Showing 138001 words to 141000 words out of 244674 words
bawa mijinta, takasa d’aukar nauyi da jib’antan al’amuransa, impact ma takasa tsaida zuciya da tunaninta akansa, alhali kuma tasan cewa bashi da laifi ko makusa ajikins
a, shima cikakken Namiji ne, me aji da kuma nutsuwa, Namiji ne shima irin wanda mata da yawa ke mafarki da fatan samu, haka zalika Namiji ne wanda ba kowacce mace bane keda arzikin samu, sauda dama takanso ta tambayi kanta cewar “Menene Laifin Najeeb ko ku
ma aibunsa?
‿
Saidai amsar akoda yaushe shine “Babu.
‿
Abunda har yanzu zuciyarta ke zaune akansa kuwa shine SOYAYYAR MALEEK.
Abazata taji sauk’an tafukan hannayensa akan fatar wuyanta, hakanne kuwa yasa ta bud’e idanunta da sauri ta sauk’esu akansa,wanda
tuni har ya zauna abakin gadon batare da ta Ankara da hakan ba.
“Har yanzu jikinki akwae zafi sosae, ko zamuje hospital?.
‿
Yafad’i hakan yana me k’ok’arin zare hannayensa daga wuyanta.
Yayinda ita kuwa takasa d’auke idanunta daga kansa, Dan yau akaron f
arko kenan da taji wani abu na daban adangane dashi wanda wannan abun kuma ba komai bane face tausayi da kuma raunin da zuciyarta tayi.
Hakanan taji ajikinta cewa tanason kasancewa tare dashi, ma’ana tana buk’atar ya zame mata mafaka ta yanda zata shiga j
ikinsa tayi masa kuka sosae ko hakan zaisa taji sauk’in abunda takeji.
Shikuwa Najeeb jin tayi shirune yasashi d’ago idanunsa ya kalleta, ganin da yayi kuma shi take kallo ne yasashi k’ak’alo murmushi ya d’aura akan fuskarsa, cikin muryarsa da tayi sanyi
sosai yace.
“Yadai Laylerh ko akwae wani abu bayan fever da yake damunki ne?
‿
Kai ta girgiza masa alaman a’a, azahirance kuwa y’an k’ananan labb’an bakinta ta soma motsawa da alama kuma wani abu takeson cewa, amma amon maganan nata ya kasa fitowa fili.
Idanunsa ya d’an lumshe ahankali, domin ganin hakan da tayi yasan cewa bazata yi masa wani magana ba.
“LAYLERH.
‿
Yak’ira sunanta da d’an k’arfi tare dasa hannayensa ya kama kafad’unta.
Cikin wani irin sabon yanayin da tasamu kanta aciki ta fad’a jikins
a tare dasa hannayenta akaron farko dan kanta ta rungumesa, tare da sakar masa wani kuka me d’auke da zallan sakalci da shagwab’a.
Tabbas kuwa yaji runguman da tayi masa d’in har acikin jikinsa, hakan yasa ahankali shima yasa hannayensa ya rungumeta, cik
in sanyin yanayi yakai fuskarsa daidai saitin kunnenta, ahankali kuwa ya d’an soma sakar mata numfashinsa adaidai cikin kunnen nata, cikin muryarsa da ta d’an sanja amo lokaci guda yace.
“Kidaina kuka please, ko kinaso na kaiki hospital doctor ya miki all
ura?
‿
Cikin yanayin sheshshek’an kukan nata ta girgiza masa kanta, alaman “A’a
‿
“Good to kiyi shiru kinji My beautiful Laylerh nah, kinci abinci?.
‿
Ya fad’i hakan yana me d’an d’ago innocent face d’inta.
“A’a nak’oshi.
‿
Tafad’i hakan tana me mamul mamu
l da d’an k’aramin bakinta.
“Mekikeso kici to? za kisha chocolate da ice cream?.
‿
Da sauri ta kad’a masa kai alaman “Eh.
‿
Murmushin daya k’arawa fuskarsa kyau yayi, cikin son kwaikwayon yanayinta yace.
“Good girl gueen of shan zak’i.
‿
Saketa yayi tar
e dasoma k’ok’arin tashi daga kan gadon, amma ga mamakinsa sai yaga ta rik’o hannunsa, yayinda hawaye suka zubo daga cikin idanunta.
Hakan da yagani ne kuma yasashi dawowa ya zauna akusa da ita, tare dasa hannu ya jawota jikinsa,
fuskarsa ya kawo kusa da
nata, har takai ga suna jin d’umin numfashin juna.
D’ayan hannunsa yasa ya rik’o waist d’inta, cikin sabon feelings d’inta da ya samu kansa aciki ya had’e fuskarsu waje d’aya, hakanne kuwa yasa sajen dake kwance akan fuskarsa ya soma gogan nata fuskar.
Amatuk’ar sanyaye ya d’aura lips d’insa akan nata, tare da sauk’e mata wani kiss me had’e da sucking lips.
Wanda yasa gaba d’aya tsikar jikin Laylerh’n mimmik’ewa, saboda hakan da yayi mata d’in yazo mata amatuk’ar bazata, saidai kuma ayau d’in ko kad’an
bataji haushinsa dan yayi mata hakan ba, hasali kuma batayi yunk’urin k’wace bakinta daga nasa ba.
Shikuwa Najeeb ganin hakanne yasashi sake kamo lips d’inta ya tsotsa, batare kuma daya tsawaita hakan ba ya zare bakinsa daga nata, sakamakon sanin abunda z
ai biyo baya da yayi, yasan ba bashi kanta zatayi ba, saidai ta barshi da azababben ciwon mara, gashi kuma lokacin Sallah yayi har ansoma k’iraye k’irayen sallan magriba.
Janye jikinsa yayi ahankali tare dasa hannu ya shafi gefen fuskarta, cikin kulawa ya
ce.
“Kishirya idan nadawo daga sallah sai muje kisha ice cream.
‿
Batare kuma da ya jira amsar da zata bashi ba ya wuce toilet, minti kad’an ya fito da alwalansa ya wuce masallaci.
Itakuwa Laylerh duk da cewar batajin k’warin jikinta haka ta sauk’o daga
kan gadon itama ta wuce toilet, sama sama tayi wanka da ruwa me d’an d’umi, bayan ta fitone kuma ta shirya kanta cikin wata simple Dubai Abaya me ratsin gold da ash sosae kuwa kayan yayi mata kyau.
Tana kammala sa kayannata kuwa Najeeb d’in ya dawo, ganin
kuma yanda tayi kyau sosae ne yasashi kama hannunta suka fice daga cikin d’akin.
Direct compound d’in gidan inda motarsa ke fake suka nufa, koda suka k’arasa shida kansa ya bud’e mata murfin motar b’angaren me zaman banza ta shiga, saida kuma yaga ta zau
na kafun ya zagaya ya shiga b’angaren driver, anutse ya tada motar mai gadi ya wangale musu gate d’in gidan suka fice.
Har tafiyar tasu kuwa tayi nisa babu wanda yace da d’an uwansa k’ala, domin kowannensu da abunda yake sak’awa acikin ransa, ahaka har su
ka iso Shoprite.
Atare suka shiga cikin shoprite d’in inda ya bata daman d’aukan duk abunda takeso.
Kasancewarta ma’abociyar son zak’i ne kuma yasa ta d’aukan dangin chocolates da sauransu.
Shikuwa abubuwan da yasan zai buk’ata ya saya sannan suka fito
daga cikin shoprite d’in.
Kaitsaye hanyar dawowa gida suka nufa, yayinda tun acikin motar kuwa Laylerh ta shanye roba d’aya na Ice cream.
Koda suka dawo gida a fridge ta saka sauran ice cream d’innata, bayan ta rage kayan dake jikinta ne kuma ta hau kan
gado ta kwanta, saboda yanda takejin kanta agajiye ne kuma yasa tana kwanciya bacci ya d’auketa.
Najeeb kuwa ganin da yayi tayi bacci ne yasashi zuwa bayanta ya kwanta, ahankali yake wasa da dogon gashin kanta har bacci ya d’aukesa shima.
2:30 am
Mat
sanancin gumi ne ke ketowa daga kowani sashi na jikinta, yayinda kuma alokaci d’aya duk gaba d’aya jikinta ya d’auki rawa, cikin matsanancin firgita had’i da razana tafasa wani irin k’ara me tada hankali wanda kuma acikin sautin k’aran nata ta ambaci sunan
MALEEK da wata irin murya, wanda hakan yasa Najeeb dake kwance tashi arud’e, daidai lokacin kuwa itama ta tashi azabure daga baccin da takeyi cikin kid’ima da tashin hankali marar misaltuwa.
*1February/2021*
8:00 pm
2/4/21, 8:44 AM - Ummi Tandama:
*LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*Chapter 47*
“LAYLERH!
‿
Najeeb wanda gaba d’aya k’ara da kuma sautin ihun nata yasa shi tashi afirgice ya k’ira sunanta cikin yanayin d’an d’aga murya tare dasa hannunsa ya soma k’ok’arin kama nata ha
nnun.
Saidai kuma yanayin yanda gaba d’aya jikinta ke b’ari yasa shi kasa yin hakan, musamman da yaga ta dunk’ule hannayen nata waje d’aya, da d’an k’arfi take jijjiga kanta, yayinda lokaci d’aya hawaye suka shiga zirya akan fuskarta kaman an kunna famfo,
cikin yanayin tsoro da kuma firgicin da ta samu kanta tasoma k’ok’arin dirowa daga kan gadon.
Ganin haka yasa cikin sauri Najeeb ya rik’o hannunta, hankalinsa ad’an tashe yace.
“Lafiyanki k’alau kuwa Laylerh? What’s wrong with you?
‿
Yayi mata tambayar y
ana me d’an girgiza kafad’unta daya rik’esu da hannayensa.
Kai ta soma girgizawa tare da soma yunk’urin ya kice hannayensa dake kan kafad’anta, saboda a yanda yanayin nata yake ayanzu bazata iya ce masa komae ba.
Gane hakan da yayi da kuma fahimtar cewa
bata cikin hayyacinta, yasa shi matsowa kusa da ita ahankali, ya shiga shafa bayanta, cikin muryarsa me d’auke da yanayin kwantar mata da hankali yace.
“Please Laylerh ki nutsu kinji, ki dawo cikin hayyacinki, babu abunda zai sameki gani atare dake, kuma
bazan tab’a bari wani abu yazo ya cutar dake ba, kidawo hayyacinki kinji!!
‿
Ya k’are maganan yana me kamo hannayenta, da har yanzu suke b’ari.
Fuskarta ya k’urawa ido, saboda yanda yaga labb’an bakinta na motsawa duk da karkarwan da sukeyi da alama wani a
bu take son fad’a.
Tabbas kuwa abunda ta gani amafarkin nata takeson bayyanawa, saidai kuma hakanan taji harshenta yayi mata nauyi, da k’yar cikin wata irin murya me d’auke da shaking tace.
“Yah M.Jay ne, ina tunanin wani abu ya sameshi, wata mota ta bu
ge shi na gansa da jini ajikinsa, baya numfashi, komae nasa ya tsaya, wayyo Yah Najeeb dan Allah kabarni naje na dubashi, Inaso na gansa, Inaso naga ko yana lafiya, banason wani abu ya same sa banasoo!!!!
‿
Ta k’are maganan nata cikin wani irin matsanancin
kuka, me tada hankali da kuma bayyanar da gaskiyar abunda ke cikin zuciyarta.
Idanu Najeeb d’in ya zuba mata cike da mamakin jin abubuwan da take fad’a.
“Anya kuwa Laylerh bata da aljanu?
‿
Yayiwa kansa tambayar da dagashi sai zuciyarsa da ta sak’a masa
hakanne suka sani, azahirance kuwa wata irin sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e, ganin yanda Laylerh’n ke kuka sosaine kuma yasashi jawota jikinsa, inda ya d’aura kanta akan faffad’an chest d’insa, tabbas kalaman da ta fad’a akan Maleek d’in ya daki zuciya
rsa, wanda hakan yasa yaji wani abu me kama da kishi, take ya wanzu acikin ransa, saidai kuma amma ko kad’an bayason yanda Laylerhn ke nuna damuwa akan d’an uwannata yake damunsa, har yakai ga ya haifar masa da mummunan zargi acikin zuciyarsa, duk da cewar
kuwa yana iyaka bakin k’ok’arinsa wajen gujewa zargin hakan, amma kuma yasan wani lokaci zuciya bata da k’ashi, komae yazo cikinta turawa k’wak’walwa take.
K’ok’arin sha re gurb’ataccen tunanin dake cikin ransa yayi, ahankali cikin sassanyar murya yace.
“Babu abunda ya samu Maleek Laylerh, saboda haka ki daina kuka, ko kin manta cewa da yawan mafarki ba gaskiya bane? ba lallaine abunda kika gani amafarki ya zama gaske ba, haka ko anan gaba ba lallaine hakan ya faru ba, da yawan mafarki baya tab’a zama ga
skiya, ki kwantar da hankalinki kinji nasan Maleek yana lafiya!
‿
Ya k’are maganan yana me d’an shafa bayanta da hannunsa.
Kanta tad’an girgiza, still cikin muryan sheshshek’a tace.
“Inajin tsoron kada wani abu ya faru da shi, nagani dagaske, naga wata m
ota ta bugeshi, nasan mafarki ba gaskiya bane, amma wannan mafarkin inajin tsoro kada......
‿
“Shiii!!! kiyi shiru babu abunda zae faru, ki sakeyin addu’a ki koma ki kwanta kinji.
‿
Ya fad’i hakan ta hanyar katseta daga maganan da takeyi, domin sam bayason
koda jin ta ambaci sunan Maleek d’inne, saboda fad’an hakan da kuma nuna damuwarta akan Maleek d’in, yana sawa yaji k’unci acikin zuciyarsa.
Jin abunda ya fad’a yasa ta d’ago kai da idanunta wanda suka cika tab da k’walla ta kalleshi, cikin yanayinta na
abun tausayi da kuma kukan dake cinta ta bud’e baki da niyar sake yi masa wani magiya akan yabarta taje wajen Maleek d’in.
Cikin cracking voice tace.
“Dan Allah....
‿
Saurin sa hannunsa yayi ya toshe mata baki, tunkafun ma ta ida fad’an abunda zata fad’
a d’in, lokaci d’aya kuma yanayin fuskarsa ya sanja, sake ta yayi tare da sauk’owa daga kan gadon, direct wajen k’ofar d’akin ya nufa, batare da tunanin komae ba kuwa ya murzawa k’ofar key, sanin kuma dayayi cewa idan yabar key d’in ajiki zata iya bud’ewa
ta fitane yasashi zare key d’in ya rik’e a hannunsa, dawowa kan gadon yayi ya kwanta, irin kwanciyar nan ta rub da ciki, tare da rumtse idanunsa.
Laylerh kuwa ganin abunda yayi d’inne yasa ta k’ara sautin kukanta, had’e da matsawa can gefe ta takure jikin
ta waje d’aya, da iya k’arfinta ta shiga rera masa kukan da gaba d’aya yaso haukata masa tunani.
Adaidai lokacin kuwa ya bud’e idanunsa wanda suka kwashe tsawo awanni suna rufe, ahankali ya d’an yunk’ura ya tashi zaune daga kwancen da yake, cikin wani i
rin sabon yanayin daya samu kansa aciki yasa hannu ya dafe daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da k’arfi.
D’an cije labb’an bakinsa yayi, domin kuwa ayanayi guda d’ayane yakejin irin wannan bugun zuciyar, shine idan yakasance Laylerh na cikin damuwa, ko k
uma idan yaji sautin kukanta, tabbas hakan yakansa yasamu kansa cikin bugun zuciya, ko yana kusa ko baya kusa kuwa idan Ayshnoor d’insa na cikin damuwa yakanji yanayinsa ya sauya.
“Acikin wannan daren me yake damun Laylerh?
‿
Zuciyarsa tayi masa tambayar
da Allah Ne kad’ai masanin amsarta.
Idanunsa yakai kan agogon dake aje gefen gadon.
3:00 am daidai idanunsa suka nuna masa, hakanne kuwa yasashi soma yunk’urin sauk’owa daga kan gadon, ahankali ya aje k’afafunsa ak’asa, koda yazo mik’ewa tsaye kuwa saida
ya rumtse idanunsa kafun ya iya mik’ewa, domin kwana biyunnan duk bayajin dad’in jikinsa, ko abinci baya ci daga drinks sai tea kawai yake iya sha, baya fita ko ina daga d’aki sae falo, daga gefe guda kuwa ya kashe gaba d’aya wayoyinsa, yayi hakanne kuma
gudun kada su Abbou Jaheed su sake tunkararsa da maganan jarababben auren da suke son lik’a masa.
Addaddafe ya k’arasa toilet, duk da cewar kuwa ana d’an sanyi hakan bai hanashi sakarwa kansa ruwan shower me sanyi ba.
Ak’alla kuwa sama da 20minute ya d’a
uka ruwan na dukan jikinsa, har saida ya d’anji zuciyarsa ta samu relief kafun ya kashe shower’n kana ya d’auro alwala.
Bayan yafito daga toilet d’in kuwa wata navy blue jallabiya yasaka ajikinsa, tare da shumfud’a sallaya ya tada sallah, domin so yake ya
rok’i Allah Ko hakan zaesa ya samu sassaucin abunda ke azalzalan zuciyarsa babu dare ba rana.
Acan B’angaren su Najeeb kuwa, tsawon mintuna 20 Laylerh ta kwashe tana ta faman aikin kuka, tabbas ada yaso yin k’ok’arin jure kukannata saidai kuma jin yand
a take k’ok’arin shid’ewa ya sashi kasa jure hakan.
Ahankali cikin sanyin da zuciyarsa tayi ya juyo da kallonsa zuwa gareta.
“Laylerh!
‿
Yak’ira sunanta cikin sassanyar murya me d’auke da rarrashi.
Laylerh kuwa duk da cewar tajisa amma haka ta cigaba da
kukanta, me d’auke da abubuwa da dama, shagwab’a, sakalci, da kuma tsoron faruwar abunda tayi mafarki akai d’in, saboda ba yanzune karo na farko da take mafarkin Maleek d’in acikin mawuyacin hali ba, ay’an kwanakinnan acikin mafarkinta duk haka take ganin
sa acikin damuwa.
Najeeb ko ganin da yayi bata kulasa bane yasa shi tashi zaune, asanyaye ya matso kusa da ita, cikin murya me kama da rad’a yace.
“Am very sorry My Wife, am so sorry kiyi hak’uri kinji, kuma kiyarda cewa Maleek yana nan lafiya, sannan ba
n hanaki zuwa wajensa haka kawae ba, yanzu fa tsakiyar dare ne, ke kanki idan zakiyi tunani baidace ace kinje wajensa awannan talatainin daren ba, amma I promise you gobe da safe zakije ki dubasa, but nasamma yana lafiya, amma kiyi hakuri kinji, kizo mukwa
nta, banason jin kukanki ko kad’an.
‿
Ya fad’i maganar yana me kamo hannayenta duka biyu, ya jawota jikinsa, ahankali ya shiga share mata hawayen da duk suka mata dama dama da fuska.
Ko kad’an kuwa batayi yunk’urin hanasa ba domin dama kukan da tayin yasa
mata wani irin fitinannen ciwon kae.
Kwanciya tayi akan gadon tare da juya masa baya, ahankali take sakin sheshshek’an kukan da ya zame mata dole.
Cike da tsoro da kuma fargaban abunda kunnuwanta zasu jiye mata gobe bacci yasake d’aukarta.
Jin yanda ta
ke ta faman sauk’e ajiyar zuciya ne, yasa Najeeb matsowa kusa da ita sosae tare da jan blanket ya rufa musu.
Da tunani kala kala acikin ransa shima bacci ya d’aukesa.
Washegari.
Tunda ta tashi tayi sallan asuba bata sake komawa bacci ba, sakamakon yan
da takejin matsanancin fad’uwar gaba da kuma tsinkewar zuciya na ziyartarta, ahaka dae ta daure zuciyarta, har zuwa k’arfe bakwai kafun ta shirya kanta cikin wata atamfar chiighanvy me ratsin green, wacce akayi d’inkin pencil sket da kuma riga fitted sosae
atamfar ta karb’i jikinta yayinda, kuma had’add’en d’inkin ya lafe ajikinta, duk da kuwa cewar kwana biyun ta d’anyi rama amma hakan baisa cikakkun hips d’inta komawa ba.
Batayi wani kwalliya sosae afuskarta ba, wani siririn vail me showing ta yafa ajik
inta, tare da zura wasu flat shoe marassa nauyi, cikin yanayin zak’uwa ta fice daga cikin d’akin, anan falo ta samu Najeeb yana aikin danna laptop d’insa, k’arasowa tayi asanyaye ta gaisheshi.
Fuska asake ya amsa yana me k’arewa had’add’iyar surar jikinta
kallo, hakanan tunda yaga tayi sallah yaudin yakejin kansa acikin nishad’i.
Batare da ta tsaya jira ko sauraransa ba kuwa kaitsaye ta fice daga cikin falon, shikuwa da kallo ya bita har ta b’acewa ganinsa.
Kaitsaye part d’in su Abbou Jaheed ta nufa, kod
a ta k’arasa kuwa acan ta iskesu dukansu zaune akan dining table.
Saidai rashin ganin Maleek awajen ya sake haifar mata da fad’uwar gaba.
Haka dae ta k’araso jiki asanyaye ta zauna tare da gaidasu duka, dukansu fuska asake suka amsa mata, saidai banda Mo
my wanda ita fuskartata ko alaman annuri ma babu akanta.
Bayan ta zauna akan d’aya daga cikin kujerun wajenne kuma tayi saving kanta.
Duk da cewar batajin yunwa sosae amma haka ta soma tsakalan abincin, yayinda ta maida gaba d’aya hankalinta ga k’ofar d’
akin Maleek d’in, burinta ayanzu baiwuce taga ya bud’e k’ofar d’akin ya fito.
After 20minue.
Rai adagule Abbou Jaheed ya ajiye wayar dake hannunsa tare dajan d’an guntun tsaki.
Hakanne kuwa yasa Abbou Kareem ya d’ago kae ya kalleshi, ganin kuma ran Ab
bou Jaheed d’in ab’ace ne yasashi d’anyin gyaran murya, cikin kulawa yace.
“Lafiya kuwa naga yau duk ranka ajagule?.
‿
Cikin d’an yanayin takaici Abbou Jaheed yagirgiza kansa, domin kuwa duk yanda yaso shanye b’acin ransa abun