Showing 165001 words to 168000 words out of 244674 words

Chapter 56 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

da kuma cancantar cewa ya kamata yasani, gaba d’ayanku duka k’ok’arin zama y’an Uwa muke, saboda haka nayi imani cewa matsalar d’aya daga cikinmu na mune dukan mu.

‿

D’an jinki

rtawa da maganan nasa yayi sakamakon wasu irin hawaye da kuma raunin da yaji yazo masa, domin kuwa baisan tayayane zasu fuskanci maganar tasa ba, yaya zasu d’auketa Allah Kad’ai masani, babban abun ji da tambayan kuma shine Maleek da k’addaran ta zama akan

sa ne.

Ahankali ya d’ago kansa ya kalli Maleek d’in wanda kansa ke k’asa, tsananin tausayinsa ne ya rufesa wanda har hakan yasa ya Kasa controlling kansa, harsaida wasu guntun hawaye suka sauk’a akan fuskarsa.

Cikin sanyin muryar dake bayyana zal

lan damuwarsa ya k’ira sunan Maleek d’in.

Maleek dake zaune kuwa jin yanayin yanda Abbou Jaheed d’in ya k’ira sunansa ne yasashi gane cewar Lallai akwae matsala.

Ahankali ya d’ago kansa ya kalli Mahaifinnasa.

Kai Abbou Jaheed ya d’an girgiza saboda

girman abunda bakinsa ke kokarin fad’a, yasan cewa Lallai ba abu mai dad’ine zai fito daga bakinsa ba, amma to yaya zaiyi idan bai fad’i wannan matsalar a gaban kowa ba, meye amfanin b’oyewa? hakan zai zama kaman cutarwa ne.

Kansa ya d’an sunkuyar domin

babu yanda za’a yi ya fuskanci d’annasa ya fad’a masa magana marar dad’i kaman wannan.

Cikin dauriya da kuma son ganar da Maleek d’in yace.

“Hakika Maleek nasan amatsayinka na Musulmi kayarda da k’addara mai kyau ko akasin haka, sannan kuma nasan ka

yi imani cewa Allah Yakan iya jarraba bawa takowanne siga, lallai tabbas kai kuma kalan naka Jarrabawar ahaka tazo, saidai nayi imani cewa amincewa da kuma yarda da hakan ba k’aramin karamci zai jawo maka awajen Ubangijin kaba, kayarda cewa komae Allah Ne

Ya tsarashi!!

‿

Gaba d’aya falon shiru ya d’auka yayinda dukkaninsu suka zubawa Abbou Jaheed idanu.

Kowannensu buri yake yaji abunda Abboun Zai fad’a, amma banda Abbou Khareem dayasan komae akan zancen.

Kusan mintuna 5 aka share gaba d’aya ko ina ya

d’auki shiru, rumtse idanu Abbou Jaheed yayi kana asanyaye yace.

“Kayi hak’uri Maleek asanadiyar accident d’in da ka samu Dr. ya shaidamin cewa kasa mu matsala amararka wanda hakan yasa ba zaka tab’a haihuwa ba!!!

‿

*22/2/2021*

*10:30 am*

2/24/21, 8:11 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Not editing*

#Life and Destiny

*Chapter 57*

Amatuk’ar Razane gaba d’aya mutanen dake cikin babban katafaren parlor’n suka d’ago kai dukansu suka kalli Abbou Ja

heed.

Domin kuwa maganar da ta fito daga bakinsa ba k’aramin rugurguza musu k’wak’walwa tayi ba, har hakan yakai ga kowannensu ya shiga kokonton cewa kodae baiji abunda Abbou Jaheed d’in ya fad’a da kyau bane.

Abbou Khareem kuwa da yasan kwanan zancen ka

nsa kawae ya sunkuyar tare da soma ambaton sunan Allah acikin zuciyarsa.

Idanun Maleek wanda suka matuk’ar k’ank’ance lokaci d’aya kuma sukayi wani irin ja mai ban tsoro ya zubawa Abbou Jaheed d’in, yayinda kuma sannu ahankali kalaman da Abbou Jaheed d’

in ya fad’a suka shiga yawo acikin brain d’insa filla filla, tamkar dae wanda aka bud’e aka watsasu.

Take kuwa wani irin matsanancin zufa ya shiga ketowa ta kowani sashi na jikinsa, b’angaren zuciyarsa kuwa bugawa take da k’arfin gaske tamkar zata faso ki

rjinsa ta fito waje.

Lallai hak’ik’a akaro na biyu kunnuwansa sunjiye masa magana mafi muni da kuma girma, maganan da tasa shi zama tamkar wani statue, maganar da ta tsayar da duk wani tunani da kuma gudun jininsa.

Ba kuma iya shi d’in kawae ba hatta

Laylerh dake zaune ak’asa saida gaba d’aya ilahirin jikinta ya d’auki rawa, tare da shiga cikin wani k’aton tashin hankali, duk da kuwa tafara tunanin cewa kunnuwanta basu jiye mata komae adaidai ba.

Alhaji Farouk, Oum Ayush, Fou’ad harma da Najeeb wand

a ke zaune ad’an nesa da Laylerh kad’an.

Kalmar.

“Innalillahi wa inna Ilaihirraju’un!!

‿

Kawae suke furtawa, domin kuwa ba kad’anba maganan ta tada musu da hankali, wanda har hakan yasa suka kasa furta komae bayan salatin da sukeyi.

Abbou Jaheed kuwa a

karon farko kenan bayan yayi maganan ya d’ago kansa ya kalli Maleek daya tsura masa jajayen idanunsa baya ko k’yaftawa.

Wani irin rauni da kuma matsanancin tausayin d’annasa ne ya cika masa zuciya, wanda kuma har ya kaisa ga kasa jurewa.

Ahankali ya tash

i tsaye, cikin yanayin sanyi da kuma karyewar zuciyar daya samu kansa aciki ya k’araso inda d’ansa Maleek d’in ke zaune.

Inda su Abbou Khareem suka rakashi da ido.

Asanyaye ya zauna akan kujeran da Maleek d’in ke zaune, tare dasa hannunsa ahankali ya d

afa kafad’an Maleek wanda zaman Abbou Jaheed d’in akusa dashi yasashi rumtse idanunsa.

“Kayi hak’uri Maleek Tabbas kowani bawa da irin yanda Allah Yake jarabtansa, babu kuma wanda ya isa ya tsallakewa k’addararsa, tabbas ka had’u da k’addarori masu girm

an gaske tun daga k’uruciyarka har zuwa yanzu, damuwa sunyiwa rayuwarka k’awanya, yayinda kuma rashin samun fata da muradi ke sake bibiyarka akoda yaushe, amma hakan ba shine ke nuna cewar baka da farinciki kwata kwata arayuwarka ba, sannan kuma bashi yake

nuna cewa Allah Baya sonka ba.

‿

D’an numfasawa Abbou Jaheed d’in yayi tare da zaro wani farin handkerchief daga cikin aljihunsa ya share d’an guntun k’wallan daya cika idanunsa.

Still asanyaye Abbou Jaheed d’in yace.

“Tabbas nasan kasan cewa Allah Bay

a tab’a d’aurawa bawansa abunda bazai iyaba, Ina kuma fata da ka karb’i wannan jararrabawar Insha Allah watarana zakayi nasara, watarana lallai zakayi dariya Maleek, komai yakan faru sannan kuma yakan wuce har abada kaman bai tab’a faruwa ba, bakowa ke sam

un abunda yake soba, sannan kuma bakomai Allah ke baka dan kana tsananin soba, wani lokaci musanya maka yake, ya toshe wani ya kuma baka wani, hak’ik’a nasan zakaji k’unci da kuma ciwo acikin zuciyarka, amma hak’uri da fawwalawa Allah komae shi yafi, rashi

n haihuwa abune me tsananin ciwo da kuma k’unci, amma hakan Bawae yana nufin takura kai da yawan damuwa bane, Dan Allah Maleek kada kabar hakan ya zamo silar k’unci da kuma bak’inciki arayuwarka, ko ba aje ko inaba kayi du

bi ga Abboun ka Khareem da kuma ma

tarsa Oum Ayush, wanda tunda suke arayuwarsu basu tab’a haihuwa ba, sama da shekara 20 kenan yanzu amma kuma ahaka suke rayuwarsu, duk da cewar kuma sunajin ciwon abun acikin ransu amma hakan baisa sun tauye hakk’in farincikinsu ba, babu d’aya daga cikinsu

daya daina murmushi ko dariya asanadiyar hakan, saboda sunyi imani cewa Allah Shike bayarwa shi kuma ke hanawa aduk lokacin da yaso, saboda haka kaima ka d’auki k’addararka kasa sanyi da salama acikin zuciyarka watarana Insha Allahu zakaga nasara da riban

hakan.

‿

Again sake tsagaitawa da maganan nasa yayi tare da d’an numfasawa ahankali ya d’ago kai ya kalli Alhaji Farouk da duk wani tashin hankali da kuma tausayin Maleek d’in ya bayyana k’arara akan fuskarsa.

Idanu Abbou Jaheed d’in ya d’an lumshe kan

a asanyaye yace.

“Kayi hak’uri dajin kalamaina adaidai wannan lokacin Alhaji Farouk, domin dama na gayyatokane dan kasan halin da ake ciki, domin koba komae kai ubane agaresa, sannan kuma matsayin suruki kake dashi agaresa, kaine mutumin da yake shirin ba

sa auren kafun wannan mummunan k’addaran ta shigo rayuwarsa, K’warai nasan jin wannan maganan zaisa kaji babu dad’i acikin zuciyarka, sannan zai kuma iya sawa kasanja ra’ayi akan tunaninka na baya, duk da cewar kuwa lokaci ya k’arato sosai, amma kuma babu

yanda muka iya, a irin wannan al’amarin ba ayin dole ba kuma acutarwa, saboda haka kana da y’ancin da zaka yanke ko wani irin hukuncine, zakuma ka iyayin shawara da iyalanka da kuma ita kanta yarinyar, domin abune me matuk’ar ciwo atauye mata hakk’inta mai

girma irin wannan

...

‿

Yanayin yanda Abbou Jaheed d’in ya k’are maganar cikin sanyin muryane yasa Alhaji Farouk yin shiru tare da sunkuyar da kansa k’asa, gumine kawae ke tsatstsafo masa saboda gaba d’aya ya samu kansa cikin tashin hankali.

Wasu irin

hawaye masu matuk’ar zafi da kuma k’unane suka sauk’o daga cikin idanunta zuwa kan k’uncinta, saboda tsananin yawansu ne kuma yasa har suka soma sauk’a akan k’irjinta.

Wani irin matsanancin juyawa taji kanta nayi, yayinda gaba d’aya duk wani tunaninta ya

tsaya cak.

Abu d’aya kawae brain d’inta ke nanata mata cewar.

“Yah M.Jay d’inta bazai tab’a haihuwa ba, k’wayoyin haihuwarsa sun samu matsala.

‿

Wannan tunanin kuwa shi yake k’ara mata jin jiri da kuma juyawar da kanta keyi.

Da k’yar ta iya motsa y’an k

’ananan labb’anta, cikin kuma wani irin fusgan numfashi ta soma ambaton sunan Allah acikin zuciyarta.

Domin ta shiga tashin hankali maitsanani.

Tambayar kanta take. “Shin wannan wacce irin k’addarace? wace irin jarrabawace haka mai tsananin zafi? tayaya

Maleek zai iya jure duka way’annan k’uncin rayuwar? meyasa k’addara ke wasa da rayuwarsu? sai yaushene zasu samu nutsuwa da kuma farinciki arayuwarsu? yaushe k’addara zata barsu suyi dariya ita da d’an uwannata har hak’waransu su bayyana kowa ya gani?.

‿

“Lallai tabbas Laylerh babu wannan ranan, domin kuwa munanan k’addara sun riga sunyiwa rayuwarku k’awanya!

‿

Wani sashi na zuciyarta ya fad’a mata hakan.

Kanta ta d’an soma girgizawa ahankali, domin kuwa bazata iya jure abunda takeji acikin zuciyarta ba,

Tabbas so take tayi kuka sosai, kuka irin wanda zai rage mata koda kaso d’aya daga cikin d’ari na k’uncin dake damun rayuwarta ne.

Ahankali ta had’e k’afafunta tare da cusa kanta atsakankanin cinyoyinta, batare da ta iya controling kanta da rauninta ba ku

wa ta fashe da wani irin kuka mai tsananin tab’a zuciyar mai saurare.

Oum Ayush dake zaune akusa da Laylerh’n itama hawayene suka silalo daga cikin idanunta, natsananin tausayin Maleek da kuma su kansu ita da mijinta, domin kuwa tasan zafi da ciwon dake

cikin rashin haihuwa, abune da iya juresa keda matuk’ar wahala, musamman ga Namiji matashi mai jini ajiki kamar Maleek, wanda ayanzune ya kamata ace rayuwarsa na tsaka dayi masa dad’i, amma kuma sab’anin hakan sai ya zama k’unci da damuwa ne akewaye dashi

.

B’angaren Fou’ad kuwa tuni hawaye sun fito daga cikin idanunsa, dama shi akoda yaushe me raunine, Jin matsalar da abokinnasa ya samu ne kuma ya k’ara jaddada rauninsa, tausayin Maleek d’inne kuma ya cika zuciyarsa.

Najeeb kuwa hannayensa duka biyu

yasa ya tallafi hab’arsa tare da aje idanunsa akan had’add’en carpet d’in dake malale atsakiyar d’akin, sosai jin matsalan da Maleek d’in ya samu ya sashi acikin shock, akaron farko kuma kenan da yaji tausayin Maleek d’in, tare dajin wani irin abu na musam

man acikin zuciyarsa.

Yanayin yanda falon yayi shirune kuma yasa dukansu suke iya jiyo gunjin kukan Laylerh dake tashi k’asa k’asa, kasancewar ta b’oye kanta atsakankanun cinyoyinta.

Tabbas acikin irin wannan yanayin dukansu babu wani mai iya rarrashin

ta domin kowannensu da abunda yakeji acikin zuciyarsa.

Hannayensa dake adunk’ule kusan sama da mintuna 15 ya ware, ahankali kuwa ya shiga bud’e k’ank’antattun idanunsa da suka sake rikid’ewa, kana kuma suka bayyana abubuwa da yawa acikinsu.

Lallai tabb

as ruwan hawayene kwance acikin idanunnasa wanda kuma har abada bayajin zai barsu su gangaro zuwa kan fuskarsa, hak’ik’a shikansa ayanzu bai isa fassarawa kansa gaskiyar abunda yakeji ba, domin kuwa abune da yake da tsananin girma da kuma ciwo.

Saidai kum

a akan meyasa zai k’untatawa kansa? shin baiyarda da cewar Allah shike tsara komai bane? shine kuma ya tsara masa hakan, shiya tsara masa way’annan k’addarorin acikin rayuwarsa, yasani kuma cewa kin karb’an k’addararsa butulcewa ne, ba kuma ya fatan koda s

au d’ayane na rayuwarsa ya butulcewa mahaliccinsa daya bashi ido biyu, kafafu biyu, ya bashi baki da hanci, Uwa uba rai da numfashi, wanda suke manya manyan rahamomi, idan bai gode akan wannan ba kuwa To bai cancanci yayi bak’inciki akan sabuwar k’addaran

da tasameshi ba, saboda yayi imani aduniya idan Allah Zai hanaka komai ya baka rai,numfashi,lafiya, ji da gani, da kuma tafiya, to koya hanaka sauran abubuwa ba abun d’aga hankali bane, hakan ba kuma yana nufin cewa baya sonka bane, Tabbas shikam ya aminc

ewa k’addararsa ya kuma yarda cewa zai rayu da ita, zai karb’eta hannu bibbiyu, ba kuma zai tab’a yiwa Allah K’orafi akan hakan ba.

Maida idanunsa yayi ya lumshesu ahankali, tare kuma da soma ambaton sunan Allah, saidai kuma har acikin zuciyarsa a yanzun

babu abundake azabtar da ruhinsa kamar sautin kukan Laylerh da yakeji, wanda yake hautsuna duk wani tunaninsa, Sam ko kad’anne bayason kukannata, saboda yana matuk’ar tab’a masa zuciya.

Ganin kuma yanda Maleek d’in ke motsa labb’an bakinsa ne, yasa Abbo

u Jaheed dake gefensa tsura masa ido cike da matsanancin tausayawa, kasancewarsa kuma uba mahaifi agaresa yasa take ya fahimci cewar Maleek d’in yayi imani ya kuma amincewa sabuwar k’addaran da ta sameshi.

Hakanan Abbou Jaheed yaji zuciyarsa tayi wani iri

n sanyi, wanda har hakan ya bashi k’arfin guiwar dawo da kallonsa ga Laylerh dake kuka.

Cikin sanyin murya da kuma tausasawa yace.

“Najeeb kama hannun Laylerh kutafi can sashinku watak’ila zatayi shiru idan ka rarrasheta.

‿

Jin abunda Abbou Jaheed d’in

ya fad’ane kuma yasa Najeeb mik’ewa anutse ya k’araso inda Laylerh’n ke zaune.

Cikin sanyin murya da kuma son lallab’ata yace.

“Please Laylerh stop crying ki tashi mutafi kinji, ai dama Maleek ne kuma ya dawo, sannan zai samu sauk’i Insha Allah.

‿

Ya k’

are maganar yana me k’ok’arin kama shoulders d’inta ya mik’ar da ita tsaye.

Saidai kuma yanayin yanda tatafi suuu zata fad’ine yasashi saurin kamo hannunta, ahankali ya rab’a ta bayan Oum Ayush yana rik’e da hannun Laylerh suka nufi hanyar fita daga cikin

falon.

Laylerh kuwa sam ta kasa koda d’aga idanunta ta kalli M.Jay d’inne, saboda wani irin tsananin tausayinsa da takeyi, wanda tayi imani sa kasa acikin idanunta ayanzu daidai yake da faruwar komae.

Haka dai Najeeb yaja hannunta batare kuma da tana c

ikin cikakkiyar nutsuwarta ba suka fice daga cikin falon, yayinda binsa kawai take don yana rik’e da ita, amma ko ganin gabanta batayi saboda yanda hawaye ke tururuwan fitowa daga cikin idanunta.

Fitan su Laylerh’n acikin falonne yasa Alhaji Farouk da g

aba d’aya jikinsa yayi sanyi shima ya mik’e, asanyaye cikin kuma rauni ya kalli Abbou Jaheed.

D’an gyaran murya yayi tare da zura hannayensa acikin aljihun rigar jumper’n dake jikinsa.

Cikin yanayin maganan dayasan idan yayita su Abbou Jaheed d’in zasu g

amsu yace.

“Zan wuce gida Alhaji Jaheed, domin wannan maganace da ta cancaci kowannensu ya sani, sannan kuma wannan k’addarar da ta sauk’a akan Maleek tana iya sauk’a akan kowa, babu wanda yafi k’arfinta, idan tanine kuma akan wannan bazae sa na fasa baw

a Maleek auren Munnira kamar yanda nayi niya ba, domin kuwa koba komae Maleek matsayin d’a yake awajena, saidai kuma amma bazanyi gaban kaina ba, saboda a irin wannan yanayin yarinya da kuma mahaifiyarta suna da hakk’i, wanda ya kamata ace ambasu dama sun

fad’i ra’ayinsu, matuk’ar sun amince da auren ahaka tofa Insha Allahu Za’ayisa babu fashi, domin haihuwa Allah Ne maikawowa aduk alokacin da yaso, domin koda likitotin duniya ne suka taru akan mutum suka kuma shaida cewar har abada bazae tab’a haihuwa ba,

idan Allah Ya

sa yana da rabo, tofa komai daren dad’ewa sai Allah ya bashi.

‿

Kai Abbou Jaheed ya jinjina cike da gamsuwa yace.

“Insha Allah.

‿

Mik’ewa tsaye sukayi dukansu shida Abbou Khareem tare dayiwa Alhaji Farouk d’in godiya sosai, kana suka rufa

masa baya donyi masa rakiya, hakan yasa falon yayi saura daga Maleek, sai Oum Ayush da kuma Fou’ad wanda yayi jigum.

Momy dake b’oye ajikin labule sama da yawan minutes d’in da suka kwashe suna magana, ganin su Abbou Jaheed zasu fitane yasa tayi sauri

n b’uya, tare kuma da sauk’e wata ajiyar zuciya mai k’arfi, yayinda takejin wani irin matsanancin farinciki na ratsa zuciya da gangar jikinta, lallai yau taji abunda yasata farinciki ba d’an kad’an ba.

Abbou Jaheed yak’i k’iranta saboda fushin da yakeyi d

a ita, tun jiya akan bataje ta duba Maleek a asibiti ba, amma kuma gashi hakan bai hanata sanin matsalar da Maleek d’in ya gamu da ita ba.

Wani irin murmushi tayi tare da lumshe idanunta cike dajin dad’i tace.

“Maleek ya samu matsala bazae tab’a haihuw

a ba, shikenan ya zama fankon banza, Ya Allah Nagode ma da kakawomin cikar burina asauk’ak’e batare da nasha wahala ba, ayanzu Idan nakawar da Maleek da Laylerh shikenan babu wani mai iko da tarin dukiyar nan saini kad’ai, hak’ik’a duniya zatamin dad’i sos

ae!

‿

Tak’are maganar cikin matsanancin farincikin dake cin zuciyarta, gudun kuma kada su Abbou Jaheed d’in su dawo su isketa awajenne yasa cikin sauri ta juya ta nufi b’angaren ta, zuciyarta fara tas.

Acan cikin falon Abbou Jaheed d’in kuwa Oum Ayush n

e tataso daga inda take zaune, asanyaye ta k’araso inda Maleek d’in ke zaune, wanda kuma har zuwa yanzu idanunsa alumshe suke, still kuma labb’an bakinsa suna d’an motsawa.

Matsanancin tausayinsa daya kamata ne yasa ta d’aura hannunta akan kafad’ansa.

“M

ALEEK!

‿



Ta k’ira sunansa cikin sanyin murya.

Jin muryar Oum Ayush d’in acikin kunnuwansa ne kuma yasashi d’an bud’e idanunsa, ahankali ya sauk’e ganinsa akan fuskarta, saidai kuma bai iya amsa mata ba, saidai idanu daya zuba mata kawae.

Hakanne kuw

a yasa take idanunta suka cika da k’wallan tausayinsa, still kuma cikin murya mai rauni tace.

“Nasan mekakeji acikin zuciyarka Maleek, domin nima na d’and’ani wannan d’acin kuma har yanzu Ina kan d’and’ana, amma hak’uri da fawwalawa Allah yafi dukkan wa

ni koke koke da k’unci, kayi hak’uri kaji Insha Allah Allah Yana tare dakai!!

‿

Ta k’are maganar cikin son k’arfafa masa guiwa yanda zaiji sanyi acikin zuciyarsa.

Kansa ya d’an jinjina, ga mamakinta kuma sai taga wani sihittaccen murmushi ya bayyana aka

n kyakkyawar fuskarsa, cikin dauriya da kuma shanye damuwarsa yace.

“Na aminta cewa komae muk’addari ne daga Allah Oum Ayush.

‿

Maida idanunsa yayi ya lumshe tare da fesar da wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login