Showing 171001 words to 174000 words out of 244674 words

Chapter 58 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

ce mata komae ba yasakai ya shige cikin falon, aransa yana

me tabbatarwa da kansa cewar koda ga salon maganarta kad’ai dole ta jawo hankalin d’a Namiji, ballantana kuma idan aka tafi ga tsarin halittarta, tana da wani irin body structure mai kyau da d’aukar hankali, wanda ba iya Namiji d’aya ba, maza da yawa idan

suka ganta to fa lallai zasu haukace akanta, duk da kuwa cewar bata da yawan shekaru sosae amma kuma ayanzu duk wani cikar halittar y’a mace ya bayyana ajikinta, tabbas Laylerh’n ta cika macen da dole soyayyarta bazatayiwa zuciyar da ta kama da sauk’i ba.

Saurin kauda tunanin dake zuciyarsa yayi tare da fad’in. “Astaghfirullah!

‿

domin yasan ita d’in matar wanice, haka kuma fasalta yanayin tsarin halittarta sam ba daidai bane.

K’arasowa gaban Maleek d’in da har yanzu idanunsa ke kan k’ofar falon yayi,

mik’a masa laptop d’in yayi tare da neman waje ya zauna.

Daidai lokacin kuwa ta sako k’afarta cikin falon, cikin kuma yanayin sanyin da ayanzu yake neman zame mata jiki ta ke tafiya ahankali, yayinda kanta ke k’asa tana me aikin mummurza y’an yatsun ha

nnunta.

Hakika shigowanta cikin falon shiya sanya zuciyarsa tsananta bugawa, yayinda yasakejin komai nasa ya zama very weak, ahankali ya sauk’e idanunsa akan kyakkyawar fuskarta, wanda kuma hakanne ya tilasta masa d’an lumshe idanunsa, saboda yanda yaji

wani irin sanyi na ratsa cikin jiki da b’argonsa.

Ita kuwa Laylerh duk da cewar bata d’aga kanta ta kallesa ba, amma hakanan taji ajikinta cewar idanunsa na yawo akanta, hakanne kuwa yasa takejin kamar k’afafunta zasu hard’eta ta fad’i.

Ta bayan wasu

had’add’un Royal Gothic Chairs dake cikin falon tab’i tare da k’arasawa inda ta zauna d’azun, cikin sa’a kuwa tana isa wajen taga wayartata aje akan sofa, d’aukan wayar tayi tare da juyawa cikin yanayi na d’an sauri ta soma tafiya don barin cikin falon, wa

nda tun shigowarta cikinsa heart d’inta ke abnormal beating, duk yanda idanunta ke so da mararin ganinsa kuwa ta kasa iya d’aga kai ta kallesa, Sam batasan meyasa yau d’in takejin hakan akansa ba, duk da cewar sometimes takanji hot feelings akansa, amma fe

eling dinta na yau akansa da banne, wannan dalilinne ma yasa take sauri wajen ganin tabar cikin falon.

Agarin saurinnata ne kuma batare da ta lura ba adon dake jikin d’aya daga cikin Gothic chairs din ya kama k’asan skirt d’inta, wanda bisa dole hakan ya

tilasta mata tsayawa.

Asanyaye ta b’ata fuska ganin da tayi cewar dole saita tsugunna kafun ta iya cire k’asan skirt dinnata daga jikin abun.

Kyawawan fararen k’afafunta da suka bayyana saboda d’an d’agewa da skirt dinnata yayi ya zubawa idanu, tare da

maida hankalinsa ga kallon kyakkyawan red anklet chain d’in dake sak’ale a k’afarta na dama, sosai anklet d’in ya karb’i fatar nata kasancewar sa red colour mai adon white stones.

Kallon k’afafunnata yake da kyau baya ko k’yaftawa yayinda kuma sannu aha

nkali yakejin zuciyarsa nayi masa sanyi.

B’angarenta kuwa hardai yanzun tanajin idanunsa na yawo akanta, wanda kuma hakanne yasa ahanzarce ta janye skirt d’inta, cikin sauri sauri ta fice daga cikin falon, domin tayi imani cewa matuk’ar ta k’ara mintuna

4 masu kyau acikin falon to fa lallai bazata iya controling kai da kuma abunda ke cikin zuciyarta ba.

Da rikitattun idanunsa ya bita harta fice daga cikin d’akin kuwa bai d’auke idanunsa daga kallon hanyar da tabi ta fita d’inba.

Fou’ad da tun shigow

ar Laylerh’n ya zubawa Maleek d’in idanu, gyara zamansa yayi tare da d’an kawar dakansa gefe cikin d’an d’aga murya ta yanda yasan Maleek d’in zai iya jiyosa yace.

“Mutum dai yaci gaba da d’ibawa kansa zunubi ta hanyar yiwa abunda ba mallakinsa ba kallon

k’urulla kallon haram.

‿



Jin abunda Fou’ad d’in ya fad’ane yasashi juyo da kansa, ya fuskanci Fou’ad d’in wanda yayi kamar ba daga bakinsa maganar da yayi yanzun ta fito ba.

Sam shikam Allah Ma yasani ayanzu bayida lokacin biyewa Fou’ad, saboda ya fuska

nci cewar sai mutum nada lafiyane ma yake wani abun.

Shigowar Oum Ayush cikin falon ne kuma hannunta d’auke da d’an madaidaicin tray, yasa shi maida kallonsa gareta, saboda tsabar yunwan da yakeji har wani irin jiri ne ke damunsa, yana kuma kyautata za

ton cewa cikin magungunan da Dr.Mouhammad ya basa akwai wanda yakesa cin abinci sosae.

A gabansa Oum Ayush ta ajiye madaidaicin tray d’in wanda samansa ke d’auke da plate d’in southern baked BBQ chicken da kuma d’an k’aramin glass bowl wanda ta zuba yan

kakken fruit salad mai sanyi aciki.



“Bismillah!.

‿

Tafad’a adaidai lokacin da take tura masa plate d’in gabansa.

Kasancewar kuma dama yunwa yakeji sosai hakan yasa baijirayi komae ba, cike da nutsuwa ya fara cin abincin, yayinda kuma time

to time y

ake d’an lumshe kyawawan idanunsa masu d’auke da gajiya da kuma yanayin bacci.

Oum Ayush kuwa hira suke d’anyi kad’an kad’an da Fou’ad wanda yace shi bazaici abincin ba.

B’angaren Laylerh kuwa tana fitowa daga falon kai tsaye part dinsu ta nufa, koda

ta k’arasa sashin nasu bata samu Najeeb ba, wanda kuma da ‘alama baya gidanne ma baki d’aya.

Anan kan d’aya daga cikin kujerun falon ta kwanta, tare da d’aukan trow pillow ta rungume ak’irjinta, ahankali haka takejin bugun zuciyarta na lafawa, yayinda kum

a nutsuwarta ke dawowa jikinta.

Saidai kuma har zuwa yanzun brain d’inta ta kasa daina maimaita mata kalmar da Abbou Jaheed ya fad’a cewar. “Doctors sunce Maleek bazae tab’a haihuwa ba!

‿

K’warai sosai maganar ta daki zuciyarta, tare kuma da wujijjiga tu

naninta.

Ita da kanta take tambayar kanta dalilin shigowar wannan mummunar k’addarar cikin rayuwarsu.

“Shikenan Maleek bazai samu mai sakashi farinciki ba? bazae tab’a haihuwa ba hakan kuma na nufin har abada kenan? Shin tayaya zai iya jurewa wannan k’u

nci da kuma ciwon?

‿

“Lallaine kowani bawa da irin salon k’addararsa arayuwa, amma kuma ta Yah M.Jay ta kasance mai muni da kuma cutarwa, yah Allah Kabashi iko da kuma k’arfin jure duk way’annan damuwowin!!

‿

Tafad’i hakan abayyane cikin wata raunanniyar m

urya, wanda kuma hakanne ya bayyana zuban hawaye akan kyakkyawar fuskarta.

Tabbas tasan cewa ayanzu idan tace zatayi wani tunani ko kuka zuciyarta na iya bugawa, Hutu kawai takeson saboda har yanzu tana d’anjin ciwon kai kad’an kad’an.

Wayarta dake hann

unta ta kunna tare da soma duba sak’onnin da aka turo mata, wanda cikinsu kuma harda sak’on komawarta makaranta da kuma na WAEC examination d’in da zasuyi nan da 2week.

Haka dae ta d’an duba sak’on da akayi mata d’in sama sama nanma saboda gudun kada tayi

tunani mai zurfine shiyasa, tana cikin shafa wayar nata kuwa bacci b’arawo ya d’auketa.

Acan falon Abbou Jaheed kuwa a sosae Maleek yaci abincin da a Oum Ayush d’in ta kawo masa, duk da cewar kuwa bai cinye abinci da kuma fruit salad d’in duka ba amma

yaci sosae.

Yana kammala cin abincin kuwa ya mik’e tsaye, da yake kuma y’an miskilancinnasa na kusa baice da su Oum Ayush d’in komae ba yasa kai ya fice daga cikin falon.

Kaitsaye sashinsa ya nufa, daga cikin tangamemen falonnasa kuwa direct bedroom d’in

sa ya shige.

Kayan dake jikinsa ya d’an rage tare da kutsawa cikin bathroom d’insa yayi wanka.

Bayan ya fito awankanne kuma yasaka wasu sauk’ak’akk’un riga da wando, wanda yasan cewa bazasu ta kurasaba.

Magungunansa yasha tare da hayewa saman makeken ga

donsa ya kwanta.

Lokaci d’aya kuwa wasu irin tunani suka shiga yawo acikin k’wak’walwarsa, wanda asanadinsu ne kuma yaji zuciyarsa tayi matuk’ar karyewa, saidai kuma a irin yanayin da yakejin kansa ayanzu yasan matuk’ar ya biyewa damuwar dake sukar zuciya

rsa, to bai wuce wata sabuwar matsala ta sameshi.

Sanin hakan da yayine kuma yasa lokaci d’aya yasoma k’ok’arin zeroying mind d’insa.

Kyawawan idanunsa masu d’auke da abubuwa kala kala ya lumshe, tare kuma da soma fitar da wani irin breath mai sanyi.

Ci

kin abunda bai wuce 20minutes ba kuwa wani irin nannauyan bacci ya d’aukesa, wanda kuma dama hakan shine burinsa.

Tunda ya fara baccin nasa kuwa bashine ya farkaba sai kusan magriba, haka yakejin jikinnasa gaba d’aya ba k’wari, toilet ya shiga ya d’auro

alwala bayan ya fito daga toilet d’inne kuma kai tsaye ya wuce masallaci.

Anan cikin masallacin dake jikin gidansu yayi sallan Magrib, yana kuma zaune acikin masallacin har aka k’ira sallan Isha, bayan ansallame sallan Isha d’inne kuma ya dawo gida, aga

in kuma wani baccin yakeji sosai, haka dolensa yasake komawa ya kwanta.

Awani k’arin abun mamakin kuwa shine daga shi har Laylerh yau d’in haka suka kasance kamar wasu bugaggu, domin ita d’inma bacci tayi sosai sallah ne kawae ke ta da ita, yanzun ma

koda Najeeb ya dawo akan gado ya sameta, tana ta faman aikin bacci, saidai kuma kasancewar shid’in baya cikin mood maidad’i hakan yasa bai ta she ta ba, koda ya gama abunda zaiyi rab’awa yayi ya kwanta agefenta, yayinda yakejin k’irji da kuma zuciyarsa n

ayi masa wani irin k’una da kuma tarin rad’ad’i, aduk lokacin kuwa da zuciyarsa ta hasko masa abunda idanuwansa suka gane masa yau d’in sai yaji wani irin haushi, takaici, da kuma tsanar kanshi ya rufesa.

Haka dai zuciyarsa cike da tunani kala kala bacci

ya d’aukesa.

*Washegari*

8:30 am

Wani irin juyi mai d’auke da alaman gajiya da kwanciyar nata tayi, kana ahankali ta soma ware kyawawan idanunta wanda suka d’auki kusan awa uku akulle, domin kuwa tunda tayi sallan asuba ta sake komawa sabon baccin

da sai yanzu ta farka.

Tashi zaune tayi tare kuma da soma k’arewa cikin d’akin kallo, daidai lokacin kuwa wayarta dake aje akan bedside drawer ta soma fidda sassanyar wak’an Ali Gatie na (Running On My Mind) wacce ita ta kasance ringintone d’inta, sabod

a tana matuk’ar son wak’ar sosae.

Akasalance ta kai dubanta ga wayar, ganin kuma cewa sunan Oum Ayush ne ke yawo akan screen d’in wayar, yasa cikin sauri tasa hannu ta d’auki wayartata tare kuma da picking call d’in.

Oum Ayush dake kan layi kuwa jin

Laylerh ta d’auki wayarne yasa batare da ta tsaya jin ta bakin Laylerh’n ba tace.

“Baccin ya isa haka, yanzu yanzu kizo dining area muyi breakfast.

‿



“To.

‿

Kawae tace asanyaye, Oum Ayush kuwa take ta kashe wayar.

Ahankali ta zuro da kyawawan k’affu

nta k’asa, had’i da mik’ewa tsaye, y’ar ficikar rigar baccin dake jikinta ta kalla, wanda ita kanta ma batasan ya akayi ta saka ta ba, saboda tsabar baccin dake damunta jiyan.

Kaitsaye toilet ta wuce danyin wanka, sanin da tayi kuma cewa su Oum Ayush n

a jiranta ne yasa bata wani b’ata lokaci awajen wankan nata ba.

Bayan ta fito daga wankanne kuma ta tsane jikinta, tare da zama agaban dressing mirror ta shafawa jikinta mai, kamar kullum kuma iya powder,mascara da kuma kwalli kawae ta shafa, sai wani b

rown lips gloss da ta shafawa jajayen labb’anta, hakanne kuwa yasa lips d’innata ya fito da kala maikyau.

Turaren oud ta shafa had’e da d’aukan wata doguwar rigar English wears mai kalan brown ta sanya ajikinta, kasancewar kuma rigar irin pencil gown d

’innanne maibin jiki, hakan yasa ta d’aura wani light brown denim jacket akan shigartata, sosai kuwa hakan ya k’ara bayyana yalwataccen kyawun da tayi.

K’aton agogon dake cikin d’akin ta kalla, take kuwa idanunta suka gane mata lokaci 8:55 am daidai.

Agurguje ta nannad’e dogon gashinta, tare kuma dasaka wani hulan turban mai kalan brown akanta.

Light brown shoes masu gashin kuliya tasaka ak’afanta, kana tasa hannu ta d’auki wayarta dake aje akan mirror.

Cikin sauri haka ta fice daga cikin d’aki

n.

Koda ta fito compound d’in gidan kaitsaye part d’in Momy ta nufa domin kuwa acan sukeyin breakfast.

Gaba d’ayansu zaune suke akan babban dining table d’in ciki kuwa harda Najeeb wanda sama da mintuna 15 kenan da zuwansa wajen amma yakasa kai koda

loman abincine bakinsa.

Kamar kuma yanda suka hallara awajen cin abincin haka shima ya hallara, yayinda yayi wani irin kyau cikin shigar armany jeans da kuma crazy shirt d’in dake jikinsa.

Tabbas kallo d’aya zaka mishi ka fahimci cewar akwai sanjin y

anayi atare dashi, saidai kuma amma yakasa bari idanunsa su nuna hakan.

Sab’anin mahaifinsa wanda tun zamansa awajen ya fahimci cewar Abboun nasa na d’auke da damuwa acikin zuciyarsa domin ya lura lokuta zuwa lokuta Abbou Jaheed d’in ke satan kallonsa,

duk da kuwa baisan meyene azuciyar Abboun nasa ba, amma zuciyarsa ta fad’a masa cewa bawai abubane mai dad’i.

Ahankali yake d’an jujjuya tea spoon d’in dake hannunsa, daga gefe guda kuwa baked mozzarella stick d’in dake gabansa ya zubawa ido, duk da c

ewar kuma ya d’anyi nisa atunaninsa amma hakan baihanashi ji ajikinsa cewar Laylerh’n ta shigo cikin falon ba.

Wani sassanyar k’amshin daya daki hancinsane kuma ya sake tabbatarwa da kansa cewar Lallai ita d’ince, domin awajenta kad’ai yakejin irin k’amsh

in.

Ita kuwa Laylerh ganinsu duka akan dining area d’inne yasa anutse ta k’araso wajen. Bayan ta gaishe dasu Abbou Jaheed ne kuma anutse taja kujeran dake kusa da Najeeb ta zauna.

Wanda kuma hakan yasa ya zamana ita dashi suna facing juna.

K’as

a k’asa batare kuma da ta bari idanunta sun sauk’a akansa ba, cikin shaking voice d’inta tace.

“Good morning Yah M.Jay....

‿

Shiru yayi kamar baijita ba, sannan bai kuma d’ago kansa ya kalleta ba, still tea spoon d’in dake hannunsa yake ta faman juyaw

a.

Laylerh kuwa jin bai amsa mata bane yasa ta lumshe idanunta wanda lokaci d’aya suka ciko da hawaye, Sam batasan meyasa wani lokaci idan ta gaishesa baya amsawa ba, bayan kuma yasan tasan cewar yanajinta.

“Why?

‿

Ta tambayi kanta.

“Saboda yasa

n ke mairaunice akansa.

‿

Wani b’angare na zuciyarta ya bata amsar hakan.

Fuskarta ta d’an shagwab’e, saboda sam bataji ta gamsu da hakan ba.

“Good morning!

‿

Najeeb dake gefenta ya fad’a k’asa k’asa, adaidai lokacin da yake turo mata plate d’in dak

e gabansa, wanda samansa ke d’auke da chips and ketchup, sai kuma wani d’an bowl wanda aka zuba perfect vanilla soufflé aciki.

Wani irin kunyansane ya kamata dan sai alokacinne ma take tunawa cewar sam basu gaisaba lokacin da ta tashi sallan asuba baya

nan yana masallaci.

D’an sunkuyar da kanta k’asa tayi, kana asanyaye tace.

“I’m sorry morning Yah Najeeb.

‿



Murmushin daya bayyana kyawun fuskarsa yayi batare kuma daya ce mata komae ba ya kawar da kansa gefe.

Ganin hakanne kuma yasa jiki

amace ta soma cin abincin daya turo mata d’in.

Almost 20minutes kenan yanzu da kowa yake ta hidimansa akan dining table d’in.

Ahankali Abbou Jaheed ya d’ago ya kallesu bayan kuma ya kammala goge bakinsa da tissue paper ne, yayi gyaran muryar dayas

a dukanninsu d’agowa suka kalleshi, saidai banda M.Jay wanda tun d’azu yake ta abu d’aya kaman statue.

Abbou Jaheed kuwa d’an satan kallon gefen da Maleek d’in ke zaune yayi, kana cikin tausasa murya yace.

“Kuyi hak’uri da abunda za kuji daga bakina

, domin kamar yanda na had’aku jiya na sanar daku matsalan da tasamu Maleek, haka yau ma nake mai bak’in cikin sake sanardaku wata magana wanda nasan bazata tab’a yi muku dad’i ba.

‿

Tsagaitawa da maganan nasa yayi tare da kallon Maleek wanda har yanzu k

ansa ke k’asa.

Anutse cikin kuma yanayin tausayawa yace.

“Bazan tab’a gajiyawa da baka hak’uri ba Maleek, nasan cewa kanajin ciwo da kuna acikin zuciyarka, amatsayina na mahaifinka kuwa ba zanso duk wani abu dazai cutar dakai ba, amma kasani bani da

wani zab’i ayanzu wanda ya wuce fad’a maka gaskiya, domin kuwa Tabbas abune da yake abayyane, cewar ba kowacce mace ko iyaye bane ke barin y’ay’ansu su auri wani Namji ko Mace wanda bazasu tab’a haihuwa ba, hak’ik’a kowa yana da irin k’addararsa amma kasa

ni wannan k’addarar k’addarace mai ciwo, domin kuwa asanadin ta jiya da dare Alhaji Farouk ya k’ira ya sanar dani cewa, Matarsa ta shaida cewar maganar aure tsakaninka da y’arsu Munnira babu ita, Tabbas Nikam na fahimcesa domin da ace asonshine zai iya ba

ka auren y’arsa, saidai kuma amma ita kanta uwar yarinyar tana

da nata hakk’in, shin ayanzu a kuma irin zamaninnan wace y’a mace ko kuma iyayene kake ganin zasu baka y’arsu ka aura bayan kana tare da wannan lalurar? k’addarama ace zaka samu hakan to bai za

ma lallai ya zamana son gaskiya ake maka ba, watak’ila zata aurekane Dan dukiyarka, wata k’ila kuma zata aurekane Dan kyau da matsayinka, wata k’ila kuma zata aurekane Dan kawai tayi suna, wanda ni kuma Ina matuk’ar jin tsoron hakan Maleek inajin tsoron w

ani abu dazai sake samun rayuwarka, duk da cewar inaji ajikina cewar wannan k’addarar zata sama maka farinciki watarana!!!

‿

*(Team Maleek inakuke

🗣🗣🗣🗣🗣🗣

gobe zanyi Chapter 60, kuma kusani ga duk wani masoyin Maleek gobe ranarsace)*

*28/Februa

ry/2021*

*1:45 pm*

3/1/21, 8:56 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Not editing*

#divorce

💔

*CHAPTER 60*.

Tsagaitawa da maganan Abbou Jaheed yayi tare da d’ago kansa ya kalli Maleek d’in wanda har yanzu

bai d’ago kai ya kalli mahaifinansa ba, duk da kuwa cewar yaji batun fasa auren nasa.

Yayinda awajen su Abbou Khareem da kuma Oum Ayush abunda sukaji d’in ya kasance sab’anin tunaninsu, domin kuwa sam koda wasa basu tab’a kawowa aransu cewar wannan k’ad

darar takai matsayin da har za’ana hana Maleek d’in aure ba, wani irin sabon tausayinsa ne sukaji ya lullub’e musu zuciya, saboda sunsan dolene zaiji ba dad’i, hatta Oum Ayush da dama tuncan bawae zuciyarta ta aminta da auren Maleek

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login