Showing 135001 words to 138000 words out of 244674 words
k’ofar office d’innasa aka shigo.
Fou’ad wanda shin
e ya shigo cikin office d’in ganin yanda M.Jay d’in ke zaune ya rumtse idanunsa ne yasa shi d’an tsayawa tare da kafesa da idanu.
Ganin da yayi kuma kaman Maleek d’in baisan da zuwansa bane, ya sashi sauk’e wata irin ajiyar zuciya, ahankali kuma ya shiga
takowa zuwa tsakiyan office d’in.
D’aya daga cikin kujerun da aka tana da musamman dan zaman bak’i ya ja ya zauna, har zuwa lokacin kuwa Maleek bai bud’e idanunsa ya kalli Fou’ad d’in ba, duk da kuwa cewar ya ji shigowansa, k’amshin turaren D&G kuma da ya
ji ya shiga hancinsa ne ya sashi gane cewa Fou’ad d’inne ya shigo, saboda aduk mutanen dayasan zasu iya shigo masa office kai tsaye, Fou’ad ne kad’ai ya fiye amfani da turaren na kamfanin Dolce & Gabbana.
“Captain.
‿
Fou’ad ya k’ira sunansa cikin d’an d’
aga murya ta yanda zai jisa da kyau, saboda atunaninsa Maleek d’in yayi nisa ne acikin tunanin da yakeyi shiyasa baiji shigowarsa ba.
“M.Jay.
‿
Fou’ad ya sake k’iran sunansa akaro na biyu, tare da d’ansa hannu ya buga table d’in dake gaban Maleek d’in.
“
What?.
‿
Maleek d’in ya fad’a cikin cushewar murya, domin sam baiyi farinciki da zuwan Fou’ad d’in ba, because yasan zuwan Fou’ad d’in babu abunda zae k’ara masa sae yawan tension.
Fou’ad d’in kuwa jin abunda Maleek d’in ya fad’a ne yasa shi, d’age kafad’
ansa cikin yanayin mamaki yace.
“Dama kenan kanajina amma kashareni kayi kaman baka ji ba? anyway duk ma ba wannan ba, Ashe har babban abu me girma zai taso maka amma ka kasa fad’amin, atunani na dai baka da wani aboki aduniyarnan sama dani, meyasa ka b’o
yemin hakan?.
‿
Idanunsa wanda ke alumshe ya bud’e kana ahankali ya sauk’e su akan Fou’ad d’in dake zaune facing d’insa.
Hannunsa yasa ya d’an shafi gefen fuskarsa, inda lafiyayyen sajen daya k’arawa fuskartasa kyau ke kwance lub.
“Me na b’oye ma?
‿
Ya fa
d’a cikin muryarsa dake bayyana zallan miskilancinsa, wanda kuma da alama yau miskilancinnasa ne ya motsa fiye dana kullum.
“Abubuwa da yawa ciki kuwa harda maganan aurenka da Munnira y’ar gidan Alhaji Farouk, na tabbatar da ace Abbou Jaheed bai k’irani y
a fad’amin akan mufara shirye shirye da wuri ba da bazaka tab’a fad’amin ba, why Maleek meyasa kake shashantar da duk wani abu naka me mahimmanci ne?
‿
Cewar Fou’ad da ya tsaresa da idanu.
“Abu me mahimmanci? meye shi? Aure shine abu me mahimmanci? Hmmm.
‿
Idanunsa ya d’an lumshe tare dasa teeth d’insa ya ciji jajayen labb’ansa, cikin wata irin murya dake bayyana gaskiya da kuma zallan abunda ke cikin zuciyarsa yace.
“Ba yanzu ba ko agaba bana tunanin akwae wani abu me mahimmanci’n da zai sake tunkarar ra
yuwata, duk way’annan abubuwan sun isa Fou’ad nagaji da komai, ba kuma nason komai da kowa banason wata mace ta rab’eni domin ban tsarawa kaina rayuwa da wata ba, impact ma babu zanen k’addara da sunan wata mace daban acikin jinina, so please leave me alon
e banason sake jin wani zance na daban akan wata!!
‿
Yanayin yanda ya k’are maganar yana me dunk’ule hannayensa ne yasa Fou’ad sakin murmushi.
Cike da takaicin halin da M.Jay d’in ya jefa kansa aciki yace.
“Da kyau komae ka tsarawa rayuwarka daidai ne awa
jenka, bakason sake jin wani zance na daban akan wata, amma kana son sake jin wani zance akan matar da take mallakin wani, kana kuma da lokacin da zaka b’ata sama da awanni kana tunaninta, koda sau d’aya ne kuma baka tab’a tunanin yawan zunubin da kake kwa
sawa kanka bako? Good Maleek bazan hanaka gudanar da rayuwarka daidai da irin yanda kakeso ba, amma kasani amatsayina na abokinka dole ne na fad’a ma gaskiyar abunda ke akwae, koda kuwa hakan zaisa kaji ba dad’i, nasan cewa kanason Laylerh so kuma matsanan
ci, amma cire ta acikin zuciyarka shine abu me sauk’i, domin tariga ta haramta agareka karka manta ita fa ayanzu matar wani ce, kuma......”
‿
“Enough is enough Fou’ad, banason jin komae, domin babu wani abu da zaka fad’a wanda zaiyi tasiri acikin rai da zu
ciyata, saboda ba kasan menene SO ba, Fou’ad nayi imani cewa koda da second d’aya ne bakasan hak’ik’anin abunda nakeji acikin zuciyata ba, soyayyar zuciya kawae kasani bakasan ta jini ba, bakasan komae ba Fou’ad, ba kuma zaka tab’a sani ba, saboda nasan ba
bu wani wanda za’a k’ara halitta masa matsanancin so azuciyarsa kaman yanda aka halittamin na Laylerh acikin jiki da jinina, ka tashi kaje Fou’ad banason ganinka please!!
‿
Yafad’i hakan cikin wata irin raunannan zuciya, wanda kuma salo da yanayin maganar
tasa ta matuk’ar bayyana rauninsa, saboda hakan kuwa harsaida yasa hannu ya dafe daedae saitin zuciyarsa.
Fou’ad kam kasa koda motsa k’afarsa yayi saidai idanu kawae daya zubawa Maleek d’in.
K’warai yana mamakin irin sonda Maleek keyiwa Laylerh, soyayyar
da har rana me kaman ta yau yakasa furta mata, soyayyar da yakeyinta da gaba d’aya rayuwarsa, tabbas shikam baya fatan Allah Ya d’aura masa k’addaran so me tsananin zafi irin ta Maleek, domin kuwa rashin samun abunda kake so d’in ba k’aramin nakasar maka
da rayuwa zaiyi ba.
“Maleek!!!
‿
Fou’ad ya k’ira sunansa da wata irin sassanyar murya.
Bai d’ago kansa ba haka kuma bai amsawa Fou’ad d’inba, domin kwata kwata bayason jin kalaman Fou’ad d’inma acikin kunnuwansa, saboda yasan ba abunda Fou’ad d’in zai i
ya cemasa face ya cire son Laylerh azuciyarsa.
Soyayyar Laylerh azuciyarsa kuwa abune da har abada bazae tab’a fita ba, domin ayanzu soyayyar tata ce kad’ai ke rik’e dashi, rashinta rasa rayuwarsa ne gaba d’aya.
Fou’ad kuwa ko kad’an baidamu da rashin am
sawan Maleek d’in ba, domin yasan halin Maleek d’in sometimes ma baicika yawan son adameshi da magana ba, saboda kamar yanda yake bazai yiba haka ma bayaso amasa.
Saidai kuma ayanzu tunanin da zuciyarsa tayi masa ya sashi d’anjin sanyi acikin ransa, domin
yana ganin cewar idan Maleek d’in yayi aure komae zaizo da sauk’i, duk dama dae yasan cewa abune me wahala Maleek d’in ya iya jure kallon Munnira amatsayin mata, amma yasan yau da gobe k’addara zata sa ya k’arbi Munniran dan dolensa, ko ba komae kuma zata
d’an rage masa zafi.
Tabbas zuwan sa wajen Maleek d’in da yayi yanzu ya sashi fahimtar cewa Maleek bazae tab’a shigowa ayi sha’anin bikin auren tare dashi ba.
Wannan yasa shi yanke hukuncin cewa shi da kansa zai tsara duk wani abunda ya dace har zuwa lo
kacin bikin, zai kuma gayyaci iya mutanen daya sani, duk da cewar yasan zai buk’aci me tayasa, amma zaiyi iya nasa k’ok’arin shima, saboda daga shi sae SOORAJ ne Maleek d’in ya aminta dasu, saidai daga Maleek d’in har SOORAJ jirgi d’aya ne ya d’ebosu, afan
nin halayya kamar uwa d’aya uba d’aya suke, domin koda sun had’u kowannensu zai iya sha re 40 minute baice da d’an uwansa k’alaba, sunan kuma waisu manyan abokai, amma kuma magana wahala take basu, wannan yasa bazae ma nemi SOORAJ d’inba shikad’ai zai tsar
a komae.
Ahankali ya mik’e tsaye daga zaunen da yake, kallon Maleek d’in da har yanzu ke dafe da daidai saitin zuciyarsa yayi, kamar kuma zai ce dashi wani abu, amma sae ya fasa tare dajan bakinsa yayi shiru, kaitsaye kamar yanda Maleek d’in ya buk’ata ya
fice daga cikin office d’in da yake kamar wani hamshak’in falo, anzuba masa komae da komae na burgewa.
Jin ficewar Fou’ad d’inne kuma yasa shi bud’e idanunsa ahankali.
K’ofar office d’in ya k’urawa ido, kamar me nazartar wani abu, yayinda acikin zuciy
arsa kuwa tunani yake daban daban, akan auren da Abbou Jaheed ke k’ok’arin lik’a masa, saidai kuma kaman yanda yake har acikin zuciyarsa baya son auren, haka baya tunanin zai shiga koda hidima d’aya ne da za’ayi abikin hasalima ko ganinsa babu me sakeyi, d
aga Abbou Jaheed d’in har kowa.
Kyakkyawan idea d’in daya zo masa ne yasashi mik’ewa tsaye, ahankali ya k’arasa gaban wani d’an sif da yake aje abubuwansa masu amfani, wata bak’ar jaka ya d’auko tare da bud’e ta ya zuba duk wasu abu nasa masu amfani nasa
aciki.
Wayarsa dake kan table ya d’auka, kaitsaye kuma ya fice daga cikin office d’in nasa.
Koda ya fito daga office d’in nasa duk inda ya wuce soldiers ne ke sara masa, yayinda sauran soldiers d’in da suka kasance securities d’insa suka take masa baya.
Direct babban compound d’in wajen da yake kaman camp d’insu ya fito, Abdoul dake zaune yana ganin Ogan nasa ya taho da sauri.
Saidai kafun ma ya k’araso Maleek d’in yayi masa alama akan ya tada mota, take kuwa ba b’ata lokaci ya shiga motar ya tayar.
Ka
mar yanda ya saba gidan baya ya shiga, bayan ya dakatar da sauran soldiers d’in dake take masa baya, ta hanyar nuna musu cewar yau d’in b’aya buk’atar rakiyar kowa.
Sanin halinsa da sukayi ne kuma yasa duk suka dakata.
Abdoul kuwa a 360 yaja motar suka b
ar farfajiyan wajen gaba d’aya.
Saeda sukayi d’anyi nisa atafiyar tasu kuwa kafun Maleek d’in ya fad’awa Abdoul d’in inda yakeso ya kaesa.
Kaitsaye kuwa can d’in suka nufa, wato Maitama Estate, inda acan b’oyayyen gidan na Maleek yake, wanda ko su Abbou
Jaheed d’in basu san dashi ba, yayi gidanne kuma musamman dan hutawa, saboda dama shi ba mutum bane me son hayaniya, kasancewar sa soldier kuma shiyasa ako da yaushe yake matuk’ar son privacy.
Isowarsu katafaren gate d’in gidanne yasa Abdoul fitowa daga c
ikin motar ya wangale had’add’en gate d’in, saboda babu maigadin da zae bud’e musu.
Bayan sun shiga cikin gidan da yake kaman aljannar duniya ne kuma Abdoul ya koma ya rufe gate d’in.
Zuwa lokacin kuwa Maleek ya fito daga cikin motar.
Kallon Abdoul d’in
yayi, cikin halinsa na ko da yaushe fuskarnan babu alaman dariya yace.
“Banason kowa yasan inanan, idan nace kowa kuma Ina nufin harda mahaifina, da kuma Fou’ad, sannan ka tabbatar kana kulawa da cutie yanda ya kamata, kana bata abinci sosae.
‿
“Okay Sir
.
‿
Abdoul ya fad’a ahanzarce yana me d’an jinjina kansa, alaman yaji.
Baisake cewa komae ba kuwa ya juya kai tsaye ya nufi cikin gidan.
Abdoul kuwa juyawa yayi ya fice daga cikin gidan baki d’aya.
K’arasowansa cikin had’add’en falon wanda ko wani kusurw
a na cikinsa ke d’auke da hotunan Laylerh da yayi ne yasashi d’an lumshe idanunsa tare da sauk’e wata sassanyar ajiyar zuciya, hakanan yaji wani irin sanyi na ratsa gaba d’aya jikinsa, har zuwa tafin k’afarsa, wannan yasa
ahankali ya shiga takowa har zuwa
tsakiyan falon da had’uwarsa ya zama abun burgewa.
Akan d’aya daga cikin hotunan nata ya sauk’e idanunsa, wanda take sanye da wani riga da sket na atamfa, tana zaune ne kuma ak’asan carpet, yanayin yanda fuskarta ya kasance acikin hotonne kuma yasa duk w
anda ya kalla zaigane cewar tana cikin yanayin damuwa ne aka d’auki hoton.
Idanunsa ya k’urawa hoton nata baya ko k’iftawa, domin a irin yanayin da fuskar nata ke ciki haka shima yanzu yakeji acikin zuciyarsa.
Janye idanunsa daga kan hoton nata yayi, kan
a asanyaye ya zauna akan d’aya daga cikin had’add’un original royal cushions d’in dake cikin falon.
Hannunsa yakai yad’an shafa idanunsa, adaidai lokacin da suka sauk’a akan hoton mahaifiyarsa dake cikin falon.
Akaron farko kenan da murmushi ya bayyana
akan fuskarsa, take kuma yaji zuciyarsa ta karye, hakanan yaji wani abu me kaman ruwa na neman cika masa idanu, wannan yasa shi saurin d’auke kansa daga kallon hoton, y’ar k’aramar jakar da ya shigo da ita ya jawo, tare da bud’e ta ya ciro wani Ledan cocai
ne.
B’ud’e ledan yayi tare dakai hancinsa ya shak’i cocaine fowder d’in ta yanda har saida yajita acikin kansa.
Haka ya lumshe idanunsa tare da ci gaba da shak’an cocaine d’in har saida yajisa acan sararin samaniya, cikin wata duniya ta daban, duniyar im
agine.
Shi kad’ansa haka yayita bulayi acikin falon hardai ya zamana ma hankalinsa yabar jikinsa, inda yatafi wata duniya ta gushewan hankali me kama da bacci.
After 2 days
Acikin kwana biyun nan gaba d’aya mood d’in Laylerh ya sanja, domin tunda taji
maganan auren Maleek ta kamu da wani irin zazzab’i me zafi, ga kuma ciwon maran period dake damunta, abu kaman wasa kuwa sai gashi takai ga kwanciya, acikin Kwanaki biyun kuwa Najeeb koda sau d’aya baisake zuwa mata da wata buk’atarsa ba, koda kuwa romanc
ing d’inta ne, saidai kuma yana iyaka bakin k’ok’arinsa wajen bata kulawa.
B’angaren su Oum Ayush da Abbou Jaheed harma da Fou’ad kuwa shirin biki sukeyi sosae, hakama b’angaren gidansu amarya, sukamma abunnasu yafi na kowa, Dan tuni amarya munnira ta far
a karb’an gyaran amarya, yayinda tabi kan k’awayenta tasanar musu irin mijin da zata aura, kyau da had’uwa had’i da matsayinsa duk ba wanda ta b’oye musu, hakanne kuwa yasa suka k’ara fasa mata kai, hakan yasa takejin kanta tafi kowa.
Awajen Momy kuwa har
yanzu wasu makirci take shirin k’ullawa, saidai kuma jin Maleek d’in zaiyi aure ne yasa ta sauya akalan makircin nata zuwa wani waje na daban.
(Uhummm su Maleek za’a angwance
😝
Insha Allah Gobe zaku samu update saboda da yardar Allah Mungama biki yanz
u Ina free, duk dama ankoma school amma hakan ba damuwa bane.)
*31January/2021*
2/2/21, 8:42 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*Chapter 46*
Sassanyar iskan yammacin da ake kad’awa wanda ahankali yake ratsa dukk
an sassan jikinta ne yasa ta soma bud’e idanunta ahankali ta sauk’e ganinta akan had’add’en zanen p.o.p’n dake saman d’akin wanda aka k’awata jikinsa da zane me kyau.
Amatuk’ar kasalance da kuma irin yanayin da ta samu kanta aciki ta janye idanunta daga k
allon da takeyiwa saman d’akin.
Wani irin numfashi me fitar da hucin zafi ta fesar tare da maida kallonta ga agogon bangon dake mak’ale acikin d’akin.
5:45 pm dai dae da agogon ya nuna mata ne yasa ta d’an yunk’urawa ta tashi zaune, hannunta takai daidai
saitin mararta da takejin yana d’an murd’awa kad’an, kasancewar kuma yau zata gama period d’innata ne yasa ciwon keyi mata da kad’an kad’an, wanda ayanzu kuma abunda yafi damunta shine yawan fad’uwar gaba da take samun kanta aciki kwana biyun, da kuma zaz
zab’in da har yau yakasa barinta ya huta, ko yanzun ma zazzab’in takeji ajikinta wanda kuma shiya kwantar da ita har na tsawon mintuna 40 batare da ta motsa ba sai yanzun.
Kanta ta jingina da jikin saman gadon, tare da sake jan lallausan blenket ta rufe j
ikinta dashi.
Idanunta wanda suka sanja kala ta lumshe.
“Saura y’an kwanaki ne kawae suka rage.
‿
Ta fad’i hakan ahankali, kana cikin wata irin murya me sanyi sosae, da alama kuma abunda ke zuciyarta ne ya fito fili batare da ta sani ba.
Lokaci d’aya ku
ma hawaye suka cika idanun nata, domin aduk lokacin da zata tuna da auren Maleek d’in ko shakka babu sae taji hawaye sun cika idanunta, take kuma duk wani d’an ragowan farinciki da yayi mata saura zae gudu.
Jin alamun turo k’ofar d’akin da akayi ne kuma y
asa tayi saurin kawar da kanta gefe tare dasa hannu ta murza idanunta gudun kada hawayen dake cikinsu su samu daman zubowa.
Ahankali ya maida k’ofar d’akin ya rufe, ganin da yayi mata azaune ne kuma yasa shi d’an jingina bayansa da jikin k’ofar ya zuba ma
ta ido, duk dama baisamu daman kallon cikakkiyar fuskarta ba, kana kuma duk da kasancewar ta lullub’e rabin jikinta da blanket amma hakan bai hana idanunsa gane masa raman da tayi ba, domin acikin y’an kwanakin har wuyanta saida ya k’ara tsawo saboda yanda
gaba d’aya komae nata ya sanja.
Idanunsa ya d’an lumshe ahankali tare da sakin wata b’oyayyar ajiyar zuciya, tabbas sha’anin damuwa da kuma rashin lafiyan Laylerhn na matuk’ar damunsa, musamman idan ya tuna cewa amanarta aka bashi, kuma sannan hakk’insa
ne ya bata kulawa, da kuma cire ta acikin duk wata damuwa, saidai amma saudayawa yakan ga kamar ya kasa yin hakan, saudayawan lokuta yakan tambayi kansa menene dalilin da yasa tun da sukayi aure da Laylerh’n rayuwa tasoma tafiyar musu ahaka, domin shi sam
ba haka ya tsara musu ba, farinciki da kuma jin dad’in rayuwa ya tsara musu sab’anin yanzu da gaba d’aya kowannensu zuciyarsa ke d’auke da abubuwa maban banta.
Ayanzu shida Laylerh’n suna neman cimma sati guda da aure amma koda sau d’aya wata alak’a ta au
ratayya bata tab’a shiga tsakaninsu ba, ba kuma don baya buk’atar hakan ba, hak’ik’a amatuk’ar buk’ace yake da ita, ako wacce rana, a kuma duk lokacin da zaisata acikin idanunsa sae yaji wani irin feeling me k’arfi yazo masa, ko yauma saida yasha tablet ka
fun yasamu matsanancin sha’awarta da yakeji ya d’an kwanta, Saidai kuma wani k’alubale daya fara fahimta shine zuwa yanzu hak’urinsa ya kusa k’arewa akanta, faruwar hakan kuwa zai iya sashi ya aikata mata komae, dan ayanzu shikansa baya control d’in sha’aw
arsa akanta, koda sau d’aya ne kuwa baya so ace ya gwada mata k’arfi saboda hakan zai iyasawa ta zamana koda yaushe cikin matsanancin tsoronsa.
Saidai kuma ayau d’in yana tunanin yin amfani da shawarar da zuciyarsa ta basa, ta hanyar lallab’ata ta yanda z
aisa ta saba da zama ajikinsa ko yaushe, domin hakan ba k’aramin sauk’i zai kawo masa wajen yin Disvirgin nata ba, kuma zuwa lokacin ta riga da ta saba bazata wani ji zafi sosae ba.
Yarda da shawaran da zuciyartasa ta basane kuma ya sashi, sakin wani d’an
guntun murmushi, ahankali ya shiga takowa zuwa kan gadon da Laylerh’n ke zaune.
Laylerh kuwa jin ya iso wajen gadon ne yasata lumshe idanunta, domin har acikin zuciyarta kunyan had’a idanu dashi take, musamman sanin da tayi cewar bata kyautata masa, ta h
anashi duk wani hakk’insa dake kanta, takasa basa farinciki kamar yanda kowacce mace ke