Showing 189001 words to 192000 words out of 244674 words
2019, wanda acikinta ne zaikai M.Jay d’in airport.
Shiga cikin motar yayi ya zauna, tare kuma da jingina bayansa ajikin kuj
eran motar, ya saki wani irin sassanyan numfashi, idanunsa ya d’an lumshe kamar yanda hakan ya zama wata d’abi’arsa, batare kuma daya bud’e idanun nasa ba, cikin halinnasa nason rashin tsawaeta magana yace da Abdoul.
“Kawomin cutie.
‿
“To.
‿
Kawae Abdoul
yace had’e kuma da juyawa cikin sauri ya nufi d’aya daga cikin gardens d’in dake cikin gidan, wanda ananne cat d’innasa take hutawa.
Shikuwa Maleek tafiyan Abdoul d’inne yasashi d’ago kansa tare da bud’e idanunsa, ya sauk’esu akan part d’in su Laylerh’
n, hakanan yakejin wani irin abu na yawo acikin rai da zuciyarsa, duk da yasan cewar adaman abunda yakeji d’in akwae babban rauni, amma koda wasa bazae tab’a bari zuciyarsa ta cigaba da kassara ba, duk da kuwa yasan cewar zaiyi kewarta sosae.
Dawowan Ab
doul wajen hannunsa d’auke da cutie ne kuma yasashi tsayar da duk wani tunaninsa, bud’e murfin motar yayi tare dasa hannu ya k’arb’i cat d’innasa, lallausan gashin jikinta ya soma shafawa ahankali, kamar dai yanda ya saba yi mata akoda yaushe.
Wanda gani
n hakanne kuma yasa Abdoul shiga cikin motar, batare daya tsaya wani b’ata lokaci ba kuwa yayiwa motar key, had’e dayin reverse tayanda zai fita daga cikin gidan asauk’ak’e, dan tuni maigadi ya wangale musu makeken hate d’in gidan.
Cilla hancin motar ka
n titi da Abdoul d’in yayi ne kuma yasashi sake maida bayansa ya kwanta ajikin kujeran motar, still har yanzu kuma cutie d’innasa na jikinsa yana shafa gashinta ahankali.
Yayinda Abdoul kuwa cike da k’warewa yake murza steering motar, kaitsaye suka nufi a
irport.
Kamar kuma yanda suke akan hanya haka ya kasancewa ga su Laylerh ma, saboda kuma gidan Aunty Zee d’in nada nisa sosae ne yasa basu isa da wuri ba.
Tunda suka kama hanya kuwa Laylerh bata sake koda wani k’wakk’waran motsi ba, kasancewar zuciyar
ta cike take da abubuwa maban banta, duk yanda Aunty Zee d’in taso janta da hira dan d’ebe mata kewa kuwa, sam takasa sakin rai da zuciyarta, Tabbas ayanzu Bawae sakin da Najeeb d’in yayi mata bane ke damunta, wani irin matsanancin kewa da takeji ne ke dam
unta, dan gani take kaman bazata sake had’uwa da Yah M.Jay d’innata ba.
K’aran da taji da kuma alaman cewar sun iso gidan Aunty Zee d’inne yasa ta bud’e idanunta ahankali.
Daidai lokacin kuwa maigadi ya wangale musu gate d’in gidan, Aunty Zee ta shiga
da motar ciki.
Anutse ta gama daidaita parking d’in motar tata, cikin kuma fari’a da sakin fuska ta dawo da kallonta ga Laylerh’n.
“Muje ko.
‿
Tafad’a tana me k’ok’arin bud’e murfin motar.
Asanyaye ta jinjina kanta alaman.
“To.
‿
Tare kuma da b
ud’e murfin motar itama ta fito waje.
Sannu ahankali take k’arewa had’add’en gidan Aunty Zee d’in kallo, wanda sosae aka kashe masa mak’udan kud’ad’e wajen k’awatasa.
Trolleybag d’inta dake gidan baya Aunty Zee d’in ta ciro, ita da kanta ta rik’e tr
olley d’in tare kuma da kama hannun Laylerh’n sukayi cikin gidan da ita.
Da sallama abakinta suka kutsa kai cikin babban falon gidan.
Aliya dake zaune afalon tana kallon film d’in Nollywood, jin sallaman Auntynta ne yasata d’agowa da sauri, tare da m
ik’ewa tsaye tana fad’in.
“Oyoyo Aunty Zee sannu da dawowa.
‿
“Yauwa Aliya sannu.
‿
Aunty Zee ta bata amsa adaidai lokacin da suka k’arasa shigowa cikin falon.
Wanda kuma sai alokacinne idanun Aliya suka sauk’a akan Laylerh.
“Masha Allah ji wata k
yakkyawa!
‿
Tafad’i haka acikin ranta, tana me sakarwa Laylerh’n murmushi.
Itama Laylerh’n murmushi tayiwa Aliya’n wanda bazata tab’a finta ashekaru ba, haka kuma itama kyakkyawace duk da kasancewarta Brown skin amma tana da kyau sosae.
Trolleybag d’
in Laylerh’n Aunty Zee ta mik’awa Aliya, kana cikin kulawa tace.
“Ki kaimata trolleybag d’inta d’aki, daga yau kinsamu k’arin y’ar uwa, saura kuma ki dameta da shegen surutunki, domin Laylerh ba mai yawan son hayaniya bane.
‿
Murmushi Aliya tayi tare
da amsar trolleybag d’in, cikin matuk’ar jin dad’i tace.
“No bazan dameta da surutu ba, ae sometimes kina bani labarinta, yau dai kam gashi Allah Yayi naga Beautiful Night da idanuna.
‿
Idanu Aunty Zee da Laylerh suka d’an zaro, cikin kuma yanayin mam
aki Aunty Zee tace.
“Beautiful night kuma Aliya?
‿
Kai Aliya ta gyad’a, kana tana dariya tace.
“Eh mana Aunty Zee beautiful night, ma’anan Laylerh ai dare ne, to ita kyakkyawan dare ne mai yawan stars.
‿
Dariya Aunty Zee tayi, tare kuma dajan wani d’
an guntun tsaki, domin kuwa idan da sabo to ta saba da halin Aleeya, always acikin shirme da yawan surutu take.
Laylerh ma murmushi tayi, saidai batace komae ba, hannunta Aleeya ta kama suka nufi d’aya daga cikin d’akunan dake k’asa wanda acikinsane d’a
kin Aleeya d’in yake.
Har sunkai bakin k’ofar muryar Aunty Zee ya tsaidasu inda take cewa.
“Idan sun shiga d’akin Aleeya ta shiryawa Laylerh kayanta acikin drawer, sannan kuma ta taimaka mata tayi wanka, daganan sai suzo suci abinci.
‿
Da “To.
‿
Ale
eya ta amsa sannan suka shige cikin d’akin, itakuwa Aunty Zee sama ta haura, Dan anan bedroom d’inta dana mijinta da kuma na two kids d’inta suke.
*M.Jay*
Shigowarsu cikin airport d’in kenan aka soma k’iraye k’irayen sallan magrib, hakan yasa Abdoul
na gama parking ya bud’e murfin motar ya fito.
Saidai ma tun kafun ya gama fitowa abokan aikinsa wanda dasu za’ayi tafiyar, sukayi saurin k’arasowa wajen tare da sara masa, kasancewar dukansu shine ogansu, duk da cewar kuwa suma sunada babban matsayi amma
nasa matsayin ya fi nasu, kuma akowanni tafiya shine shugabansu, haka ko awajen horarwa ma shine mai horar dasu.
Yana gama fitowa daga cikin motar tasa kuwa Fou’ad na k’arasowa wajen, wanda shima yau shirye yake tsab cikin soldiers uniform d’insa, da
suka k’ara bayyana zallan kyawunsa, wanda har idan ka kallesa ba zaka ce shine wannan mai raunin ba.
Hannu ya mik’awa Maleek d’in suka gaisa, tare da soma yi masa wani irin kallo mai d’auke da tambayar.
“Har yaushe ka warke da zaka iyayin wannan tafi
yar?
‿
Gane abunda Fou’ad d’in ke nufine kuma yasa Maleek d’auke kai daga kallonsa, murfin motarsa ya bud’e ya d’auko goran ruwa, batare daya kula kowannensu ba kuwa ya soma gabatar da Alwala’n sallan Magriba.
Ganin hakan da sukayine kuma yasa dukkani
nsu kowa ya nemi ruwa yayi alwala.
Bayan dukansu sun kammala alwalan ne kuma dukansu suka had’a jam’i sukayi sallan magriba.
Daganan gaba d’ayansu suka nufi jirgi, domin tuni wasu harsun fara shiga.
Kasan shine yayi na k’arshen shiga jirgin, wanda yana
shiga baijimaba kuma aka kulle k’ofar jirgin.
Kamar kuma yanda yake atsare 7:00 pm daidai jirginnasu ya d’aga zuwa sararin samaniya.
Abdoul kuwa ganin tashinsu ne yasashi komawa cikin mota inda ya tarar da kuliyar Maleek d’in nata harkokinta kamar ya
dda ta saba, tuna halin Captain d’innasu ne kuma yasa shi sakin murmushi, tare da yiwa motar key kaitsaye ya kama hanyarsa ta dawowa gida.
Kallon Momy Aunty Aina’u tayi fuskarta d’auke da tsananin mamaki tace.
“A gaskiya bangane abunda kike son fad’a
minba Aunty Suwaeba, wai kina nufin da gaske Najeeb ya saki Laylerh, yanzu kwata kwata babu aure atsakaninsu?.
‿
Wani irin Murmushi mai d’auke da ma’anoni daban daban Momy dake zaune akan kujera tayi, Tabbas ayanzu ita kad’ai tasan abunda take sak’awa a
cikin rai da zuciyarta, domin alk’awari tayi cewar bazata tab’a bari wannan lokaci da kuma daman da tasamu su tafi abanza ba.
D’an k’walin dake kanta tad’an turo gaba, cike kuma da son bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarta tace.
“Abune da kika
sani Aina’u akan wannan bazan tab’a gaya miki ba gaskiya ba, Tabbas Najeeb ya saki Laylerh, wanda kuma dasa hannuna hasalima ninayi duk wani abu dayasa ya saketa, Nina bankad’a masa sirrin da ke b’oye, har kuma nasa yaga hakan da idanunsa, yanzu kuma na
samu abunda nakeso.
‿
Takai k’arshen maganar nata da wani irin alfahari.
Wanda yasa Aina’u zuba mata ido, domin kuwa har yanzu bata gane inda kalaman Yayartata suka dosa ba.
Saidai kuma k’aguwa dason sanin mene plan d’in yayartata na gaba yasa ta
cewa.
“Yanzu Mekika shirya musu anan gaba? Sannan kuma mekika aikata haka dahar yasa Najeeb ya saketa? Saboda meyasa kuma kikayi hakan?.
‿
Jin tambayar da Aina’un tayi matane yasa ta mik’ewa tsaye.
Tare da d’an soma tafiya, saidai kuma ko taku uku
batayi ba ta tsaya da tafiyan da takeyi d’in.
Still wani shu’umin murmushi ta sakeyi tare da had’e hannayenta waje d’aya.
Cikin muryar dake bayyanar da gaskiyar mummunan manufarta tace.
“Saboda inason na maida ita karuwarsa, tayanda zasu kusanci
juna batare da aure ba, idan kuma har baki fahimci abunda nake nufi ba, to ma’ana ina nufin su aikata ZINA kenan, so nake nasa musu wani abu na daban, wanda har abada zuciyarsu bazata tab’ayin sanyi ba.
‿
*13/3/2021*
*8:14 pm*
3/16/21, 8:55 AM -
Ummi Tandama: *L.M*
*Note editing*
*Chapter 67*
Idanu Aunty Aina’u ta d’an zaro waje, domin ita kanta mummunan fatan da kuma mugun nufin da Yar uwarta ta ke bin su Maleek d’in dashi ayanzu ya fara tsoratata, saboda ta fahimci cewa da gaske Momy’n
keyi, burinta d’aya kawae shine taga ta kawar da duk wani farincikin daya shafi rayuwar LAYLERH MALEEK.
Juyowa Momyn tayi ta kalli Aunty Aina’u, wanda tayi shiru ta kasa cewa komae.
Baki ta bud’e daniyar yiwa Aunty Aina’un magana, amma kuma wani abu d
a ta tuna ne yasa ta fasa fad’in maganan dake cikin bakinta, juyawa tayi direct d’akinta ta nufa, tana me sakin wani munafukin murmushi.
Aunty Aina’u kuwa da idanu tabita, domin kuwa ayanzu itakan takanji zuciyarta ta karaya daga aikatawa su Laylerh’n mug
unta, saboda taji awa’azi babu kyau cutar da Maraya, tana kuma tsoron abunda zaije ya dawo, dan abune dayake abayyane duk wani mai mugun nufi da aniya baya k’arewa k’alau.
Acan gidan Aunty Zee kuwa tsab Aleeya ta gama jerewa Laylerh kayanta dake cikin
trolleybag zuwa drawer, sannan kuma ita tayiwa Laylerh’n jagora har tayi wanka.
Yanzuma zaune take bisa sallayan da tayi sallah’n magriba akai.
Idanunta wanda suke d’an bayyana kasala ta lumshe, Yayinda kuma sannu ahankali takejin wani irin sanyi na
ratsa duk ilahirin jikinta, duk da cewar kuwa bawani sanyi sosae ake busawa ba, amma ita sanyin takeji.
Yanayin yanda ta lumshe idanunnata da kuma shirun da tayi ne, yasa idan mutum ya kalleta zai tsammaci cewa tayi nisa acikin tunani ne, wanda kuma ahak’
ik’anin gaskiya bawai hakan bane.
Ta daiyi shirune kawai tana me sauraran yadda kowani bugun zuciyarta d’aya, ke mu’amalantuwa da tsananin soyayyarsa, ta yadda takejin kamar soyayyar tasa ce ke sake ruruwa acikin zuciya da gangar jikinta, Yayinda daga g
efe guda kuwa takejin wani abu na musamman a kansa me kama da kewa.
D’an muskutawa tayi tare da sanya hannayenta duka biyu ta k’ank’ame jikinta waje d’aya, danji take kaman ana cakan k’ahon zuciyarta.
“Laylerh.
‿
Aleeya dake tsaye tun d’azu agefenta
ta k’ira sunanta.
Jin muryar Aleeya’n da tayi acikin kunnuwanta ne kuma yasa tayi saurin bud’e idanunta, tare da d’ago kanta ta fuskance ta.
Murmushi Aleeya ta sakar mata tare kuma da d’an rank’wafowa ta kama hannun Laylerh’n, cikin tausasa murya
da kuma nuna alaman tausayawa tace.
“Tunanin me kike? Kodae baki da lafiyane na fad’awa Aunty Zee takaiki hospital?.
‿
Murmushin daya bayyana kyawawan teeth d’inta tayi, hak’ik’a yau ne zuwanta gidan, amma acikin abunda bai wuce 1hour ba ta fahimci ce
war Aleeya na sonta.
“Babu komae kawai dai sanyi nakeji, kuma shid’inma bawani sosae ba.
‿
Tafad’i hakan cike dason kawarwa da Aleeya kokwanton dake cikin ranta.
Jin hakanne kuma yasa Aleeya, kamo hannunta suka mik’e tsaye atare, batare kuma da taj
ira komai ba tace.
“To Muje falo muci abinci idan muka gama saikiyi sallan Isha ki kwanta, naji ma Aunty Zee tace wae jibi zaku fara WAEC (West African Examination Council), dole kina buk’atar time d’in da zakiyi karatu.
‿
Kai kawae Laylerh’n ta iya
jinjina mata, daga haka suka fice daga cikin d’akin.
Koda suka fito falo kuwa direct dining table suka nufa, wanda tuni house girl d’in Aunty Zee d’in ta rigada ta shirya komae.
Coconut rice and fruit salad Aleeya ta zuba musu, tare da matsowa kusa da L
aylerh’n tace suci.
Sam bata wani jin yunwa sosae, amma kuma saidai ganin yanda Aleeya’n keta d’awainiya da itane yasa ta d’aukan spoon ta soma cin abincin.
Yayinda Aleeya ke ta bata labarai kala kala, wanda yawancinsu duk labaran Films ne, saboda Ale
eyan bayan zuwa school bata da wani aiki sai kallon films.
Tunkuwa Laylerh’n bata enjoying labaran films d’in da Aleeya’n ke bata, har ta fara enjoying, ahaka har suka kammala cin abincin daidai lokacinne kuma aka fara k’iraye k’irayen sallan Isha.
Haka
n yasa dukansu atare suka mik’e dan zuwa gabatar da salla’n Isha.
*Washington DC
🇺🇸
*
Kusan kota Ina dake cikin babban airport d’in d’auke yake da jama’a wanda kuma kusan gaba d’aya mutanen dake wajen suka kasance fararen fata, Yayinda kuma kowannen
su da abunda yakeyi.
Saidai kuma isowar babban jirgin da Kusan dukkaninsu shi suke jirane yasa gaba d’ayansu kowa ya nutsu.
Sannu ahankali kuma jirgin daya sauk’a ya gama daidaita tsayuwarsa.
Bayan kuma sauk’arsa da mintuna kad’an aka bud’e babban
k’ofar fita daga cikinsa.
Wanda hakanne ya bawa mutanen dake cikinsa daman soma firfitowa anutse.
Ahankali ya bud’e idanunsa wanda suka b’ata tsawon some minutes arufe, wani irin sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e, had’e da zare sit belt d’in dake jik
insa ya mik’e tsaye.
Ganin hakanne kuma yasa Fou’ad dake zaune shima ya mik’e tsaye, tare dabin bayan Captain Maleek d’in wanda tuni ya riga daya fara tafiya, kasancewar tuni sauran abokan aikinsu da suka taho tare sun riga dasun sauk’a.
Cikin taku
nsa mai d’auke da izza yake sauk’owa daga kan matattakalan jirgin, Yayinda hannunsa na dama ke d’auke da jakarsa.
Jin yanda Fou’ad dake bayansa ke d’an magana k’asa k’asane yasashi d’an juyawa ya kalleshi, saidai kuma bai tankawa Fou’ad d’inba ya k’arasa
sauk’owa daga kan steps d’in jirgin, duk da kuwa yasan cewar dashi Fou’ad d’in yake.
Yana gama sauk’owa daga kan steps d’in kuwa, sauran soldiers d’in da yake wakilta, da kuma way’anda suka zo tarbansa suka soma sara masa, wasu daga cikinsu kuwa murfi
n had’add’iyar motar da suka zo d’aukansa aciki suka bud’e masa, batare daya jira komae ba kuwa ya Sakai ya shige cikin motar.
Ganin hakanne kuma yasa duk sauran soldiers d’in suma suka shishshiga motocinsu, kaitsaye suka nufi waje na musamman daya kasan
ce masauk’insu.
Koda suka k’arasa wajen dayake kaman camp d’insu, cike area’n wajen yake da soldiers hakan yasa hayaniyan dake wajen ya d’anso yin yawa.
Kasancewarsa kuma ba maison yawan hayaniya ba shiyasa yana fitowa daga cikin mota kaitsaye yanufi
can cikin gurin, inda anan room d’insa mai number 15 yake.
Yana shiga cikin d’aki me kaman aljannar duniyar kuwa, ya turo k’ofar d’akin ya rufe, tare dasa key domin kwata kwata bayason damuwa, ya kuma san yana barin d’akin abud’e to fa Fou’ad zaizo y
a takura rayuwarsa.
Bud’e wani glass drawer’n dake cikin d’akin yayi tare da jefa jakar dake hannunsa aciki.
Anutse ya soma rage kayan dake jikinsa, bayan kuma ya kammalane ya d’aura wani white towel akan waist d’insa, cikin zak’uwa da kuma son hutaw
a gajiyar dake jikinsa ya wuce toilet d’in dake cikin d’akin wanda ya kasance shima na zallan Glass ne, saidai kuma amma na waje sam Bazai tab’a iya ganin na ciki ba, saidai kuma wanda ke cikin toilet d’in zaiga wanda ke waje.
Sassanyan ruwan dake ciki
n shower ya sakarwa kansa, batare kuma daya damu da irin sanyin da akeyi a garin ba.
Bawae kuma dan bayajin sanyin bane, kawai k’arfin hali da kuma taurin zuciyane irin nasa.
Batare kuma daya b’ata lokacinsa sosae ba ya kammala wankan nasa tare da d’auro
alwala, dan gabatar da sallan Isha.
Ahankali ya bud’e k’ofar toilet d’in ya fito, hannunsa rik’e da d’an madaidaicin towel yana goge ruwan dake jiki da kuma kansa.
Bayan ya kammala goge jikinnasa ne kuma yayi amfani da wani new edition handryer ya b
usar da tarin suman kansa.
Gaban wani makeken dressing mirror ya kalla, wanda aka ci kasa da kayan shafa irin wanda ya ke amfani dasu, wanda hakan kuma yasan ba aikin kowa bane, sai na mutanen dake k’asa dashi, domin kowa yasansa to yasan halinsa, idan
har zayyi tafiya to baya d’aukan wasu shirme, yafison atanadar masa da komae a inda zaije d’in.
Body lotion da kuma turaren D&G kawae ya shafa ajikinsa, yana tsaye agaban mirror d’in kuwa aka soma yi masa knocking k’ofa.
Sanin wanda ke knocking d’inne
kuma yasashi k’arasawa ya bud’e k’ofar, tare kuma da d’an matsawa, ya bawa
D’aya daga cikin ma’aikatan soldiers d’in nasu daman shigowa cikin d’akin, anan kan gado ya ajiye masa manya manyan ledodin da cikinsu ke d’auke da new clothes, cikin harshen tura
nci kuma ya tambayesa ko akwae wani abunda yake buk’ata.
Kansa kawai ya girgiza alaman “Babu.
‿
Ganin hakanne kuma yasa soldier d’in juyawa ya fita, shi kuwa atake yasake locking door d’in.
Tare da bud’e d’aya daga cikin manya manyan ledodin clothes d
’in.
Wani dogon wandon combat had’e da white shirt wanda agabanta aka rubuta “To be a strong
‿
da blue painting ya ciro tare da sanyawa ajikinsa.
Sosae kuwa kayan sukayi