Showing 129001 words to 132000 words out of 244674 words
nuna masa ita wayayyace tace.
“Please say something kodai bakajin Hausa ne, nayi maka magana da English?
‿
M.Jay kuwa jin abunda ta fad’a d’inne yasashi d’an d
akatawa da abunda yakeyi, cikin zuciyarsa yace.
“Wae English, har wannan tsigigiyar yarinyar tana da bakin turancin da zata iya min magana dashi.
‿
Idanunsa ya d’an lumshe kana kuma ya bud’e su alokaci guda, batare daya damu da d’ago kai ya kalleta ba yac
i gaba da danna wayarsa.
Munnira kuwa abunnasa mamaki yasoma bata, cikin zuciyarta tace.
“Anya kuwa ba kurma bane?
‿
Da sauri kuma ta girgiza kanta, cikin son k’arfafawa kanta guiwa tace.
“No nasan ba kurma bane saboda Abbana bazai tab’a kawomin kurma a
matsayin wanda zan aura ba.
‿
D’an gyaran muryarta tayi cikin son jawo hankalinsa tace.
“Sunana Munnira, kuma Ina fata zamu kasance atare kamar yanda mahaifanmu suke fata da buri? I promise you kuma bazaka tab’a samun matsala dani ba, sannan...,
‿
“Kindam
eni da surutu!!
‿
Ya katseta daga maganan nata ta hanyar fad’in haka cikin d’an d’aga murya.
Munnira kuwa amatuk’ar bazata maganan nasa ya shiga kunnenta hakanne kuwa yasa ta bud’e baki tana kallonsa, domin tabbas da farko batayi tunanin cewa da gaske yan
a jin hausa ba, domin harta fara tunanin idan tayi magana yanzu bae amsa mata ba to zatayi masa da turanci, still I dan bai amsa mata ba saita zuba masa idanu, dan ko za’a samata wuk’a awuyanta ace za’a yankata bata iya larabciba, abu d’aya kawai tasani ak
almar rabaci shine ta’al da yellah suma kuma dan tana yawanji ana fad’a acikin series film na larabawa ne, shiyasa ta rik’e amma bayan haka batasan komae ba.
Tabbas jin amon sautin muryarsa da tayi yasa ta shiga shock sosae, domin kuwa sound d’in muryarsa
daban yake dana mutanen da ta saba ji.
Lokaci d’aya taji wani irin matsanancin sonsa ya daki zuciyarta.
“Wallahi Inasonshi.
‿
Tafad’a acikin zuciyarta saidai kuma batasan maganan nata ya fito fili ba.
Idanunsa ya rumtse asakamakon jin hakan daga bakinta
.
“Wae har k’ananan y’an mata marassa aji irin way’annan suna da zab’i?
‿
Ya fad’i hakan acikin zuciyarsa adaidai lokacin dayake mik’ewa tsaye, dan bayajin zai iya cigaba da zama acikin falon, saboda yanda warin parfume d’inta ke neman hautsuna masa ciki,
yeah yana son k’amshi amma bakowani irin mahaukacin k’amshi ba.
Sam bayajin yarinyar ta ishesa kallo shiyasa ko juyawa baiyi ya kalleta ba, tun kallon farko kuwa da yayi mata baisake yin na biyu ba, nafarkon ma kuma yabarsa amatsayin tsautsayi ne, cikin i
sa da tak’ama ya fice daga cikin falon.
Haka Munnira ta bud’e baki da ido tana kallonsa harya fice.
Wani irin murmushi tayi cikin yanayin jin dad’i tace.
“Tabbas ayanzu nasan nasamu Mijin aurena, Mijin da babu wata wacce zata sameshi saini kad’ai, wow g
askiya ni Munnira me sa’ace.
‿
Tafad’a tana me mik’ewa tsaye cike da farinciki tasoma zagaye falon.
Maleek kuwa yana fitowa daga cikin falon direct wajen da motarsu ke fake ya nufa, inda kuma anan jikin motar Abbou Jaheed da Alhaji Farouk ke tsaye.
“Baz
an tab’a auren wannan yarinyar ba mace kaman 1 babu komae na burgewa ajikinta, kai ni ko akwaima bana sonta, banason kowacce mace aduniya sai Laylerh.
‿
Abunda yake fad’a acikin zuciyarsa kenan adaidai lokacin da ya k’araso inda su Abbou Jaheed d’in suke.
Ganinsane yasa Alhaji Farouk washe baki, cikin jindad’i yace.
“Masha Allah Kaga Munniran ko, inafatan kun daidaita.
‿
Jin abunda Alhaji Farouk d’in ya fad’ane yasa shi sake had’e fuskarsa, tare da kawar da kansa gefe.
Sanin halin Maleek d’in kuma da Abbo
u Jaheed yayine yasashi yiwa Alhaji Farouk bankwana domin dama sungama duk maganan da zasuyi.
Cikin fari’a kuwa suka rabu, saidai Maleek kuwa fuskarsa atsume suka bar cikin gidan.
Buzuwa Ne ta shigo cikin falon inda ta taradda Munnira nata imagine ray
uwar da zatayi da Captain Maleek.
Shigowarta cikin falonne kuma yasa Munnira rik’o hannunta cikin zumud’i tace.
“Inasonsa Sosae Ummi inasonsa.
‿
Murmushi Buzuwa tayi domin dama tasan dolene Munnira taso shi, to wayema zata k’isa.
Shigowar Alhaji Farouk
cikin falonne yasa suka juya suka kalleshi.
Murmushi ne kwance akan fuskarsa har ya k’araso kusa da Buzuwa, jakan dake hannunsa ya mik’a mata, tare da neman waje ya zauna cikin bayyana farincikinsa afili yace.
“Sadakin Munnira ne naira million d’aya 1,0
00,000 yanzu Alhaji Jaheed ya bada, munkuma tsaida lokaci nanda sati 2 za’ayi biki, saboda yace bayason jinkiri, b’angaren mu ma kuma babu amfanin yin jinkirin saboda ashirye muke, inason kusan rasa Captain Maleek Jaheed Gwani amatsayin suruki baban asaran
e, saboda haka kada mubari murasa wannan daman.
‿
*(
😭😭😭😭😭
Hak’ik’a Inatsananin buk’atar taimakon ku, dan Allah Ina rok’onku da babban murya kutaimakawa YAYANA da addu’o’inku wallahi yana cikin halin matsanancin ciwon k’afa shekara da shekaru dan Alla
h Kutaimaka mana da addu’a akan Allah Yabasa Lafiya dan Allah idan kunyi sallah kuyimin wannan alfarmar dan Allah
😭😭😭😭😭😭
Wallahi Burina aduniya shine naga Yayana ya samu lafiya !!)*
*24January/2021*
1/28/21, 9:43 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEE
K*
*Writting By*
fatymasardauna
*Note edit*
*Chapter 43*
Wani irin gud’a me k’arfi Buzuwa ta sake tare da zuge zip d’in jakan dake hannunta, take kuwa mak’udan kud’ad’en dake cikin jakan suka bayyana.
Murmushin dake nuna tsananin farincikin ta ta
yi, cikin bayyana jin dad’inta tace.
“Dama ni nasan cewar banyi haihuwar banza ba, gaskiya Y’ata Munnira me sa’ace.
‿
“Sosae kuwa, yanzu dae zama bata kama muba dolene mu fara shirye shiryen biki domin satin biyu kaman yanzu ne, kinsan lokaci yanzu saurin
gudu ne dashi.
‿
Cewar Alhaji Farouk dake k’ok’arin mik’ewa tsaye ya wuce d’akinsa dake cikin falon.
Munnira kuwa ganin irin mak’udan kud’ad’en da aka kawo amatsayin sadakinta yasa ta fad’a jikin mahaifiyartata, cikin matsanancin farincikin da takejin ka
nta aciki tace.
“Ashe burina zai cika Momy? ashe zan samu irin namijin da nake mafarki da buri?.
‿
D’an tsagaitawa da maganan nata tayi tare da d’agowa ta kalli mahaifiyar tata, cike dason bayyana abunda ke cikin ranta tace.
“Yana da kyau sosae Momy, aga
skiya ban tab’a ganin wani Namiji me kyau irinsa ba, inasonsa Momy ina tsananin sonsa, domin na fahimci cewa aurensa zae sa na zama kamar sarauniya, zan banbanta da sauran mata, lallai zan samu future me kyau agaba, yanzu ne nagane dalilin dayasa zuciyata
takasa aminta da Sadeeq, ashe rabon samun wani had’add’en gaye ne yake jirana, kai gaskiya am so so happy.
‿
Tafad’a tana me kissing goshin mahaifiyar nata.
Murmushin dake bayyana zallan nasara Buzuwa tayi, kamo hannun Munnira’n tayi cikin son k’arfafawa
y’ar nata guiwa tace.
“Insha Allah bazamu rasa shiba Munnira, bakuma zamu tsaya sanyin jiki ba daga yau d’innan zamu fara shirye shiryen biki, domin so nake muyi biki irin wanda ba’a tab’a yinsa acikin garin Abuja ba, gaba d’aya sati biyunnan zamu sharesa
acikin hidiman biki, tun yanzu kuwa zan fara sanar da y’an uwa da kuma abokan arziki.
‿
Murmushin jin dad’i Munnira tayi domin jin abunda mahaifiyartata ta fad’a yasa taji zuciyarta tayi sanyi, tare kuma da k’arajin son Maleek d’in acikin ranta.
Haka dae
suka zauna ita da mahaifiyarta ta suka shiga tsara yanda suke so hidiman bikin ya kasance.
Laylerh.
Sama da 30 minute ta d’auka kwance akan makeken gadonnata tana ta juyi tare da murk’ususu, gaba d’aya batajin dad’in komae, saboda zuwa yanzu ciwon da ma
rar nata keyi ya tsananta sosai.
Ahankali ta zuro da k’afafunta k’asa daga kan gadon, yunk’urin mik’ewa tsaye ta somayi amma kuma jin yanda marar nata ya rik’e waje d’aya ne yasa ta d’an rumtse idanunta, tare da danne jajayen labb’anta, cikin son daure ci
won da takeji d’in tayi yunk’urin daidaita nutsuwarta tare da mik’ewa tsaye, hannunta ta d’aura adaidai saman mararta anutse ta soma taka k’afafunta zuwa gaban makeken drawern dake cikin d’akin, wani hulan turban ta d’auka tasa akanta, wanda hakan yasa dog
on gashin dake kanta, ya sake bajewa akan gadon bayanta.
Ahankali ta k’arasa bakin k’ofar d’akin, tare da d’aura hannunta akan handle d’in k’ofar, cikin yanayin sanyin daya rusketa ta bud’e k’ofar ta fice gaba d’aya daga cikin d’akin.
Kasancewar kuma bat
ajin dad’in jikinta ne yasa cikin yanayin sand’a ta k’araso cikin had’add’en falon nata, wanda aka k’awatasa da had’add’un kayan furnitures masu kyau da tsada, k’amshin turaren Najeeb d’in daya daki hancinta ne yasata d’an lumshe idanunta tare kuma da bud’
esu alokaci guda, tabbas taji k’amshinsa amma kuma ko alamarsa bata gani acikin falon ba.
D’an soma k’arewa falonnata kallo tayi, tare kuma da tunanin inda Najeeb d’in ya tafi, domin kuwa tun tashinta bata sashi acikin idanunta ba, ajiyar zuciya ta sauk’
e batare kuma da ta kula da kayan break fast d’in daya ajiyemata akan dining table d’in dake cikin falon nasu ba, tasa kai ta fice.
Saboda yanayin yanda takejin jikinnata yasa ta kwad’aita dason jin d’umin rana, dan sanyi akeyi sosai, ya waitan jin sanyin
nata kuma ya k’arune saboda wani irin zazzab’i na daban da yake k’ok’arin kamata.
Ahaka kuma tana tafiya ahankali har ta iso babban compound d’in gidan.
Wanda kwata kwata yau d’in babu yalwan mutane acikinsa, domin dama yawanci soldiers d’in M.Jay ne,
wanda yanzu duk sun koma bakin aiyyukansu, saura y’an tsiraru masu kula dashi ne kawae suka rage.
Ayanayin da takejin kanta ne yasa sam bata damu da irin shigar riga da wandon dake jikinta ba, kaitsaye ya wuce inda M.Jay d’in ke parking cars d’insa, kasan
cewar wajen ya d’anfi rana shiyasa ta zab’i zama anan d’in ko hakan zai rage mata sanyi da kuma ciwon da takeji, anan kuwa gaban wata had’add’iyar corolla d’insa ta tsugunna tare dasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta.
B’angaren Captain kuwa tunda suk
a baro gidan Alhaji Farouk d’in ya kasa sakin rai da fuskarsa, hakanan yakejin wani irin k’unci acikin zuciyarsa, yayinda gaba d’aya takaicin yarinyar da ake k’ok’arin lik’a masa dan ya aura yabi ya cika masa zuciya, domin kwata kwata baiyi tunanin cewa ir
in wannan zab’in Abbou Jaheed zaiyi masa ba, shin wai ma tayaya zai fahimtar da Abbou Jaheed cewar agaba d’aya rayuwarsa bayason kowacce irin mace idan ba Laylerh ba? Hak’ik’a baya mafarki da burin mallakan wata na daban arayuwarsa, so da k’auna acikin zuc
iyarsa guda d’aya ne kuma ya riga daya bawa Laylerh su, duk da cewar bai sameta amatsayin mata ba kuwa soyayyarta bazata tab’a fita daga cikin zuciyarsa ba, tabbas yasan cewa ayanzu cigaba da tunani ko kuma muradin Laylerh zunubi ne agaresa, amma kuma bash
i da ikon hana kansa sonta, tabbas soyayyarta acikin jini da tsokansa take, haka kuma halittaciyar abace da aka halicceta tun shekaru masu yawa da suka shud’e, yayarda cewa soyayyar Laylerh k’addarace agaresa, yayarda ya d’auki hakan amatsayin k’addara, da
ga haka kuma baya fatan wata sabuwar k’addaran ta sake shigowa rayuwarsa. Arayuwa Laylerh yaso kuma ita zaicigaba da so har zuwa k’arshen rayuwarsa.
Jin wani irin burkin da drivern ya taka ne yasashi d’ago kansa dake duk’e, ganinsu da yayi agaban tamfatse
tsen gate d’in gidan nasu ne yasashi maida idanunsa ya lumshe.
Akasalance yasa hannu ya bud’e murfin motar yafice, kasancewar tun fitowarsu daga gidan Alhaji Farouk Abbou Jaheed ya sanar dashi cewa zasu sauk’eshi abakin gate ne dan zai wuce office.
Hakan
kuwa akayi domin yana fita daga cikin motar Abbou Jaheed yasa drivern yaja motar suka bar wajen.
Ahankali yasa hannu ya tura y’ar k’aramar k’ofar dake jikin gate d’in.
Maigadi kuwa dake zaune jin alaman za’a shigo cikin gidanne yasashi tashi azabure cik
in fad’a fad’a yace.
“Waye haka yake tab’a mana k’ofa.....
‿
Sauran maganganun dake cikin bakinnasa ne suka mak’ale asakamakon ganin Maleek d’in da yayi, cikin sauri ya k’ame jikinsa waje d’aya, duk da cewar kuwa shid’in ba soja bane, amma yayi hakanne da
n girmamawa da kuma son kare kansa, kasancewar tunda yake agidan baitab’a ganin murmushin Maleek d’inba, wannan dalilin yasa yake masifar tsoronsa, domin yasan irinsune da idan suka tashi lokaci d’aya suke raba k’ashin mutum gida biyu, abu me sauk’ine shig
a huruminsu yasa su b’abb’allaka.
“Barka da dawowa Sir.
‿
Ya fad’a cikin yin k’asa da murya, domin a yanda yaga fuskar M.Jay d’in amurtuk’e, lashakka zai iya bindigesa ma.
Duk da cewar kuwa baya cikin mood me dad’i, amma haka yasamu kansa da jinjinawa g
ateman d’in kai, alaman ya amsa gaisuwar tasa, wanda yayi hakanne kuma saboda sam wulak’anta mutane baya d’aya daga cikin halayyarsa, saidai wanda ya zubar da kansa, yasani cewa shi miskiline na k’arshe sannan babu ruwansa da rayuwar kowa, amma kuma baya w
ulak’anta na k’asa dashi, hakan kuma ya zame masa d’abi’a da kuma al’ada because zuciyarsa akwae rauni sosai, shi mutum ne me matuk’ar tausayi, saidai kuma amma tausayin nasa ba abayyane yake ba, yakanyi ne kawae idan yanayi yazo da hakan.
Da kallo gatema
n d’in ya bisa, yayinda shi kuma cikin takunsa na isa, ya k’arasa shigowa cikin gidan, kaitsaye part d’insa ya so nufa, amma kuma saidai tunawa da yayi cewar yau tun safe baiyi training bane yasashi fasa shiga b’angaren nasa kaitsaye ya juya akalan tafiyan
nasa zuwa inda yake aje motocinsa.
Tunkafun ya k’araso wajen kuwa ya gama yankewa kansa hukunci cewar, babbar Corolla d’insa zai hau, kasancewar tunda aka kawo masa ita sau uku kawai ya tab’a hawanta, duk da kuwa cewar motar me tsadace sosae amma baiwani
damu dason shiganta ba.
Isowarsa jikin motar ne kuma idanunsa suka sauk’a akan Laylerh wanda har yanzu ke durk’ushe awajen yayinda tafukan hannunta ke kan fuskarta.
Sauk’e idanunsa akanta da yayi kuwa yayi daidai da bugawar zuciyarsa, yayinda kuma atake
yaji wani irin sanyi na ratsa gaba d’aya ilahirin jikinsa, har zuwa k’asan k’afarsa, wani irin abu da yaji acikin zuciyarsa ne yasashi d’an lumshe idanunsa tare da jan wani dogon numfashi.
“Metakeyi anan?.
‿
Yayiwa kansa tambayar yana me sake bud’e idanun
sa ya sauk’esu akanta.
“Tana da damuwa.
‿
Cewar zuciyarsa wanda akoda yaushe take jib’antan al’amuran Laylerh’n.
Labb’ansa yad’an cije tare da zuba mata, tsumammun idanunsa, take kuwa yanayin na yanzu ya juye masa zuwa wasu shekaru dasuka wuce, wani loka
ci daya saba ganinta tana zaune cikin kad’aici da k’unci, lokacin da take kuka.
Tabbas Laylerh GARKUWA take so, bawai iya miji kad’ai ba, dole kafun tasamu wanda zai sata farinciki sai tasamu wanda yasan gaba d’aya yanayinta.
Wanda yasan kukanta ya kuma
san dariyarta, tabbas ya taso acikin maraici amma kuma maraicin Laylerh yafi komai tsaya masa arai, yanajin matsanancin tausayinta fiye da kowa da komai, har idan aka cire soyayya irinta So da So, to k’aunan da yakeyiwa Laylerh ta y’an uwantaka tana da mat
uk’ar yawa, saboda yayi imani cewa akanta zai iyaba da komai nasa, ciki kuwa harda rayuwarsa, kamar yanda baya iya manta sunansa, haka ako da yaushe baya manta kalaman da Mahaifiyarta ke fad’a masa ashekarun baya, koda yaushe cewa take zata bar masa Layler
h ya kula mata da ita, ya sama mata farinciki marar yankewa, domin Laylerh tasace har abada, ko da kuwa wata k’addara tasa ya rasata, wata k’addara zata sake had’asu.
Tabbas akullum yana tuna wannan maganganun, wanda suke sa yaji zuciyarsa tayi matuk’ar r
auni sosae, yanayin idanunsa ne suka sanja launi, wanda kuma hakan alamace dake bayyana asalin hak’ik’anin abunda ke cikin zuciyarsa.
Ahankali ya sake murfin motar dake hannunsa, cikin yanayin sanyi yayi takun da baiwuce taku hud’u ba, ya iso gareta.
Tsa
yawa akanta yayi duk da cewar kuwa yanajin zuciyarsa na bugawa sosae, haka ya d’aure ya d’an rank’wafo kanta.
Almost 2 minute yanason had’a kalman sunanta abakinsa, amma ya kasa, hakanan yaji harshensa ya masa nauyi, cikin sabon yanayin daya samu kansa ac
iki, ya d’aura hannunsa adaidai kan nata hannun, ahankali cikin wata irin murya me kama da rad’a ya k’ira sunanta.
Tabbas taji motsin mutum akusa da ita, saidai kuma kwata kwata bata kawo aranta cewar shi d’in bane, duk da cewar kuwa dadddad’an k’amshinsa
ya kawowa hancinta ziyara amma tayi tunanin cewa kwad’aituwa da tayi dason jin k’amshin nasa ne yasa ta jin hakan.
Sauk’an sautin muryarsa acikin kunnuwanta kuwa shiyasa duk taji tsikar jikinta sun mimmik’e, ahankali ta d’an janye tafukan hannunta daga k
an fuskar nata.
Cikin sa’a kuwa tajefa idanunta acikin nasa idanun, idanun da har abada bazasu tab’a daina yi mata gizo
ba, idanun da suka zama tamkar sinadari acikin rayuwarta.
Sam bazata iya jurewa kallon cikin rikitattun idanunsa dake sauya mata tuna
ni akoda yaushe ba, wani irin fitinannen yanayin da ta samu kanta aciki ne kuma yasata d’an lumshe idanunta, wanda hakan da tayin kuma ya bawa hawayen dake cikin idanun nata daman gangarowa kan k’uncinta.
Maleek kuwa ganin hawayen da yayi akan fuskarta ne
, yasa shi rumtse idanunsa, batare kuma daya bud’e idanun nasa ba, da muryarsa wanda baya fita sosae yace.
“Me yake damunki?.
‿
Jin tambayan da yayi mata d’inne kuma yasa ahankali ta bud’e idanunta, masu d’auke da zallan yanayin shagwab’a, wuyanta ta kary
ar gefe tare da d’an soma mamul mamul da bakinta, dagani kasan ba iya ciwo ne ke damunta ba harma da zallan shagwab’a.
Ganin kuma yanda takeyi da bakinnata ne yasa shi gane irin yanayin da take ciki, ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya me tafiya da jan numfa
shi.
Hakanan yaji kaman ya jawota jikinsa yayi mata kyakkyawan hugging ko hakan zaisa ta samu relief daga damuwan dake cin zuciyarta, saidai kuma bashida iko da kuma daman hakan.
Hannunsa dake kan fuskarta ya janye, cikin son daidaita nutsuwarsa yace.
“
Oum Ayush na k’iranki.
‿
Yanayin yanda ya fad’i maganar yana me juya bayansa ne yasa ta k’ura masa ido, domin kuwa bak’aramin kyau taga yayi mata acikin sigar yanayin maganar tasa ba.
Shikuwa Maleek ya fad’i hakanne dan rage mata damuwa, musamman yasan