Showing 132001 words to 135000 words out of 244674 words

Chapter 45 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

c

ewa idan taje wajen Oum Ayush bazata barta ta zauna da damuwa aranta haka ba, duk da cewa k’arya ba d’abi’arsa bane, amma gashi akanta dan dolensa saida yayi.

Ko juyowa kuwa baiyiba haka ya shige cikin motarsa.

Ganin hakan kuwa yasa ta mik’e tsaye duk da

cewar kuwa har yanzu tanajin ciwon marar na damunta, amma ganinsa da tayi yanzu yasa tanemi kaso 40 na daga cikin ciwon nata ta rasa, dan kafun yanzu ko mik’ewa da kyau batayi amma gashi yanzu ta mik’e.

Asanyaye ta juya tare da kama hanyar sashin Oum Ayu

sh d’in, dan amsa k’iranta kamar yanda ya fad’a mata.

Murfin motar tasa ya mayar ya rufe tare da bin bayanta da idanunsa masu d’auke da matsanancin soyayyarta, kasancewar sai ayanzune ma ya lura da shigar dake jikinta yasashi d’an lumshe idanunsa, saboda

sauk’a akan had’add’iyar surar jikinta da sukayi, yasa shi jin wani iri ajikinsa.

Take kuma wani abu me kama da matsanancin kishi ya tokare masa k’irji.

Saidai kuma babu yanda ya iya, dole haka ya ja motar tasa da reverse yabar wajen.

Laylerh kuwa dire

ct sashin Oum Ayush d’in ta nufa.

Ahankali ta murd’a handle d’in k’ofar falon ta shiga, bakinta d’auke da sallama.

Shigowar nata cikin falon kuwa yayi daidai da fitowar Oum Ayush daga cikin d’aki tana waya.

Saidai kuma ganin Laylerhn yasa bata wani ja w

ayan yayi tsayi ba ta kashe.

Kallon Laylerh’n tayi cikin kulawa tace.

“Yau amarya ne kuma da yawo.

‿

D’an K’aramin bakinta ta turo gaba, sakamakon Jin da tayi Oum Ayush d’in ta k’irata da sunan amarya.

Saidai kuma ganin Oum Ayush d’in acikin farinciki

da tayi ne yasa ta neman waje ta zauna, cikin halin nata na shagwab’a tace.

“Oum Ayush gani, amma naga kamar kina cikin farinciki sosai, Allah Yasa Abbou Kareem ne yace bazaku sake komawa wata k’asa ba anan zaku ci gaba da zama.

‿

Jin abunda Laylerh’n t

a fad’a yasa Oum Ayush sakin murmushi, had’e da neman waje itama ta zauna, cikin nuna jin dad’in labarin dake bakin ta kuwa tace.

“Ko d’aya ba abunda kike tunani bane, domin yanzu nagama waya da Abbou’nki (Abbou Jaheed) yace Nafara had’a kayan lefe domin

nanda sati biyu masu zuwa auren Yayanki yau yaje yaga yarinya ta masa kuma har anbada sadaki.

‿



*(Chab gaskia akwae biki ashe yarinyar ma ta masa amma bamuda labari

😹

team Maleek kunshirya kuwa? Gaskia yau comment nake bukata dan inason sanin ko kun sh

iryawa hakan)*

1/31/21, 9:06 PM - Ummi Tandama: *L.M*

*Writting By*

fatymasardauna

*Note Edit*

*Chapter 44*

A wani irin yanayi taji sauk’an kalaman Oum Ayush d’in acikin kunnuwanta, wanda kuma hakanne yasa tayi saurin d’ago kai ta kalli Oum d’

in, domin hakanan taji kaman kunnuwanta basu jiye mata gaskiyar abunda Oum Ayush d’in ta fad’a ba.

Lokaci d’aya kuma tasamu kanta cikin tsinkewar zuciya, da kuma tarin fargaba, had’i da k’unan k’irji, yanayin yanda take kallon Oum Ayush d’inne yasa itama

Oum d’in tsayawa tana kallon ta.

Cikin muryarta wanda yayi sanyi sosae tace.

“Aure kuma Oum auren waye?

‿

Jin tambayan da Laylerh’n tayi matane yasa ta sakin murmushi, batare kuma da ta lura da halin da Laylerh’n ta shiga asakamakon jin maganan nata ba t

ace.

“Auren Maleek mana kodai bakiji abunda na fad’a da kyau bane, ko bayan shi kina da wani yayane?.

‿

D’an tsagaitawa da maganan tayi ta hanyar d’aukan fruit juice d’in dake gabanta ta d’anyi sipping kad’an, fuskarta d’auke da murmushi tace.

“Tabbas na

ji dad’in wannan al’amarin domin kuwa batun yau ba nafahimci cewa, rashin mace akusa da Maleek shiyasa duk ya zama wani k’aton miskili, baidamu da kowa ba, bayason kowa yasan damuwarsa, koda kuwa zai shekara acikin k’unci bazai tab’a furtawa ba, shi kad’ai

yake shanye duk wata damuwarsa komin d’acinta, da yardar Allah Yanzu komae zaizo da sauk’i, saboda ko ba komai matarsa zata zama k’awa kuma abokiyar d’ebe masa kewa.

‿

Idanunta wanda suka ciko da k’walla ta rumtse, ahankali kuma ta had’e labb’an bakinta w

aje d’aya ta taune su, hak’ik’a sosae maganganun Oum Ayush d’in suka daki zuciyarta, yayinda kuma sukayi fatali da duk wata nutsuwarta.

“Zaiyi aure? hakan na nufin cewa lallai tilas zai rayu da wata kenan amatsayin matarsa? shin dagaske ne kuma abunda Oum

Ayush ta fad’a na cewar ya amince da wata tazamo mata, kuma abokiyar rayuwarsa?.

‿

Abunda zuciyarta ta tambayeta kenan wanda ahak’ik’anin gaskiya bata da amsar sa.

Lallai shigowarta cikin barayin Oum Ayush d’in ya jawo mata tashin hankali, domin kuwa mag

anganun da taji daga bakin Oum Ayush ba k’aramin gigita mata tunani sukayi ba, wanda har hakan yasa hawayen dake cikin idanunta kasa control d’in kansu, saida suka gangaro kan k’uncinta, lokaci d’aya kuma taji wani irin masifaffen sanyi na shiga jikinta, y

ayinda kuma har yanzu bugun zuciyarta ya kasa dawowa normal.

D’ago kai Oum Ayush dake faman danna wayarta tayi, asakamakon jin Laylerh’n tayi shiru ne yasa ta d’an gyara zamanta, cikin kulawa ta k’ira sunanta, tare dason ganin fuskar Laylerh’n kasancewar

ta d’an bata baya kad’an.

Laylerh kuwa jin da tayi Oum Ayush d’in ta k’ira sunanta ne, yasa cikin sauri ta kai hannu ta share hawayen dake kwance akan fuskarta, ahankali ta juyo da kanta ta fuskanci Oum Ayush d’in, saidai kuma duk da cewar ta goge hawayen

nata hakan baihana Oum Ayush fahimtar cewa Laylerh’n kuka tayi ba.

D’anjim tayi tare da kafe Laylerh’n da ido,domin kuwa so take ta fahimci wani abu daga gareta.

Ganin hakanne kuma yasa Laylerh yin k’asa da kanta, asanyaye ta soma wasa da y’an yatsun ha

nnunta.

Murmushin da yake iya kan labb’an baki Oum Ayush tayi, domin dama tasan dole hakan zai iya faruwa, wannan dalilinne ma yasa tafad’awa Laylerh’n cewa Maleek ya yaba da zab’in da Abbou Jaheed yayi masa, domin ta hakanne kad’ai take ganin cewa Layler

h’n zata saduda ta cire Maleek daga cikin ranta, saboda ci gaba da rayuwa da sonsa acikin zuciyarta babban haramci ne saboda tana da aure.

“Tunanin me kike?.

‿

Oum Ayush ta fad’a ta hanyar katseta daga tunanin da take.

“Babu.

‿

Ta fad’a asanyaye tana me w

asa da y’an yatsun hannunta.

“To yayi kyau, amma meyasa kika baro Najeeb shikad’ai kika taho nan?

‿

Oum Ayush ta fad’i hakan tana me sake zubawa Laylerh’n idanu.

Shagwab’abbiy’ar fuskarta ta kwab’e cikin muryarta dake d’an rawa tace.

“Bayanan bansan ind

a yake ba, kuma ba Yah M.Jay ne yace nazo kina k’irana ba.

‿

Idanu Oum Ayush ta zaro waje, cikin yanayin mamaki tace. “Ni nace ina k’iranki?.

‿

“Eh mana haka Yah M.jay ya fad’a.

‿

Ta fad’i hakan tana me d’an mammatse cinyoyinta, saboda yanda taji ciwon mara

r nata na neman dawowa.

Shiru Oum Ayush tayi ta kasa cewa komae, saboda Jin abunda Laylerh’n ta fad’a ya d’an sata mamaki kad’an, saidai kuma rashin sanin dalilin da yasa Maleek d’in yayi hakan yasa, ta sauk’e ajiyar zuciya.

Gyara zamanta tayi had’e da f

uskantar laylerh’n cikin yanayin sanyi ta k’ira sunanta tare da kamo hannayenta, anutse ta yanda ta tabbatar da cewa Laylerh’n zata fahimceta tace.

“Kada ki bari koda wasa damuwa ko k’unci suyi tasiri acikin rayuwarki Laylerh, tabbas nasan halin da kuke

ciki dukanku keda Maleek, amma hakan bawai yana nufin akoda yaushe kuyita biyewa son zuciyarku bane, hak’ik’a nasan zuciyarki na sak’a miki abubuwa da yawa akan d’an uwanki Maleek, amma komai zai faru dake Laylerh ki daure, kada wani abu na daban ya hanaki

kulawa ko bawa mijinki hakk’insa, domin yin hakan zaisa Allah Yayi fushi dake, sannan kuma nasan zakiji ba dad’i saboda Maleek zaiyi aure, amma inaso kusani aduniya babu wani d’an Adam da yake da ikon yin abu dan kansa, komai Allah Ne ke tsarawa bawansa,

sannan babu wani me iya canja k’addara, abunda Allah ya tsara kuma ya hukunta shine kawai ke faruwa, sannan ako yaushe ki rik’e cewar saudayawa bako w

ani abu da kakeso kake samu ba.

‿

D’an numfasawa da maganan nata tayi, kana kuma cikin sakeyin k’asa da mu

rya tace.

“Babu buk’atar na tsaya tambayanki akan hakk’in Najeeb dake kanki, shid’in Mijinki ne, idan har baki basa hakk’insa dake kanki ba watace daban zata basa? Tabbas Najeeb Namiji ne me nutsuwa, dan Allah Laylerh kada kiyi gangancin rasa Namiji me na

garta kaman Najeeb, domin samun kamarsa acikin sauran maza ba abu bane me sauk’i, saboda haka ki tashi ki koma d’akin ki, ki kuma aikata duk abunda Najeeb ya umarceki dashi, matuk’ar bai sab’awa Allah ba, ya kamata kuma kisan cewa yanzu ba lokaci ne da zak

i tsaya kuka ko damuwa ba, kamata yayi kimanta komai, domin damuwarki bazae tab’a sanja komae ba.

‿

Takai k’arshen maganan nata tana me d’an bubbuga kafad’un Laylerh’n, wanda tuni sabin hawaye sun sake cika idanunta.

K’asa tayi da kanta ahankali tare da

sa hak’waranta ta datse labb’anta, hak’ik’a ayanzun ita kad’ai tasan abunda takeji acikin zuciyarta, so take tayi kuka sosae dan rage rad’ad’i da kuma zafin abunda takeji acikin zuciyarta.

Saidai kuma awannan karon sam bataso Oum Ayush tasake ganin hawaye

nta, dan faruwar hakan alamace dake nuna gazawarta, sam ita kuma bata fata hakan yakasance.

Ahankali kuma cikin yanayin sanyi ta zare hannayenta daga cikin na Oum Ayush d’in.

Sanin da tayi kuma cewa idan tace zatayi magana wani sabon kukane zai zo mata b

abu controll yasa ta jan bakinta tayi shiru, asanyaye ta mik’e daga zaunen da take, batare kuma da ta kalli Oum Ayush ko ta sake cewa wani abuba kaitsaye ta nufi hanyar fita daga cikin falon.

Da kallo me d’auke da tsananin tausayi Oum Ayush ta bita, harta

fice daga cikin falon kuwa bata d’auke kanta ba.

Ajiyar zuciya ta sauk’e tare dasa hannayenta ta tallafi hab’arta, sam takasa gano wace irin soyayya ce haka, me k’arfin gaske da ke tsakanin Laylerh da Maleek d’in, saboda zuwa yanzu al’amarin nasu sosai y

ake bata mamaki, ita dai addu’a da kuma fatanta d’aya shine kada Allah Yasa watarana Najeeb yafahimci hakan, harta kaisa ga rabuwa da Laylerh’n ko kuma ya fara yi musu mummunan zargi.

Laylerh kuwa tun fitowarta daga sashin Oum Ayush d’in tafiya kawai take

tana jefa k’afafunta batare da tasan inda take takawa ba, hak’ik’a abu d’aya ne keyi mata yawo acikin ranta shine auren Maleek, hakanan taji duk wata nutsuwarta ta k’aurace mata tunda taji batun auren nasa, yayinda a gefe guda kuwa kalaman Oum Ayush ne ke

yawo acikin k’wak’walwarta.

Da tunani kala kala acikin ranta haka ta iso part d’in su.

Ahankali ta tura k’ofar falon tashiga, kamar kuwa dama hawayen dake cikin idanunta jira suke ta shigo cikin falon, take suka soma gangarowa kaman ana turosu.

Maida k

’ofar tayi ta rufe, ahankali kuma ta zame ta zauna abakin k’ofar dab’as.

Tayaya ma zata iya jure duk way’annan matsalolin? Tayaya zata iya cire soyayyar Maleek acikin jikinta? Soyayyar da ta zame mata kamar numfashi, soyayyar da ta zama itace gaba d’aya r

ayuwarta, lallai tayi imani cewa koda kashe ta za’ayi har abada bazata tab’a iya daina so da tunanin Maleek ba, domin saida tunaninsa kad’ai take samun nutsuwa, tunaninsa ne abincin ruhinta, yayinda kuma akullum idan ta ganshi take k’ara jin matsanancin so

yayyarsa na k’ara shiga zuciyarta.

Asanyaye sautin sheshshek’an kukanta ya fara fitowa, saboda takai wani matakin da bazata iya jurewa ba.

“LAYLERH!

‿

Najeeb dake tsaye tun d’azu acikin falon ya k’ira sunanta, da muryarsa wacce tayi sanyi sosae, domin

tun shigowarta cikin falon yake tsaye abakin dining table, saboda dawowansa shima kenan, ganin kuma food flask d’in abincin daya ajiye mata a yanda ya barshi ne, yasashi k’arasowa wajen ya duba dan yaga ko taci abincin.

Jin amo da kuma sautin muryarsa aci

kin kunnuwanta ne yasa tayi saurin bud’e idanunta wanda suka b’aci da hawaye, saboda kwata kwata bata kawo aranta cewar akwae wani acikin falon bayan itaba

Ahankali ta janye idanunta daga kallon da yake mata, tare da sunkuyar da kanta k’asa.

Shikuwa Naj

eeb anutse ya shiga takowa zuwa gareta, har ya k’araso inda take kuwa bata sake d’ago kae ta kalleshi ba.

Isowarsa kusa da ita ne kuma yasashi d’an durk’usawa agabanta, cikin yanayin sanyi yasa hannayensa ya d’ago hab’arta, hakanne kuwa ya bashi daman kal

lo full face d’inta.

Ahankali yasa d’ayan hannunsa ya shafi gefen fuskarta.

“Me yake da munki?

‿

Ya fad’a asanyaye tare dasa hannayensa ya share mata hawayen dake mak’ale atsakankanin eye lashes d’inta.

“Babu.

‿

Ta fad’a da k’yar cikin muryar ta dake fit

ar da sheshshek’a.

Ahankali ya maida hannayensa kan kafad’unta ya d’agota saboda dama yasan cewa ba lallaine ta fad’a masa gaskiya da kuma hak’ik’anin abunda ke damunta ba.

K’ok’arin mik’ar da ita tsaye yayi ta hanyar rik’o hannunta, ahankali yajawota z

uwa tsakiyar falon.

Zama yayi akan d’aya daga cikin kujerun falon, still kuma hannunsa na rik’e da nata ya jawota ta fad’a jikinsa.

Hannayensa duka biyu yasa yayi hugging d’inta.

Ahankali ya kawo bakinsa daidai saitin kunnenta, cike da kulawa yace.

“Me

yasa har yanzu bakiyi breakfast ba, kodai baki ga kayan breakfast d’in dana ajiye miki bane?

‿

Yanayin yanda yayi mata tambayan cikin rad’a ne yasa ta sake shagwab’e fuska, y’an yatsun hannunta ta shiga murzawa cikin muryarta da bata fita sosae tace.

“Nak

’oshi ne.

‿

“Me kikaci da har yasa kika k’oshi haka? bakisan cewa rashin cin abinci yana sa mutum ya kamu da ulcer ba? koda yake ma duk ba wannan ba, meyasa meki kike kuka? saboda na tabbata bazakiyi kuka haka kawae babu wani daliliba, fad’amin idan kuma b

ankai na sani bane shikenan.

‿

Jin abunda ya fad’a d’inne yasa ahankali ta d’ago kai ta kalleshi, ganin kuma shid’in ma ita yake kallo ne yasa tayi k’asa da idanunta, tabbas baicancanci shariya ko k’arya awajen ta ba, amma kuma saidai wani lokaci bisa dole

ake aje gaskiya ayi k’arya, musamman idan akayi duba da cewar fad’an gaskiyan kan iya ruguza komai.

“Marana ne yake ciwo.

‿

Ta fad’a atak’aice domin gudun kada ya gano cewa ba gaskiya ta fad’a masa ba.

“Meya samu marar naki yake ciwo?

‿

Ya jefo mata tamb

ayar da sam batayi tsammanin jinta daga garesa ba, hakan yasa ta kau da kanta gefe, Dan ayanzu kam bata da amsar da zata basa.

Gane hakan da yayine kuma yasa baisake tambayar taba, saima tashi da yayi ya k’arasa gaban dining table d’in, da kansa ya had’o

mata breakfast d’in acikin plate.

Zuwa yayi har gabanta ya zauna, tare da sata agaba dole saida yaga ta d’anci abincin kafun ya k’yaleta.

Itakuwa Laylerh anan cikin falon ta kwanta, haka zuciyarta ta dinga sak’a mata abubuwa da yawa acikin ranta, cikin m

intuna k’alilan kuwa bacci b’arawo ya d’auketa.

Tunda tafara baccin kuwa Najeeb ya tsura mata mayun idanunsa, baya ko k’iftawa, tunani daban daban kawai yake tayi acikin zuciyarsa, shima ahaka bacci ya d’aukesa.

Har yayi baccin nasa ya farka kuwa Laylerh

bata tashi ba, wanka ya je yayi tare da sake shirya kansa cikin shiga me kyau, batare kuma da ya ta she ta ba ya fice daga cikin gidan na gaba d’aya, saboda ya lura zamansa atare da Laylerh’n shine ke k’ara haukatar dashi yayi ta jin feelings.

Laylerh k

am bacci tayi sosae dan sai wajajen 3 tatashi, hakanan taji duk duniyar batayi mata dad’i.

Wanka ta sakeyi inda ta shirya kanta cikin kaya marassa nauyi.

Atak’aice dai haka ta k’are gaba d’aya wuninta na wannan rana batajin dad’in yanayinta, domin kuwa d

a zaran tatuno cewar Maleek zaiyi aure nanda 2 weeks saitaji komae ya tsaya mata.

Ahaka har dare yayi, yau dai kam Najeeb ko kusa da ita baizoba akan doguwar kujeran dake cikin d’akin yayi kwanciyarsa saboda ya lura dagaske cewa Laylerh’n batajin dad’i,

idan ya matso kusa da ita kuwa ba k’aramin azabtuwa yakeyi ba, wannan dalili yasashi samawa kansa nutsuwa ya kwanta akan kujera.

Laylerh kuwa sosae taji dad’in hakan saboda yau d’in duk adagule take.

Washegari.

Awayewan garin na yau ne kuma su Abbou J

aheed da Oum Ayush suka tashi da shirye shiryen auren Maleek haik’an, inda Oum Ayush ta shiga shirye shiryen abubuwan da ya kamata ayi, b’angaren kayan lefe kuwa tunjiya ta bada order’nsu wa k’awarta Hajiya Nana dake can k’asar Dubai, wanda kuma nan da kwa

na hud’u kayan zasu iso.

(kuyi hakuri muna biki bansamu zama ba shiyasa, wannan page dinma atsatstsaye nayi ba editing.)

29January/2021

2/1/21, 3:27 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Chapter 45*

Wayarsa k’irar S

amsung wanda ke aje bisa saman wani had’add’en table ne ke ta faman kuwa, da’alama dae k’iran wayannasa ake babu k’akk’autawa.

Ahankali ya d’ago kansa daga durk’uson da yake, wanda hakanne kuma ya bani daman kallon idanunsa wanda sukayi jajur, kallo d’aya

kawai zakayi masa ka fuskanci cewa d’auke yake da damuwa me tarin yawa.

Kasancewar yanzu kusan sama da 40min kenan da ya d’auka zaune awajen, yayinda ya duk’ar da kansa k’asa.

Hakanan yakejin gaba d’aya duniyar batayi masa dad’i, yayinda ajikinsa yakeji

n sauyin yanaji, wanda hakan ke yawan haifar masa da fad’uwar gaba, saboda yanda yakejin wani abu na daban na neman haukata tunaninsa, yayinda yakeji ajikinsa cewar wani abu na daban na shirin tunkaro rayuwarsa.

Daga gefe guda na zuciyarsa kuwa tunani da

kuma k’aunar Laylerh ne ke hura masa wuta, wanda har hakan yasa yakejin kamar zuciyar tasa zata buga.

D’ago kansa yayi tare da jingina bayansa ajikin had’add’iyar kujeran da yake kai, wanda ke cikin katafaren office d’insa.

Hannunsa yakai kan wayarsa dak

e ta faman tsuwa, batare kuma da ya duba wanda ke k’irannasa ba ya kashe wayar tasa gaba d’aya.

Idanunsa wanda sukayi ja sosai ya lumshe, tare da fesar da wani irin zazzafan numfashi.

Ahankali aka turo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login