Showing 201001 words to 204000 words out of 244674 words

Chapter 68 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

ta auri wani Namiji mai tawaya kamar Maleek d’in ba, zai so ace ta gina rayuwarta akan dogon tsauni ta yanda zata cimmawa nasarori da yawa.

Amma kuma k’ad

dara ta riga fata, k’addarar soyayyar dake tsakaninta da Maleek, wanda girmanta ya zarce tunanin mai tunani.

Asanyaye yasa hannayensa ya share hawayen dake kwance akan fuskarsa, hannun Laylerh’n da har yanzu ke kuka ya kamo, cikin sanyin murya da kuma

wata irin sabuwar k’aunarta da yaji ta sake shiga zuciyarsa yace.

“Kinason zama da Maleek duk da kinsan lalurar da yake d’auke da ita?.

‿

Kanta ta jinjina masa alaman “Eh.

‿

Still kuma bata daina kukan da takeyi d’inba.

Tsananin tausayin tane ya

lullub’e zuciyar Abbou Jaheed, musamman da yayi imani cewa, har abada bazai tab’a samun y’a irin Laylerh’n ba, komai na rayuwarta daban ne, Tabbas yasan cewar koda ace babu soyayya atsakanin LaylerhMaleek d’in, zata iya zama dashi tare da duk irin k’adda

rar da tazo mai.

Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da sauk’e wata sassanyar ajiyar zuciya.

Hannunsa yasa ahankali ya shafa kanta, cikin nuna tsananin kulawa agareta yace.

“Nagode miki Laylerh, nagode sosai da Allah Ubangiji Yabani ke, Allah Ya miki

albarka, domin badan keba nasan abune mai wahala Maleek ya samu macen da zata zauna dashi, saidai kuma har yanzu inaji ajikina faruwar hakan tamkar cutar da kanki ne.

‿

Kanta tayi saurin girgizawa, tare da d’an motsa labb’an bakinta da takejin sunyi mat

a nauyi sosai.

Araunace tace.

“Babu cuta ko takurawa, Abbou Jaheed Yah M.Jay ne fa!!

‿

Takai k’arshen maganar nata cikin wata irin sangartacciyar murya, mai tafiya da sautin sheshshek’an kuka.

Idanu Abbou Jaheed ya tsura mata, Yayinda abayyane ya

ke nazartar wani abu adangane da ita.

Adaidai lokacin kuwa Abbou Khareem da kuma Oum Ayush, wanda suke tsaye abakin k’ofar shigowa falon, almost 15mn ago suka kalli juna, gaba d’ayansu hawaye ne kwance acikin idanunsu, kasancewar sunji duk abunda Abbou

Jaheed da kuma Laylerh’n suka tattauna.

Cikin jin dad’i da kuma k’arfafa guiwa suka k’arasa shigowa cikin falon.

Akusa da Abbou Jaheed Abbou Khareem ya zauna, Yayinda Oum Ayush kuwa ta kamo hannun Laylerh dake ta sakin sheshshek’an kuka, cikin kul

awa tare da kuma son dakatar da kukan Laylerh’n tace.

“Kukan ya isa haka muje kici abinci.

‿

Kasancewar gaba d’aya jikinta asanyaye yake ne kuma, yasa bata musawa Oum Ayush d’in ba suka fice daga cikin falon.

Abbou Jaheed kuwa fuskantar Abbou Kha

reem yayi, cikin yanayin fahimtar juna suka shiga tattaunawa akan sabuwar magana da kuma al’amarin daya fuskantosu batare da sun shiryawa hakan ba.

Abbou Khareem ne ya gyara zamansa, tare da duban yayannasa fuska asake, cikin kuma son bawa d’an uwannas

a k’warin guiwa yace.

“Naji duk abunda kuka tattauna da Laylerh, na kuma fahimci komai, saidai inaso ka goge kallon cutarwa da kakewa abun, domin Laylerh da Maleek abu d’aya ne, mun riga da munsan hakan tuntuni, kowanne yana rayuwa da soyayyar d’an uwan

sa acikin zuciyarsa, kaima kuma shaidane akan hakan, ko azaman da yayi a hospital ka shaida Son da yake mata, wallahi matuk’ar muka sakeyin wani ganganci zamu iya rasa su gaba d’aya, domin bawai yanzu ne suka fara son juna ba, kowannensu an haliccesa ne d

a soyayyar d’an uwansa acikin jini da tsokarsa, saboda haka amatsayina na Yayan Mahaifin Laylerh, na bawa Maleek auren ta, batare kuma da kokonto ko wani shakka ba, mun kuma amince da lalurar da ta sa mesa, domin munyi Imani cewa k’addarace dake iya sauk’a

akan kowa, saboda haka a

fara shirye shiryen yin aurensu Insha Allah Next Saturday za’a d’aura musu aure.

‿

Ajiyar zuciya mai k’arfi Abbou Jaheed ya sauk’e, tare dasa bayan hannunsa ahankali ya goge hawayen da suka cika idanunsa, hawayen dake d’auke da m

a’anoni daban daban, saidai kuma abu mafi rinjaye na dalilin hawayennasa shine, matsanancin tausayin LaylerhMaleek d’in daya cika zuciyarsa.

Agefe guda kuwa sosai ya gamsu da kalaman Abbou Khareem, Insha Allah Kuma auren Laylerh da Maleek za’ayi shi kama

r yanda Abbou Khareem ya tsara.

Acan sashin Oum Ayush kuwa, afalo Oum din ta zaunar da Laylerh’n, tare da ajiye mata plate d’in abinci agabanta.

Saidai kuma kwata kwata lomanta biyu ta ajiye spoon d’in abincin, hakan ya faru ne kuma saboda wani irin c

iwon kai da takeji, ba komae ne ya jawo mata ciwon kan ba kuwa face kukan da tayi.

Lura da cewar batajin dad’ine kuma yasa bayan tayi sallan la’asar Oum Ayush ta bata maganin ciwon kai tasha, bayan tasha maganinne kuma ta wuce d’aki ta kwanta, sanin ku

ma da tayi cewar ba kyau yin bacci bayan Salla’n la’asar ne, yasa ta kunna karatun Al’minshawy, asanyaye ta soma bin karatun.

*Washington DC*

Sake gyara kwanciyarsa yayi akaro na barkatai, tare kuma da lumshe idanunsa wanda sukayi jajur, sosai yakej

in wani irin sauyi ajikinsa, musamman acikin kwana biyun da suka wuce, duk da cewar kuwa yasan yana da k’arfin feeling amma ayanzu abunda yakeji d’in ya soma zarce tunaninsa.

Wanda har yakaisa ga fara tunanin iya jurewa abubuwa biyun dake damunsa, wanda a

sanadinsu yake neman zama zautacce.

Hannunsa ya d’aura akan k’irjinsa, daidai saitin zuciyarsa dake wani irin bugawa, sam baisan meyasa ayanzun yake samun kansa da rashin iya b’oye rauninsa ba, abubuwa da yawa suna damunsa, wanda idan ya tuna sai yaji z

uciyarsa tayi masa rauni sosai.

Again sake gyara kwanciyarsa yayi, wanda hakan kuma ne yasa Fou’ad dake zaune k’ura masa ido, tun d’azu yana ankare da yanayin Maleek d’in, saboda ya fahimci cewa, tunda suka zo USA d’in kwata kwata hankalin Maleek ba a

jikinsa yake ba, koda yaushe abu d’aya kawai yakeyi, sam shikam bai tab’a sanin cewa Soyayya nasa hauka ba, sai akan M.Jay.

Wayarsa da tayi k’ara ne yasashi janye idanunsa akan Maleek, tare da kai hannunsa ya d’auki wayar, jin kuma da yayi Abbou Jaheed

ne akan layi, yasashi daidaita kansa tare da gaishe da Abbou’n.

Daga haka kuwa bai sake cewa komae ba, sai shiru da yayi yana me sauraren abunda Abbou Jaheed d’in ke fad’a masa.

Wanda ni kaina bansan abunda Abbou’n ya fad’a masa ba.

Ak’arshe dai “

To.

‿

Kawai Fou’ad d’in yace, tare da zame wayar daga kan kunnensa, fuskarsa d’auke da murmushi yasa ke kai dubansa ga Maleek.

Dake ta faman juyi akan gado.

Wani irin murmushi mai d’auke da ma’anoni daban daban yayi, batare kuma daya cewa M.Jay d’in k

omai ba ya mik’e tsaye, direct wajen drawer’n dake Cikin d’akin ya nufa, bud’e murfin drawer’n yayi, anutse ya soma tattare duk wani abu na Maleek daya sani, kama daga kan k’ananun kayan amfani harma dasu laptop.

Maleek kuwa dake kwance jin motsin Fou’a

d d’in yayi yawa ne yasashi bud’e idanunsa ahankali ya tsaida ganinsa akan Fou’ad d’in.

Fou’ad dake zuge zip d’in jakan dake hannunsa, shima kallon Maleek d’in yayi, gane nufin kallon tambayan da Maleek d’in keyi masa ne kuma yasashi, gyara tsayuwarsa,

cikin yanayin dake nuna alaman maganan da zaiyi d’in serious ne yace.

“Gobe da safe zamu bar USA hakan kuma umarnine daga Abbou Jaheed bawai daga ni ba, lallai yace mubar kome mukeyi mu koma Nigeria agobe gobe.

‿



Maida idanunsa yayi ya lumshe, batar

e kuma daya ce k’ala ba, hakanan kuma yaji bazai iya musawa tafiyar tasu ta gobe ba, duk da kuwa basu gama kammala aikin daya kawo su USA d’in ba.

Fou’ad kansa yayi mamakin ganin Maleek bai musa akan tafiyar tasu ba, saboda sanin halinsa da yayi na yawa

n musu da kafiya, idan kuma bai shiryawa abuba to babu wanda ya isa sakashi.

Da haka dai ya cigaba da kimtsa duk wasu abubuwansu, shi kuwa Maleek tamkar mai bacci haka yayi, saidai kuma bawai baccin yake ba.

*Washe gari.*

Tun tashinta daga baccin y

au d’in takejin gaba d’aya jikinta amace, ga kuma ciwon kan da tun jiya yake damunta, duk da tasha magani kuwa har yanzu yak’i sauk’a.

Wani abun daya bata mamaki kuwa shine, lura da tayi da yanda y’an gidan keta hidima, sam kuma bata kawo aranta cewar

wai hidiman aurenta da Maleek ne aka somashi tun yanzu ba, domin bata da labari ma akan antsaida ranar auren.

Ko yanzuma fitowarta daga wanka kenan, inda take zaune akan gado, daga ita sai wani mini towel a jikinta.

Turo k’ofar d’akin Oum Ayush ta

yi ta shigo, hannunta d’auke da wani tray, wanda samansa ke d’auke da wasu k’ananan 3cups.

Ganin Laylerh’n da tayi zaune abakin gado ne kuma yasa ta, fad’ad’a murmushin dake kan fuskarta, tare kuma da k’arasowa ta zauna a gefen Laylerh’n.

“Ina kwan

a.

‿

Laylerh’n ta fad’a asanyaye, kasancewar tun tashinta bata had’u da Oum Ayush d’in ba.

“Lafiya kalau ya ciwon kan naki, fatan yayi sauki?

‿

Fuskarta tad’an shagwab’e, kana cike da sakalci tace.

“Da d’an sauk’i.

‿



Murmushi Oum d’in tayi hade

da fad’in.

“Allah Ya k’ara sauk’i, karb’i wannan kishanye.

‿

D’aya daga cikin cups d’in ta mik’o mata, wanda cikinsa ke d’auke da tatacciyar madarar shanu.

Idanunta ta d’an zaro waje, Kamar zata ce wani abu kuma sai ta fasa, karb’an cup d’in tayi tak

ai bakinta, kamar yanda Oum Ayush d’in ta buk’ata kuwa saida ta shanye tas, kafun ta ajiye kofin.

Again wani cup d’in ta sake mik’o mata, shid’in ma dai wani abu me kamar pure honey ne acikinsa, kasancewar kuma yana da zak’i sosai ne yasa take ta shanye

sa.

D’ayan cup d’in daya rage kuwa ajiyesa agefen bedside Oum Ayush d’in tayi, tare da ce mata tana shan maganin dake cikin kofin duk bayan 20minutes, saboda yana da k’arfi sosai nema yasa ba’aso ashanyesa nan take.

Ita dai To kawai tace, duk da akwai

magana abakinta kuwa, kasa furtawa tayi, domin sam ba d’abi’arta bane, yawan tambaye tambaye.

Fita kuma da Oum Ayush tayi acikin d’akinne, ya bata daman tashi ta sakawa jikinta riga da sket na wani turkish material mai kyau, wanda suka matuk’ar karb’an

jikinta.

Wayarta ta d’auka, har takai bakin k’ofar fita daga d’akin kuma sai ta dawo, cup d’in magani mai kaman yoghurt d’in da Oum Ayush ta ajiye mata ta d’auka, atsorace ta d’an lasa, wani irin zaki da kuma gard’in madarar da taji ya maye bakinta ne,

yasa ta kafa kai har saida tasha Kusan rabin cup d’in kafun ta ajiye ta fita tana lashe baki.

Tana fitowa falon kuwa direct dining area ta nufa, saboda sosai takejin yunwa, harta zubawa kanta abinci sai kuma ga Oum Ayush hannunta d’auke da bowl na yan

kakkun kayan fruits.

Abincin dake gaban Laylerh’n ta d’auke, cikin yanayin lallami da kulawa tace.

“Daga yau kayan fruits zaki na sha, madadin wani chips and ketchup da omlet.

‿

Takai k’arshen maganan nata tana me ajiye mata bowl d’in fruits d’in aga

banta.

Domin itakam Allah Yasani ayanzu so take ta gyara Laylerh’n sosai fiye da wanda tayi mata abaya, duk dama tasan still she’s virgin.

Laylerh dake jin yunwa kuwa babu musu, ta jawo bowl d’in fruits d’in ta soma sha.

Saida tasha fruits d’in sosa

i kafun taji ta k’oshi.

Dawowa cikin falon tayi ta zauna, tare da zubawa TV idanu, Tana kallon series film na Money Heist. (Lacasa De Papel)

Yayinda Oum Ayush kuwa ke zaune agefe tana waya, da dukkan alama kuma furnitures takeyin order, domin asabo

da bikin, za su sanja gaba d’aya furnitures d’in gidan.

*10:00 am daidai jirginsu ya sauk’a acikin garin Abuja Nigeria, tun kafun ya gama sauk’owa daga kan matattakalan jirgin kuwa ya hangi Abbou Khareem yazo d’aukarsu, mamaki ne yad’an kamasa asakamak

on ganin Abbou Khareem d’in da yayi, saidai kuma bai nuna ba, haka suka shiga motar Abbou Khareem d’in.

Aikuwa mamakinnasa bai kankama ba, saida yaga sun d’auki hanyar d’aya daga cikin gidajensa dake Wuse zone 6.

Sosai k’warai yayi mamaki, amma kuma

saidai cewa da Abbou Khareem d’in yayi ana gyaran wancan gidan nasu ne, yasa shi katse mamakin nasa.

Abbou Khareem na gama daidaita parking, ya bud’e murfin motar ya fito, tare kuma da wuce wa cikin gidan kaitsaye.

Saboda dama time to time yakan zuwa

gidan yad’an huta.

Abbou Khareem kuwa da Fou’ad Koda suka shigo cikin falon, basu iskeshi ba, domin tuni ya shige bedroom d’insa dake cikin gidan danyin wanka.

Saboda kafun su iso din Abbou Khareem yasa masu aiki sun tsabtace ko ina na gidan.

Foo

d flasks na abinci kala kala Abbou Khareem ya ajiye musu, wanda musamman yasa Oum Ayush ta yisu, duka kuma favorite d’in Maleek d’inne.

Saida ya sake jaddadawa Fou’ad maganan kulawa da Maleek d’in kafun ya juya ya tafi.

Maleek kuwa koda ya fito awan

ka wani 3quater jeans and blue shirt ya saka, batare kuma daya tsaya yin wani abuba ya fito zuwa falo.

Inda ya samu Fou’ad ya shiga wanka.

Zama yayi akan had’add’un cushions d’in dake cikin falon, tare da jawo food flasks d’in ya bubbud’e, duk da cew

ar baya wani jin yunwa sosai, haka ya d’ebi abincin yaci, domin bama sai an fad’a masa ba yasan cewa Oum Ayush ne tayi girkin.

Koda Fou’ad ya fito awanka shima zama yayi yaci abincin sosai.

Bayan ya kammala cin abincinne kuma ya soma kokarin Jan Malee

k d’in da hira.

Saidai shikad’ai yake ta magana, Maleek baya cewa ko k’ala, hasalima lumshe idanunsa yayi tamkar maiyin bacci, shikuwa Fou’ad dama ya saba hakan.

Acan gida b’angaren Laylerh kuwa gaba d’aya wunin yau haka tayisa, afalon Oum Ayush ta

na kallo, saidai idan lokacin sallah yayi takan tashi taje tayi sallah.

Akuma yau d’inne takejin labarin tafiyan Maleek da kuma dawowansa, taji hakanne kuma awajen Abbou Khareem da yake sanarwa awaya cewar Captain M.Jay d’in ya dawo.

Yayinda agame da

harkar shirye shiryen biki kuwa abun keta kankama, arana d’aya kawai har sunci k’arfin shirye shiryen nasu.

Bayan kuma anyi sallan magriba ne Abbou Jaheed ya damk’awa Abbou Khareem tsabar kud’i na Two Million amatsayin sadakin Laylerh, wanda ya cire y

a biya a aljihunsa, domin dama alk’awari ya d’auka cewar shi zai biyawa Maleek d’in sadakin aure’n Laylerh’n, saboda awannan karon so yake dukansu yayi musu gata sosai, tare kuma da fad’in cewa za’a kawo lefen Amarya ranar d’aurin aure.

Abbou Khareem ku

wa duk da yasan cewa bayar da kad’an d’in sadaki nada matuk’ar mahimmanci, amma haka ya karb’i two million d’in, saboda abune da yake abayyane cewa, Laylerh Macece mai matuk’ar daraja, sannan kuma har yanzu tana tare da budurcinta, baya ga haka kuma yayi

Na’am da kawo lefen ranar d’aurin aure.

Acan cikin gida kuwa Laylerh ce zaune akan sallaya, domin idar da sallah’n Magriba d’inta kenan, saidai k’ara da kuma tsuwan da wayanta keyi ne, yasa ta mik’ewa tsaye, tare da k’arasawa inda ta ajiye wayartata.

Idanunta da suka sauk’a akan screen d’in wayarne, suka wani irin k’ara girma, take kuma taji zuciyarta ta soma bugawa.

Rubutun dake yawo akan screen d’in wayar ta tsurawa ido, cikin kuma wata irin muryarta dake shaking tace.

“NAJEEB

‿

*(He

y guys kun shiryawa tomorrow Idan darai da lafiya kuwa?)*

*8:20 pm*

*23/March/2021*

3/26/21, 8:37 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

#WEDDING FATIHA

*Chapter 72*

*”NAJEEB

‿

*

Ta k’ira sunan dake yawo akan screen d’in wayar, cikin zallan

yanayi na mamaki, domin ko kusa bata tab’a kawowa aranta cewar k’iran Najeeb d’in zai shigo wayarta adaidai lokacin ba.

Tsurawa screen d’in wayar nata idanu tayi, had’e kuma da tsayawa ta kasa picking call d’in, tamkar kuma yanda numfashinta ke fita d

a sauri sauri haka ma bugun zuciyarta, idanunta ta d’an lumshe ahankali, tare da kai hannunta ta d’auki wayar nata k’irar iPhone11, saidai kuma cikin rashin sa’a tana d’aukar wayar, k’iran Najeeb d’in na katsewa.

Ai kuwa katsewar k’iran nasa ne ya bata

daman sauk’e wani irin k’akk’arfan ajiyar zuciya, lumsassun idanunta ta bud’e tare dajan jikinta ta zauna akan wani Gothic chair dake kusa da gadon dake cikin d’akin.

Kunna hasken screen d’in wayar nata tayi, still kuma sunan Najeeb d’in take kallo, Y

ayinda a zuciyarta take tunanin sake bin k’iran nasa, saidai kuma idan ta bi k’iran nasa ya d’aga tace masa me?

Samma ita batayi tunanin k’iransa ba, tun bayan abunda ya faru atsakaninsu, sai kuma gashi shid’in akaron farko ya k’irata.

D’an sake lums

he idanunta tayi alokacin da hoton fuskarsa ya fad’o mata, murmushin daya sabayi akullum ne ya shiga yawo acikin tunaninta, wanda hakan yasa itama batare da tasani ba tad’an saki murmushi, Tabbas batajin soyayyarsa acikin zuciyarta, haka kuma batajin k’iya

yyarsa, cause ma bashi da wani aibu ko tawaya da zaisa mace ta k’isa, kawai dai ta tsaida zuciyarta awaje d’aya ne, sannan kuma zuciyartata akan abu d’aya kawai ta ginu, wanda kuma har abada batajin zuciyartata zata tab’a sauyawa daga kan abunda ke rayuwa

acikinta.

Turo k’ofar d’akin da akayine kuma yasa tayi saurin bud’e idanunta, ganin kuma cewar Oum Ayush ne ta shigo cikin d’akin yasa tayi saurin kawar da tunanin da takeyi.

Oum Ayush kuwa cikin kulawa ta dubi Laylerh’n tare da tambayarta ko tayi

sallah.

Kai Laylerh’n ta jinjina mata alaman “Eh.

‿

“Yauwa to taso muje a fara miki wankan Amarya, saboda na kula idan ba mufara yanzu ba, to anan gaba bamu da wani isashshen lokaci.

‿



Ta kai k’arshen maganan nata, tana me kamo hannun Laylerh’n.

Laylerh kuwa jin abunda Oum Ayush ta fad’ane yasa ta d’an shiga mamaki, cikin kuma son samun gamsuwa tace.

“Wankan Amarya kuma Oum Ayush? Meyasa? Ni yanzu ai ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login