Showing 168001 words to 171000 words out of 244674 words
sassanyan numfashi.
Hakan kuwa shiyasa Oum Ayush ta kasa hak’uri bisa do
le saida ta fashe da kuka.
Jin sautin kukan Oum Ayush d’inne kuma yasa shi saurin bud’e idanunsa, ahankali ya kamo hannayenta tare da girgiza mata kai, domin kuwa har cikin zuciyarsa yakejinta kamar mahaifiyarsa, ahankali ya d’an matso kusa da ita, cik
in sanyi da kuma son samawa kansa nutsuwa ya d’aura kansa bisa cinyarta, tare da maida idanunsa ya lumshe.
Hakanne kuwa yasa Oum Ayush d’in tayi saurin tsaida kukanta, tare dasa hannunta ahankali ta shiga shafa tarin suman kansa, wanda yasha aski irin na
turawa, wai ahakan an aske amma kuma kamar ba’a aske ba.
Idanu Fou’ad ya zuba musu yana mejin tsananin tausayinsu.
*Najeeb.*
Bud’e k’ofar d’akin yayi ahankali tare dajan hannunta suka shiga ciki, anan kan luntsumemen bed d’insu ya zaunar da ita, tar
e kuma da zama agefenta.
Ahankali ya kamo hannunta, cikin kuma sanyin murya me had’e da ban baki yace.
“Har abada kuka baya tab’a maganin damuwa Laylerh, kiyi hakuri ki daina kuka kinji!
‿
Kai ta shiga girgizawa tare da juyowa ahankai ta fuskancesa, ci
kin sheshshek’an kukannata ne kuma murya na shaking tace.
“Tayaya zan daina kuka Yah Najeeb? tayaya zuciyata zatayi sanyi? Wannan wacce irin k’addarace haka da take wasa da rayuwar d’an uwana? hak’ik’a nasan cewar ni yarinyace amma kuma hakan bashi zais
a na kasajin zafi akan duk wani abu daya samu Yah M.Jay ba, ya yakeji? meyakeji? shi kad’aine ya sani, amma kuma bashi kad’ai yakejin zafin ba, hardani zafin yana k’ona zuciyata!
‿
Tsagaitawa tayi tare da rumtse idanunta wanda suke fitar da zafafan k’walla
.
Duk da kuwa tana da abun cewa amma hakanan taji bakinta yayi mata nauyi, bisa dole ta sa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta.
Najeeb kuwa mik’ewa tsaye yayi tare da takawa ahankali ya k’arasa gaban dressing mirror tare da tsayawa ya k’urawa mirror d
’in idanu yana me kallon kansa aciki, yayinda wani sashi na zuciyarsa ke ci gaba da sak’a masa abubuwa masu yawa, wanda batun yauba zuciyartasa take yawan sak’amasa hakan.
Wanda ayanzu yayi imani cewa acikin biyu za’a yi d’aya.
B’angaren Alhaji Farouk
kuwa zuciyarsa cike da tarin tunani kala kala haka ya nufo gidansa, bakinsa d’auke da al’amari mai girma wanda baisan taya iyalannasa zasu fahimci maganar ba.
Wanda yasan dolene ma acikin biyu za’a yi d’aya ko fahimta ko kuma rashinsa, haka amincewa ko ku
ma akasinsa.
K’warae yasan cewa rashin haihuwa abune me girman gaske, kuma dama ana aurene dan a hayayyafa, asamu abunda za’a yi alfahari dashi anan gaba.
Shin tayaya matarsa BUZUWA da kuma MUNNIRA zasu d’auki wannan zancen? Idan son da y’arsa Munnira ke
yiwa Maleek tana da yawa hakan yasa ta amince, shin mahaifiyarta zata amince?
Munnira ita kad’aice y’a agaresu bayan ita babu wata, dole ne kuma zasu so ganin jika daga gareta, domin idan ba awajenta d’inba basa saran ganin jika daga wajen kowa, aurenta d
a Maleek kuwa yana nufin cewa har abada kenan bazasu tab’a samun jika ta wajenta ba.
“Anya kuwa koda amincewarta aura mata Maleek bazai zamo cutarwa agareta ba??
‿
Yayiwa kansa tambayar, kana abayyane yace abune me matuk’ar wahala.
Daidai lokacin kuwa ya
shigo cikin falon matarsa wato Buzuwa dan sanar da ita dukkan halin da ake ciki.
*24/February/2021*
*7:52 pm*
2/26/21, 8:07 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*Not editing*
*Chapter 58*
Gaba d’ayansu za
une suke acikin falon daga Buzuwa har Munnira wacce ke zaune akan sofa tana ta shirye shiryen event d’in da zasu yi yau ita da k’awayenta na Bride To Be.
Ganin yanda Alhaji Farouk d’in ya shigo cikin falon duk gaba d’aya jikinsa asanyaye ne yasa Buzuwa
k’ura masa ido cikin yanayin mamaki kuma tace.
“Alhaji lafiya kuwa naganka duk jikinka asanyaye, meke faruwa?.
‿
Sauk’akk’ar ajiyar zuciya ya sauk’e tare da neman waje anan kusa da ita ya zauna.
Kallon Munnira dake ta faman izurin gabanta yayi, kana ci
kin sanyi ya k’ira sunanta wanda hakanne kuma yasa bisa dole ta tsaida abunda takeyi d’in tare da d’agowa ta kalli mahaifinnata.
Buzuwa kuwa idanu ta zuba masa cike da mamakin ganin sabon yanayinsa domin kuwa tasan kafun fitansa ya sanar da ita cewar g
idan Alhaji Jaheed zaije, fuskarsa kuma dauke da fari’a ya fita sab’anin yanzu da damuwa ta maye gurbin fari’ar.
“Wai meke faruwane Alhaji kodae wani abune na daban ya samu Maleek d’in?.
‿
Tayi masa duka tambayoyin ta hanyar cigaba da tsura masa ido.
Asanyaye cikin kuma taraddadin yanda zasu d’auki abun ya d’an jinjina masu kai, kana cikin nutsuwa yace.
“Tabbas wata matsala ta kunno kai wacce bamusan tayayane zamu maganceta ba, ban kuma san wani ba hagon fahimta zakuyi wa maganar ba.
‿
Shiru yayi tar
e da kallonsu duka biyu, wanda kuma sud’inma kallonsa sukeyi basa ko k’yafta ido.
Shi kuwa gyara zama yayi kana asanyaye yace.
“Asanadiyar hatsarin motar da Maleek ya samu likita ya tabbatar da cewar bazae tab’a iya haihuwa ba, bi ma’ana k’waya k’wayan h
aihuwarsa sun samu matsala, duk macen da zata zauna dashi saidai ta zauna da hak’uri amma bazae tab’a haihuwa ba!!
‿
Darammm dammm haka zuciyoyi da k’irjin Buzuwa da kuma Munnira suka buga, saboda tsananin mamaki da kuma al’ajin jin maganan daya fito dag
a bakin Alhaji Farouk d’in.
Amatuk’ar razane Buzuwa ta zazzaro idanunta waje, kana cikin yanayin tashin hankali tace.
“Subahanallah, Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, Maleek bazai tab’a haihuwa ba? Ya samu matsala amararsa? Ya ilahi yanzu ya zamuyi ken
an wannan wani irin sabon tashin hankaline da ba’a samasa rana ya tunkaro mu.
‿
Ta k’are maganar tana me sharce gumin dake tsatstsafo mata.
Munnira kuwa gaba d’aya cikin wani irin shock ta samu kanta, lokaci d’aya kuma taji har wani ciwon kai da jiri na
neman kwasheta, domin kuwa sosae maganan Abban nata ya bata tsoro, idan dagaske Maleek ya samu matsala ita meye makomarta kenan?
Tayiwa kanta tambayar da bata da amsarta.
Alhaji Farouk kuwa matartasa ya kalla kana cikin sanyin murya yace.
“Lallai tab
bas Maleek ya had’u da k’addara, ayanzu kuwa zab’i ya rage garemu, nidai kam idan asonane bazan hanashi auren Munnira ba, duk da kuwa ita kad’aice y’a d’aya tilo da Allah Yabamu, dole za musu muga jika ta wajenta, amma kuma to ya zamuyi k’addara ta riga fa
ta, saidai kawai mujira Allah yayi ikonsa.
‿
Kallo mai d’auke da ma’anoni Buzuwa ta watsawa mijinnata, lallai kuwa Tabbas sunga samu sunkuma ga rashi nan take, hakika ita macece maison dukiya da kuma jin dad’in rayuwa, kasancewar kuma munnira itace y’a d
’aya tilo da Allah Yabata wannan yasa ta d’iga duk wani burinta akan Munniran, tana matuk’ar son y’artata ta auri mai dukiya, wannan dalili yasa koda Alhaji Farouk d’in ya kawo maganar Maleek sanin irin tarin dukiyar da Alhaji Jaheed da kuma shi kanshi Mal
eek d’in ke dashi yasa tayi saurin amincewa, Tabbas tasan cewa ayanzu idan Munnira ta auri Captain M.Jay d’in bak’aramin dukiya da arziki zasu tara ba, kasancewarsa wanda bazai tab’a haihuwa ba hakan zaisa ya sakewa Munniran kud’i, saidai kuma amma bazata
tab’a iya jurewa tanaji tanagani y’arta lafiyarta k’alau amma ace bazata haihu ba, Tabbas tana da burin ganin jinin Munniran.
“Lallai wannan shine tsaka me wuya, ga arziki b’aro b’aro ga kuma tawaya.
‿
Tafad’i hakan cikin yin k’asa da murya tare kuma dasa
hannu ta dafe kanta da lokaci guda ya d’au charge.
Alhaji Farouk kuwa Munnira wanda idanunta suka ciko da k’walla ya kalla, cikin tausasa murya yace.
“Duk da inason aurenki da d’an Aminina Maleek, amma hakan bazai tab’a sawa na tauyeki ba, lallai dole
kina da zab’i, shin kinaga zaki iya rayuwar aure da Maleek duk da wannan lalurar da ta sameshi? zaki iya zama dashi batare da haihuwa ba har abada?.
‿
Shiru gaba d’aya falon ya d’auka duk da kuwa taji tambayar da Abban nata yayi mata.
Kanta ta sunkuyar
k’asa tare da lumshe idanunta tana me tuno tsananin had’uwa da kyawun Maleek d’in, wanda ayanzu ke tayi mata gizo acikin idanunta.
K’warae shid’in Miji ne na nunawa sa’a, sannan kuma atattare dashi akwae abubuwan burgewa, ya had’u tako ta ina, yayinda ku
ma komai nasa ya kasance anutse, tayaya wata mace da ta samu dama zata bari cikakken gwarzon Namiji kamarsa ya sub’uce mata? Tabbas rasashi asarace babba, domin tayi imani auren Namiji kamarsa ba k’aramin d’aga mata darajarta zaiyi ba, aurensa sa’ane kuma
samun hakan sai mace mai sa’a, Ina batajin zata barsa waidan kawae saboda baya haihuwa, itakam wallahi tana kwad’ayin zama dashi ahaka, Kodan fitinannen kyaun dayake dashi kuwa, duk da kuwa cewar zata so ace ta haifa masa kyawawan yara masu kama dashi.
D’
ago kanta tayi kana cikin sauri tace.
“K’warai nikam na amincewa aurensa ahaka Abba, zan zauna dashi.
‿
Idanu Buzuwa ta zazzaro cike da mamaki had’i da tsoron abunda y’arta ta ta fad’a, hatta Alhaji Farouk d’in kuwa idanu ya zubawa y’ar tasa, sakamako
n jin abunda ta fad’a.
Buzuwa kuwa kai ta d’an soma girgizawa, domin kuwa ta riga da ta gama yanke hukunci, duk da cewar tasan zasuyi asara sosae amma kuma gwara wannan asarar da wata asarar, fuskarta babu alaman wasa tace.
“Lallai yau Munnira nasake
tabbatarwa da kaina cewar baki da hankali, ke shashasha ce, kina tunanin cewar wae kyau da kud’i sunfi haihuwane? hmmm to idan ma haukane yasa kika amincewa auren Maleek ahaka to ki dawo hayyacinki ki jini, bazaki tab’a aurensa ba, matuk’ar yana tare da w
annan lalurar, maganar kud’i da kyau kuwa duniyarnan da fad’i take, domin kuwa bashi kad’ai bane kyakkyawa, akwai kyawawa da yawa ciki da wajen k’asarnan, saboda haka Allah yasa shid’inma ba mijinki bane, duk da cewar kuwa yanzu aurennan saura kwana uku am
ma hakan bashi zaisa afasa soke shiba, naji nayarda zan fuskanci jama’ar dana gayyata na fad’a musu cewa an fasa auren, yaje Allah Ya had’asa da mai aurensa amma bawai keba.
‿
Tsaida maganar nata tayi tare da juyowa ta kalli Alhaji Farouk cikin nuna babu
sauyi akan maganarta tace.
“Batare da wani dogon nazari ba kak’irasu kasanar dasu cewa anfasa maganar auren, har abada babu aure tsakanin Y’armu munnira da kuma d’ansu wanda baya haihuwa.
‿
Idanu Alhaji Farouk ya d’an zazzaro waje cikin yanayin damuwa
kuma asanyaye yace.
“Kada kiyi haka dan Allah ko kinmanta cewa Alhaji Jaheed Gwani abokinane, tayaya zan k’i basa auren y’ata akan wannan dalilin, koba komai kuma Maleek matsayin d’a yake awajena, kuma ya kamata mu tausaya masa kodan lalurar da ta samesa.
‿
Saurin girgiza kanta tayi kana cikin kafiya tace.
“Wallahi awannan zancen babu wani batun tausayawa, shin atunaninka yau idan da ace Munnira ce ta samu wannan matsalan Maleek d’in zai iya yarda ya aureta ne? musamman yasan cewa yana tashen kyau da du
kiya mai zaiyyi da macen da bata haihuwa? to haka muma y’armu bazata auri Namijin da baya haihuwa ba, dama can ahalinsu bayawane dashi ba, basu da wani dangi shiyasa sukeso muma su yankemu ya zama bamuyi gaba ba, nidai na gama magana kakira danka sanar das
u ma ehe.
‿
Tana gama fad’in haka ta mik’e tsaye tare da kamo hannun Munnira ta wuce da ita d’akinta.
Alhaji Farouk kuwa haka ya zauna shiru acikin falon shi kad’ai, zuciyarsa cike da nauyin yanda zai fuskanci mutum mai kamala da mutumci kamar Abbou Jahee
d yace, suyi hakuri da alk’awarin auren da yayiwa d’ansu, yanzu bazai iya basu yarsa ba, lallai abun da matuk’ar kunya sosae, amma kuma to ya zaiyi? Allah ma yasani yana matuk’ar bin maganan matarsa, duk abunda ta fad’a koba mai kyau bane babu yanda ya iya
bisa dole haka zaibi.
Jikinsa duk amace haka ya mik’e ya nufi bedroom d’insa.
Acan cikin d’akin Buzuwa kuwa munnira ta kalla, wanda duk tayi jugum zuciyarta cike da alhinin matsalar da ta samu Maleke d’in, Allah yasani itakam tana jin wani feelings d
’insa, duk da cewar ayanzu tasan ta rasasa kenan amma zata so ace koda sau d’ayane ta rab’i jikinsa, bi ma’ana tasamu shiga jikinsa ta yadda zata mallaka masa kanta koda kuwa babu aure atsakaninsu, domin kuwa tun da ta sakashi acikin idanunta kullum da fee
lings d’insa take kwana take tashi, jarababben sha’awarsa takeji, saboda tasan cewa maza irinsa sam basu da wasa, duk macen da ta shiga hannunsu to ba makawa sai sun zautar da ita da salonsu.
Buzuwa kuwa kafad’an y’ar tata ta dafa, cikin son bata nutsuw
a tace.
“Ko kad’an kada kiji wani abu akan barin Maleek, saboda akwae maza kyawawa da zasu soki har kuma ki mori dukiyarsu, Tabbas kam nasan munyi rashin abunda muke so, amma ae akwae gaba, rashin haihuwa ba abubane da za’a iya shanyewa, balle ma matsalar
badaga gareki take ba, can daga wajensane kuma har abada ake kira Bawae na k’alilan d’in lokaci bane, ninasani zaki samu wani wanda ya fisa.
‿
Saurin girgiza kae Munnira tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Har abada Momy har abada bazan tab’a samun wan
da ya kaisa ba, saboda ko tantama banayi cewar irinsa shi kad’aine, tayaya ma kike tunanin zan samu wani Namiji irin Maleek? mutumin daya had’a komae da komae na rayuwa, mutumin da ganinsa ma sai mai sa’a arayuwa, mutumin da ko kusa ban tab’a tunanin taka
inda ya taka ba, kin kuwa sam wayeshi Momy? Wallahi irinsa ko babu dukiya kuka still ba haihuwa mata rububinsa za sukeyi, saboda shid’in na dabanne komai nasa na musammanne, kuma Momy keda kanki ma kinsan hakan.
‿
Ta k’are maganar tana me lumshe idanunta h
ad’e da rungume hannayenta, saboda wani irin shauk’in da takeji akansa, duk da cewar kuwa baya kusa da ita amma haka takejin feelings d’insa.
Ganin hakanne kuma yasa Buzuwa tab’e baki, tare da soma tattare kayayyakin dake baje akan gadonta, Dan itakam A
llah Yasani ta gama magana ba kuma zata tab’a bari y’arta ta auri wanda likitoti suka tabbatar da cewa bazae tab’a haehuwa ba.
*Maleek*
Ahankali ya d’ago kansa wanda ya kwashe sama da 20min kan cinyar Oum Ayush,
Kallon Oum Ayush d’in yayi tare da d’a
n gyara zamansa, ahankali kuma cikin sanyi kamar wani k’aramin yaro yace.
“Please Oum Ayush zanci abinci.
‿
Kallonsa Oum Ayush d’in tayi cike da kulawa, tare kuma dajin sanyi aranta, sakamakon jin cewar da kansa yau d’in ya buk’aci abinci, sab’anin saur
an kwanakin da saidai ayita binsa da abincin amma yana sharewa.
Cikin yanayin dake bayyana samun nutsuwarta tace.
“To Maleek mekakeson ci sae na dafa ma.
‿
Idanunsa ya d’an lumshe kana akasalance yace.
“Southern baked BBQ chicken and fruit salad kawae!
‿
Yanayin yanda ya k’are maganar yana d’an taune jajayen lips d’insane yasa cikin sauk’i zagane cewar mararsa ce ke ciwo, musamman saboda yanda ya dafe kan marar da tafin hannunsa.
Take kuwa tausayinsa ya kama Oum Ayush wanda hakan yasa cikin kulawa tac
e.
“Sannu ko bari naje yanzu na had’a maka, amma akwae chicken biryani dana dafa d’azunnan kona kawoma kafaraci?
‿
Kansa ya d’an girgiza alaman “A’a.
‿
hakanne kuwa yasa ta juya cikin sauri ta fice daga falon don sama masa abunda ya buk’ata d’in.
Shi
kuwa sake lumshe tsumammun idanunsa masu kyau yayi, kana ahankali cikin daure ciwon da yakeji amarar tasa yace, da Fou’ad wanda ke zaune acan gefe kad’an yaje d’akinsa akwae laptop d’insa ya d’auko mae.
Hakan kuwa akayi babu musu Fou’ad ya mik’e tsaye tar
e da ficewa daga falon kaitsaye yanufi sashin Maleek d’in.
Shikuwa Maleek sake jingina bayansa yayi da jikin kujera, tare da sauk’e wata irin sassanyar ajiyar zuciya, sannu ahankali yakejin wani irin sanyi na ratsa duk ilahirin jikinsa yayinda wata irin s
assanyar iska ke shiga kowani sashi na jikinsa.
Lallai tabbas koda ace bai bud’e idanunsa ya sauk’e ganinsa akanta ba babu makawa yasan cewa itace tazo, domin yayi imani cewa akanta kad’ae yakejin irin wannan difference mood d’in, matuk’ar kuwa tana kusa
dashi to koda bai bud’e idanunsa ba yasan itace.
*25/February/2021*
*7:40 pm*
2/28/21, 10:13 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*Not editing*
*59*
Sanyayyun idanunta wanda suke d’auke da danshin hawaye ta
lumshe, tare dasa hannu ahankali ta dafe daidai saitin zuciyarta.
Duk da cewar ta fita ta barshi afalon sam batayi tunanin sake da wowa ta sameshi ba, musabbabin dawowarta falon kuma shine manta wayarta da tayi.
Saurin mannewa ajikin kofar falon tayi tay
anda tasan koda ya bud’e idanunsa bazai ganta ba.
Shikuwa ahankali ya bud’e kyawawan idanunsa tare da sauk’e ganinsa adaidai saitin k’ofar shigowa cikin falon, saidai kuma rashin ganin kowa awajen yasa shi sauk’e wani irin gauron numfashi, tare kuma da
tsaida idanunsa adaidai k’ofar shigowa cikin falon, domin kuwa Tabbas zuciya da gangar jikinsa sun shaida masa cewar lallaine tana kusa dashi, because akanta kad’ai yakejin irin wannan yanayin.
Ita kuwa Laylerh ba koma one ya hanata k’arasa shigowa ciki
n falon ba kamar yanda taji zuciyarta na bugawa da sauri sauri, musamman ma ganinsa da tayi ayanzun, ahankali tasa hannunta ta dafe kirjinta dake tsalle kaman zai fad’o waje, tare kuma da sake lumshe idanunta.
Asanyaye ta fitar da wani numfashi mai sauti,
yayinda kuma lokaci d’aya duk taji jikinta yayi relax.
“Laylerh!!.
‿
Fou’ad ya kira sunanta, wanda yanzu dawowansa daga sashin Maleek d’in, ganin Laylerh’n da yayi atsayene kuma yasashi jin mamaki k’warai.
Ita kuwa Laylerh jin muryar Fou’ad dinne ya
sa tayi saurin bud’e idanunta, wani irin kunyansa da tajine kuma yasa tayi k’asa da kanta tare da soma wasa da y’an yatsun hannunta.
Fou’ad kuwa kallon tsab ya mata tare da d’an gyara tsayuwarsa anutse yace.
“Halan Oum Ayush kike nema ko?.
‿
Kanta ta
d’an girgiza kana asanyaye tace.
“Aa phone d’ina nazo d’auka.
‿
Jin yanda tayi maganan asanyaye cikin fusgan numfashine kuma yasashi saurin jinjina kai alaman ya fahimta, batare kuma daya sake