane kamar jini, wand
a kuma akoda yaushe zai iya zugasu su aikata b’arnan da zaijawo b’acin zuciya, sam kuma agaba d’aya rayuwarsa baya fatan hakan takasance, domin Laylerh amanace awajensa, duk abu na rashin dad’i da zai tab’a rayuwarta zai zamana akwae sakacinsa aciki, bawae
yana zargin wani abu na daban bane adangane dasu, kawae dai yasan zuciya bata da k’ashi, wannan yasa tun tana k’arama yake guje mata mu’amala da maza any how, badan komae ba kuwa saidan son tsare mata mutumcinta.
Tunawa kuma da hukuncin da yayanke akan M
aleek d’inne yasashi sauk’e ajiyar zuciya, tare da kawar da duk wani tunani dake ransa, ahankali ya d’auki spoon d’insa ya cigaba da cin abinci.
Ganin kuma yaci gaba dacin abincinne yasa Momy yin k’wafa dan sam bahaka taso ba, koba komae taso ace Abbou Ja
heed din yayi fad’a sosae, saidai kuma duk da haka bata fad’iba domin akwae dama masu yawa da zasu zo mata, dan abubuwan da ta shirya musu sunada yawa.
Najeeb kam gaba d’aya yakasa cewa komae dan zuwa yanzu zuciyarsa tafara yi masa zafi.
Laylerh kuwa d
a kasancewarta da Maleek d’in ya shagaltar da’ita, Ahankali ta d’aga kansa cikin nutsuwa tasaka masa pillown dake rik’e ahannunta, d’an rank’wafowa kansa tayi, anutse cikin muryarta da tayi sanyi sosae tace. “Kayi mafarki me dad’i kaji Yah M.Jay.
‿
Tana gam
a fadin haka ta D’ago daga durk’uson da tayi flask din data shigo dashi ta d’auka tare da matsar dashi can gefe.
Juyowa tayi ta kalleshi wani murmushi ta sakarmasa, batare kuma da tasakeyin komae ba tafice daga cikin dakin, yayinda takejin zuciyarta wasai
babu wani damuwa.
Sam tama manta cewar tazo part dinne danyin breakfast.
Bata kuma ankare dasu Abbou Jaheed ba har saida ta karaso dining area’n.
Najeeb kuwa K’amshin turaren dayaji na Maleek ahancinsane yasashi d’ago kansa.
Ganin Laylerh da yayi da k
uma gane cewar k’amshin turaren Maleek d’in daga jikinta yake fitane yasashi rumtse idanunsa da k’arfi.
*5:56 pm*
1/19/21, 8:29 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*(
🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Kuyi hak’uri dan Allah Wllhy sim d’
ina danake chat dashine yasamu matsala yau 3days kenan da kyar aka gyaraminshi, shiyasa kukajini shiru saboda ya riga yasamu matsalan da bazan hau whatsapp dashi ba, amma yanzu naje angyaraminshi Kuyi hak’uri please nasan kunsha zaman jira)*
*Chapter 38
*
Ganin Laylerhn da kuma gane cewar k'amshin Maleek d'in dake tashi daga jikinta yake fita ne yasa shi rumtse idanunsa k'am, yayinda take yaji wani irin abu me suka ya caki k'irjinsa, lokaci daya wani irin kishinta ya Kama sa.
Wanda har yakaisa ga cije l
abb'ansa, hakika shi kansa baisan cewar yana kishin Laylerh'n sosai har haka ba sae yau, saboda jin k'amshin Maleek ajikinta bak'aramin k'untata masa zuciya yayi ba.
Itakuwa Laylerh k'arasowanta dinning table d'in ganin su Abbou Jaheed da tayi ne yasa t
a tsayawa tare da dan daidaita nutsuwarta, cikin yanayin sanyi ta k'araso dab dasu, hakan kuma ya farune saboda lura da tayi da irin Kallon da Abbou Jaheed ke mata.
"Good morning Abbou Jaheed." Ta fad'a cikin yanayin nutsuwarta.
Abbou Jaheed kuwa dake
goge bakinsa da tissue jin gaisuwar Laylerh'n ne yasa batare daya motsa bakinsa ba, ya jinjina mata kai alaman ya amsata.
Ganin hakanne kuma yasa jikin Laylerh K'arayin sanyi duk da kuwa batasan meye ma'anar hakan ke nufi ba.
D'ago Kanta tayi ta dubi Ab
bou Kareem tare da gaishesa, fuskarsa amatuk'ar sake kuwa ya amsa mata, tare da nuna mata kujeran dake facing ta Najeeb, alama yayi mata akan ta zauna, babu musu kuwa taja kujeran ta zauna tana me gaishe da Oum Ayush.
Murmushi Oum Ayush tayi cikin sakin f
uska tace. "Ina fata kindai tashi lafiya?."
"Lafiya lau." Tafad'a tana me gyara zamanta akan kujeran.
Plate d'in soyayyen chips da kuma plaintain Oum Ayush ta turo mata gabanta.
Abbou Jaheed kuwa kasancewar ya gama cin abincin nasa tuntuni mik'ewa ts
aye yayi batare da yace da kowansu k'alaba yabar dining table d'in.
Murmushi me d'auke da ma'anoni daban daban Momy tayi domin koba komae manufarta ya isa inda takeson ya isa.
Jan kujeran da take kai baya tayi tare da mik'ewa tsaye ta rufawa Abbou Jaheed
baya.
Ganin hakane kuma yasa Abbou Kareem ma mik'ewa tsaye dan dama dukansu sun kammala cin abincin nasu.
Kusan kuma atare suka mik'e tsaye shida Oum Ayush, dan itama tanaso tabawa Laylerh da Najeeb d'in waje, duk dama bataji dad'in zuwan da Laylerh'n t
ayi wajen Maleek ba, domin Sam bataso zargi ya fara shigowa tsakaninta da Najeeb.
Hakan yasa batare da sunce da kowannensu wani abuba suka nufi hanyar barin falon.
Ganin haka kuwa yasa Laylerh'n ta bisu da kallo har saida suka b'acewa ganinta, sassanyar
ajiyar zuciya ta sauk'e tare da maida kallonta ga plate d'in abincin dake gabanta, fork d'in dake cikin abincin ta d'auka tare da tsakalo chips d'in takai bakinta.
Jin test d'in abincin daban da wanda ta saba cine yasa ta gane cewar girkin Oum Ayush ne ba
na laure me aiki ba. Batare da ta gama tauna abincin dake bakinta ba, ahankali ta d'ago kai ta kalli Najeeb dake zaune suna facing d'in juna, wanda kuma har yanzu bai d'ago kansa ya sake kallonta ba, tunkuwa kallon farko daya mata, ahankali yake d'an jujju
ya spoon d'in dake hannunsa, domin hakanan yaji abincin yafita aransa duk da kuwa bawai wani sosae yaci ba.
D'auke idanunta tayi daga garesa, dan kwata kwata bata fahimci yanayin nasa ba.
Azahirin gaskia abincin takeci, yayinda acikin zuciyarta kuwa tuna
nin M.Jay ne yayi tasiri, kana kuma shi ya maye duk wani gurbin nutsuwarta, tuna yanda kyakkyawar fuskartasa take idan yana baccine yasa ta sakin murmushi me sauti tare da d'an lumshe idanunta.
Sauti da kuma amon murmushinta da yaji ne yasa shi d'ago kans
a, tare da zuba mata idanunsa wanda suka d'anyi ja, kana kuma suke bayyana zallan abun dake zuciyarsa.
Murmushin kuma daya gani kwance akan fuskarta ne yasa shi sake jin wani abu ya tokare masa k'irji.
"Mekenan me hakan yake nufi? tana farinciki ne sabod
a wani abu daban, wani abu dake b'oye acikin zuciyarta, meyasa bata farinciki alokacin da take tare dashi sai akasin haka?" Yayiwa kansa tambayar yana me yawo da idanunsa akanta, tabbas wani abu me kama da zargine ke neman mamaye zuciya da tunaninsa, wanda
kuma yarda da hakan zai iya lalata rayuwar aurensu, because aure da zargi haramunne.
K'ok'arin daure zuciyarsa yayi ta hanyar mik'ewa tsaye daga zaunen da yake, domin yasan zamansa awajen bazai k'ara masa komai ba sai zafin zuciya.
Jin alaman tashinsa n
e kuma yasa Laylerh d'ago kai ta kalleshi.
Ganin yana k'ok'arin barin dining area d'inne yasa ta tsura masa ido, domin tuni ya d'auke idanunsa daga gareta.
Kansa tsaye kuwa ya nufi hanyar fita daga falon, batare dako waiwayenta yayi ba.
Laylerh kuwa har
ya fice daga falon bata d'auke idanunta daga kallon hanyar da yabi d'in ba, hakanan duk taji ta tsargu da irin mood d'in da tagani akan fuskar kowannensu.
Saidai kuma rashin son tsanantawa Kanta damuwa yasa ta share duk wani tunani dake ranta, tare da ma
ida hankalinta ga abincin dake gabanta.
Fitarta daga cikin d'akinne yasa shi bud'e idanunsa, wanda suka d'an k'ank'ance ahankali ya sauk'e wata sassanyar ajiyar zuciya, tare da fesar da wani sassanyan numfashi ta bakinsa, duk da kuwa cewar baya cikin mo
od maidad'i amma hakan bai hanasa bayyana wani k'awataccen murmushi akan fuskarsa ba, tare da shak'an daddad'an k'amshinta da ya cika d'akin.
Maganganun sakalcinta da tayi ta fad'a masane suka shiga dawowa cikin kunnuwansa, wanda hakan yasa shi d'an lumsh
e sexy eyes d'insa.
Cikin wata irin kasalalliyar muryar dake bayyana abunda ke cikin zuciyarsa yace.
"Yeah before zuwanki am not okay Laylerh, amma yanzu da kikazo am okay!"
Ya k'are maganar yana me yun k'urin tashi zaune, duk da kuwa yana jin jikinsa
very weak, hannunsa yakai ya shafi gefen wuyansa inda Laylerh'n ta tab'a.
Still murmushin da baizamo al'adarsa ba ya sakeyi, domin yasan da ace Laylerh'n tasan cewa baccinsa baiyi nisa ba da bazata tab'a sakin jiki dashi har haka ba, ganin tasaki jiki di
nne kuma yasashi yin shiru tare dayin kamar bacci me nauyi ne ya d'aukesa, alhalin kuma duk abun da takeyi yana jinta.
Ahankali ya d'an yunk'ura ya mik'e tsaye, hannayensa duka biyu yasa ya kama waist d'insa,
Kallon pillown da Laylerh'n ta ajiye masa ya
yi, maganarta da take cewa. ya daina kwanciya ak'asa ne ya dawo masa, take kuwa sauti da amon zazzak'ar muryarta suka shiga dawo masa, tamkar alokacinne abubuwan ke faruwa, d'an murmusawa kawai yayi, ahankali ya soma rage kayan jikinsa, saida ya rage daga
shi sai dogon wandon dake jikinsa kafun ya wuce bathroom dan watsa ruwa.
B'angaren Laylerh kuwa anutse ta kammala cin abincin nata, tare da d'aukan tissue ta goge bakinta.
Mik’ewa tsaye tayi tare da k’arasowa cikin falon nasu ta zauna, hankali da Kuma
idanunta ta tsaida akan k’aton tv plasman dake cikin falon, tashar MBC Bollywood take kallo inda suke haska film d’in Force 2 na john abraham, kallon yanda murd’add’iyar surar JohnAbraham d’in yake ne yasa take Maleek ya fad’o mata saboda shima irin jikin
John dinne dashi, saidai kuma fuskar Maleek d’inta yafi na John Abraham d’in kyau, samun kanta acikin sabon Shauk’i da tayi ne yasata lumshe idanunta tare da jingina bayanta da jikin kujeran da take kai, lokaci d’aya kuwa ta fad’a duniyar tunani.
Naje
eb kuwa koda ya fita daga falon direct part d’insu ya koma, hakanan yakejin zuciyarsa duk ba dad’i shiyasa duk yaji zaman gidan ya ishesa, key d’in motarsa k’iran Benz ya d’auka kaitsaye ya fito daga part d’in nasu, babban parking space d’in dake gidan ya
fito tare da bud’e motarsa ya shiga, ganinsa da maigadi yayi ne kuma yasashi wangale masa gate d’in gidan ya cilla hancin motar tasa waje, duk da kuwa cewar baiyi niyar fita yau d’inba amma dole haka zaije ya zaga gari ko hakan zaisa ya d’anji sanyi acikin
zuciyarsa.
Asashin Maleek kuwa baiwani d’au lokuta masu tsawo acikin bathroom d’inba, koda ya fito towel ne d’aure akan waist d’insa, yayinda gaba d’aya jikinsa ke d’auke da danshin ruwa, Wanda kuma hakan yasa gargasan jikinsa kwanciya sukayi lub lub d
asu, cikin takunsa me d’auke da nutsuwa ya k’araso gaban tabkeken dressing mirror d’insa Wanda yake wadace da kayan shafa kala kala.
Saida ya d’auki wani d’an k’aramin towel ya goge jikinsa, kafun ya murzawa jikinsa had’adden body lotion d’insa me dad’in
k’amshi, kana kuma yabi fatar jikin nasa da turaren oud na jiki.
Handryer yajona tare dayin amfani dashi wajen busar da lallausan gashin kansa, bayan ya gama ne kuma kaitsaye yanufi wajen da drawer’nsa yake, direct b’angaren da yake ajiye Kayan training
d’insa ya bud’e, kamar kuma yanda yasaba yawancin lokuta idan zaiyi training tracksuit yake sawa, yau d’inma hakance takasance domin tsab yagama shirya kansa cikin wani had’add’en riga da wandon tracksuit masu kalan red yasanya, yayinda ak’afansa kuwa yas
a wasu fararen snickershoe masu ratsin ja, duk da kuwa cewar shid’in mai kyaune, amma shigar dake jikin nasa ya k’ara masa kyau Sosae.
Wayoyinsa dake aje akan bedside ya d’auka yasanya acikin aljihunsa, jakar da yake zuwa training da ita ya rataya akan ka
fad’arsa na dama, makullin motarsa ya d’auka cikin takunsa na nutsuwa ya fice daga cikin d’akin.
Kasancewar kuma bayason had’uwa da kowa ne yasashi zagayawa yabi ta k’ofar baya.
Koda ya fito compound d’in gidan part d’insu Oum Ayush ya kalla, dan sai alo
kacinnema ya tuna cewar tun zuwansu baije ya gaisheta ba, tuna hali da kuma kirkin OumAyush d’inne yasashi sakin murmushi, hakanan yaji zuciyarsa ta bashi umarni da zuwa b’angaren su Oum Ayush d’in, dama kuma yunwa yakeji, yasan kuma Bazai rasa abinci awaj
en Oum d’inba.
Cikin takunsa na nutsuwa yak’arasa bakin k’ofar da zata sadashi da babban falon dake part d’in.
Knocking k’ofar yayi saidai kuma jin ba’a amsa masa bane yasashi murd’a handle d’in k’ofar ya shiva bakinsa d’auke da sallama.
Shiru falon bak
owa sai k’amshin turaren wuta dake dashi, k’arasowa cikin falon yayi tare da sauk’e jakan dake kafad’ansa, batare da damuwa kowani shakku ba ya k’arasa dining area d’in dake cikin falon.
D’aya daga cikin yankakkun apple d’in da aka jera akan wani plate ya
d’auka tare da kaiwa bakinsa.
Oum Ayush dake cikin kitchine kuwa jin motsi afalon nata ne yasata tsayawa da abunda take yi tare da lek’owa dan ganin ko waye.
Saidai kuma rashin ganin mutum acikin falon yasa ta tsayawa tare da d’ansoma yin nazari, domin
tabbas taji motsi acikin falon amma kuma gashi ta lek’o bataga kowa ba.
“Gani nan fa anan.
‿
Cewar Maleek dake tsaye abayanta, kasancewar dama dining area d’innasu yashiga lungu shiyasa bata gansa ba.
Jin muryar Maleek d’inne yasa Oum Ayush sauk’e wata ir
in nannauyar ajiyar zuciya, saboda kafun yayi maganan ta d’an tsorita.
“Yadai kinji tsorone?.
‿
Ya fad’a adaidai lokacin da yake sake gutsuran apple d’in dake hannunsa.
Kallo me kama da harara Oum Ayush ta watsa masa, cikin yanayin hasala tace. “Bansani b
a.
‿
Murmushin daya bayyana kyawawan hak’oransa yayi cikin halinsa daya saba mata yace.
“I miss you so much.
‿
“Miss yo mata, koda yake ma ai idan da sabo nasaba da wannan halin naka, sai yau kaga daman dubani kenan?.
‿
Still murmushi yayi batare kuma da
yace komae ba, yaja d’aya daga cikin kujerun dining table d’in ya zauna, kallon Oum Ayush d’in yayi, cikin yanayin d’an yamutsa fuska yace. “Am hungry, kuma zanfita training please Oum ki had’amin ko tea ne Nasha.
‿
Murmushi Oum Ayush tayi tare da k’arasow
a dining table d’in, cikin sigar tsokana tace. “Ae dole dama kayita fama da yunwa, tunda har yau kakasa tsaida matar aure.
‿
Tafad’a tana me k’ok’arin bud’e d’aya daga cikin kulolin dake saman table d’in.
Jin Oum Ayush d’in tayi masa batun aure ne, yasashi
yin k’asa da kansa, cikin yanayi me kama da k’osawa yace.
“Please Oum Ayush ki had’amin Lokaci na k’urewa zantafi training ne.
‿
Yafad’i hakan yana me kallon agogon dake d’aure atsintsiyar hannunsa, wanda kuma yayi hakanne dan son kawar da zancen da Oum A
yush d’in keyi.
Gane nufinsa ne kuma yasa Oum Ayush d’in ta saki murmushi, batare kuma da