Showing 120001 words to 123000 words out of 244674 words

Chapter 41 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

tasake cewa komae ba, ta zuba masa chicken pepper saup d’in da ta gama girkawa yanzun, tare da had’a masa tea, har gabansa kuwa ta kawo masa abincin ta ajiye, batare

da ya tsaya b’ata lokaci ba kuwa ya soma cin abincin.

Anan gefensa Oum Ayush ta zauna tana kallon yanda yake cin abincin, wanda yanayin yanda yake d’iban abincin da kad’an kad’an ya tabbatar mata da cewar baya kulawa da kansa sosai, tausayinsu takeji Mat

uk’a shida Laylerh, saboda yanda rayuwarsu ke cike da maraici da kuma zallan kad’aici, Bazata ce Abbou Jaheed baya k’ok’arin kulawa dasu ba, saidai kuma ba kulawan Abbou Jaheed d’in kad’ai suke buk’ata ba, kulawan Uwa shi dukansu suke buk’ata acikin rayuwa

rsu, domin Uwa itace ginshik’in y’ay’anta.

Ahankali ya cire hannunsa daga cikin abincin, tare da d’aukan kofin tea d’in dake gefensa yakai bakinsa.

Batare kuma daya wani sha tea d’in sosae ba ya mik’e tsaye tare da d’aukan tissue ya goge bakinsa.

“Thank

you

‿

Ya fad’a cikin yin k’asa da murya tare dasa hannunsa acikin aljihun wandonsa ya ciro sweets guda biyu, b’are sweets d’in duka biyu yayi ya jefa d’aya abakinsa, kallon Oum Ayush yayi cikin sigar tsokana tace. “Bud’e bakinki nasa miki sweet.

‿

Jin ab

unda ya fad’a yasata watsa masa hararan wasa, cikin maganarta da baikai zuci ba tace. “Akan ina wasa dakai?

‿

Awannan karon kam murmushi maikama da dariya yayi, batare da Oum Ayush d’in tayi zato ko tsammani ba kuwa ya matso gab da’ita, bakinta ya bud’e ya

jefa mata sweet d’in aciki, baijira me zata ce masa ba kuwa yayi saurin k’arasawa cikin falon ya d’au jakarsa, ahanzarce ya fice dan yayi latti sosae, kasancewar kuma yaud’in akwae soldiers d’in da yakeson horarwa ne, yasa yana fitowa daga part d’in Oum A

yush d’in motarsa ya fad’a, batare kuma da yanemi Abdoul ba da kansa yayi driving motar, maigadi na wangale masa gate d’in gidan ya cilla hancin motar tasa waje.

Jin k’aran tashin motarsa ne kuma yasa Oum Ayush sakin murmushi, sweet d’in daya sa mata ab

aki ta cire tare da d’aukan ledan sweet d’in daya zubar anan falon, sunan sweet d’in ta karanta tare da amfanin da yakewa mutum, ganin cewar sweet d’in na k’arawa mutum kuzari da kuma k’arfi ne yasata sake sakin murmushi abayyane tace.

‿

Mai hali baya tab

’a sanja halinsa, wato yabani sweet me k’ara kuzari nasha, dannayita jibgan aiki, d’an baccin rana dana sabayi ma bazan samu nayi ba to bazan shaba, dama aina sani Maleek baya kyauta haka kawae miskilin soja kawai.

‿

Ajiye mintin tayi akan table tare da mi

k’ewa ta shige d’aki dan so take tad’an huta.

Ab’angaren Laylerh kuwa sama da awa d’aya ta kwashe zaune acikin falon tana kallon film d’in da Bollywood ke haskawa, jin bacci yacika idanunta ne yasata tashi asanyaye ta nufi part d’insu zuciyarta cike da

fatan kada Allah Ya had’ata da Najeeb.

Bak’aramin dad’i kuwa taji ba alokacin da tashiga part d’innasu ta tarar da Najeeb d’in bayanan, hayewa saman gado tayi cikin abunda baiwuce mintuna kad’anba kuwa bacci ya d’auketa.

Bacci sosai tayi domin ba ita ta

farka ba sai k’arfe 2:56 pm, ganin kuma irin lokacin da ta d’auka tana baccin ne, yasa ta shiga mamaki, dan bata tab’a bacci me nauyi irin haka ba, ahanzarce ta wuce toilet ta d’auro alwala koda tafito kuwa sallaya ta shumfud’a tare da hawa kai ta tada sal

lah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayanba saida ta sallame sallan la’asar, azkhar d’in yammaci tayi tare da mik’ewa tsaye ta soma rage kayan jikinta, bayan ta gama cire kayan nata ne kuma, ta wuce toilet wanka tayi tare da d’auro sabon alwala,

koda ta fito ganin yamma tayi sosai ne yasa sama sama tashafa lotion ajikinta, powder da kuma lipstick wanda ya saje da kalan labb’anta ta shafa.

Ahanzarce ta k’arasa gaban sif d’in kayanta, kasancewar kuma bata fiye son kaya masu nauyi sosai bane yasa t

a zaro d’aya daga cikin had’add’un dogin rigunan da Oum Ayush takawo mata tsarabarsu, duk da kuma kasancewar rigar nada d’an fad’i kad’an amma hakan bai hana had’add’iyar surar jikinta bayyana ba, yayinda kuma adon fararen duwatsun dake gaban rigar keta fa

man shining suna d’auke ido.

Anutse ta nad’a vail d’in rigar akanta kasancewar kuma vail d’in nada d’an girma kad’anne yasa ya sauk’o har kan k’irjinta, cool perfume ta shafa ajikinta tare da komawa kan gado ta zauna, d’an k’aramin handbag d’inta dake aje

saman bedside ta jawo, wanda tun daren jiya da Oum Ayush ta ajiye mata shi bata sakebi takansa ba, zuge zip d’in jakan tayi, ganin kud’ad’e masu yawa acikin jakanne yasata d’an zaro idanunta, cike da yanayin mamaki kuwa ta sa hannu ta d’ebo kud’ad’en wand

a bandir biyu na cikinsu suka kasance 2/2 hundred K, d’ayan bandir d’in kuma 100k ne.

D’an soma jujjya kud’ad’en tayi tare da sake lek’a cikin jakan ta zaro car key d’in da tagani aciki, sai kuma wayarta, maida kud’ad’en tayi tare dajan zip d’in jakan ta

rufe, wayarta dake kashe ta kunna take kuwa sak’onnin Teemah suka fara shigowa, wanda dayawan sak’onnin kuma d’auke suke da zallan tsokana.

Share sak’onnin tayi batare da ta kulasuba ta somayin game dan shid’inne kad’ae zaihana k’wak’walwarta yin tunani

marassa amfani.

Tana nan zaune kuwa har aka k’ira sallan magriba, sanin kuma da tayi cewar tana da alwala ne yasata shumfud’a sallaya ta tada sallah.

Tana nan zaune akan sallaya aka k’ira sallan Isha, bayan ta sallame sallan kuwa batawani tsaya yin dogon

addu’aba ta mik’e tsaye saboda tun tashinta take jin cikinta na kukan yunwa.

Turare ta sake fesawa ajikinta tare da d’aukar wayarta tafice daga cikin d’akin, kaitsaye babban parlor’n gidan ta nufa, kasancewar tasan adaidai wannan lokacin ne sukeyin dinne

r.

Acan cikin falon kuwa zaune suke su dukansu ciki kuwa harda Maleek wanda ya maida gaba d’aya hankalinsa ga wayarsa dake rik’e ahannunsa.

Shigowarta cikin falonne kuma yasa Najeeb dake zaune ya d’ago kansa ya kalleta, hakan yafarune kuma saboda daddad’

an k’amshinta da yaji ya ratsa cikin hancinsa.

Tabbas duk da cewar fushi yakeyi da’ita amma ganinta da yayi yanzun yasa shi jin zuciyarsa tayi masa sanyi, hakanan yaji ya nemi duk wani b’acin ransa ya rasa, kallon tsab yayi mata, tunawa kuma da abunda ke

cikin zuciyarsa ne yasakashi sakin murmushi, domin alk’awari yayiwa kansa cewar ayau a kuma awannan daren babu abunda zai hanashi disvirgin d’inta.

Anutse ta k’araso dining table d’in, tare da d’agawa su Abbou Jaheed gaisuwa, saidai kuma wannan karon fu

ska asake Abbou Jaheed ya amsa mata.

Kujeran daya zamana shikad’aine awajen taja ta zauna, daidai lokacin kuwa idanunta suka Sauk’a akan Maleek wanda shigar jumper’n dake jikinsa tayi matuk’ar yimasa kyau.

Azahirance kuwa zaman nata, yayi daidai da mik’

ewarsa tsaye, k’ok’arin barin dining area d’in yayi, domin matuk’ar Laylerh zata kasance akusa da Najeeb to bazae tab’a iya jurewa ba, saidai kuma k’iran sunansa da Abbou Jaheed yayi ne, yasashi tsayawa, batare kuma daya juyoba ya amsa k’iran Abbou Jaheed

d’in.

Abbou Jaheed kuwa da ya tsaya dacin abincin da yakeyi, Sam baidamu darashin juyowan Maleek d’inba, cikin muryarsa da sam bata d’auke da alamar wasa yace.

“Kashirya gobe da safe za muje kaga matar dana zab’a maka, ma’ana wacce zaka aura, inason kasa

ni kuma ba shawara bane umarni ne.

‿

*(Nasan dayawanku kunayiwa Abbou Jaheed kallon mutum meson kai, amma anan gaba kad’an zaku fahimci komae, then kada kuji haushi dan Abbou Jaheed yace zaiyiwa Maleek Aure, saboda saida wata hanyar k’addaran ake samun w

ani cikar burin, sannan kuma wata k’addara takan rikid’e tazamo alkhairi, please banaso kuyi saurin yanke hukunci domin bakusan wani future M.Jay da Laylerh kedashi agaba ba. Sannan ku k’ara hak’uri dani please danaso na bud’e WhatsApp dawani new sim saiku

ma naga abun bazaiyiwuba shiyasa na hak’ura har aka gyara wannan d’in.)*

*16/Jan/2021*

1/19/21, 9:09 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Chapter 39*

Tamkar sauk’an rugugin aradu haka su biyun sukaji sauk’an kal

aman Abbou Jaheed d’in acikin kunnuwansu, wanda kuma ba iya su bama harta su Oum Ayush saida sukaji maganar Abbou Jaheed d’in tazo musu abazata.

“What!!!

‿



Ya fad’a cikin wata irin murya dake bayyana zallan tashin hankalinsa, tare da juyowa cikin sauri

ya fuskanci Abbou Jaheed d’in, wanda jin kalaman da ya fad’a d’inne kuma yasa shi saurin juyowa tare da zazzaro idanunsa waje, cike kuma da rashin fahimtar inda kalaman Abbou Jaheed d’in suka dosa, cikin mauryarsa da tasanja amo lokaci guda ya maimaita kal

mar ta. “Aure!!

‿

abakinsa dan hakanan yajita wata iri, duba da irin yanda shigar Kalman cikin kunnuwansa ta haifar masa da matsanancin bugun zuciya, da kuma fad’uwar gaba.

Abbou Jaheed kuwa ganin yanayin tashin hankalin da Maleek d’in ya shiga ne yasashi

d’aure fuskarsa tamau, batare kuma da alaman wasa ko wargi ba akan fuskartasa yace.

“Eh Aure zakayi kamar yanda kaji na fad’a, saboda bazan zuba maka idanu ka zauna haka ba, inaso kuma kasan cewa hakan umarnine ba wai shawara ba, na riga dana gama yanke

hukunci, ba kuma zan tab’a sanjawa ba, saboda haka koda Yaushe yazamana kana cikin shiri, saboda ba neman amincewa ko yardarka nake da buk’ata ba, domin na baka dama amma kayi wasa dashi, atunaninka haka zanzuba maka ido, ina kallo kanayimin duk abunda kag

a dama acikin gida? bayan kuma kasan cewar bazan tab’a lamuntar hakanba, sannan zab’i ya rage naka ko kaso ko karka so aurenka babu fashi, domin kai ba k’aramin yaro bane da za’a tsaya tambayar amincewarka ko akasin haka.

‿



Idanunsa da sukayi jajur loka

ci d’aya ya rumtse da k’arfi, domin hakanan yaji k’afafunsa na neman gaza d’aukar nauyinsa, yayinda kuma take guiwowinsa suka yi sanyi, shikam idan ba yaudarar kansa yakeyi ba saiyakejin kamar kunnuwansa basu jiye masa maganganun Abbou Jaheed d’in adaidai

ba, kansa ya d’an soma girgizawa ahankali, cikin cijewa da kuma k’ok’arin daure zuciyarsa ya had’e labb’an bakinsa ya ciza, wani irin tafasa da yaji zuciyarsa nayi ne kuma yasashi juyawa cikin sauri ya soma sauk’a daga kan y’an k’ananan steps d’in da zai n

esanta ka da dining area’n.

Laylerh kuwa dake zaune wanda tuni kalaman Abbou Jaheed d’in sun sa tazama kaman statue, bayan Maleek d’in tabi da idanunta wanda suka cika da ruwan hawaye batare da ta sani ba, yayinda kuma taji wani irin abu mekaman dutse ya

tokare k’irjinta.

“Mekenan me hakan yake nufi, M.Jay aure zaiyi kaman yanda itama tayi aure? Wannan wace iriyar k’addarace me matsanancin girma?

‿

Tayiwa kanta tambayar da har acikin zuciyarta bata da gamsuwa akan hakan, meyake shirin faruwa da’ita ita ka

nta batasani ba, raunannun idanunta wanda suke shirin zubo da k’wallan dake cikinsu ta lumshe, cikin karyewar zuciyar daya risketa ta kifa kanta anan saman table d’in dake gabansu, tare kuma dasa hannu ta dafe daedae saitin zucuyarta dake bugawa da sauri,

tabbas wani abu me kama da matsanancin fad’uwar gaba da kuma tsoro takeji, wanda hakanne kuma yasa ta keji ajikinta kaman tarasa wani babban kaso na babin nutsuwarta.

Saidai kuma jin da tayi Abbou Jaheed d’in na fad’awa su Abbou Kareem cewar y’ar gidan ab

okin aikinsa ne ya zab’awa Maleek d’in, wato Alhaji Faruk yasa tayi saurin d’ago kanta, domin kuwa tasan cewa Alhaji Farouk d’in baida wata y’a sai Munnira, matashiyar budurwar dake matsanancin jin kai, da kuma isa had’i da d’agawa wacce akoda yaushe take

ganin tafi kowa, duk da kuwa cewar baza’a k’irata da sunan mummuna ba amma bata da wani kyau irin na fitar hankali.

Lips d’inta ta ciza tare da d’anyin kasa da kanta, domin sam bataso wani daga cikinsu yakaranci yanayin da take ciki.

Saidai kuma duk yand

a taso ga b’oye yanayin nata hakan baisa Najeeb kasa fahimtar sanjawar da mood d’inta yayi lokaci d’aya ba.

Saidai kuma sanin abunda ya shirya acikin zuciyarsa yasa shi kasa ce mata komae, saima maida hankalinsa da yayi akan plate d’in abincin dake gabans

a.

Ab’angaren Maleek kuwa zuciyarsa cike da k’una haka ya k’arasa part d’insa, kaitsaye bedroom d’insa ya wuce, ahankali ya maida k’ofar bedroom d’in nasa ya rife, cikin yanayin daya samu kansa ya jingina bayansa ajikin k’ofar tare da rumtse idanunsa da

k’arfi, yayinda kalaman Abbou Jaheed kedawowa cikin kansa filla filla.

Abayyane ya tambayi kansa cewar.

“Meyasa k’addara zata zab’a masa irin wannan rayuwa me cike da k’uncin?

Shin tayaya nema zuciyarsa zata iya jure d’aukan way’annan manya manyan k’add

arorin da suke tunkarosa?

Meyasa Abbou Jaheed zaiyi masa haka? Meyasa!!!

‿

Yafad’a cikin k’araji tare dasa hannunsa ya naushi k’ofar d’akin, tabbas da ace zai iya bud’e baki ya furta rashin amincewarsa ga kalaman Abbou Jaheed d’in ayau da yayi hakan, ko d

a zaiji sanyi da nutsuwa acikin zuciyarsa, saidai kuma amma bashi da wani zab’i domin kasantuwar Abbou Jaheed amatsayin mahaifinsa yasa ya zame masa dole yin biyayya agaresa.

Asanyaye ya tako zuwa tsakiyar d’akin nasa, hakanan yakejin duk zuciyarsa ba dad

’i.

Abakin gadonsa ya zauna tare da sa tafukan hannayensa ya rufe fuskarsa, magana ta gaskiya shine baya ji ajikinsa cewar zai iya zama da wata mace amatsayin mata, saboda fata da kuma buri d’aya kawae yake dashi, wanda kuma ya riga da yayi losing d’insu

tuntuni, hakan yasa sam bayajin wata mace amatsayin abokiyar zamansa, tabbas ya yarda cewa soyayyar Laylerh tana d’aya daga cikin manyan k’addarorinsa haka ma kuma rasata, shima k’addara ne me d’auke da k’alubale na musamman, hak’ik’a yasan cewa akoda yaus

he Allah Ne ke tsarawa bawa fad’uwa da kuma nasararsa, shi ne kuma ya tsara masa komae, amma bayajin acikin tarin k’addarorinsa akwae wata bayan Laylerh, saboda yayi Imani cewa Laylerh ita kad’aice mace da aka rubuta masa acikin k’addaransa, kuma itace rau

ninsa, samunta nasara ne rashinta kuma nak’asu ne acikin rayuwarsa, ya yarda cewa zae rayu da dafin sonta acikin zuciyarsa, zafi k’una da kuma radad’in da yakeji na soyayyarta akoda yaushe k’onasa suke, k’una me tsananin zafi, duk da hakan kuwa akullum sal

on soyayyarta sanjawa yake acikin zuciyarsa, wanda ayanzu shi kansa baisan wani irin soyayya bane yakeyiwa Laylerh’n, abu d’aya kawai yasani shine, da gaba d’aya zuciya da rayuwarsa yake sonta, zai kuma ci gaba da sonta har k’arshen rayuwarsa, saboda soyay

yarta agaresa babban garkuwa ne dake k’arawa zuciyarsa k’wari.

Wani irin numfashi me tafiya da ajiyar zuciya ya sauk’e, ahankali ya sulale jikinsa ya kwanta akan gadon tare da lumshe kyawawan idanunsa, wanda suka sanja launi daga farare zuwa ja.

Sama da

mintuna 10 ta d’auka tana aikin jujjuya spoon d’in abincin dake hannunta, duk kuwa ga yanda taso samawa kanta nutsuwa ta kasa, yayinda kuma ta kasa sa koda lomar abinci d’aya ne abakinta.

Tana nan ahaka kuwa harsu Abbou Jaheed suka kammala cin abincinsu

suka tashi, hakan yasa daga ita sai Najeeb ne suka rage akan dining table d’in.

Wanda kuma gaba d’aya a ankare yake da yanayin Laylerh’n, duk da baisan asalin dalilin dayasa tasamu kanta ahakan ba, amma yaji ba dad’i saboda ko kad’an bayason ganin damuwa

akan fuskarta.

Ahankali ya d’ago kansa tare da sauk’e idanunsa akanta.

Ganin yanda ta sadda kanta k’asa ne yasashi k’iran sunanta asanyaye, batare kuma daya d’auke idanunsa akanta ba.

Jin amo da kuma sautin muryarsa ne yasa ahankali ta d’ago kanta cik

in muryarta da tayi sanyi sosae ta amsa masa, saidai kuma sam bata yarda ta sauk’e k’wayoyin idanunta acikin nasa ba, tayi hakanne kuma dan gudun kada ya karanci yanayinta.

“Tunanin me kike?

‿



Ya jefo mata tambayar da bata shirya amsa masa ba, saidai k

uma gudun kada ya zurfafa har yakai ga gano asalin abunda ke damunnata ne yasa asanyaye tace. “Ba komai!

‿



“Kin tabbata?

‿

Yafad’a yana me yawo da idanunsa akanta.

Kai ta jinjina masa alaman “Eh.

‿



“To kici abincinki idan kuma kin k’oshi kitashi kije ki

kwanta dare yayi.

‿

Ya fad’i maganar yana me kai dubansa ga agogon dake d’aure atsintsiyar hannunsa, wanda yake nuna k’arfe 8:45 pm.

Jin abunda yace dinne kuma yasata mik’ewa tsaye da sauri, domin dama neman hakan take, duk da cewar kuwa acikinta tanajin

yunwa saidai bata da dama ko nutsuwar cin abinci, Jan kujeran da ta zauna baya tayi, cikin yanayin sanyin daya rusketa ta soma k’ok’arin barin wajen cin abincin.

Da wani irin kallo ya bita har ta fice daga cikin falon, ajiyar zuciya me k’arfi ya sauk’e t

are da d’aukan bottle water ya soma sha.

Laylerh kuwa cikin yanayin sanyi ta k’arasa part d’innasu, ahankali ta tura k’ofar bedroom d’in ta shiga, direct gaban had’add’en dressing mirror ta nufa, hakanan tasamu kanta tana me k’urawa kyakkyawar innocent fa

ce d’inta idanu ta cikin madubin, take kuwa abubuwa da yawa suka shiga yawo akwanyarta, hannu tasa ta dafe k’irjinta dake dukan uku uku, hakanan takejin wani irin yanayin tsoro na sauk’ar mata, yayinda maganar auren Maleek d’in yayi mata tsaye acikin ranta

, wanda yasa duk takejin komai ba dad’i.

“Mezai faru idan Yah M.Jay yayi aure? Then me auren nasa yake nufi? Rayuwa zaiyi da wata mace na har abada? kyakkyawar fuskarsa, da kuma murmushinsa, had’i da komae da komae nasa wata dabance zata ke gani, hakan na

nufin kusancina dashi yazo k’arshe?

‿

Abayyane tayiwa kanta duka tambayoyin, wanda kuma hakan yasa wasu irin hawaye masu zafi suka biyo kan k’uncinta, hak’ik’a tana da fata da kuma buri akan Mah Boo d’inta, dukkuwa da cewar akwae auren Najeeb akanta, amma

koda da sau d’ayane bata tab’ajin d’igo d’aya na zazzafar soyayyarsa ya ragu acikin zuciyarta ba, akullum kuma tanajin cewa lallai watarana zasu kasance atare kamar yanda take gani amafarkinta yawancin lokuta, wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login