Showing 147001 words to 150000 words out of 244674 words

Chapter 50 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

samu kanta aciki ta koma cikin d’aki, wani black half cover shoe me tsananin kyau tasa ak’afanta, cikin sauri ta fito.

Sake kamo hannunta Oum Ayush tayi suka fice daga cikin falon.

Ita dai kam kamar rak’umi da akala haka take bin bay

an Oum Ayush d’in.

Har saida suka iso jikin mota kafun Oum Ayus d’in ta sake mata hannu.

Nanfa Oum Ayush ta shiga wajen driver itakuwa ta shiga gefen me zaman banza.

Da wani irin speed Oum Ayush ta ja motar yayinda maigadi ya wangale musu gate suka hau

saman shumfud’add’en titin dake malale a k’ofar gidan.

Tunda suka shiga motar Laylerh ke kallon Oum Ayush da gaba d’aya yanayinta ya nuna cewa tana cikin damuwa.

Asanyaye kana cikin voice d’inta dake cracking tace.

“Oum tun safe k’irjina bugawa yake, ga

ba na yana ta fad’uwa, tsoro nakeji matsananci, Dan Allah Oum kifad’amin meke faruwa? Kuma Ina zamuje haka?.

‿

Shiru Oum Ayush tayi ta kasa amsawa Laylerh’n tambayoyinta, daidai lokacin kuwa suka kawo cikin asibitin.

Ganinsu acikin asibiti ne kuma yasa La

ylerh zaro manya manyan idanunta, cikin matsanancin tsoro tace.

“Wayene bashi da lafiya Oum, Dan Allah Karki cemin Yah M.Jay ne, karki cemin mafarkina na jiya ne yakeson zama gaskiya, pleaseee.....

‿



da katawa da tafiyan Oum Ayush tayi tare da juyowa ta

fuskanci Laylerh’n, cikin muryarta da yayi sanyi sosae tace.

“Shi ne Laylerh Maleek ne yayi accident!

‿

Wani irin bugawa zuciyar Laylerh tayi wanda yayi sanadiyar durk’ushe wanta awajen, tare da zub’e guiwowinta ak’asa.

8February/2021

*7:30 pm*

2/1

3/21, 7:53 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Chapter 50*

Kyawwwan idanunta ta runtse da k’arfi wanda hakan ya bawa hawayen dake cikinsu daman gangarowa kan fuskarta, cikin matsanancin tsoron da ya shigeta ne kuma,

ta soma girgiza kanta ahankali, yayinda take kuma lokaci guda jikinta ya soma b’ari, tamkar wacce aka jonawa shocking, ahankali labb’an bakinta suka soma d’an motsawa, da’alama kuma wani abu take son fad’a daga bakinnata, amma takasa.

Ganin hakanne kuwa

yasa Oum Ayush da gaba d’aya jikinta ya riga da yayi sanyi tasa hannu ta dafa kad’an Laylerh, cikin muryarta dake bayyana zallan tausayin ta tace.

“Ki kwantar da hankalinki Laylerh, domin kuwa Ina da yak’inin cewa da izinin Ubangiji mai sama da k’asa bab

u wani abu da ya samu Maleek, koda ma kuwa ace yana cikin wani hali na rashin dad’i, ayanzu addu’ar mu yake da buk’ata bawae kuka ko firgicewa ba, ki tashi mu k’arasa cikin asibitin kinji, Dan Allah Karki ce zakiyi kuka.

‿

Tak’are maganan nata tana me yunk

’urin mik’ar da Laylerh’n tsaye, wanda tuni hawaye sun wanke mata fuska, yayinda wani hawayen na korar wani.

D’agota Oum Ayush d’in tayi, wanda hakan kuwa yasa tsab ta mik’e tsaye kamar yanda Oum Ayush d’in ta buk’ata, saidai kuma ko kad’an ta kasa iya d

aidaita nutsuwarta, wani irin tsalle k’irji da zuciyarta keyi kaman zasu fito waje, domin kuwa ta sake samun kanta acikin k’arin fargaba da kuma tashin hankali, asakamakon jin da tayi cewa M.Jay d’inta ne bashi da lafiya.

Cikin wata irin muryar dake shaki

ng, kana kuma wanda take bayyana tsananin tsoron dake cikin zuciyarta, murya ararrabe tace.

“Tsoro Nakeji Oum Ayush, Wallahi tsoro nakeji, nasani dama tunjiya nakeji ajikina cewar wani abu zai sameni, nayi mafarki cewar Yah M.Jay yayi accident, amma kuma

da na fad’awa Najeeb sai ya k’aryatani, nasani dama da yawan mafarkaina akansa gaskiya ne, wayyo Allah Na tayaya zan iya d’aukar wannan k’addaran? Tayaya zan iya jurewa? Tabbas nasan cewa aduniya babu wanda zaisan me nakeji ajikina aduk sanda wani abu na c

utarwa ya samu Yah M.Jay, wallahi nayi imani cewa akansa zan iya mutuwa, Oum Ayush ki tab’a zuciyata kiji, Wallahi gab take da rabewa gida biyu, menakeji wazai san me nakeji babu, babu wanda zai gane hakan sai ni kad’ai, tabbas K’addarorin Ubangiji sun cik

a rayuwarmu ....

‿

kasa k’arasa maganan nata tayi, saboda wani irin kuka daya so kwace mata.

Hakanne kuma yasa Oum Ayush tayi saurin sanya hannu ta toshewa Laylerh’n baki, domin kuwa itama tuni idanunta sun ciko da kwalla, yayinda wani irin matsanancin ta

usayin Laylerh’n ya cika mata zuciya, k’warai tasan cewa akwae wata soyayya me tsananin zafi dake tsakanin Laylerh da Maleek d’in, amma sam batasan da cewar k’arfin d’i maucewar Soyayyar tasu har takai haka ba.

Cikin son arawa kanta jarumta da kuma bawa L

aylerh’n k’arfin guiwa tace.

“Ya isa haka Laylerh, kuka da fad’an wasu maganganu ba naki bane, muje ciki kawae.

‿

ta k’are maganan agajarce tana me kuma kama hannun Laylerh’n batare da ta jira ta bakinta ba suka kutsa kansu cikin asibitin, domin dama tuni

Abbou Khareem yayiwa Oum Ayush d’in kwatancen d’akin da aka kwantar da Maleek d’in kuma ta gane, shiyasa ma bata tsaya tambayar kowa ba, kaitsaye suka nufi sashin da zai sadasu da d’akin, duk da cewar wajen privet waje ne babu yawan hayaniyan mutane da ku

ma sawunsu.

K’warai da gaske Laylerh bata gamsu da cewar akwae wani abu wai shi tsoro, fargaba da kuma bugun zuciya ba saida ta ga sun tsaya adaidai bakin wata k’ofa wanda take akulle gam, ahankali tasa hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta dake wani iri

n bugawa akaron na barkatai, lokaci d’aya kuma taji numfashinta nayin sama da k’asa cikin yanayin fusga tamkar wanda zae d’auke gaba d’aya.

Daidai lokacin ne kuma Oum Ayush da ita kanta jikinta ke ta faman tsuma tasa hannu ta bud’e k’ofar d’akin, ahankali

ta kutsa kanta ciki, yayinda bakinta ke d’auke da sallama.

Su Abbou Khareem dake zaune akan wasu fararen kujerune suka amsa mata, ciki kuwa harda Najeeb wanda da zuwansa asibitin zuwa yanzu da yake cikin d’akin bai wuce 14 minutes ba, kasancewar lokacin

da Abbou Khareem ya k’iarasa ya fad’a masa yana kusa da asibitin shiyasa bai wani d’au lokaci ba ya taho.

Turus haka Oum Ayush d’in taja ta tsaya adaidai lokacin da idanunta suka sauk’a akan Maleek dake kwance flat akan gado kamar gawa.

Cikin muryarta da

tayi sanyi sosai, kana cike kuma da tausayin Maleek d’in tace.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un!

‿

Kalmar da ta fad’a kenan wanda ya sa zuciyar Laylerh dake waje sake harbawa da k’arfi.

Wanda kuma sanadin jin hakan ne ya bawa hawayen dake cikin idan

unta daman gangarowa kan k’uncinta, ahankali cikin wani irin yanayin da ita kanta bazata tab’a iya fassarasa ba, ta soma d’an jan k’afafunta dake rawa zuwa cikin d’akin.

K’afarta ta fara sakowa cikin d’akin kafun kanta ya biyo baya, tana shigowa kuwa idan

unta wanda ganinsu ya d’an disashe saboda hawayen dake cikinsu, suka sauk’a akan mutumin dake kwance, wanda tayi imani cewa koda makancewa tayi Indai yana kusa da ita to babu abunda zai hanata iya zayyano halittar kyakkyawar fuskarsa dama murd’add’iyar sur

ar jikinsa dake cike da matsanancin kwarjini.

Hawayen dake cike a cikin idanunnata ne suka samu daman soma yi mata ambaliya akan k’uncinta, hakanne kuwa yasa ganinta ya sake disashewa, yaza mana bata iya tantance yanayin tsarinsa.

Ahankali ta d’aga k’afa

funta wanda take jinsu kamar an sark’e mata su da igiyan kaca, cikin yanayin dake bayyana zallan rashin nutsuwa da kuma firgicin da take ciki, ta shiga takawa kaitsaye zuwa inda Maleek d’in ke kwance, tayi hakan kuwa batare da ta iya rarrabe inda take jefa

k’afafun nata ba.

Jin sautin tafiyan nata ne kuma yasa duk hankalin su Abbou Jaheed ya dawo kanta, ganinta acikin mawuyacin hali yasa suka zuba mata ido, saidai kuma dukansu kaman an kulle musu baki. babu wanda ya iya koda k’iran sunanta ne, haka suka zu

ba mata idanu.

Laylerh kuwa tunkafun ta k’arasa kusa dashi taji wani irin jiri mai k’arfi na neman kada ita, saidai sam a irin yanayin da take jin kanta aciki batajin zata iya bawa wani abu daman katse mata hanzarinta nason zuwa garesa.

Isowarta jikin ga

don nasa da tayi kuwa yayi daidai da sauk’an wasu hawaye masu tsananin zafi akan fuskarta.

Ahankali kana kuma cikin rawan da hannayenta dama duk jikinta keyi, ta matso gab dashi, hannunta takai ahankali ta d’aura akan kyakkyawar fuskarsa da ko d’igon tabo

ko kwarzane babu akanta.

Batare kuwa da tasan me takeyi ba ta soma d’an yawo da hannun nata akan kyakkyawar fuskarsa harzuwa kan faffad’an chest d’insa dake abayyane, kasancewar doctors d’in sun cire masa rigar dake jikinsa, domin duk ta b’aci da jini, k

uma akwai y’an kananun raunuka da yaji, wanda dole sai sunyi treating d’in wajen, shiyasa ma gaba d’aya suka rabashi da rigarsa.

Isowar hannunta da har yanzu keta faman b’ari daidai kirjinsa inda zuciyarsa take ne yasa gaba d’aya ilahirin jikinta ya sake

d’aukan rawa, har yakai ga hak’waranta na kartan juna is....

Da k’yar cikin wata irin murya me d’auke da wani rikitaccen amo, sannan kuma mai fitar da shaking sound d’in dake d’auke da matsanancin raunin zuciya tak’ira sunansa, in a slowly tone.

“Y...A..

.H M...J...A...Y!!

‿

Yanda sauti da kuma amon muryar nata ya fita ne yasa su Abbou Jaheed kafesu da ido basa ko k’yaftawa.

“Y...A...H M...JAY......!!!

‿

Still Ta sake k’iran sunan nasa, saidai kuma awannan karon amon muryar nata yafi na farko fitarda rau

ni.

Again bud’e labb’an nata tayi,da niyar sake k’iran sunansa saidai kuma awannan karon harshenta bazae tab’a iya motsa kansa ba, domin kuwa takai wani stage da yin maganarta zai iya haifar mata da d’aukewar numfashi.

Ahankali ta sauk’e tattausan tafin

hannunta akan nasa hannun, batare kuma da tunanin komai ba ta d’ago hannun nasa tare da kawosa daidai saitin bakinta, labb’an bakinta ta d’aura akan lallausar fatar hannun nasa, cikin wani irin yanayi ta fashe da wani kuka me tsananin ban tausayi da kuma t

sayawa arai, duk da cewar kuwa har yanzu jikinta na b’ari, amma hakan bai hanata rik’e hannun nasa da k’arfi, ta shiga rera wani irin kuka me sauti da kuma tsuma zuciya ba, tabbas kukan da ya amsa kuka Laylerh’n keyi, ma’ana irin wanda ke fitowa daga ciki

n zuciyar mutum me d’auke da matsanancin rauni, haka zalika kuma kukane dake bayyana yanda wanda keyinsa yakeji acikin rai da zuciyarsa, sannan kuma kukane da zautattun mutanen da zuciyarsu ta narke acikin zazzafan soyayya keyi, Kuka take irin wanda bata t

ab’a yinsa ba aduniya, kukan da ya firgita zuciyar su Abbou Jaheed, kukan daya saka kowannensu acikin matsanancin shock, har ya kai ga sun tsaya kallonta tamkar gumaka babu wanda yake motsi acikinsu.

Laylerh kuwa kukanta take sosae wanda gaba d’aya sautin

sa ya cika d’akin, yayinda kuma har yanzu take rungume da hannun Maleek, wanda tayi masa wani irin rik’o, tun tana fitar da sheshshek’a kuwa acikin kukan nata har ya zamana ta fara shid’ewa, yayinda numfashinta ya shiga ja baya yana me k’ok’arin d’aukewa.

Ganin hakane kuma yasa Oum Ayush da tuni hawayen tausayin Laylerh Da Maleek d’in sun zubo kan k’uncinta, cikin rawan murya ta k’ira sunan Laylerh’n, da ko kad’an bataji k’iran Oum Ayush d’in ba.

“LAYLERH.

‿

Oum Ayush ta sake k’iran sunanta akaro na biyu

, tare da soma k’ok’arin danne kukan da ya zo mata.

Still Laylerh bata amsa taba, bata kuma tsaya da kukan nata dake nuna musu zaucewarta ba, haka kuma har yanzu tana rik’e da hannun Maleek d’in bata sake ba.

Saurin juyawa Abbou Jaheed yayi da k’arfi y

a rumtse idanunsa wanda suke cike tab da k’walla, k’wallar kuma dake d’auke da abubuwa da yawa, wani irin karaya da rauni zuciyarsa tayi, wanda hakan yasa dole yasa hannu ya dafe zuciyartasa, saidai kuma duk yanda yaso hana hawayen dake cikin idanun nasa f

itowa, abun yaci tura, dole haka yanaji yana gani wasu hawaye suka ziraro masa.

Awajen Abbou Khareem ma kuwa hakan take domin shima tuni idanunsa sun cika da k’wallan tausayin y’ay’annasu.

Fou’ad kam dama shi mai raunine sosae akan abokinnasa, sanin kum

a abundake cikin zuciyar Laylerh da Maleek d’inne da kuma yanda Laylerh’n ke kukane yasashi sanya hannu ya kama kansa, domin kwata kwata bashi da ikon hana idanunsa kuka ayau, watarana abanza ma haka yake kuka, bare yau da abun kukan ya samu, shi Soja ne a

mma yasan yana da raunin zuciya sosai.

Najeeb.

Tayaya zai iya d’auke idanunsa daga kallon Laylerh’n, hak’ik’a duk da cewar kukan da Laylerh’n keyi yana matuk’ar tab’a masa zuciya, amma hakanan ya samu kansa da kasa janye idanunsa daga gareta, duk da ku

wa cewar idanun nasa sun kad’a sunyi jajur tamkar wanda aka watsawa borkono, k’warai a yanzun shi kad’ai yasan meyakeji acikin zuciyarsa, wanda ayanzu bazai tab’a iya fassarawa kansa ma’anan hakan ba.

Ahankali cikin son tausasa harshe da kuma bawa Layler

h’n baki, Oum Ayush ta k’arasa zuwa gareta, hannunta tasa ta dafa kafad’an Laylerh’n, cikin muryarta da ke cike da tsananin tausayin su asanyaye ta k’ira sunan Laylerh’n, wanda har yanzu bata daina kukan da takeyi ba.

“Laylerh!!

‿

Oum Ayush ta sake kiran

sunanta akaro na uku, hade dasa hannunta ta jawo Laylerh’n jikinta.

Jin da tayi kuma Oum Ayush din ta rik’e ta ne yasa Cikin sheshshek’an kuka ta d’aura kanta akan kafad’an Oum Ayush d’in, k’ok’arin fad’in wani abu takeson yi amma ta kasa, saboda tuni kuk

a ya riga da yaci k’arfinta.

Ahankali Oum Ayush ta soma kokarin zare hannun Maleek d’in daga rik’on da Laylerh’n tayi masa.

Cikin sa’a kuwa ta samu Laylerh’n ta saki hannun Maleek d’in.

“Muje ki huta kinji, ya isa haka ki daina wannan kukan, ai Maleek

d’in ba mutuwa yayi ba, yana da rai kuma zai bud’e idanunsa Insha Allah.

‿

Oum Ayush ta fad’i hakan cikin tausasa murya tare dajan Laylerh’n anutse ta zaunar da ita akan wani kujera dake d’an gefe da gadon da Maleek d’in ke kwance kana itama ta zauna a ge

fen Laylerh’n, hakanne kuwa yasa ahankali Laylerh dake ta faman sakin sheshshek’an kukanta da har yanzu ya kasa tsayawa ta d’aura kanta akan cinyar Oum Ayush d’in. Saidai kuma karfin kukan nata ya d’an ragu ba kaman d’azu ba da gaba d’aya sautinsa ya cika

d’akin.

Haka gaba d’aya d’akin ya d’auki shiru, ba abunda ke tashi acikinsa sai fitan numfashi da kuma amon gunjin kukanta.

Hakika gaba d’ayansu duk acikin wani irin yanayi suke musamman ma Abbou Jaheed da zuciyarsa ta riga da tafi na kowa rauni awajen,

bakuma iya rauni kawai ba, wani abune na daban ayanzun ke damun zuciyarsa akan Laylerh da Maleek d’in.

Ahankali Dr.Mouhammad ya turo kofar dakin ya shigo, bakinsa dauke da sallama, wanda hakanne kuma yasa duk hankalinsu ya koma kansa.

Ganin irin kallon d

a sukeyi masa ne kuma yasa shi d’an fad’ad’a murmushi akan fuskarsa sab’anin da da yanayin fuskartasa ke d’auke da damuwa.

“Ya naga duk kuna kallona kodai ya Far fad’one?

‿

Dr.Mouhammad d’in ya fad’i haka cikin raha da kuma d’an sakin fuska.

Kusan kowann

ensu ajiyar zuciya ya sauk’e, asanyaye Abbou Khareem yace.

“Aa har yanzu dai bai farfad’o ba, fatan mu dai shine Allah Yasa ya farfad’o d’in.

‿

“Karka damu Insha Allah Zai farfad’o, wannan matarsa ce?.

‿

again Dr. Mouhammad ya tambaya adaidai lokacin da ya

d’aura idanunsa akan kyakkyawar matashiyar budurwar dake sakin kananan sheshshek’a wato Laylerh kenan.

Tabbas tambayar tasa tazo musu awani irin siga, hakan yasa suka d’anyi shiru, saida aka d’an d’au sakanni kafun Abbou Jaheed ya numfasa, asanyaye yace.

“Aa k’anwarsa ce.

‿

Wata irin gagarumar ajiyar zuciya Dr.Mouhammad ya sauk’e tare da sake kallon Laylerh’n da kyau, sosai kuma amsan da Abbou Jaheed d’in ya basa ya sashi samun gamsuwa, tare dajin wani sanyi aransa, domin kuwa da ace kyakkyawar yarinyar d

a yake gani d’in ta kasance matar Maleek d’inne dakuwa akwai matsala sosae, domin asonsa zaifi son jin cewa Maleek d’inma bashi da mata, domin kuwa sabuwar matsalan daya fuskanta ta sanadiyar accident d’in da yayi bak’aramin ci baya zata kawo garesu ba.

A

hankali ya kawar da kansa daga kallon Laylerh’n, tare da k’arasawa gaban gadon da Maleek d’in ke kwance, ruwan allura da kuma sirinjin alluran dake hannunsa ya had’a, anutse ya so kawa Maleek d’in alluran akan damtsen hannunsa, wanda jijiyoyinsa suka fito

sukayi rad’au akai.

Bayan ya gama yi masa alluran ne kuma ya juyo ya kalli Abbou Jaheed.

Kasancewar kuma yasan cewa Abbou Jaheed d’in babban mutum ne da sunansa ya zagaye wajeje da dama, saboda kud’i da kuma halin k’irkinsa hakan yasa cikin basa girma ya

ce.

“Alhaji Jaheed Gwani idan babu damuwa ko zaka iya biyoni office d’ina?

‿

Jin abunda Dr.Mouhammad d’in ya fad’a ne kuma yasa Abbou Jaheed jinjina kae ahankali yace.

“Ba damuwa Doctor muje.

‿

Kai Dr.Mouhammad ya jinjina kafun ya wuce gaba, Abbou Jaheed

kuwa ya bisa abaya, domin Jin cikakkiyar rahoto akan d’ansa Maleek.

*(Afuwan bansamu daman turowa da wuri ba wallahi two days ba anutse nake ba shiyasa, duk typing d’in rabi da rabi atsaye nake kareshi, amma Insha Allah Zanyi k’ok’ari na gobe yafi nay

au yawa.)*

*Friday12/2/2021*

*11:33 am*

2/13/21, 9:39 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Not Editing*

*Chapter 51*

Fitan su Abbou Jaheed da kuma Dr. Mouhammad daga cikin d’akinne yasa Najeeb da gaba d’aya

yaji duk tsayuwar da yake ta isheshi ya juya tare da kama hanya ya fice daga cikin d’akin, Laylerh kuwa da zuwa yanzu kukan nata ya tsagaita sosai, sake kwantar da kanta akan cinyar Oum Ayush tayi tare da lumshe idanunta, saboda kukan da tayi d’inne kuma

yasa lokaci d’aya cikin abunda bai wuce 15 minutes ba bacci me nauyin gaske ya d’auketa, duk da cewar kuma bacci take, amma hakan bai hanata sakin wani gunjin kuka acikin baccin nata ba, yayinda daga gefe guda kuwa ajiyar zuciya kawai take ta sauk’ewa akai

akai.

B’angaren Abbou Jaheed kuwa direct office d’in Dr.Mouhammad suka nufa, suna shiga cikin office d’in kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login