Showing 162001 words to 165000 words out of 244674 words
bak’i shiyasa suka k’ara bayyana hasken fatarsa.
Laylerh kuwa
da har yanzu take zaune akan sallayan da tayi sallah, kyawawan k’afafunsa ta zubawa ido, ba abundake d’aukar hankalinta agaresa kuma kamar yanda yake taka k’afafunnasa ahankali.
Isowarsa kusa da itane kuma yasa tayi saurin lumshe idanunta, tare dajin wani
irin bugun zuciya wanda bata tab’a jin irinsa ba.
Shikuwa Maleek kaitsaye ta gefenta ya rab’a ya wuce ya d’auki sallayan da Oum Ayush tayi sallah akansa, shumfud’a sallayan yayi tare da fuskantar gabar ya tada sallah.
Ganin haka yasa asanyaye tatashi
daga zaunen da take tare kuma da nannad’e sallayan da take kai ta ajiye agefe.
Daidai lokacin kuwa su Abbou Jaheed suka dawo daga tafiya masallacin da sukayi.
Kallon Oum Ayush Abbou Khareem yayi cikin kulawa yace.
“Likita yace bazai sallamemu yau ba sai
zuwa gobe, saboda haka ni zan kwana da Maleek d’in, ku kuma zuwa yanzu ya kamata ku koma gida, domin dare na k’ara yi.
‿
Jin abunda ya fad’a d’inne yasa Oum Ayush ta d’an jinjina kanta, tare da mik’ewa tsaye, domin dama itama harta fara jin bacci, koba do
n haka bama ya kamata ace sun koma saboda ayanzu tasan duk inda Najeeb yake to yana buk’atar dawowar Laylerh gida, hakanan kuma bazasu tauye masa hakk’insa ba.
Fou’ad dake zaune agefe kuwa jin Abbou Khareem yace shi zai kwana a asibitinne yasashi kafewa
akan cewar lallai shi zai kwana tare da a Maleek d’in idan yaso su Abbou Khareem d’in dukansu sai su koma gida.
Abbou Khareem kam yaso cewa aa amma kuma sai Abbou Jaheed yace ba damuwa abar Fou’ad d’in ya kwana.
Haka dai suka tsaida magana akan cewa Fou
’ad d’inne zai kwana.
Laylerh kuwa tunda taji ance sutafi duk ta k’ara sururucewa, sam hakanan taji batason koda fita daga d’akinne balle ma daga cikin asibitin gaba d’aya, amma kuma sanin da tayi cewar babu yanda zatayine yasa ta gyara rufin mayafin da
ke jikinta.
Asanyaye ta saci kallonsa ta gefen idanunta, domin kuwa har yanzu sallah yakeyi bai idar ba, kasancewar yana ramakon sallan azahar da kuma na la’asar ne da ake binsa, wanda lokacin da akayi su baya cikin hayyacinsa.
“Muje ko.
‿
Muryar Oum
Ayush ta katseta daga d’an guntun tunanin da takeyi.
Haka dole batare da ranta ya soba tabi bayan Oum d’in da har ta isa bakin k’ofa suka fice.
Koda suka fito compound d’in asibitin kai tsaye wajen da Oum Ayush tayi parking motar ta suka nufa.
Asanyaye
Laylerh ta bud’e murfin motar ta shiga.
Cikin d’an yanayin sauri kuma Oum Ayush taja motar suka tafi.
Har sukayi nisa da tafiyan nasu kuwa babu wanda yace da d’an uwansa k’ala, kowannensu da irin abunda yake sak’awa acikin zuciyarsa, yayinda acikin zuciy
ar Laylerh ya kasance tunanin Maleek ne zallan, Oum Ayush kuwa mamaki da kuma tunanin abunda ya hana Momy zuwa hospital d’in take.
Da wannan tunanin nasu ahaka har suka iso gida.
Acan asibiti kuwa Koda ya idar da duka sallan da ake binsa bai tashi akan
sallayan ba har saida ya sallan Isha.
Bayan ya idar da sallanne kuma ya d’auki magungunan da Dr. Mouhammad ya kawo masa yasha, tare da komawa saman gadonsa ya kwanta, domin kuwa wani irin ciwo yakejin jikinsa da mararsa nayi masa, ga kuma wani irin bac
ci mai k’arfi dake fusgarsa, hakan kuwa yana da nasaba da allurar da Dr. Mouhammad yayi masa d’azu, saboda alluran tanabin jikin mutum ne da sannu saita saka macewar jiki da kuma bacci.
Ahankali Fou’ad ya turo k’ofar d’akin ya shigo, dawowansa daga masa
llaci kenan, yayinda su Abbou Jaheed kuwa suna idar da sallah’n Isha suka wuce gida shida Abbou Khareem.
Ganin Maleek d’in da yayi kwance akan gadone yasashi k’arasowa cikin d’akin tare dajan kujera ya zauna akusa da M.Jay d’in wanda yasa hannayensa duka
biyu ya dafe mararsa, duk da kuwa cewar idanunsa alumshe suke, amma Fou’ad yasan cewa ba bacci yakeyi ba, domin duk wani kwanton b’aunan Maleek d’in babu wanda baisani ba.
Idanu ya zuba masa nad’an wasu sakanni kafun daga bisani ya kawar da kansa gefe,
cikin tausasa murya yanda yasan Maleek d’in zai fahimcesa yace.
“Bai kamata ace har yanzu kabar zuciyarka taci gaba da son Matarwani ba, Laylerh fa matar wani ce Maleek kuma kasan hakan, kana kasan zunubin dake cikin hakan amma kuma kake aikatawa, meyasa
ba zakayi k’ok’arin cireta acikin rayuwarka ba? ko kamanta cewar ba lallaine abunda kakeso shi kake samu ba? Kada kayi tunanin wai don kanason Laylerh watarana dole saika sameta, Tabbas nasan kanajin k’una da kuma radad’in rashinta amma hakan bawai shi yak
e nufin cewa bazaka rayu idan ba itaba zakayi rayuwa cikin farinciki da inganci Idan har kaso hakan, Dan Allah Captain M.Jay kamanta da Laylerh ka k’yaleta tayi rayuwa da mijinta, saboda ta sanadiyarsa ne zata samu aljannarta, shin tayaya kake tunanin Layl
erh zata iyayin zaman aure matuk’ar tana ganinsa akusa da ita? sa
nnan kuma idan kana bibiyarta hakan bazae tab’a yiwuwaba, na tabbata ganin da nayi muku d’azu da ace Mijintane yayi muku da zuwa yanzu labari ya sanja salo, shin kanason Najeeb yafara zargin
Laylerh da aikata fasik’anci da aurensa ne? Kasani basai na fad’a maka ba Laylerh yarinyace k’arama duk abunda aka koyar da ita dashi zata tashi, kada ka koyar da Laylerh wannan d’abi’ar Maleek sam kada ka fara.
‿
Idanunsa wanda suka rune sukayi ja kaman
Jan barkono ya bud’e, tare dajan wani irin dogon numfashi, ahankali ya kamo hannun Fou’ad dake gefensa ya d’aura akan kirjinsa daidai saitin inda zuciyarsa take.
Sauk’an hannun Fou’ad akan saitin zuciyar Maleek d’inne kuma yasashi zaro idanunsa waje, c
ike da mamaki had’i da tsoro yake kallon k’irjin Maleek d’in.
Asakamakon wani irin mummunan bugawa da yaji zuciyar Maleek d’in nayi fast fast kaman zata faso k’irjinsa ta fito.
“Yin shiru zaifi sauk’i Fou’ad akan kacemin na daina son Laylerh, bakasan y
a nakeji ba aduk kwanan duniya idan na tuna cewar Laylerh tana ak’ark’ashin inuwar wani sai naji zuciyata tana k’una kaman ana gasamin ita, Ya nakeji me nakeji babu wanda ya sani Fou’ad saini kad’ai, cire soyayyar dake yawo acikin gangar jiki da jini ba ab
u bane me sauk’i, nayi imani cewa da soyayyar Laylerh acikin zuciyata zan mutu, so yakan tashi ya k’aura zuwa wani waje na daban amma ba irin soyayyar da nakeyiwa Laylerh ba, wannan soyayyar daban take, soyayyar Ayshnoor tafi gaban kwatancen kowa, ta wuce
hasashe Fou’ad, ba kuma zata tab’a misaltuwa ba, halittace da bazata tab’a mutuwa ba, domin kuwa koda babu rai ajikina soyayyar Ayshnoor bazata daina rayuwa ba!!
‿
D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, saboda yanda yaji k’irjinsa na rik’ewa, Sam yawan ma
gana ba d’abi’arsa bace, wannan dalilin yasa sanadin maganan da yayi yanzun yaji k’irjinsa ya rik’e.
Idanunsa wanda suka cika da ruwan hawaye ya mayar ya lumshe, tare da sakin hannun Fou’ad dake kan k’irjinsa, gyara kwanciyarsa yayi tare da juyawa ya bawa
Fou’ad d’in baya.
Fou’ad kuwa hawayen da suke kokarin zubowa daga cikin idanunsa ya shanye, asanyaye ya zubawa bayan Maleek d’in idanu.
K’warai sosai tsananin soyayyar da Maleek keyiwa Laylerh ke basa mamaki, wacce irin soyayyace wannan da k’arfinta y
ake neman zarce hankali? shikam Allah Ya sani zuwa yanzu tsoron soyayyar LaylerhMaleek d’in yakeyi, domin kuwa soyayyace Bawae mai hankali ba.
Sanin cewa sha’anin su Layerh’n yafi k’arfinsane yasa baisake cewa komae ba, jingina bayansa ajikin kujeran da
yake kai yayi tare da lumshe idanunsa.
Almost 20minute kenan yanzu da shigowarta cikin d’akin, amma gaba d’aya har yanzu ta kasa daidaita nutsuwarta, Sam batasan me yake damunta ba, amma saidai tayi amanna cewa moment d’inta dashi na d’azune duk ya riki
ta ta.
Domin kuwa har yanzu idan ta tuna da yanda lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa ya gogi nata fuskar saitaji tsikar jikinta ya tashi.
Idanunta dake bayyana zallan gajiya ta lumshe ahankali tare kuma da bud’esu alokaci guda, kana ta sauk’e wata
irin sassanyar ajiyar zuciya, agogon bangon dake sak’ale acikin d’akin ta kalla.
8:30pm daidai da idanunta suka nuna matane yasata mik’ewa tsaye, tare da nufan toilet donyin wanka, saboda asonta sam bataso Najeeb ya dawo gidan ya sameta idanunta biyu.
K
oda ta shiga cikin toilet d’in kayan dake jikinta ta rage tare da had’awa kanta ruwan wanka mai d’an d’umi a bathtube.
Sam bata wani b’ata lokaci awajen wankan nata ba, bayan ta gama wankanne kuma ta fito daga cikin toilet d’in jikinta sanye da bathrobe.
Ad’an hanzarce ta tsane ruwan dake jikinta, tare da k’arasawa gaban dressing mirror ta shafa wani body lotion dinta tare da turaren body spray maidad’in k’amshi.
Yanayin kuma yanda takejin kanta agajiyene yasa akasalance ta k’arasa gaban makeken drawer
d’inta, wani sauk’akk’en doguwar rigar bacci mai kalan light blue ta saka ajikinta wanda gaba d’aya jikinsa ya kasance na net ne, sosai kuwa rigar ta amshi jikinta tare kuma da bayyana zallan kyawunta.
Koda ta kalli madubi kuwa ita kanta tasan cewa tayi k
yau.
Hasken wutan daya cika d’akin ta rage tare da hayewa saman gado ta kwanta.
Mintuna kad’an da kwanciyarta kuwa bacci mai nauyi ya d’auketa, duk da cewar rabonta da tasa wani abu abakinta tun safe, amma haka ta gwammacewa kwana da yunwa.
Ahankali N
ajeeb ya turo k’ofar d’akin ya shigo, ganin kuma babu wadataccen haske acikin d’akinne yasashi k’arasawa jikin makunnin wutan ya kunna, take kuwa haske ya mamaye d’akin.
Yalwatan haske acikin d’akinne kuma yayi sanadiyar sauk’e idanunsa akanta.
Baccinta
take cikin kwanciyar hankali yayinda ta dunk’ule duka hannayenta ak’irjinta.
Wani irin murmushine ya sub’uce masa sakamakon yanda yaga tayi masa matuk’ar kyau, ahankali ya k’arasa shigowa cikin d’akin, tare da ajiye ledodin dake hannunsa akan bedside.
Ba
tare kuma daya yi abunda zai tashetaba ya shiga rage kayan jikinsa, saida ya cire komai sannan ya d’aura towel kaitsaye ya wuce bathroom.
Wanka kawae yayi batare kuma daya d’au wani dogon lokaci acikin bathroom d’inba ya fito duk gaba d’aya jikinsa d’auke
da danshin ruwa.
Zama yayi na musamman a gaban dressing mirror ya kimtsa kansa, bayan ya gamane kuma ya zura wasu simple riga da wando wayanda basuda nauyi.
Haka ya nufo kan gadon yana ta zuba k’amshi.
Sanin kuma da yayi cewar Laylerh’n bataci abinci b
ane yasashi soma k’iran sunanta.
Acikin magagin bacci kuwa ta amsa masa batare da ta tashi zaune ba, ganin hakanne kuma yasashi d’agota ya zaunar da ita.
Hannunsa yasa ya shafa gefen fuskarta, cikin matsanancin so da kuma sha’awarta dake cinsa ko wacce r
ana yace.
“I’m sorry na tasheki ko, nasan bakici abinciba shiyasa, kici idan yaso saiki koma baccin.
‿
Fuska ta shagwab’e tare da karyar da wuyanta gefe, cikin yanayinta na bacci da kuma zallan shagwab’a tace.
“Nifa nak’oshi.
‿
Kansa ya d’an girgiza ta
re da jawo ledan daya shigo dashi babban robar vanilla ice cream din daya sayo mata ya bud’e tare da d’aura mata roban akan cinyarta.
Cikin kulawa yace.
“Naji kin k’oshi to amma kisha Ice cream.
‿
Jin ya ambaci ice cream ne yasa ta bud’e idanunta, ganin
kuma da gaske Ice cream d’inne agabanta yasa ta d’an saki murmushi, batare da ta sake cewa komae ba kuwa ta d’auki robar ice cream d’in ta shiga sha tana wani lumshe idanunta masu yalwar lashes asamansu, sosae kuwa take enjoying shan ice cream d’innata.
S
hikuwa Najeeb kwalin pizza’n da yayi ordering ya ciro tare da bud’ewa ya soma ci.
Time to time yake kallon Laylerh’n da zuwa yanzu Tasha kusan fiye da rabin roban ice cream d’in.
Kusan mintuna 20 ya d’auka yana cin abincin saidai kuma jin shiru babu mots
in Laylerh’nne yasashi juyowa ya kalli b’angaren da take.
Cike da mamaki ya d’an zaro idanunsa sakamakon ganin da yayi cewa Laylerh’n har ta sake komawa bacci, ga hannunta kuwa rik’e da robar ice cream d’in da zuwa yanzu ya kusa zama ruwa dukansa.
Yana
yin yanda take baccin azaune ne yasashi d’an sakin murmushi, asanyaye yace.
“I’m sorry kingaji sosae ko kuma nazo na tasheki.
‿
Hannunsa yasa ya dauke robar ice cream d’in tare da gyara mata kwanciyan da tayi.
Sauran pizza d’in dayaci ya d’auka yakai k
itchine.
Bayan ya dawone kuma ya rage musu hasken wuta, had’e da hayewa saman gadon ya kwanta agefen Laylerh, tattausan blanket ya rufa musu ajikinsu, ahankali kuma ya lumshe idanunsa yana me shak’an daddad’an k’amshin dake fita ajikinta, duk da cewar ya
ud’in baiyi kusa da ita sosae ba, amma kuma hakan baihanashi jiyo sassanyan k’amshin dake fita ajikinta ba.
Hakika yana matuk’ar buk’atar ta, yana tsananin son yajita acikin jikinsa, yanason ya Santa acikakkiyar y’a mace, amma har yau yakasa samun
daman hakan, saudayawa yakan tambayi kansa cewar.
“Shin meyasa har yau ya kasa kusantar Laylerh’n duk da cewar bataso?.
‿
Saidai bashi da amsar dayake bawa kansa, haka dai yabar abun acikin zuciyarsa.
Da tunani kala kala bacci b’arawo ya d’aukesa.
Was
hegari.
Tun tashinta yau d’in ta gyara komai nata, duk da cewar babu wani abu na part d’in nata dake da datti amma haka ta gyara komae.
Yayinda acikin zuciyarta kuwa Allah Allah Take Oum Ayush ta k’irata tace tazo suje asibiti, hakanne kuwa yasa ta
yi wanka ta kuma shirya kanta cikin riga da sket na atamfa wanda sukayi mata kyau sosae.
Saidai abunda batasani ba kuwa shine tuni har Oum Ayush ta bada breakfast ankai asibitin domin tunda sassafe Abbou Khareem da kuma Abbou Jaheed suka tafi asibitin kas
ancewar Dr.Mouhammad yace yau zai bawa Maleek d’in sallama.
B’angaren Najeeb kuwa yau da sassape ya tafi office kasancewar yana da wani aiki mai mahimmanci dazai gudanar, shiyasa koda Laylerh’n ta tashima bata sashi acikin idanunta ba, saidai yabar ma
ta sak’on breakfast.
Ganin da tayi shiru Oum Ayush bata k’irata bane yasa kaitsaye ta wuce sashin Oum Ayush d’in, koda taje afalo ta samu Oum d’in.
Ganintane yasa Oum Ayush fad’ad’a murmushin dake kan fuskarta cikin kulawa tace.
“Laylerh yana ganki
kodae su Maleek d’in sun isone?
‿
Kanta ta girgiza ahankali cikin sanyin murya tace.
“Aa amma Oum Ayush baza muje asibitin bane?
‿
“Eh ae zuwa asibiti ya k’are mana saboda anjima kad’an za’a sallamo Maleek d’in, Dr. yace babu wata damuwa kuma kinsan
halin Maleek baicika son takuraba kinga kuma zama a asibiti koya yake akwae ta kura acikinsa.
‿
Kanta ta d’an rausayar gefe tare da neman waje ta zauna acikin falon, hakanan duk sai taji wani iri domin kuwa burinta ayanzu shine taga Maleek d’in.
Aca
n asibiti kuwa Dr. Mouhammad ne yashigo d’akin shida sauran wasu doctors suka sakeyiwa Maleek wasu gwaje gwaje bayan sun kammala gwaje gwajen nasune kuma suka rubuta masa irin magungunan da zaisha dama ta kardar sallamansa, duk da cewar akwae buk’atar yak
e zuwa duk bayan 1 weak suna duba lafiyar mararsa.
Godiya sosai su Abbou Jaheed sukayiwa doctors d’in, tare da d’aukan duk wani abubuwan da suka zo dashi suka kai mota.
Koda sukazo tafiya d’in kuwa har bakin mota Dr.Mouhammad ya rakosu sukayi sallama
ta mutumci, tare da shaidawa Maleek cewar lallai yake zuwa suna dubashi.
Shidai kam da kai kawae yake amsawa Dr. d’in domin kuwa sam bayason yawan magana.
Koda suka kama hanyar dawowa gida jingina bayansa da jikin kujerar motar yayi tare da lumshe ts
umammun idanunsa.
Bai bud’e idanun nasaba kuwa har saida suka iso compound d’in gidan nasu.
Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito, wanda kuwa hakan yayi daidai da shigowar motar Alhaji Farouk cikin compound d’in gidan.
Da Mamaki Ya shiga kallon mota
r, yayinda Abbou Jaheed kuwa yaje ya taro abokinnasa cikin karramawa.
Juyawa Maleek d’in yayi danufin tafiya sashinsa, amma saidai jin Abbou Jaheed na cewa dukansu su wuce falonsa ne yasashi da katawa badon ransa ya soba kuma haka yabi bayan su Abbou J
ahedd d’in.
Koda suka k’arasa falon Abbou Jaheed d’in mai yanayi da aljannar duniya, zama kowannensu yayi.
Nanfa Abbou Jaheed da kuma Alhaji Farouk suka shiga sabon gaisawa.
For the second time kenan dayaji gabansa na d’an fad’uwa, wanda kuma tun ac
ikin asibiti yakejin hakan, baikuma san dalili ba, ahankali ya shiga addu’a da kuma fatan cewa koma meyene yazo masa cikin sauk’i.
Shigowar Oum Ayush da kuma Laylerh dake biye da ita abayane yasashi d’an lumshe idanunsa, domin kuwa duk da bai d’aga idan
unsa ya kalleta ba amma k’amshinta ya isar masa.
Laylerh kuwa da k’irjinta keta faman dukan uku uku ahankali ta nemi waje anan k’asan sofa ta zauna, Sam batasan meyasa tunda Oum Ayush ta fad’a mata cewar Abbou Jaheed na nemansu ba, taji gabanta na fad’u
wa domin kuwa tasan cewa Abbou Jaheed baya neman mutum haka kawae.
Ae kuwa zuciyarta bata k’ara tsinkewa ba saida taga Najeeb ya shigo cikin falon, hakanan taji wani irin tsoro ya lullub’eta, take kuwa zuciyarta ta raya mata cewa.
“Kodae Najeeb ne
ya kawo k’aranta akan cewa bata basa hakk’insa
‿
Tabbas hakan zaiyiwu, amatuk’ar tsorace ta hade jikinta waje d’aya tare da sunkuyar da kanta da sauri.
Abbou Jaheed kuwa ganin dukansu sun ballara acikin falonne yasashi gyara zamansa tare da duban kowann
ensu, lokaci d’aya kuma yanayinsa ya sanja, ahankali cikin karyewar zuciya da kuma sanyin yanayi yace.
“Tabbas ban had’aku awajennan don maganan da zanyi ya zamo tashin hankali agareku ba, K’warai nasan cewa zakuji babu dad’i kamar yanda nima naji kuma
har I yanzu nake kan ji.
Lallaine kuma Tabbas kamar yanda dukkaninku kukasani K’addara takan iya zuwawa bawa tako wanni siga, haka kuma Allah Yakan jarraba bawansa ta hanyar da duk yaso, da bara ko wayo kuma bazaisa ka kub’ucewa hakan ba.
Sannan kuma in
ason kowannenku yasan cewar zan fad’i maganan nan a gabansa ne saboda matsayi