Showing 213001 words to 216000 words out of 244674 words
mutane da yawa soma yi mata video ba.
Hannun Laylerh’n Oum Ayush ta mik’awa Aunty Zee, tare da yi mata alama akan taje tasa Laylerh’n amota.
“To.
‿
kawai
Aunty Zee d’in tace, tare kuma da kama hannun Laylerh’n kamar yanda Oum Ayush ta buk’ata, haka suka fito daga cikin falon, Aunty Zee na rik’e da Laylerh wanda take d’an sakin sheshshek’an kuka, abayanta kuwa Theemah da Aleeya ne, wanda sune zasuyiwa Layle
rh’n rakiya, sai kuma y’an uwansu dake Egyft wanda suka zo.
Fou’ad wanda ya d’ebo abokanansa suka zo d’aukan auren, batare da Maleek d’in ma ya sani ba, shida kansa ya bud’ewa Laylerh’n k’ofar had’add’iyar White Range Rover car, Aunty Zee ta sanyata aci
ki, tare da shiga itama ta zauna.
Ganin hakanne kuma yasa y’an tsirarun mutanen da zasuyiwa Laylerh’n rakiya suka shiga sauran motocin, saboda kuma tsabar yawan motocin da Fou’ad d’in ya kawo ne yasa kowacce mota mutum d’aya ne kawae ya shigeta, sauran
kuwa haka suka zauna empty babu kowa acikinsu, domin koda ma ace mutanen suna da yawa, To dole akwai cars d’in da zasu koma empty.
Fou’ad dake k’ok’arin driving motar da Laylerh’n ke ciki ne, idanunsa suka hango masa Aleeyah wacce ke shirin shiga wata m
ota ta daban, idanunsa yad’an tsaida akanta, tare kuma da soma k’arewa gaba d’aya halittar jikinta kallo, saboda lokaci d’aya yaji wani feeling akanta, Tabbas yarinyar tayi mishi sosai, domin tana da irin structure’n da yake matuk’ar so awajen Mace, kasanc
ewarta brown skin kuma shine ya k’ara sawa yaji zuciyarsa ta narke akanta sosai.
Har ma yaji ajikinsa cewar inama da ace motarsa ta shiga ba na wani can daban ba.
Saidai kuma tunawa da yayi cewar duk guri d’aya zasuje ne, yasashi jin sanyi acikin zuci
yarsa, anutse ya tada motar.
One by one kuwa haka cars d’in suka soma fi cewa daga cikin gidan.
Adaidai lokacin da suka mik’a kan titi ne kuma Laylerh, da kejin wani irin bacci na fusgarta Ahankali ta kwantar da kanta akan cinyar Aunty Zee.
Hakanan
bata san meyasa ba takejin wani irin abu mai kama da fargaba, tsoro da kuma fad’uwar gaba na yawan tunkararta, wanda har hakan yasa zuciyarta ke beating fast fast, awani bak’on yanayi na musamman takejin kanta, yanayin da sam bataji makamancinsa alokacin
da aka d’aura mata aure da Najeeb ba.
Gaba d’aya tunaninta ya tafi ga yanda zata fuskanci Maleek d’in amatsayin mijinta, har yanzu ganin abun takeyi tamkar amafarki.
Batare kuma da sunyi tafiya mai tsawo ba duk motocin suka tsaya, adaidai lokacin d
a suka iso tsakiyar Maitama, agaban wani makeken gate mai masifar kyau da tsari, sauran cars d’inne sukayi parking awaje, Yayinda matashin maigadin gidan, ya wangale gate d’in, Fou’ad kuwa da Laylerh’n ke cikin motarsa anutse ya tura hancin motar cikin ma
keken gidan, da had’uwarsa ya zarce duk wani misali.
Kasancewar kuma compound d’in gidan nada girma sosai ne, yasa saida Fou’ad ya d’anyi tafiya maitsawo kafun yayi parking motar, agaban wani katafaren dogon gini dake cikin compound d’in gidan.
Yana
gama daidaita parking d’in kuwa, ya fito tare da zagayowa cikin sauri ya bud’ewa su Aunty Zee k’ofar motar.
Anutse Aunty Zee ta kamo hannun Laylerh, wacce zuwa yanzu sautin kukan nata ya tsaya, saidai hannunta na dama dafe yake da saman mararta.
Ah
aka suka fito daga cikin motar Aunty Zee na rik’e da hannunta, kaitsaye suka nufi wannan had’add’en ginin.
Aunty Zee ne ta bud’e had’add’en k’ofar babban falon tare da cewa Laylerh tayi bismillah sannan kuma ta shiga da k’afar dama.
Hakan kuwa akayi
cikin zuciyarta tayi bismillah’n tare da saka k’afarta na dama acikin had’add’en falon da kaitsaye za’a k’iransa da sunan Aljannar duniya, musamman yanda aka k’awata cikinsa da 2021 Austin classic sofas masu matsanancin kyau da tsada.
Two bedroom ne a
cikin falon, sai kuma stairs d’in da zaka taka wanda zai kaika sama, kasancewar kuma asaman d’akin Laylerh’n yake, hakan yasa direct Auny Zee ta wuce saman da ita.
Again kuma wani babban falon suka Tatar asaman, wanda shima aka k’awata cikinsa da kay
an furnitures masu kyau, saidai kuma sofas d’in dake cikin falon sun banbanta dana falon k’asa, kasancewar su way’annan d’in Culliana Victoria’n sofa ne.
Kamar kuma yanda yake two bedrooms afalon k’asa haka ma ya kasance acikin falon saman, d’akin da ya
ke ana biyu Aunty Zee ta nufa da ita, wanda kuma shima aka k’awata cikinsa da furnitures masu kyaun gaske.
Ko ina dake cikin falo da d’akin kuwa daddad’an k’amshin turaren wuta ne ke tashi, sai kuma sanyin A/C’n dake tashi.
Kan lallausan bed d’in daya
sha bedsheet na alfarma Aunty Zee ta zaunar da Laylerh’n, tare kuma da gyara mata rufin mayafin dake jikinta.
Daidai lokacin kuwa aka soma k’iraye k’irayen sallan magriba.
Kallon su Theemah dake ta santin kyau da kuma had’uwar gidan Laylerh’n Aunty
Zee tayi, tare dayi musu alama akan suje falo su jirata, babu musu kuwa haka suka juya ita da Aleeya suka fice daga cikin d’akin, Theemah kuwa da gaba d’aya bakinta ya kasa rufuwa, kallon Aleeya tayi cikin yanayin zumud’i tace.
“Lallai Yau akwai show
agidannan, da ace Ina da dama to da yau na zama sauro ta yanda zan morewa idanuna, Domin kuwa ko nayi imagine this night abun nasan sai yafi tunani na
‿
Dariya Aleeya tayi tare da d’an girgiza kanta, domin ad’an sabon da sukayi da Theemah’n ta fahimci ce
war, Theemah’n irin mutanen nanne da basa iya b’oye gaskiyar abunda ke cikin rai da zuciyarsu.
Acan cikin d’akin kuwa hannun Laylerh’n Aunty Zee ta kamo, cikin kulawa tace.
“Mu zamu koma please Laylerh ki kula da kanki da kuma Mijinki kinji, duk abun
da ya buk’ata awajenki kada kice masa a’a, domin komai dake jikinki halal d’insa ne, ke d’in yanzu mallakinsa ne, sannan kuma basa ingantacciyar farinciki ayanzu yana wuyanki ne, please Laylerh ki kula kinji Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya!!
‿
Haway
e masu sanyine suka fito daga cikin idanunta, lokaci d’aya kuma taji kuka mai sauti na shirin k’wace mata.
Fahimtar hakan da Aunty Zee tayi ne kuma yasa ta juya, cikin sauri ta fice daga cikin d’akin, saboda tasan idan ta tsaya kukan Laylerh’n zai iya k
arya mata zuciya.
Kallon su Theemah da kuma sauran y’an uwa dake zaune a cikin falon tayi, Cikin kulawa tace.
“Kutashi mu tafi ko, kada Ango yazo ya samemu, har haushi ya kamasa ya bindigemu, kunsan wani lokaci masu bindigan nan birkitattun mutane ne
.
‿
Dariya gaba d’ayansu sukayi, had’e da mik’ewa tsaye duk sukayi waje, kasancewar way’anda suka kawosu sune zasu maidasu.
Koda suka fita kuwa already sun samu dama su ake jira, hakan yasa basu wani b’ata lokaci ba, suka bar gaba d’aya arean unguwar
.
Jin k’aran mota da kuma alaman tafiyansu ne yasa Laylerh, sakin wani irin marayan kuka, me cike da tsananin kewarsu, saida tayi kukannata kuma kafun ta sauk’o daga kan gadon, kasancewar tana da alwala ajikinta ne kuma yasa, ta d’aukan wani hijab dak
e aje agefen gadon nata, kan wani lallausan carpet dake Malale agefen gadon ta hau, tare da tada sallah’n magriba.
Still kuma Koda ta idar da sallah’n ci gaba da zama akan carpet d’in tayi, har aka kira sallan Isha, bayan ta sallame sallan ne kuma ta k
oma saman gadon ta takure kanta waje d’aya.
Domin yanayin yanda taji gidan ya d’auki shiru, shine abunda ya k’ara fad’ad’a tsoron da ke kwance acikin zuciyarta.
Tabbas akullum akuma koda yaushe burinta shine ta kasance dashi, amma meyasa yau gashi da ta
san cewar Lallai zata kasance dashi takejin tsoro, da kuma wani irin fargaba na lullub’eta after 1second?
*8:30 pm*
Ahankali cikin kuma yanayin daya saba gudanar da al’amuransa, ya zura babbar rigar tsadadden shaddan dake jikinsa, wanda tayi masa ky
au sosai ta kuma k’ara bayyana kwarjininsa, kasancewar kuma shadda getzner d’innasa nada colour’n grey, shi yasa hasken fatarsa sake bayyana, Yayinda lallausan black beard d’in dake kwance akan fuskarsa ke shining.
Had’add’iyar hula ya saka akansa, wacce
take yanayi da kaya da kuma takalmin Lolu soft leather dake k’afansa, wanda ak’alla kud’ad’en takalman yakai 50k, sae kuma silver colour original Rolex watch daya d’aura akan tsintsiyar hannunsa.
Tabbas shikansa yasan yayi kyau sosai fiye ma da shigar
da yayi d’azu, turaren Ouds d’insa masu sanyin k’amshi ya fesa wa duk jikinsa, wanda hakan yasa gaba d’aya cikin bedroom d’in nasa ya d’auki sassanyan k’amshi.
Wayoyinsa da kuma car key d’insa dake kan mirror ya d’auka, cikin takunsa dake bayyana nuts
uwa da kuma cikar kamalansa ya fice daga cikin d’akin.
Kaitsaye compound d’in gidan nasa ya fito, sam babu kowa aharabar gidan daga Abdoul sai kuma gateman d’insa dake zaune abakin gate.
Abdoul kuwa dake tsaye ganin Ogan nasa ya fito ne yasashi sau
rin k’arasowa kusa dashi, tare da d’aga hannu ya sara masa.
Car key d’in sabuwar motarsa k’irar 2021 Mercedes Benz GLE450 dake hannunsa ya mik’awa Abdoul, cikin sauri Abdoul ya karb’i key d’in, tare da k’arasawa parking space ya ciro motar, wanda ko ta
b’a hawanta ba ayi ba.
Agaban Maleek d’in yayi parking motar, tare kuma da fitowa ya bud’e masa murfin motar, anutse ya shiga gidan baya ya zauna.
Yana gama daidaita zaman nasa kuwa Abdoul yaja motar suka fice daga cikin gidan.
Kaitsaye Maitama suka n
ufa, yau akaron farko yana jin kansa acikin wata sabuwar duniya da kuma sabuwar rayuwa.
*(Please Ina buk’atar addu’arku
🙏🏻
because two days I’m in a bad mood
😰
)*
*29/3/2021*
3/30/21, 8:48 PM - Ummi Tandama: *75*
Sassanyun idanunsa ya lumshe tare
da sake jingina bayansa da jikin kujerar motar.
Wani irin bugawa yakejin zuciyarsa nayi, Yayinda abubuwa da yawa ke yi masa yawo acikin k’wak’walwarsa, akaron farko yanajin kansa amatsayin wani na daban, bawai Captain Maleek ba.
Har yanzu jin kansa yake
tamkar acikin mafarki.
Komai na tunaninsa ya tsaya, saboda haka yana buk’atar wanda zai taimaka masa, saboda shi
Baisan komai agame da abubuwan da zasu faru yau d’in ba, baisan tayaya kuma ya inane zai fara ba.
Hannunsa dake d’an rawa ya d’aura akan
saman k’irjinsa, daidai saitin heart d’insa dake beating da sauri.
“Tsoro kakeji Maleek?.
‿
Wani sashi na zuciyarsa tayi masa tambayar da yasashi, saurin bud’e idanunsa, ahankali ya d’an soma girgiza kansa, domin sam bayason gangar jikinsa su amince a
kan lallai tsorone ke damunsa, bayason hakan kwata kwata.
Tabbas ayau yana buk’atar confidence, confidence d’in da zai tunkari Laylerh’n dashi, duk da kuwa cewar shid’in mai tsananin weakness ne akanta, but amma yau yakanji kamar bakinsa bazae iya furta w
ani abu agareta ba.
Lallai yana buk’atar zama strongman, Domin yayi imani cewar, da irin wannan raunin zuciyartasa babu abunda zai iya.
Maida kansa yayi k’asa ahankali, tare da sake lumshe idanunsa, wanda cikinsu ke bayyana abubuwa da dama.
Daidai
lokacin kuwa yaji Abdoul ya rage gudun motar tare da tsayawa, wanda hakan ke nuna masa alaman cewar sun iso gidan.
Ahankali ya d’ago kansa, Inda ya sauk’e idanunsa akan Fou’ad dake tsaye ajikin motarsa, hannayensa rik’e da wasu manyan ledodi guda biyu.
Saurin fitowa daga cikin motar Abdoul yayi, tare da zagayowa ya bud’ewa Ogannasa k’ofar motar.
Ahankali ya sako k’afa da gangar jikinsa waje, adaidai lokacinne kuma zuciyarsa ta tsananta bugawa.
Sassanyar iskar hadarin dake busawa ne ya daki fuskars
a, wanda hakan yasa shi d’an lumshe idanunsa.
K’arasowa inda MALEEK d’in ke tsaye Fou’ad d’in yayi, tare da soma k’are masa kallo, domin zai iya cewa kyau da cikar halittar Maleek d’in bai tab’a bayyana irin na yau ba.
Hannunsa ya kamo cikin nuna tsa
nanin farincikinsa yace.
“Kowani mutum aranar aurensa sai yayi kyau, komin miskilancinsa kuma sai annuri ya bayyana akan fuskarsa, amma kai naka kyaun daban yake M.Jay, kyawun da kayi ayau mai d’auke da sirruka daban dabanne, gashi kuma Ubangiji Ma naso
nku, saboda zai raya muku wannan daren da ni’imarsa ta ruwan sama, ka daure Maleek domin Laylerh farinciki take buk’ata awajenka.
‿
Yakai k’arshen maganar nashi yana me d’an bubbuga kafad’an Maleek d’in, saboda bashi k’warin guiwa.
Batare kuma daya ji
ra abunda Maleek d’in zaice ba, ya ja hannunsa kai tsaye suka nufi cikin gidan.
Yayinda kowani taku d’aya zaiyi sai yaji bugun zuciyarsa ta tsananta.
Ga kuma wani irin yanayi dake kokarin mamaye duk wani kafar sadarwa na jikinsa.
Lokacin da suka samu
kansu acikin baban falon k’asan kuwa, gaba d’ayansu saida suka lumshe idanunsu, saboda wani fitinannen k’amshin turare da kuma sanyin AC daya bugesu.
Fou’ad ne ya ajiye ledan dake hannunsa, tare da kallon Maleek d’in, fuskarsa d’auke da murmushi yace.
“Amaryarka tana sama d’aki na biyu, saboda haka nidai daga nan bazan k’ara gaba ba, please M.Jay kakula da Laylerh, kasani Kusan kama fi
Kowa sanin wacece ita, kasani cewar itad’in yarinyace da batasan komai ba, sai abunda ka koya mata, za kuma ta cigab
a da rayuwa ne akan kowani irin abu daka d’aurata akai, saboda haka ka kula da ita sosai, Domin ayanzu itace ta zab’eka bawai kaine ka zab’eta ba, then duk abunda kake buk’ata naka yana d’ayan dakin dake gefen na Laylerh, saboda haka ni zan tafi Allah Yaba
ku zaman lafiya da zuri’a mai albarka.
‿
Idanunsa dake alumshe wanda suka d’anyi ja ya bud’e, tare kuma da sauk’e wani irin nannauyar ajiyar zuciya, ahankali ya d’an soma motsa jajayen labb’ansa, da dukkan alama kuma wani abu yake son fad’a, amma saidai
kuma ya kasa.
Ganin hakanne kuma yasa Fou’ad sakin murmushi, tare da juyawa batare da yace komae ba, ya fice daga cikin falon da d’an sassarfa, kasancewar zuwa lokacin har an d’an fara yayyafi, bakuma yaso ruwan ya samesa ahanya batare daya koma gida
ba, baya ga haka ma Allah Allah Yake ya koma gida, saboda ya samu ya k’ira Aleeyah, domin ya samu daman karb’an phone number’n ta, d’azu da zai maida ita gida.
Almost 5minute kenan yanzu da tafiyan Fou’ad amma ya kasa Koda d’aga k’afarsa daga inda yake
tsaye, saidai idanunsa daya zubawa had’add’en stairs d’in da zaka bi ta kansa dan haurawa sama.
Ganin abun yake tamkar bada gaske ba, Kamar amafarki haka yake ganin komai, Yayinda wani irin abu ke yawo acikin sassan jikinsa, wanda kuma kaitsaye bazae k’
irasa da sunan feeling ba.
Duk da kuwa abun yafi yi masa kama da feeling, amma kuma yanajin k’arfi da kuma tasirin abun tamkar acikin jininsa yake gudana.
Aro jarumta yayi ya sakawa kansa, cikin yanayin nutsuwa ya shiga takawa Ahankali, har zuwa kan st
airs d’in.
Koda yakai k’arshen steps d’in hannunsa yasa ahankali ya murd’a wata door wanda kuma itace zata sadashi da falon saman.
Sassanyan k’amshin daya daki hancinsa ne yasashi sake lumshe idanunsa akaro na barkatai, lokaci d’aya kuma yaji yanayin
k’amshin ya sauk’ar masa da feeling.
K’ofar d’akin da yake zaton acikinsa Laylerh’n take ya k’urawa ido, domin ayanzun shikad’ai yasan meyakeji ajikin zuciyarsa.
Musamman ma gangar jikinsa da ta amsa masa da wani irin fitinannen feeling.
Ci gaba da
takawa yayi har zuwa, bakin k’ofar, still kuma har yanzu baiji zuciyarsa ta daina bugawa ba.
Hannunsa na dama ya d’aura akan handle d’in k’ofar, tare da d’an lumshe idanunsa, cikin yanayin nutsuwa kuma ya murd’a handle d’in, take kuwa k’ofar ta bud’e.
Wa
nda hakan ya bashi daman sako kansa, tare kuma da shak’an k’amshin dake tashi acikin d’akin.
Rikitattun idanunsa masu bayyanar da zalla’n yanayin da yake ciki, ya sauk’e akanta.
Zaune take akan gadon, Yayinda ta jingina bayanta da saman gadon, yanay
in yanda tayi zaman nata ne kuma, yasa gaba d’aya k’afafunta da suka sha zanen jan lalle suka kasance a k’asa.
Still kuma har yanzu vail d’inta na jikinta, wanda ya rufe mata jiki, da gaba d’aya fuskarta.
Ahankali ya sauk’e ganinsa akan kyawawan far
aren k’afanta, wanda suke cikin had’add’en hill shoe.
Lucky eyes d’insa yad’an lumshe, sakamakon wani fitinannen k’amshin jikinta daya doso shi.
Cikin wani irin kasalallen yanayi ya shiga takowa zuwa cikin d’akin.
Har yanzu ganin abun yakeyi tamkar
amafarki, gani kuma yake tamkar idan ya d’age mayafin dake kan fuskarta, ba Laylerh’n zai gani ba, wata mace zai gani daban.
Isowarsa jikin gadonne kuma yasa shi jin tsanantawar bugun zuciyarsa, ahankali cikin wani irin fitinannen yanayin da baisan da
me zai k’irasa ba, ya durk’usa guiwowinsa akan lallausan carpet d’in dake Malale agaban gadon, wanda kuma akansa ne Laylerh’n ta ajiye k’afafunta.
Idanunsa ya zubawa kyawawan yatsun k’afan nata baya ko k’yaftawa, yayinda daga gefe guda kuwa yakejin wan
i irin sanyi na ratsa duk ilahirin jikinsa.
Asanyaye yasa hannunsa ya d’ago k’afarta na dama, tare da ajiye k’afar nata akan cinyarsa, igiyan dake jikin shoes d’in ya soma warwarewa, wanda hakanne kuma ya bashi daman cire mata takalmin daga k’afarta.
Ah
ankali ya saka duka tafukan hannayensa ya rik’o k’afafun nata, tare kuma da d’ago kansa ya k’urawa mayafin dake jikinta idanunsa wanda lokaci d’aya suka koma kalan bacci.
Sassanyan k’amshin turare da kuma wani daddad’an sanyin da taji yana shiga cikin
tafin k’afarta ne yasa ta d’an bud’e idanunta ahankali, domin dama baccin da takeyi d’in baiyi nisa ba, saboda yanayin yanda mararta ke murd’awa akai akai, sam ya kasa barin bacci mai k’arfi ya d’auketa.
K’afanta dake cikin tafukan hannayensa tad’an motsa
, asakamakon jinsu da tayi acikin wani abu mai laushin gaske.
Atake kuma zuciya da k’irjinta sukayi wani irin bugawa saboda k’amshin turarensa, da taji ya cika mata hanci, wanda kuma hakan alama ce dake nuna mata cewar, lallai Maleek d’in yana cikin
d’akin.
saurin maida idanunta tayi ta lumshe, tare dasa hannunta ta dafe daidai