Showing 210001 words to 213000 words out of 244674 words

Chapter 71 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

so kikeyi akaiki d’akin mijin naki da yunwa acikin ki? kin sandai waye Maleek cikinsa ma baikula ba bare naki.

‿

Idanunta tad’an zazzaro waje cikin yanayin mamakin da ya kasa b’uya akan fuskarta tace.

“D’akin mijina? Kuma Yah M.Jay?.

‿

Still wa

ni harara Oum Ayush ta watsa mata, tare da cewa.

“Oh Allah yarinya saikace bakece da bakinki kikace a aura miki shi ba, To finally yau dai an d’aura muku aure yanzu ya zama mijinki ke kuma kin zama matarsa, idan kuma bakyaso yanzu sai nafad’awa su Abbou

’nki su warware auren.

‿

Wani irin dokawa k’irji da zuciyarta sukayi, musamman da maganganu biyun suka fito alokaci d’aya, take kuma taji wani irin abu mai tsananin sanyi ya shiga yawo acikin gangar jikinta, wanda hakan yasa Idanunta cikowa da k’walla,

yayinda akan fuskarta kuwa wani irin sahirtaccen murmushi ne ya bayyana, wanda ita kanta batasan dashi ba.

Ahankali tasa ta fukan hannayenta ta rufe fuskarta, domin wani irin shauk’i, kunya da kuma raunin zuciya ne suka lullub’eta alokaci guda, wanda h

ar hakan yasa takejin kunyan Oum Ayush ta kalli fuskarta.

Oum Ayush kuwa gane hakanne yasa ta saki murmushi, tare da mik’ewa tsaye, cikin kulawa tace.

“Kici abincin sosai kinji Laylerh na, kinga masu meckup din dana dauko suna hanyan zuwa, idan kuma

so kike akaiki wajen Maleek d’in babu kwalliya to.

‿

Batare kuma da ta jira me Laylerh’n zata ceba, ta bud’e k’ofar d’akin ta fice.

Laylerh kuwa jin fitar Oum Ayush d’in daga cikin d’akinne yasa ta bud’e fuskarta, wanda tuni ma harta b’aci da ruwan

hawaye.

“Shikenan yanzu da gaske Yah M.Jay ya zama mijina?

‿

Tayiwa kanta tambayar abayyane, Yayinda azahirance kuwa takejin wani irin matsanancin soyayyarsa na k’aruwa acikin zuciyarta.

Wayarta ta dauka da sauri tare da lalub’o hotonsa dake ciki

n wayar, kyakkyawar fuskarsa ta tsurawa idanu bata ko k’yaftawa.

Cikin wata irin hot feeling voice dake fita slowly tace.

“Alhamdulillah Zan kasance dakai har abada My Boo, da kaine kawai Zanyi rayuwa, sannan zan jurewa duk wata k’addararka!!!

‿

K’arar wayarsa dake cikin aljihunsane ya dawo dashi daga cikin wata duniyar da yashiga, wanda batare daya ankara ba, har ruwan dake dukan jiki da kansa ya soma kokarin yi masa illa.

Janye jikinsa daga bakin shower’n yayi, tare dasa hannunsa ya kashe sho

wer’n.

Gaba d’aya jikinsa ya jik’e tako ta ina, saboda tsabar sanyin daya shigesa kuwa harta hak’waran bakinsa karkarwa suke, amma da yake zuciyarsa tatafi zuwa wani waje na daban sam bayajin hakan ajikinsa.

Saima k’arasawa gaban sink da yayi ya d’auro a

lwala.

Bayan ya kammala alwalan ne kuma ya fito daga cikin toilet d’in, duk inda ya taka kuwa ruwan jikin kayansa ne ke d’iga awajen.

Samun kansa kuma da yayi akan Lallausan carpet d’in dake Malale a k’asan d’akinne yasa ka shi lumshe idanunsa.

Ta

re da zamewa ya durk’usa guiwowinsa.

Hannayensa dake ta karkarwa ya sa ya dafa k’asa, tare kuma da kai goshinsa k’asa yayi Sujjada, Lokaci d’aya kuma yaji wasu irin hawaye masu tsananin zafi sun zub’o daga cikin idanunsa.

Labb’an bakinsa dake rawa ya

d’an soma matsawa, saidai sam harshensa bai basa daman fad’an wata kalma ba, Allah Ne kad’ai yasan abun dake Cikin zuciyarsa ayanzun, yau rauninsa ya bayyana sosai, zuciyarsa ta karye, karyewa irin wanda bata tab’a yi ba, da wani bakin da wasu kalmomin za

i godewa Allah? kowani kalma dake bakinsa jinta yake tayi kad’an.

Yau ya zama wani na daban, yanajin kansa amatsayin wani ba Maleek da rayuwarsa ke cike da tarin k’addarori ba, yanajin kansa amatsayin raunataccen bawa mai raunin zuciya da gabb’ai.

Su

nan Allah Ya k’ira adaidai lokacin da wani irin kuka, mai tsananin tab’a zuciya ya k’wace masa, kukan dake bayyana asalin abun dake cikin zuciyarsa.

Tabbas yayi rauni sosai, ya kuma kai wani mataki wanda bazai iya gujewa wannan kukan ba, ayau babu maganan

miskilanci, hali, ko kuma rashin yawan magana da jarumta, sam bayajin way’annan ajikinsa, musamman ayanzu daya san yana a gaban Ubangiji’n daya fi, kowa sanin sirrin zuciyarsa, Ubangijin daya ke d’aura masa k’addara ya kuma yaye masa, Ubangijin daya basa

numfashi da lafiyar halitta dana ji da gani.

Shin dame zai godewa Ubangiji’n daya basa Laylerh ayau?

Ya rayu da matsanancin sonta, sonta ya zame masa abinci da kuma ruwan shansa.

Ya rasata adaidai lokacin da yake buk’atar ta, again gashi kuma yau

ya sake samunta a lokacin da yafi da tsananin buk’atar ta.

Sunayen Allah ya soma k’ira acikin zuciyarsa, yana meyi masa godiya game da ni’imar da yayi masa ayau, yana godiyar acikin zuciyarsa ne kuma saboda, kukan dake ci gaba da taso mai, wanda hakan

yasa harshensa kasa iya sarrafa maganganu.

Almost 20minute yana ahaka still kuma har yanzu idanunsa basu daina zubar da hawaye ba, saidai kuma zuwa yanzu bugun zuciyarsa ta soma tsagaitawa, tare da rage gudun da takeyi.

Ahankali ya d’ago daga suj

jadar da yakeyi d’in, tare da zama ya tank’washe k’afafunsa, saboda har yanzu sanyi sosai yakeji.

Takure jikinsa waje d’aya, tare da juyar da kansa ya tsaida idanunsa akan hoton Ayshnoor d’insa, Ayshnoor d’in da ayanzu ta zamo mata agareshi.

Jajayen

idanunsa da ke d’auke da danshin hawaye ya lumshe, tare da d’an ware hannayensa ahankali, Ita d’in kawai yanzu yakeson ji acikin jikinsa, yana so ya ganta, kallo d’aya kawai, kallon da zaiyi mata amatsayin matarsa.

Idanunsa ya d’an sake rumtsewa, sab

oda tunawa da yayi cewar, ayanzu Laylerh’n ta shigo rayuwarsa alokacin da yake d’auke da larura, larurar da bazai tab’a iya bata y’ay’an da zatayi alfahari dasu ba.

Kansa ya d’an soma girgizawa ahankali, tare kuma da had’e labb’an bakinsa waje d’aya y

a taunesu.

Daidai lokacin kuwa aka fara knocking k’ofar d’akin.

Hannayensa yasa da sauri ya goge hawayen dake kan fuskarsa, duk da cewar kuma idanunsa sunyi jajur, dole duk wanda ya kalleshi zai san cewa yayi kuka.

Ahankali duk da karkarwan da j

ikinsa keyi, haka ya mik’e tsaye tare da k’arasawa ya bud’e k’ofar.

Kallonsa Fou’ad dake tsaye yayi from head to toe, ganin kuma yanda kayan jikinsa ke jik’e da ruwa ne ya sashi d’an zaro idanunsa, cikin yanayin mamaki yace.

“M.Jay what’s wrong with

you? idanunka sunyi ja, then kayi kuka ga kuma kayanka ajik’e why?

‿

Kansa kawai ya girgizawa Fou’ad d’in alaman babu.

Murmushi kawai Fou’ad din yayi tare da kamo hannunsa, cikin kulawa yace.

“Mu tafi, domin anjima nan za’a kawo maka amaryarka,

saboda haka baidace ka zauna anan d’in ba, wai koma baka ga ansawa ko ina dake cikin nand’in sabon furnitures bane?

‿



Kansa ya jinjina alaman baigani ba, duk da cewar kuwa ya gani d’in.

Murmushi Fou’ad yayi, saboda dama yasan mai hali baya tab’a fas

a halinsa.

Batare kuma daya sake cewa komae ba ya kamo hannun Maleek d’in suka fice daga cikin dakin.

Duk da kuwa yasan cewa Bawae nan part d’inne za’a kawo Laylerh’n ba, kawai dai yayiwa Maleek d’in hakanne, saboda ya samu subar gidan.

Kamar kuwa

yanda suka shigo ta kofar baya, haka yanzun ma suka fita.

Kaitsaye gidan Maleek d’in dake wuse suka nufa.

*(Sorry wallahi bani da enough charge kuyi manage amma ba’anan naso tsayawa ba)*

*9:7 pm*

3/29/21, 11:25 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEE

K*

*Chapter 74*

Kaitsaye gidan Maleek d’in dake Wuse suka nufa.

Koda suka isa gidan kayan dake jikinsa ya sanja, tare da neman k’wayoyin da zasu sauk’ak’a masa wajen rage masa ciwon kan da yakeji, domin barin da yayi ruwa ya dakesa sosai ya haifar m

asa da ciwon kai.

Yanashan maganin kuwa wani irin bacci mai tsananin dad’i ya d’aukesa.

Acan b’angaren su Oum Ayush kuwa, kayan lefen Laylerh’n da sukayi order ne, suka iso, wanda hakan yasa suka baje kayan anan cikin babban falon gidan, kowa sai Ma

sha Allah yake fad’i, domin ba kad’anba aka narka mak’udan kud’ad’e wajen had’a kayan lefe’n akwatuna 26 kowannensu kuma cikinsa cike yake da kaya, Yayinda aka Ware akwatuna 2 musamman, aka zuba wasu had’addun Dubai and Turkish abayas masu tsananin kyau d

a tsada.

Bayan kuma kowa ya gama kallon kayan lefen ne, Oum Ayush d’in ta k’arasa zuwa d’akinta, wanda anan cikinsa Laylerh’n ta kwana, Koda ta k’arasa cikin d’akin nata kuwa, akwance ta tarar da Laylerh’n, ganin kuma da tayi cewar, Laylerh’n batajin d

ad’in jikinta sosai ne yasa, da kanta yau d’in ta taimaka mata tayi wanka da wani irin ruwa mai fitinannen k’amshi, bayan ta fito awankanne kuma Oum Ayush d’in ta turara mata jiki da turaruka masu k’amshin gaske, wanda hatta ita kanta Laylerh’n idan k’am

shin turaren ya daki hancinta sai taji idanunta na lumshewa.

Still ga kuma wani irin fitinannen feeling da ke taso mata, duk da cewar har yanzu bata daina jin ciwo a marar nata ba, saidai pain relievers d’in da take sha, sosai suke kashe mata zafin ciwon,

amma daga zangar aikinsu ya k’are tofa ciwon marar nata zai dawo.

Zaune take akan wani d’an madaidaicin abu me kaman kujera, inda take sanye da wani d’an k’aramin towel ajikinta, daga gefe guda kuwa d’aya daga cikin mata masu gudanar da gyaran jikin

nanne, ke shafe mata duk jikinta da wani sassanyan turare mai dad’in k’amshi.

Bayan matar ta gama shafa mata turarenne kuma tayi mata parking dogon gashinta da yasha saloon.

Wata doguwar rigar atamfar Chiganvy wanda akayiwa had’add’en d’inkin boubou g

own matar ta ajiyewa Laylerh’n, batare kuma da tace komai ba ta juya ta fice daga cikin d’akin.

Ganin hakanne kuma yasa ahankali ta zame towel d’in dake jikinta, kasancewar kuma already dama ta shirya cikin jikinta ne, yasa anutse ta d’auki rigar boubo

u gown d’in ta saka ajikinta.

Kasancewar kuma atamfar nada kalan red ne yasa ta bayyana tsananin hasken da skin d’in Laylerh’n ya k’ara.

Yayinda kuma d’inkin ya zauna mata ajikinta cib cib.

Still kuma D’an kunnayen gold d’in da aka ajiye mata bisa sam

an mirror ta d’auka ta sanya a kunnenta, ganin da tayi kuma cewar lokacin sallan azahar yayi ne, yasa ta d’aukan hijab ta zura ajikinta, kasancewar kuma dama tana da alwala ajikinta ne yasa ta tada sallah.

Tun kan ta idar da sallah’n nata kuwa takejin

mararta na d’an juyawa, wanda ko tantama batayi tasan ciwon marar nata ne ke kokarin dawowa, wannan dalilin yasa koda ta idar da sallah’n, komawa saman gado tayi ta kwanta.

Abu kamar wasa kuwa sai gashi ciwon yanata cinta.

Tana ahaka kuwa Theemah da A

leeya suka shigo cikin d’akin, ganinta da sukayi akwance ne kuma yasa suka shiga tsokanarta wai ciwon dad’ine ke damunta.

Ita dai ido kawai ta lumshe domin ita kad’ai tasan me takeji, ahaka har wani bacci ya d’auketa.

Ba’itane tatashi daga baccin b

a kuwa sai 4, still kuma har zuwa yanzun bataji wani sauyi daga ciwon marar nata ba, hakanne kuwa yasa duk gaba d’aya jikinta yayi sanyi.

Sallah’n la’asar tayi bayan kuma ta Idar da sallah’nne, Aunty Zee da Oum Ayush suka shigo cikin d’akin, abayansu kuw

a k’wararriyar mai yin meckup ce da Oum Ayush ta kashe mak’udan kud’ad’e wajen d’aukota, musamman Dan tayiwa Laylerh’n meckup.

Duk da cewar kuwa bata wani jin dad’i sosai, haka ta sakeyin wani sabon wanka, again turaruka masu k’amshi aka sake shafa mata

ajikinta, tare kuma da zaunar da ita awani waje na musamman, cikin k’warewa kuwa meyin meckup d’in ta shiga zana mata akan fuskarta.

duk yanda takejin ciwo amararta kuwa haka ta daure, domin ita d’inma ayau taji cewar tana buk’atar meckup d’in.

Almo

st 1hour and 15 minutes aka kwashe ana meckup d’in, daya k’ara bayyana asalin kyau, da kuma had’uwarta, domin hatta ita kanta meckup artist d’in zata iya rantsuwa cewa, bata tab’a yiwa wata meckup d’in daya zauna akan fuskarta ba, Kamar Laylerh’n, saboda k

yau ne dama ya had’u da ado.

Ita kanta Laylerh da taga fuskarta acikin mirror saida ta tsaya k’urawa kanta ido, domin tasani tunda take bata tab’ayin kyau irin na yau d’in ba.

Wani had’add’en blue d’in yadi mai kaman material, wanda akayiwa wani iri

n fitinannen outfit daga favoritefashion bintaberry ta saka ajikinta, d’inkin riga da sket ne amma ba wai irin normal sket d’innan bane, domin saboda tsawon sket d’innata har bayansa najan k’asa, Yayinda kuma aka k’awata jikin yadin da wani had’add’en ado

mai colourn grey, daga ta saman rigar nata kuwa, wani had’add’en net akan samata, wanda ya bayyana gaba d’aya surar k’irjinta, kana kuma ya sake k’arawa shigar nata kyau, musamman da kayan suka zauna mata cib ajikinta, har kuma sukayi nasarar bayyana asali

n kyau da kuma tsarin halittarta.

Aunty Zee da Oum Ayush kuwa kansu bakinsu saida ya kasa rufuwa musamman da suka ga irin kyawun da Laylerh’n tayi.

Oum Ayush d’inne ta kamo hannunta ta zaunar da ita, tare da bud’e wani d’an madaidaicin box, wanda aka

k’awata jikinsa da ado.

Wani tsadadden sark’a da d’an kunnen gold mai adon grey colour ta ciro, tare da d’aurawa Laylerh’n sark’an awuyanta, d’an kunnen kuwa akunnenta ta saka mata shi.

Take kuwa walwali da kyaun sarkan suka k’arasa bayyana kyawun

Laylerh’n.

Meckup artist d’innan ne tayi mata wani d’aurin d’an kwalin turban da ya sake fidda kyawun kwalliyar nata.

Oum Ayush kuwa k’afar Laylerh’n ta kamo, anutse ta zura mata wasu had’addun grey shoes masu kyau da tsini.

D’an madaidaicin grey v

ail mai d’auke da adon duwatsun white stones Oum Ayush ta rufa mata, akai zuwa jikinta, yanayin yanda Oum Ayush d’in ta rufa mata vail d’inne kuma yasa kusan rabin fuskarta ya zamana arufe.

Hakanne kuwa ya k’ara bayyana asalin matsayinta na had’add’iyar

amarya.

Turaruka masu dad’in k’amshi Oum Ayush ta fesa mata, tare kuma da kamo hannayenta ta rik’e acikin nata.

Fuskarta d’auke da tsananin farinciki tace.

“Masha Allah Laylerh kinyi kyau sosai, lallai yau ko Maleek idan ya ganki sai yayi da gask

e kafun zai iya ganeki.

‿

Murmushi gaba d’aya Aunty Zee da su Theemah sukayi, domin su kansu sun yaba da irin kyaun da Laylerh’n tayi.

Mik’ar da ita tsaye Oum Ayush tayi, cikin nutsuwa kuma suka shiga takawa har suka fice daga cikin d’akin.

Kaitsa

ye d’akin dake gefen na Oum Ayush d’in suka shiga, kan wani lallausan kujera Oum Ayush ta zaunar da ita, kana itama ta zauna akusa da ita.

Hannayenta ta sake kamowa, cikin nuna tsananin farinciki da kuma nuna godiyarta ga Allah Tace.

“Alhamdulillah

hakika kowani tsanani yana tare da sauk’i, sannan babu wani k’unci ko kuma bak’inciki da yake d’orewa acikin wannan duniyar, ba kuma lallaine idan ka rasa abu, ya zama ka rasa shi ba kenan har abada, sannan acikin rayuwa fad’uwa da nasara na bibiyarmu aku

llum akuma koda yaushe, watarana mai nasara zai zamanto ak’asa, wanda yake k’asa kuma ya zamanto asama, rasa abunda kakeso afarko bawai shike nuna cewar har abada bazaka tab’a samun abunda kakeso ba, lallai idan kayi hakuri watarana zaka samu..

‿

D’an nu

mfasawa tayi, had’e da sake gyara zamanta, hannayen Laylerh’n dake cikin nata ta rik’e da kyau, cikin yanayin tausasa murya, da kuma nuna k’aunarta ga Laylerh’n tace.

“Laylerh yau Allah Yayi kinzama mata ga Maleek, wanda hakan ke nuna cewar wani babban

nauyi ya rataya awuyanki ke dashi, yana da hakk’i akanki haka kuma kema kina da hakk’i akansa, wajibinki ne kuma ki aikata duk wani abunda ya saki, matuk’ar bai kaucewa addinin musulunci ba, wajibinkine kulawa da ci da shansa, haka kuma hakk’inkine kulawa

da kuma basa farinciki, Laylerh kinfi kowa sanin cewar Maleek mai rauni ne, duk da kuwa cewar a idanu shid’in cikakken jarumine, amma har acikin rai da zuciyarsa shid’in mai raunine, musamman akanki, domin duk wani masomin rauninsa kece Laylerh, amadadin k

omai nasa kece, ke kuma d’ince dai kad’ai zaki iya jib’anta al’amuransa, kasancewarsa d’an uwa kuma Yayah agareki, sannan dole sai kinyi hakuri kin kuma jurewa, duk wata jarrabawa da zata fuskanto ku, domin kasantuwarku amatsayin ma’aurata yanzu ya goge d

uk wani Nisan dake tsakaninku, ayanzu zaku kasance tamkar abu d’aya ne, dole buri da kuma fatanku zasu kasance atare da juna.

Nasan kuma kinyi kokari sosai Laylerh, domin duk da irin k’addarar da ta same da, baki guje masa ko sanja tunani ba, haka kika

amincewa aurensa, lallai Tabbas Allah Ne kad’ai zai baki ladan abunda kika aikata masa, na kuma yi imani cewar koda da second d’aya har abada bazaki tab’ayin danasanin kasancewar Maleek amatsayin mijinki ba, nasani k’warai cewar zai baki farinciki marar ya

nkewa, da izinin Allah Kuma zakuyi rayuwa mai dad’i, rayuwar da babu munanan k’addara acikinta, rayuwar da zaku mantar da junanku cewar kud’in marayune, sannan rayuwar da haskenta zai haskaka kowa insha Allah....

‿

Dakatawa da maganan nata tayi, tare kum

a dad’an sanya hannu ahankali ta share hawayen daya cika idanunta, wanda batare kuma da ta saniba har ya gangaro kan fuskarta.

Saurin share hawayen nata tayi, gudun kada Laylerh’n taga hawayen, murya atausashe tace.

“Tashi muje tun d’azu Fou’ad da a

bokansa suka zo d’aukarki, Tabbas amma nasan zanyi kewarki sosai Laylerh na!!

‿

Wasu irin siraran hawaye ne suka tsiyayo daga cikin idanunta, domin itama tasani tabbas zatayi kewar Oum Ayush da kuma su Abbou Jaheed, k’warai zatayi kewarsu sosai.

Hannu

nta Oum Ayush ta kamo tare da mik’ar da ita tsaye, ahankali kuma cikin nutsuwa ta shiga takawa da ita har suka fice daga cikin d’akin.

Koda suka fito cikin babban falon gidan kuwa, gaba d’aya kallo kansu ya dawo, musamman yanda mayafi da kuma shek’in su

turar Laylerh’n ke d’auke idanu.

Duk da cewar kuwa Rabin fuskarta arufe yake, amma hakan bai hana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login