Showing 195001 words to 198000 words out of 244674 words

Chapter 66 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

gaba.

Kasancewar kuma yau itace ranan k’arshe, shiyasa d’aliban suka b’ata lokaci mai tsawo b

asu fito a exam d’in ba, domin ba kad’an ba paper’n da ta kasance na Maths ta basu wahala.

Wanda hakan yasa sai k’arfe 11am suka fito.

Gaba d’aya compound d’in school d’innasu cike yake da d’alibai maza da mata, Yayinda kuma fiye da rabin students d’

in suka b’ata uniform d’insu da zanen maka different colours.

Tabbas awannan lokacin zuciyar gaba d’aya d’aliban cike take da farinciki.

Saidai kuma ita acikin nata zuciyar banbanci ne da nasu, dake d’auke da wani irin yanayi.

Yanayin da akowacce

rana yake gudana acikin jikinta kamar jini.

Tabbas ba zata iya fad’in sunan yanayin nata kaitsaye ba, domin akullum salo da zafinsa sanjawa yake, saboda yana hurting d’in zuciya da gangar jikinta sosae.

Duk da kuwa cewar yanayin ada bai zamo bak’o agar

eta ba, amma ayanzu tanajinsa wani daban.

Domin kuwa koda Idanunta ta lumshe saitaga nasa idanun acikin nata.

Tabbas kuma hakan shi ne ke k’ara haddasa mata matsanancin kewarsa.

Koda sau d’ayane kuwa tanason sake sanyashi acikin idanunta, Kamar dai

yanda sau d’aya tak kawai ya bar mata wani azababben yanayin da har abada bazata tab’a iya mantawa dashi ba.

Yanayin daya zamo sanyi kuma Garkuwa agareta, kana kuma yanayin da tunda take aduniya bata tab’a sanin akwaesa ba.

Wani irin tashi tsikar ji

kinta ya shiga yi, haka ma y’an hairs d’in dake jikinta suka mimmik’e, lokaci d’aya sweet moment d’in ya shiga yawo acikin Brain d’inta, wanda hakan ya haifar mata da wani irin bugun zuciya.

Hakanan taji tamkar yazune abun ke faruwa.

Hannayenta duka

biyu tasa ta k’ank’ame jikinta, tare kuma da lumshe idanunta, wanda suke dake dawo mata da ganin lokacin daya sauk’e lips d’insa akan nata, acikin yanayin sanyi kuma ya tura sweet tongue d’insa acikin bakinta.

Wayyo Allah Tayaya ma zata iya mantawa da

wannan best moment d’in?

Lallai jure hakan abune mai wahala, domin tayi imani a zuciyarta cewa idan irin hakan ya sake faruwa, babu ko tantama zata iya rasa numfashinta, domin abune mai matuk’ar girma da daraja samun professional kiss daga wajen wanda zu

ciya da gaba d’aya gangar jiki keso.

Tabbas wani lokaci magana bata aika sak’o zuwa ga inda zuciya keso, domin wani lokaci magana a iya kunne kawae take tsaya wa, bata kaiwa izuwa gangar jiki, madadin hakan kuwa abu biyune kawae ke tasiri wa gangar jik

i da kuma k’wak’walwa, wannan abu biyun kuma sune KISS and HUGGING.

Amatuk’ar kasalance ta bud’e idanunta dake lumshe, tare da zubawa wayarta dake ringing idanu.

Ganin kuma numbern da ake k’iranta dashi d’in ba na Nigeria bane yasa ta d’an tsurawa w

ayar idanu.

Saidai kuma ganin k’iran na shirin katsawa ne

Yasa tayi saurin d’aukan wayar tare da kara ta akan kunnenta.

Hakan kuwa yayi daidai da samun kanta da tayi cikin wani irin bugun zuciya, take kuma taji wani irin sanyi mai tsananin dad’i

na ratsa duk ilahirin jikinta, irin dai sanyin da awajen mutum d’aya kawae take samunshi, Tabbas wannan yanayin shi ya sauk’ar mata da kasala, wanda har hakan yasa ta kasa cewa komae.

Daga can b’angaren kuwa sauk’an numfashinta acikin kunnuwansa ne , y

asa shi lumshe idanunsa wanda sukayi jajur, tare dasa hannunsa ahankali ya dafe saman mararsa.

Cikin wani irin sabon yanayin daya samu kansa aciki kuwa ya d’an saki wani silent growing tare da bud’e gaba d’aya labb’an bakinsa.

*18/March/2021*

*6:32 pm*

3/19/21, 9:08 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Chapter 69*

Hak’ik’a shiru da kuma dad’in yanayin da ta samu kanta aciki ya masifar shagaltar da ita, wanda har hakan ya sata maida idanunta ta lumshe, kana ahankali ta cigaba da sauk’e wa

ni irin breath, wanda ita kanta batasan tayaya akayi sautin numfashin nata ke tashi har haka ba, sassanyar iskar dake ci gaba da k’ara ratsa duk ilahirin jikinta ne, kuma yasa ahankali cikin yanayi mai kama da zallan shagwab’a ta bud’e y’an k’ananun jajay

en labb’anta.

Da muryarta wanda ke fitar da shaking sound tace.

“Assalamu Alaekum!!

‿

Adaidai lokacin kuwa, yaji wani irin abu me kama da shocking ya ratsa duk ilahirin jikinsa, wanda hakan yasa take kwantattun gargasan dake jikinsa suka soma mimmik’e

wa tsaye, haka ma tunaninsa ya tsaya cak, hakan ya faru ne kuma saboda sauk’an, da daddad’a da kuma kasallliyar muryarta a cikin kunnuwansa.

Ahankali ya fusgo numfashinsa dake k’ok’arin d’aukewa, tare kuma da saurin zare wayar daga kan kunnensa, batare

kuma daya amsa sallaman nata, ko yace wani abu ba ya k’urawa gaban screen d’in wayar tasa idanu.

Hak’ik’a yanzu shi kad’ai yasan meyake ji acikin jikinsa, domin jin muryarta da yayi ya goge masa duk wani lissafi da nutsuwarsa, musamman yanayin yanda m

aganan nata ke d’auke da wani irin salo na daban, salo mai cike da kasala, da kuma bayyana abunda ke cikin zuciyarta, domin kasancewarsa ma’abocinta, ad’an jin muryar ta da yayi yanzu, har zuciyarsa ta fassara masa yanayin da Laylerh’n nasa ke ciki.

Wa

ni irin abune yaji nayi masa yawo acikin zuciya da kuma gaba d’aya gangar jikinsa.

Duk kuma ga yanda yaso motsa harshe da kuma labb’an bakinsa abun yaci tura, atak’aice ma dai haka yakejin kamar an nannad’e masa tongue d’insa.

K’warae yanason bayyana ab

undake cikin zuciyarsa, ko da hakan zaisa ya d’anji sanyi.

Saidai kuma amma tayaya zai iya furta hakan?

Yau sama da 2weeks kenan da yakejin wani irin matsanancin kewarta na Adda ae zuciya da gangar jikinsa, duk da cewar tunda yazo USA d’in bai zauna ba,

amma kome yake yi tana nan acikin zuciyarsa, da tunaninta yake kwana, haka kuma da matsanancin kewarta yake wuni.

Sau dayawan lokuta yakan tambayi kansa shin yaushe ne zasu ji dad’in rayuwa shida ita? yaushe ne munanan k’addara zasu daina bibiyar rayu

warsu? sai yaushe ne zai sake samun wannan daman da ya samu abaya?

Daman kusantarta akullum akuma koda yaushe, hakika ada yana sake tsammatawa kansa rayuwa da ita, ko da sau d’aya yana buk’atar sake shagwab’ata kamar yanda yayi abaya lokacin tana k’arama

, yana buk’atar zama da ita, ta yadda jikinsa zai zame mata wajen bacci, sannan idan tayi kuka ya bata, finger d’insa ta tsotsa kamar yadda yakeyi mata abaya.

Tabbas yasani aduniya ita kad’ai ce macen da zata fuskanci al’amuransa, sannan ita kad’aice ma

cen da zai iya fuskanta da koma wacce irin damuwarsa, duk da cewar babu wanda yasan hakan amma shi ya sani, k’warae yasani cewar Laylerh ce kad’ae zata san damuwa da kuma abunda ke cikin zuciyarsa koda bai furta mata ba, ita ce kawae zata jurewa al’amurans

a, itace wacce har abada yasani baza ta tab’a gajiyawa dashi ba, domin yayi imani cewa zuciyarsa da nata abu d’aya ne.

Duk kuwa yanda yaso jurewa abunda yakeji ayanzu baya tab’a iyawa, domin acikin y’an kwanakin nan, zuciyarsa na yawan sak’a masa cewar

bazai rayu da Laylerh ba, ba dan komae ba kuwa saidan lalura da kuma k’addarar da ta sameshi, domin yanaji ajikinsa cewa zama da ita ahaka tamkar cutar da rayuwar ta ne, duk da yasan Laylerh’n babu wata irin k’addararsa da bazata iya jib’anta ba.

Saidai

kuma amma akwae cutarwa aciki, ita yarinya ce k’arama da babu abunda ta sani, zuciyarta da kuma tunanin ta basu san komae ba sai abu d’aya, wanda kuma kullum akansa ne kawae take rayuwa.

Idanunsa dake kan wayar tasa wanda suka sakeyin jajur, ya rumtse

da k’arfi, tare dasa hannunsa d’aya ya katse k’iran.

Sam ba zae iya jurewa abunda yakeji ba, saboda ayanzun zuciyarsa tayi rauni sosai, har yakai ga yanajin wani abu mai kaman ruwa na yawo acikin idanunsa.

K’warae bashi da bakin da zai iyayi mata magana

, saboda kowani magana d’aya da zaiyi mata, zai zama tamkar b’allewan bugun zuciyarsa ne.

Acan b’angaren Laylerh kuwa jin an katse k’iran da akayi mata d’inne, yasa ahankali ta zare wayar daga kan kunnenta, kamar wanda ke na zarin wani abu kuwa haka ta

k’urawa screen d’in wayarta ta idanu.

Saidai kuma sam ta kasa fahimtar komae.

Domin hatta tunaninta ma tsayawa yayi, saidai kuma still har yanzu bata dae na jin wannan sanyin na ratsa cikin jikinta ba.

“Laylerh mekikeyi anan tun da muka fito paper

nake ta nemanki, amma ban ganki ba.

‿

Muryar Teemah dake k’arasowa wajen ya katse mata duk wani yanayi da take ciki.

Ahankali ta d’ago kai ta kalli Teemah’n, Kamar kuma zata ce wani abu saita fasa, saboda hakanan taji duk jikinta yayi sanyi, Yayinda w

ani irin mood ke fusgarta.

Teemah kuwa idanu ta d’an k’urawa Laylerh’n domin ta fahimci kamar tana cikin damuwa.

Saidai kuma sanin da tayi cewar ako da yaushe, labarin da kuma damuwar Laylerh’n bata wuce ta Maleek shiyasa bata tambayeta agame da abun

da ke damunta ba.

Saima kamo hannun Laylerh’n da tayi ta mik’ar da ita tsaye.

Kallon Laylerh’n tayi sosae kafun tad’anyi k’asa da muryarta, cikin siga da kuma salon tsokana irin nata tace.

“Tun d’azu Aunty Zee tazo d’aukanki, gashi kuma yau dai

munyi final exam saboda haka sai munzo bikin L&M I mean LaylerhMaleek kenan.

‿



Teemah’n takai k’arshen maganan nata tana d’an kashewa Laylerh’n idanu.

Wanda hakan yasa Laylerh’n zuba mata idanunta dake bayyanar da abubuwa kala.

Teemah kuwa sam ba

ta damu da shirun da Laylerh’n ba, because hakan Bawae bak’on abu bane awajenta, itama bata sake cewa komae ba taja hannun Laylerh’n suka tafi.

Direct wajen da motar Aunty Zee ke fake suka nufa.

Koda suka k’arasa Aunty Zee d’in murmushi tayi, tare da

tambayan Laylerh’n ya jarrabawa.

Da “Alhamdulillah!

‿

kawae ta amsa daga haka ta bud’e murfin motar ta shiga, bayan sunyi sallama da Teemah akan cewar next week zata zo gidan Aunty Zee d’in.

Still yauma kuma saida Teemah’n taga fitansu acikin school

d’in kafun ta koma wajen sauran students din makarantar suka ci gaba da celebration.

Acan gidansu Laylerh’n kuwa

Abbou Jaheed da kuma Abbou Khareem ne ke zaune akan d’aya daga cikin had’addun royal chairs d’in dake cikin falon, idanu suka zubawa Oum

Ayush dake zaune.

Wanda da dukkan alama kallo d’aya zakayi mata kafahimci cewa akwae magana abakinta.

Duk da cewar hakanne kuma amma yanzu tsawon 10mn kenan da zamansu awajen takasa cewa komae.

Abbou Khareem wanda ya gaji da zamanne ya sake d’ag

o kae ya kalleta, cikin kuma yanayin k’osawa yace.

“Ayush kince akwae muhimmiyar maganan da zaki fad’a mana amma kuma naga kinyi shiru, kodai wani abu ya faru ne?, ki fad’i koma meyene duk ke muke saurare.

‿

Ahankali Oum Ayush ta d’an sunkuyar da kan

ta, Tabbas duk da cewa batasan a yanda zasu fahimci maganar nata ba, ya zama tilas ta fad’a musu, domin kuwa ita tasan tayi nakanne

Bawae da mummunan manufa ba, Idanunta ta d’an lumshe tare da tausasa murya, cikin kuma son bayyanar da gaskiyar abunda ke

cikin ranta tace

“Kuyi hak’uri domin akwae abunda na b’oye ban sanar muku ba, ban kuma yi hakan da wata manufa ba, saidan duba cancanta da kuma dacewar hakan, hakika duk da cewar bani ce na haifi Laylerh ba amma har acikin zuciyata, inajin soyayyarta ka

mar y’ar ciki na, kasancewar ta yarinya k’arama kuma yasa dole tana da buk’atar samun nutsuwa, musamman idan muka duba irin k’addarar daya sameta ayanzu, akwae buk’atar musa ma mata Hutu, da kuma yin abun da zai sanyaya zuciyarta, aciki kuwa harda nesan ta

ta da gidan nan, domin kuwa matuk’ar tana zaune cikin agidannan dole ne rayuwar da tayi da Najeeb zai dinga dawo mata, hakan kuwa zai iya shafar karatun ta.

‿



D’an tsagaitawa da maganan nata tayi, wanda hakan yasa Abbou Khareem cewa.

“Har yanzu dae

baki fad’i abunda kikeson fad’ad’in ba, sannan kuma mu sam bamu fahimce ki ba, ba mu kuma gane abunda kike nufi ba.

‿

Jin abunda Abbou Khareem d’in ya fad’ane, yasa ta sauk’e ajiyar zuciya, cikin kuma confidence d’in abunda ke cikin zuciyarta tace.

“

Abunda nake nufi shine kwata kwata Laylerh bata da Iddah akanta, saboda wata mu’amala ta aure bata tab’a shiga tsakaninta da Najeeb ba, ma’ana Najeeb bai tab’a kusantarta ba, saboda haka babu Iddah akanta, nasan hakanne kuma aranar da Najeeb d’in ya sake t

a, koda na tambayi Najeeb d’in kuwa shima ya tabbatar min da hakan, saboda haka

Laylerh bazatayi Iddah ba, na b’oye muku maganar ne kuma saboda, sai ta dalilin yin iddah’n ne kad’ae zata nesanta da gidannan, wanda hakan zae sa tayi karatun exam d’inta a

nutse, gashi kuma Alhamdulillah yau sun kammala exam d’in, dan haka ko ayau kuka buk’aci dawowanta gidannan zata dawo batare da wani miki ko ciwo acikin zuciyarta ba, sannan kuma

Ko agobe za’a iya d’aura mata wani sabon AURE.

‿

Wani irin nannauyan ajiya

r zuciya gaba d’aya su Abbou Jaheed d’in suka sauk’e, asakamakon jin maganganun da Oum Ayush d’in ta fad’a musu, Yayinda fuskonkinsu kuwa suka cika da tarin mamaki da kuma al’ajabin faruwar hakan, domin acikinsu babu wanda ya tab’a kawo tunanin cewar wai

Najeeb bai tab’a kusantar Laylerh ba.

*(Sorry page din yau ba yawa, just na samu time ne kawae nace bari na yi)*

*19/3/2021*

*7:43pm*

3/22/21, 7:59 AM - Ummi Tandama: *LAYLERHMALEEK*

*(Page d’in yau dai sai kun had’a da hakuri gaba daya i

na busy ban zauna na nutsu ba)*

*Chapter 70*

Gyara zama Abbou Jaheed yayi tare kuma da sake sauk’e wata sabuwar ajiyar zuciya, Tabbas maganganun da Oum Ayush d’in ta fad’a sun matuk’ar shiga jikinsu, kana kuma sun sauya tunaninsu.

Domin kuwa abune

da dukkansu basu tsammata ba.

Saidai kuma sam basuga laifin Oum Ayush akan b’oye musu gaskiyar al’amarin da tayi ba, saboda koba komai hakan da tayi d’in ya bawa Laylerh’n daman yin karatunta cikin nutsuwa.

Still ajiyar zuciya Abbou Jaheed d’in yayi,

cikin kuma nuna cewar ya fahimci abunda Oum Ayush d’in ta aikata yace.

“Tabbas nafahimceki Ayush, na kuma san bazaki tab’ayin wani abu da zai cutar da rayuwar Laylerh ba, na kuma ji dad’in hakan k’warae, domin kuwa koba komae Laylerh zata samu nutsuwa

acan gidan, saidai kuma aanzu duk wani abunda ya faru ya riga daya wuce, ko akwai Iddah akan Laylerh ko babu, yanzu babban abunda ya kamata mu fara fuskanta shine rayuwar da Laylerh’n zatayi anan gaba, duk da kuwa munsan cewa Allah Ne ke tsarawa bawansa

komai da komai na rayuwa, amma ya kamata ace muma munyiwa rayuwar da zata fuskanta ayanzu kyakkyawan tanadi, domin so nakeyi kulawar da zata samu ayanzu daga garemu ya zarce na ko yaushe, ko badan maraicinta ba, Kodan saboda k’addarar da ta fuskanta da ku

ma tsananin biyayyarta.

‿

D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, tare kuma da numfasawa.

Kana yaci gaba da cewa.

“Tun bayan mutuwar aurenta, na tsara cewar baza mu sake d’auko mata maganar aure da wuri ba, har sai bayan ta kammala karatun degree d’i

nta, domin result d’inta na fitowa zan turata karatu k’asar syprus, acan nakeso tayi degree d’inta, zuwa lokacin da zata kammala kuma nasan tasan duk wani abu daya shafi rayuwar duniya, da ma sanin ciwon kai, sab’anin yanzu da ba komai ne ta gama sani ba,

saidai kuma kafun na aikata hakan dole Ina buk’atar amincewar ku, domin kasancewarta agabana, Bawae yana nufin cewa ni kad’ai nake iko da ita ba, kuma d’iyarku ce kuna da iko da ita.

‿



Gaba d’aya falon shiru ya d’auka saboda jin abunda Abbou Jaheed d’

in ya fad’a, Lallai tabbas tanadin da yayiwa Laylerh’n me kyaune, dukkaninsu kuma zasu yi fatan ace hakan ya kasance.

Saidai kuma banda zuciyar Oum Ayush da take sak’a mata wani abu na daban, saboda sam gangar jikinta bai bata cewar abunda Abbou Jaheed

d’in keso zai yiwu ba.

Saidai kuma gudun kada wani abu ya sake faruwa da rayuwar Laylerh’n kamar yanda ya faru abayane yasa ta d’an gyara zamanta, tare da d’ago kai ta fuskanci Abbou Jaheed d’in, cikin yanayin kuma da tasan zai fahimceta tace.

“Tabb

as fatan da ka yiwa Laylerh maikyau ne, kuma dukan mu zamu so ace hakan ya kasance, saidai kuma akan komai daya shafi rayuwarta dole muna buk’atar jin ta bakinta, domin ba Lallai abunda muka zab’a mata ya zama shine zab’inta ba, watak’ila tana da wani hope

d’inta na daban, saidai kuma kasancewarta yarinya mai biyayya hakan yasa kome muka zo mata dashi bazata k’i amincewa ba, koda kuwa tana da nata ra’ayin.

‿

D’an tsagaitawa da maganan nata tayi, tare kuma da sake duban su Abbou Jaheed d’in.

Murya atausas

he kana kuma cike da tausayi tace.

“Dan Allah awannan karon mubar Laylerh ta zab’i abunda takeso, mubari muji zab’inta daga bakinta, domin zai iya kasancewa bayan karatu akwai wani abu da takeso, wanda kuma take mafarkin cimmasa, saboda haka mu b’ata za

b’i akan rayuwarta tanan gaba!!

‿

Yanayin yanda ta k’are maganar nata murya asanyaye ne yasa, duk su Abbou Jaheed suka sauk’e ajiyar zuciya.

Cikin yanayin gamsuwa da kalaman Oum Ayush d’in kuwa Abbou Jaheed, yace.

“Insha Allah zamuyi hakan, saidai

kuma ayau inason Laylerh’n ta dawo, domin dama Iddah ne ya kaita to yanzu kuma babu shi, sannan sun kammala jarrabawar tasu, saboda haka Oum Ayush kije ki d’aukota ta dawo, ban kuma yarda asauk’eta akowanni sashi ba sai naku.

‿

Kai Oum Ayush da Abbou Kha

reem suka jinjina cike da gamsuwa, Yayinda Oum Ayush kuwa taji wani irin sanyi na ratsa zuciyarta, domin kuwa duk da batasan wani abune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login