Showing 150001 words to 153000 words out of 244674 words

Chapter 51 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

Dr. Mouhammad d’in yayiwa Abbou Jaheed nuni da wata kujeran da musamman aka ajiye ta dan zaman bak’i na musamman.

Zama Abbou Jaheed yayi, ta

re da d’ago kansa ya kafe Dr.Mouhammad da idanu, wanda ya zauna akan permanent sit d’insa na Office.

Ahankali ya bud’e wasu files dake gabansa ya shiga dubawa, ak’alla kuma wasu y’an mintuna ya d’auka yana duba files d’in, saida ya kammala sannan ya d’an

yi rubutu acikin kowannensu, d’ago kansa yayi ya kalli Abbou Jaheed da har yanzu baidaina kallonsa ba.

Shiru yayi tare da d’an sunkuyar da kansa, domin kuwa zuciyarsa cike take da fargaba da kuma halin da Abbou Jaheed d’in zai samu kansa aciki matuk’ar ya

sanar dashi hak’ik’anin gaskiyar abunda ya faru da d’ansa, saidai kuma yasan dole babu yanda zaiyi, wanda ya wuce ya fad’awa Abbou Jaheed d’in komai, domin babu wani bawa aduniya daya wuce wa samun irin wannan k’addaran.

“Kai nake saurare Dr. Mouhammad

amma kuma har yanzu naji baka ce komae ba, kodai akwai wata matsala babba daya samu Maleek ne wanda bakason fad’a miji?.

‿

Abbou Jaheed ya fad’i hakan cikin yanayi na d’an damuwa, domin daga yanda yaga yanayin Dr.Mouhammad d’in yasan baiwuce ace masa akwa

i wata gagarumar matsala.

Ajiyar zuciya Dr.Mouhammad ya sauk’e tare da d’an gyara zamansa, cikin yanayin sanyi yace.

“Kayi hakuri Alhaji da irin tambayoyin da zan maka dole ce tasa hakan, shin Maleek yana da mata ne ko kuma y’ay’a?.

‿

K’irjin Abbou Jah

eed ne ya buga, asakamakon jin tambayan da Dr.Mouhammad d’in yayi masa, lokaci d’aya yaji zuciyarsa ta karye yayinda kirjinsa ya shiga dukan uku uku, cikin sassanyar murya da kuma fargaban abunda kunnuwansa zasu sake jiye masa anan gaba yace.

“A’a ko d’ay

a bashi da mata kuma bashi da y’ay’a, hasalima shid’in bai tab’ayin aure ba, amma Dr. wani abune ya faru?.

‿

Idanu Dr.Mouhammad ya d’an lumshe, yayinda gaba d’aya jikinsa ya k’arayin sanyi, lokaci d’aya yaji wani irin matsanancin tausayin matashin saurayin

da ko auren fari baiyi ba amma kuma ya had’u da babbar matsala.

“Doctor Mouhammad kaifa nake saurare, amma naga kayi shiru.

‿

Abbou Jaheed ya katsesa ta hanyar fad’in hakan.

Ajiyar zuciya ya k’ara sauk’ewa akaro na biyu, kana ahankali ya d’an gyara zam

ansa, cikin nutsuwa da kuma son kwantarwa da Abbou Jaheed d’in hankali ta yanda zai fahimcesa asanyaye yace.

“Kayi hak’uri da abunda zan fad’a maka Alhaji Jaheed, hakika kamar yanda kasani kowani bawa aduniya yana rayuwane da irin k’addara da kuma jarabaw

an da Allah Ya d’aura masa, mai kyau ko akasin haka, sannan kuma Allah Baya d’aurawa bawansa abunda bazai iya ba, tabbas Maleek ya had’u da k’addara wanda jurewa hakan Insha Allah Zai kaisa ga samun kyakkyawan sakamako awajen Ubangiji...

‿

D’an tsagaitawa d

a maganan nasa yayi tare da d’ago kai ya kalli Abbou Jaheed daya zuba masa ido baya ko k’yaftawa.

Kansa ya sauk’e k’asa domin yasan abu ne me girma fad’awa Iyaye irin wannan gagarumin matsala musamman idan y’ay’ansu ne suka kasance sun samu kansu acikin i

rin matsalan.

D’an gyara zamansa yayi akaro na barkatai, cikin hikima irin tasu ta likitoti yace.

“Zan sake baka hak’uri Alhaji Jaheed, domin kuwa a bisa tsautsayin hatsarin da d’anka Maleek ya had’u dashi ya samu wata matsala, ya samu mummunan buguwa so

sae akan mararsa wanda hakan yasa abinciken da mukayi mungano cewar D’ANKA MALEEK bazae tab’a haihuwa ba, bi ma’ana k’wayoyin haihuwarsa sun samu matsala ta yanda bazasu iya riki d’ewa su zama k’wayar halittan da zata Samar da y’a ko d’a ba...

‿



k’irji da

kuma zuciyar Abbou Jaheed ne suka shiga bugawa akai akai, yayinda ya samu kansa cikin wani sabon matsanancin tashin hankalin da ya gigita tunaninsa, tabbas kalaman da suka fito daga bakin Dr.Mouhammad sun kusan tarwatsa masa zuciya, har saida yaji kansa

na yi masa wani irin sarawa.

Lokaci d’aya gaba d’aya mood d’in Abbou Jaheed d’in ya sanja, yayinda idanunsa suka cika tab da k’wallan tausayin d’ansa.

Cikin wata irin sassanyar murya me d’auke da matsanancin tausayawa ya shiga furta kalamar.

“Innalillah

i Wa’inna Ilaihirraju’un!!!

‿

Saboda yasan ita kad’aice kalmar da zata daidaita nutsuwarsa.

Ganin hakanne kuma yasa Dr.Mouhammad gyara zamansa, ahankali yace.

“Dan Allah Alhaji Jaheed kada ka tashi hankalinka, domin kuwa ba akan Maleek aka fara samun iri

n wannan matsalan ba, duk da cewa abune da baiyawaita ga maza ba, anfi samun irin way’annan case d’in ga mata, saidai kasani shi Maleek yasamu wannan matsalarne ta sanadiyar accident d’in daya samu, hak’ik’a Allah Yakan jarraba bawansa da k’addara kala k

ala, yayinda kuma wata k’addaran takanfin wata sauk’i, sannan ko acikin k’addarori Allah Yakan musanyawa bawa daga me tsananin had’ari izuwa me sauk’i, kamar dai yanda ya juyawa Maleek nasa, lallai na tsorata sosai alokacin da aka kawosa cikin asibitinnan

musamman yanda naga kansa na fitar da jini, wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar ya bugu sosae akannasa, wanda hakan yasa nafara tunanin cewa, ko ta sanadiyar hakan zai zamana cewa yayi losing memory d’insa, sai kuma da mukayi bincike sosai akansa

nida abokan aikina sai muka gano cewar kokad’an kansa da kuma k’wak’walwarsa basu samu wani matsala ba, tabbas munyi farinciki da ganin hakan, domin kuwa abune me tsananin d’aga hankali ace mutum ya manta kowa da komai nasa, tayaya rayuwa zatayi masa dad’i

? kwarai zai dawo kaman wani bak’on halittane acikin mutane, lallai nayarda cewa k’arfin ikon Ubangiji da kuma k’udurarsa ya wuce duk tunanin mai tunani, domin kuwa shine ya kawar wa Maleek da wannan matsalan, ya kuma jarrabesa da wata matsalan amararsa, w

anda da ace yaso had’a Maleek d’in da mummunan k’addara tofa da ayanzu labari ya riga ya sanja salo, domin kuwa inda matsalan ya kasance akansa ne to fa komai za

i iya faruwa ciki kuwa harda gushewar hankali ma’ana zai iya zama mahaukaci, amma da yake Allah

baiso hakan ba sai ya had’ashi da wata tawayar, tabbas lokacin da nagano cewa Maleek yana d’auke da wannan matsalan na tausaya masa k’warai, duba da cewar ya kasance jarumin matashin Soja me jini ajika, amma saidai Allah Ne kad’ai yasan me yake nufi da

faruwar hakan.

‿

Hannu Abbou Jaheed yasa asanyaye ya share hawayen da suka silalo daga Cikin idanunsa, wani irin matsanancin tausayin Maleek d’insa ne ya cika masa zuciya, wanda har hakan ya kaisa gajin kamar yayi ta rusa kuka, saidai kuma amatsayinsa na

cikakken Musulmi ya zame masa dole d’aukan hak’uri da k’addara me kyau ko akasin haka.

Duk da kuwa bai tab’a kawo wa aransa cewar watarana wai d’ansa jininsa zai iya gamuwa da wannan mummunan k’addaran ba, saidai kuma duk da haka saidai ya godewa Allah d

a bai gama d’annasa da ciwon hauka ba, domin kuwa ciwon hauka yafi kowanne ciwo Muni.

Wani irin dogon numfashi me d’auke da karyewar zuciya yaja, asanyaye yace.

“Idan har na fahimci abunda kake fad’amin Dr.Mouhammad shine Maleek d’ina bazai tab’a haihuw

a ba har abada, har ya koma ya ubangijinsa bazai ga d’ansa kuma jininsa ba, sannan kuma nima har abada bazan tab’a ganin Jika daga garesa ba, lallai tabbas Maleek ya had’u da babban k’addara wanda zatayi sanadiyar kasantuwarsa cikin k’unci, ba kuma zan iya

jure hakan ba Dr. domin kuwa Ina matuk’ar son Maleek? dan haka wannan matsalar batasa bace shi kad’ai, wai ma shin tayaya xan fara fuskantar Maleek da wannan maganan tayaya????

‿

Ya k’are maganar muryarsa na d’an rawa da’alama kuka ne ke neman k’wace masa

.

Kai Dr.Mouhammad ya girgiza cikin tausasa zance da kuma bada baki yace.

“Ayanzu Maleek Addu’ar samun sauk’i kawai yake buk’ata awajen baki d’ayan mu, domin kuwa hakan bawai yana nufin cewa har abada bazae tab’a warkewa bane, tabbas lalurar daya samu ba

bbace, wanda da yawanta ba’a tab’a warkewa, amma kuma komai na Allah Ne shike sa cuta a lokacin da yaso, haka kuma shi ke sauk’ar da waraka alokacin da yaso, saboda haka mujira komai daga garesa, kar ka manta kuma cewa Alhaji Jaheed d’aukan k’addara yana d

’aya daga cikin abunda yake k’ara inganta imanin mutum, saboda haka ka kwantar da hankalinka, sannan kuma inaso katuna cewa Allah Baya tab’a d’aurawa bawansa abunda yasan bazae iya d’aukansa ba.

‿

Wata irin nannauyar a ajiyar zuciya Abbou Jaheed ya sauk’

e, tare dasa tafukan hannayensa ya rufe fuskarsa dasu, tabbas wannan sabuwar matsalan da ta kunno musu tayi matuk’ar d’aga masa hankali da kuma gigita tunaninsa, babban abunda yake tsoro kuwa shine.

“Tayaya zai fara fad’awa Maleek wannan matsalan da ta sa

meshi? Yaya Maleek d’in zaiji? wani irin k’una da kuma zafin zuciya zai samu kansa aciki?.

Lallai Rayuwar Maleek acike take da tarin k’addarori, da fari yayi rashin mahaifiyarsa haka ya taso cikin kad’aici da kewa, bashi da y’a ko kuma k’anwar da suke uwa

d’aya uba d’aya, ahakansa yake rayuwa har kawo yanzu, da adaidai wannan lokacinne yakamata ace yayi aure ya hayayyafa ta yanda y’ay’ansa za su zame masa abokan hira da kuma d’ebe kewa, amma kuma sai gashi rana d’aya Allah Ya sauk’ar masa da wannan k’addar

an, sai yaushene Maleek Zaiyi farinciki arayuwarsa? Sai yaushe k’unci da kad’aicin da suke mamaye da rayuwarsa zasu yaye?

‿



Sam Abbou Jaheed d’in bashi da amsar tambayoyin, wanda hakan ya tilasta zubowar wasu y’an guntayen k’walla daga cikin idanunsa.

A

hankali ya mik’e daga zaunen da yake, cikin sanyin yanayi batare kuma daya ce da Dr.Mouhammad k’ala ba ya juya tare da nufar hanyar fita daga office d’in.

Dr.Mouhammad kuwa da idanu ya raka Abbou Jaheed d’in har ya gama ficewa daga cikin office d’in.

W

ani irin matsanancin tausayin ahalinne ya kamasa, domin kuwa k’warai yasan cewa abune me matuk’ar ciwo da kuma tada hankali ace mutum Namiji ya samu irin wannan matsalan na rashin haihuwa, saidai kuma sanin da yayi cewa Maleek d’in bai rasa cikakken lafiya

rsa ta zamowa d’a Namiji ba ne yasashi sauk’e ajiyar zuciya, domin yasan matsalar za tafi muni ne Idan akace Maleek d’in bazae iya biyawa Mace buk’atar taba, Alhamdulillahi kuma domin kuwa hakan bata faru ba, domin abincikensu sun gano cewa babu abunda ya

samu manhood d’insa, zai iyayin sex da mace bama d’aya ko biyu ba, kuma ta samu cikakken gamsuwa, sannan kuma k’arfin sha’awarsa Yana nan bai ragu ba, saboda haka awannan fannin baida matsala kona d’igo ne kuwa.

Matsalar tasa dai guda d’aya ce, wato rash

in haihuwa, wanda kuma ako da yaushe Allah Yakan iya sanja al’amura yanda yaso.

Abbou Jaheed kam jikinsa amatuk’ar sanyaye ya fita daga office na Dr. Mouhammad d’in, kaitsaye d’akin da aka kwantar da Maleek d’in ya nufa, haka yakejin duk gaba d’aya gan

gar jikinsa ba k’arfi, domin kuwa fargaba tausayi da kuma rauni su suka riga suka cinye masa zuciya.

Isowarsa jikin k’ofar d’akinne yasa shi soma k’ok’arin daidaita nutsuwarsa gudun kada su Abbou Khareem su gane cewar yana d’auke da damuwa, ahankali ya tu

ra k’ofar d’akin ya shiga, bakinsa d’auke da sallama.

Oum Ayush da kuma Abbou Khareem ne suka amsa masa, sai kuma Fou’ad da ya amsa murya kasa kasa, saboda damuwar dake kwance acikin zuciyarsa.

K’asa Abbou Jaheed d’in yayi da kansa ba tare da ya yarda i

danunsa sun sauk’a akan Maleek dake kwance ba, domin kuwa yasan matuk’ar ayanzu ya d’aura idanunsa akan Maleek d’in to ko shakka babu kukane me k’arfi zai k’wace masa.

Oum Ayush dake zaune Laylerh na bisa cinyarta ya kalla, asanyaye yace.

“Oum ki tada La

ylerh ku koma gida, nida Abbou Khareem zamu zauna anan, kaima Fou’ad akwai buk’atar kaje kad’an huta idan yaso ko zuwa anjima saika dawo, kema Oum zaki iya dawowa anjima ko akwai wani abu da Maleek d’in zai buk’ata bayan ya bud’e idanunsa, idan ba damuwa s

ai a taho masa dashi.

‿

Numfash Oum Ayush tad’an fesar, kana asanyaye tace.

“To.

‿

Yayinda acikin zuciyarta kuwa sam bataji tanason barin asibitin batare da taga farfad’owar Maleek d’in ba, saidai amma sam batason yiwa Yayan Mijinnata musu shiyasa.

Ahanka

li tasa hannunta ta d’an shiga tashin Laylerh’n, cikin sa’a kuwa Laylerh ahankali ta bud’e idanunta wanda suka kumbura suntum saboda kukan da tayi.

“Tashi muje gida ko Laylerh.

‿

Oum Ayush ta fad’a tana me gyarawa Laylerh’n zaman lufayan dake jikinta.

L

aylerh kuwa jin abunda Oum Ayush d’in ta fad’ane yasa ahankali ta girgiza kanta, saboda har yanzu bata dawo daidai ba, asanyaye cikin muryarta da ya d’an dashe tace.

“Bazan iya tafiya ba Oum Ayush, bazan iya koda fita daga d’akin nan ba, har sai naga Yah

Maleek ya bud’e idanunsa yana numfashi kaman yanda mukeyi, sannan kuma yana motsa jikinsa kamar yanda muke motsa namu jikin.

‿

*(Dan Allah Banason yawan k’orafi, Labarin Laylerh Maleek ahaka yake, komai dake cikinsa haka yake, sannan kuma babu wani wand

a yafi k’arfin karb’an tarin k’addarorin Ubangiji, da gani har kowa, abun so dai shine Allah Ya had’amu da kyakkyawar k’addara ako da yaushe.)*

*Saturday13/2/2021*

*8:37 pm*

2/16/21, 9:12 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymas

ardauna

*Not editing*

*Chapter 52

Oum Ayush dake tsaye, wanda jin abunda Laylerh’n ta fad’a ya sa ta sauk’e wani irin sassanyar ajiyar zuciya, k’warai ta d’anyi mamakin jin hakan daga bakin Laylerh’n, amma kuma sanin hak’ik’anin abunda ke cikin z

uciyar Laylerh’n, yasa babu wani amfanin mamakinnata. D’an gyara tsayuwarta tayi, tare da sa hannu ta dafa kafad’an ta, cikin yanayin tausasa murya da kuma salon da tasan zai taimaka mata wajen jawo hankalin Laylerh’n ahankali tace.

“Kiyi hak’uri mutafi

gida kinji, na miki alk’awarin cewa anjima kad’an zamu dawo, ko bakyaso idan Yah M.Jay d’innaki ya bud’e idanunsa, kuma yaji yana jin yunwa yaci abinci ne? kinsan dole dae zaiji yunwa ko? saboda haka muje gida ki tayani mu dafa masa abinci mai dad’i, nasa

n idan ya farfad’o zaiji dad’i sosae.

‿

Jin hakanne yasa ta d’anyi jim, tare kuma da d’ago kanta ahankali ta kalli Maleek d’in da har yanzu ke kwance kaman gawa, yayinda wata na’ura me yanayin computer dake gefensa ke tafiya yanda ya dace, wanda kuma aciki

n na’urar ne ake iya ganin bugun zuciyarsa.

D’an guntun hawayen daya fito daga cikin idanunta ta share, asanyaye ta d’an karyar da wuyanta gefe, cikin muryarta da har yanzun bata dawo daidai ba tace.

“Tsoro nakeji Oum Ayush, banason bayan natafi wani abu

ya samesa, yanzu ma haka nasan yanajin zafi, ki kalli jikinsa fa kiga, duk ya d’anji rauni glasses duk sun caccaka masa jiki, tayaya ma zai misalta irin wannan zafin da yakeji? ko yanzu ma me yakeji? Nasan ma....

‿

Kasa k’arasa maganan nata tayi, sakamak

on wani kuka daya so k’wace mata, wanda bisa dole hakan ya tilasta mata lumshe idanunta, take kuwa ruwan hawaye masu tsananin zafi suka sauk’a akan kumatun ta.

Wani abun mamaki kuwa kusan atare hawayen dake cikin idanun nata, da kuma wanda suke cikin id

anun Abbou Jaheed suka zubo, wanda duk yanda yaso hana hawayennasa fita ya kasa, saboda tsananin tausayin Maleek d’in da yakeji yasa gaba d’aya ya kasa controlling rauninsa, hak’ik’a ayau d’in da ace shi ba babban mutum bane me yawan shekaru da sanin ya ka

mata ba, to da ba abunda zai hanasa zama yayi kuka sosai kamar yanda k’ananan yara keyi, saidai kuma babu yanda ya iya, ya zame masa dole ya tausashi zuciyarsa, saboda bai isa hana Allah gudanar da Ikonsa ba.

Saurin saka hannunsa yayi ya share hawayennasa

tun kafun su lura da hakan, saidai kuma abunda bai sani ba shine, tuni Abbou Khareem ya ga hawayennasa, domin kusan akan idanunsa ma suka zubo.



Oum Ayush kuwa hannu takai ta sharewa Laylerh hawayen dake kwanace akan fuskarta, batare kuma da ta jira ce

war kowanne daga cikinsu ba ta jawo hannun Laylerh’n tare da mik’ar da ita tsaye, anutse ta nufi hanyar fita daga cikin d’akin, ba tare kuma da ta sake hannun Laylerh’n ba, haka suka fice daga cikin d’akin.

Fou’ad dake zaune Abbou Jaheed ya kalla, cikin y

in k’asa da murya yace.

“Fou’ad kuje ku huta, ka kai su Laylerh gida, zaka iya dawowa anjima kaima.

‿

“To.

‿

Kawai Fou’ad yace kana asanyaye ya mik’e daga zaunen da yake, na’urar dake bayyana bugun zuciyar Maleek d’in dake kwance ya kalla, kafun ahankali y

a sauk’e ajiyar zuciya tare dasa kai ya fice daga cikin d’akin.

Kamar rak’umi da akala haka Laylerh kebin Oum Ayush dake rik’e da hannunta, har zuwa wajen da sukayi parking motarsu.

Gefen me zaman Banza Oum Ayush ta bud’e mata, jikinta amatuk’ar sanyay

e ya shiga ta zauna, tare da juya kanta tana me kallon cikin asibitin, hakanan takeji ajikinta kamar idan tayi nesa da asibitin wani abu zai sake samun Maleek, sam Allah Yasani har acikin zuciyarta bataso ta fiya ba, amma babu yanda zatayi.

Isowar Fou’ad

garesu ne yasa Oum Ayush d’agowa ta kalleshi, asanyaye tace.

“Fou’ad Ina kuma zakaje, badai kaima tafiya zakayi ba?.

‿

Gajerar ajiyar zuciya Fou’ad d’in ya sauk’e, cikin kuma yanayin nutsuwa yace.

“Abbou Jaheed yace nazo nayi driving d’inku, amma ba damu

wa zuwa anjima kad’an zan dawo, kafun nan ma nasan Maleek d’in ya dawo hayyacinsa.

‿

Kai Oum Ayush ta jinjina cike da gamsuwa, take kuwa ta mik’a masa makullin motar, tare da bud’e murfin motar ta shiga gidan baya.

Shi kuwa Fou’ad b’angaren driver ya shig

a, anutse ya tada motar suka bar farfajiyar wajen.

Tunda suka d’auki hanya kuwa babu wanda yace da d’an uwansa k’ala, domin kuwa ko wannensu da abunda yake sak’awa acikin rai da zuciyarsa, musamman Laylerh da gaba d’aya ma tunaninta baya jikinta.

Ahaka

dai suka k’araso gaban makeken gate d’in gidan, jin k’aran horn d’insu ne kuma yasa take mai gadi ya wangale musu wawakeken

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login