Showing 243001 words to 244674 words out of 244674 words

Chapter 82 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

inda suka tarar da wani k’aton cafe, yana rik’e da hannunta suka shiga cikin cafe d’in, bayan sun zauna ne kuma yayi musu order’n coffee da abinci irin wanda yasan Laylerh’n zata iyaci.

Atak’aice dai kusan acikin cafe din suka k’arasa darensu.

Bayan sun kammala duk abunda zasuyine kuma ya kama hannunta suka dawo gida, saboda ya fahimci yanda Layerh’n kejin bacci sosai ne kuma yasa shi kwantar da ita batare daya buk’aci komai daga gar

eta ba kuma ahaka sukayi bacci.

Washegari kuwa tunda sukayi breakfast ya sake saka Laylerh’n ta shirya, the same irin shigan da tayi jiyan kuma tayi yau.

Still yau dinma hannunsu na cikin na juna suka sauk’o k’asan, saboda yanayin hasken fatarsu ne k

uma yasa gaba d’aya suka saje acikin turawan.

Direct parking space ya nufa, inda ya ciro mota k’irar Mercedes wanda musamman abokanan aikinsa suka tanadar masa.

Cikin motar suka shiga shida Laylerh’n kaitsaye OXPORD University suka nufa, wanda acann

e

Kuma ya samawa Laylerh’n gurbin ci gaba da karatu.

Bayan sun shiga cikin school d’inne kuma yayi duk wani abunda ya dace, bai kuma bar cikin school dinba harsai da ya tabbatar da cewa Laylerh’n ta shiga aji ta zauna.

Yau kuma kimanin sati guda ke

nan da zuwansu London din, a kuma cikin satin koda yaushe Laylerh sai taje university dinsu, Yayinda shi kuma Maleek din keyin aikinsa acikin camb dinsu dake nan London din.

Ba laifi kuma tana gane salon karatun nata sosai.

Yanzun ma zaune take ak

an wani Roma sofa, Yayinda ta nannad’e k’afafunta tare da maida hankalinta ga book d’in dake hannunta.

Ahankali Maleek d’in daya share sama da 15mn atsaye yana kallonta ya sauk’e wata irin sassanyar ajiyar zuciya, tare da d’an lumshe idanunsa da suka

cika da ruwan hawaye, kana kuma suke bayyana tsananin raunin da ke kwance acikin zuciyarsa.

Takowa ya Shigayi ahankali tare da k’arasowa inda Laylerh’n ke zaune.

Zama yayi ak’asa tare da mik’e k’afafunsa, ahankali kuma cikin muryarsa da tayi sanyi s

osai ya k’ira sunan Ayshnoor d’innasa.

Laylerhn dake zaune kuwa jin amo da kuma sautin fitar muryarsa ne, ya sata d’ago kai ahankali ta kalleshi tare da sakar masa wani irin sassanyar murmushi.

Shid’inma

Murmushi yayi mata, tare kuma da k’ura mata

idanunsa, wani irin abu yakeji na musamman akanta, Yayinda abayan kowani minute tausayinta ke dukan zuciyarsa, abunda yake tambayar kansa kuma akullum shine.

“Haka zasu k’are gaba d’aya dayuwarsu?.

‿

Laylerh kuwa ganin wani irin kallon da yakeyi mata

ne, yasa duk taji jikinta yayi sanyi, take kuma itama taji hawaye sun cika Idanunta, saboda abune dake yawo ajikinta akullum, matuk’ar Boo d’in nata yana cikin damuwa, lallai takanji yanayin ajikinta.

Littafin dake hannunta ta ajiye tare da sauk’owa k

’asa ta zauna akan k’afafunsa.

Tafukan hannayenta tasa tad’an tallafo, hab’arsa tare da d’an shagwab’e masa fuskarsa.

“Boo!!

‿

Tak’ira sunansa asanyaye, tare kuma da sake matsowa kusa dashi.

Shikuwa asanyaye ya janye idanunsa daga kanta, tare da

sa hannunsa acikin aljihun wandonsa ya ciro wani dan madaidaicin box.

Murfin box din ya bud’e tare da ciro waya yar gold chain dake cikin box d’in wanda agabanta, aka rubuta *L&M* da manyan bak’i, Yayinda kuma aka k’awata kan haruffan da wasu had’add’un

sky blue din stones.

Gold chain d’in ya mak’ala mata awuyanta, tare dasa hannunsa ahankali ya shafa gefen fuskarta cikin kuma muryar dake bayyana raunaninsa sosai yace.

“Akullum inajin wani iri a zuciyata Ayshnoor , duk da nasan cewar kowani abu da

ya sameka arayuwa daga Ubangiji ne, amma nakanji ajikina k’addarata tayi tsauri, bansan Meyasa nake yawan jin faduwar gaba akan hakan ba, akowacce rana Rayuwarki nake dubawa Ayshnoor, har acikin zuciyata banason ace saboda son jurewa k’addarata Kin rasa

madafa, nasani Ayshnoor nasani kowa aduniya yanason ganin jininsa, tambayar da nakeyiwa kaina akullum, shin ahaka zamu k’are rayuwarmu Ayshnoor? Banason nayi butulci ga Allah Amma kuma inajin rauni sosai azuciyata, taba heart d’ina kiji Ayshnoor kullum

yana beating da fargaba inajin wani abu na daban, Domin hakan tamkar cutar da rayuwarki ne.....

‿

Ya k’are maganar tasa yana me d’aura hannunta adaidai saitin heart d’insa, Yayinda kuma hawayen dake cikin idanunsa suka bayyana kansu.

Wasu irin hawaye

masu zafi ne suka gangaro daga cikin idanunta zuwa kan kyakkyawar fuskarta.

Araunace take kallon Yah M.Jay d’innata, wanda sonsa yake dad’a k’aruwa acikin zuciyarsa akowani second.

“Babu wata mummunan k’addara da zata tabbata arayuwa Yah M.Jay, ak

ullum akuma koda yaushe banajin komai, saboda ni kaine GARKUWA ta, Tabbas babu wata damuwa da zata dameni matuk’ar akullum kana tare dani, kaine duk wani k’arfin guiwata, da soyayyarka kad’ai zan iya rayuwa mai dad’i, akullum akuma koda yaushe kaid’in ka

wai nakeso Yah Maleek, saboda haka ina da k’arfin guiwar da zan iya jurewa kowacce irin k’addararka, bazan tab’a damuwa akan hakan ba, Domin kowani bawa da irin k’addarar da Allah ke tsara masa, baizama lallai ace dan ya hanaka shine baya sonka ba..

‿

H

annunsa ta kama ta rik’e acikin nata hannun, cikin kuma muryar kukan dake son k’wace mata tace.

“Akwai millions din mutane acikin wannan duniyar da suke d’auke da k’addara irin taka, akwai kuma millions din da girman k’addarar su ta wuce taka, har akul

lum abunda Allah ya zab’a mana shine mafi kyau da alkhairi agaremu, saboda haka zan zauna dakai aduk yanda kake, zan rayu dakai rayuwa tahar abada, kaine akomai na, jininka ne yake gudana acikin jikina, har abada bazan tab’a barinka ba, Domin matuk’ar bab

u kai rayuwata bazata tab’a cika ba, alk’awari ne da bazai tab’a warwarewa ba, saboda haka sunan LaylerhMaleek ma bazai tab’a sanjawa ba, Domin akowanni bugun zuciyata Yah M.Jay ne, shid’inne ako yaushe, yanzu dama k’arshen rayuwata, zan kuma rayu da Yah

M.jay na, batare da tunanin samun haihuwa ba, zan rayu dashi dakowani irin tabon k’addara, Domin ka

una ta gaskiya babu ruwanta, da munin k’addara ko tabon da mutum yake d’auke dashi, zama dakai akowani irin yanayi shine fata da kuma burin rayuwata!!!

‿

T

akai k’arshen maganan nata adaidai lokacin da wasu hawaye masu zafi suka zubo daga cikin idanunsa.

Hannayensa dake rawa yasa ya tallafo hab’arta tare da had’e foreheads dinsu waje d’aya.

Tabbas Sosai kalaman Laylerh’n suka daki zuciyarsa, tare dasa s

hi jin kansa tamkar wani yaro k’aramin dake zaune agaban mahaifiyarsa.

Lallai Tabbas Laylerh’n itace ta zame masa kowa, har abada kuma yayi imani babu wata mace da zata zo bayan ita.

Labb’an Bakinsa dake d’an rawa ya bud’e ahankali, cikin wata sabuw

ar amon muryarsa dake shaking yace.

“I can’t live without you Ayshnoor! Har abada rayuwata bazata tab’a cika ba idan babu ke, Tabbas zan rayu dake rayuwa ta har abada, Domin samunki yafiyemin komai, k’warai na yarda cewa ba kowani buri ne yake zama kamm

alalle ba, ba kuma komai da kakeso kake samu ba arayuwa, lallai tilas saika rasa wani abun kafun wani abun yake zuwa, abu mafi muhimmanci kuma shine samun k’arfin guiwa, da kuma nutsuwar zuciya.

‿

D’an tsagaitawa da maganganun nasa yayi, saboda yanda mu

ryarsa ke rawa.

Ahankali cikin kuma yanayin dake bayyana amincewa da k’addararsa d’ari bisa d’ari yace.

*”INASONKi Ayshnoor har abada kuma zamu rayu tare!!

‿

*

Idanunta tad’an lumshe tare da sake matse hannunta dake cikin nasa, murya araunace tace

.

*”INASONKA Yah Maleek kuma har abada zamu rayu tare, zamu kasance da juna acikin kowacce irin k’addara mai kyau ko akasinta

‿

*

Tana gama fad’in hakan kuma ta d’aura bakinta akan nasa, tare da shigewa cikin jikinsa tayi hugging nasa sosai.

Lallai

Tabbas zata kasance da Maleek, kasantuwa kuma ta dindindin.

Akullum akuma koda yaushe fata da burinsu d’aya ne, tamkar dai yanda zuciyoyinsu suke d’aya, har abada zasu ci gaba da kasancewa ahaka babu kuma wata k’addara da zasu bari damuwarta tayi tasiri

acikin zuciyoyinsu.

Tabbas *LAYLERH MALEEK* muradi da kuma fata ne adunk’ule awaje d’aya.

Sunkuma amincewa k’addararsu, had’ari bisa d’ari saboda abu mai mahimmaci shine samun junansu, Allah Kuma ya cika musu burinsu, saboda haka daga yanzu har ab

ada bazasu tab’a k’alubalantan Ubangiji akan k’addarorin daya sauk’ar musu ba.

*Alhamdulillah!!! Rayuwa babu yanda bata zuwarwa bawa, abunda kayi tunani ya juye ya koma izuwa wanda baka tab’a tunani ba, Tabbas samun abunda kakeso babbar nasarace, amma

kuma ba komai da kanema ne kake samu ba, akullum kuma k’addara takanzo ne a yanda Allah ya tsarawa bawa, babu kuma wanda ya isa sanjata, Lallai akoda yaushe abunda Allah ya tsara shiyake faruwa. Bai kuma zama lallai komai na rayuwarka ya zamanto hundred

percent ba, Kamar dai rayuwar LAYLERH da MALEEK sun mallaki juna, duk da cewar akwai tawaya acikin rayuwarsu, amma hakan bawai shi yake nuna rashin kasancewar farincikinsu ba, ko babu zuri’a zasu rayu tare saboda ahaka tsarin k’addararsu tazo musu.*

*(

Insha Allah anan nakawo karshen littafin LAYLERH MALEEK Ina rok’on Allah Kuma daya bani ladan fad’akarwar dake ciki, ya kuma yafemin kurakuren dana aikata aciki, sannan masoya littafin Laylerh Maleek nagode kwarai da nuna kauna da kuma kulawarku agareni, T

abbas nasan kunyimin uzuri sosai, Allah ya saka da alkhairi, ina sake Mika godiyata agareku sosai, tare da addu’a da kuma fatan Allah yasa Muga Ramadan lafiya mukuma k’areta lafiya Allah Ubangiji ya yafe mana duk kurakurenmu ya kuma karb’i Ibadun mu, nasa

n wasu zasuyi tunanin ko katse labarin nayi, no ba katse labarin nayi ba, haka labarin yake ahaka yazo, unexpected ending gareshi, then duk wanda na b’atawa Dan Allah ya yafemin nima na yafewa kowa, ciki kuwa harda way’anda koda yaushe suke fitarmin da lit

tafina waje, Inasonku dukanku Allah Ubangiji yabar k’auna, Insha Allah sai mun had’u a next book d’ina Ina ma kowa fatan alkhairi ayi ibada lafiya)*

*12/4/2021*

*9:14*

*fatymasardauna*

*Alhamdulillah #Ending*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login