Showing 192001 words to 195000 words out of 244674 words

Chapter 65 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

masa kyau, again wani babban sallaya ya ciro daga cikin ledan, had’e da shumfud’

asa ak’asa ya tada sallah.

Almost 13minutes ya d’auka kafun ya idar da sallan.

Saboda kuma gajiya da ciwon da yakejin mararsa nayi masane yasashi tak’aita addu’oinsa.

Mik’ewa tsaye yayi tare da cire rigan dake jikinsa, wanda kuma yayi hakanne don

ba al’adarsa bace kwana da riga, sannan kuma akwae raunuka ajikinsa wanda basa buk’atar arufesu.

K’arasawa inda ya ajiye jakarsa yayi tare da zuge zip d’inta, ya ciro pain relievers d’insa da kuma wayoyinsa da tuntuni suke akashe.

Kunna wayoyinnasa

yayi, had’e kuma da d’aukan goran ruwa, yasha magungunansa, domin zuwa yanzu har wani irin zogi yakejin cikin marar nasa nayi masa.

Bayan ya kwanta akan makeken gadon dake cikin d’akinne kuma, akasalance ya mik’a hannunsa ya kashe gaba d’aya hasken wu

tan dake cikin d’akin, saidai kuma sanin da yayi cewar babu kyau kwana acikin duhu ne, yasa ya d’an kunna electric kindle d’in dake gefen gadon, hakan kuwa shiyasa haske ya d’an bayyana acikin d’akin.

Wata irin numfashi mai sauti yaja adaidai lokacin d

aya ajiye kansa akan tattausan pillow’n dake kan gadon.

Asanyaye kuma yasa hannunsa na dama ya dafe saman mararsa.

Tabbas shi kad’ai yasan me yakeji ayanzun, duk da cewar yanayin nasa Bawae bak’o bane agaresa, amma ya d’an kwana biyu baiji hakan ba.



Ahankali ya lumshe sassanyun idanunsa masu d’auke da yanayin bacci, wani irin abu ne yakeji na yawo acikin jikinsa, wanda hakan yasa gaba d’aya gargasan dake jikinsa suka mimmik’e.

Tabbas akowacce duniya yake ita kad’ai ce acikin tunaninsa, koda da s

econd d’aya ne kuwa zuciyarsa bata tab’a bugawa batare da ita acikinta ba.

Wannan dalilin yasa har yakan kasa tantance matsayin yanda yakejinta acikin zuciyarsa, domin dayawan lokuta tunaninta kan rikid’e ya dawo matsanancin kewa.

Kamar dai ayanzu da y

akejin sonta na game duk ilahirin jikinsa, wanda kuma sanadin k’arfin hakan, ya haifar masa da wani irin feeling mai k’arfi.

Jajayen red lips d’insa ya d’an ciza, tare dasa hannunsa ya sake dafe saman maransa.

Tayaya zai misalta irin hot feeling d’in

ta da yakeji yau d’in? sannan kuma tayaya zai iya jurewa imagine d’inta da eye balls d’insa keyi?

Sake matse jikinsa waje d’aya yayi, had’e da d’aukan pillow ya d’aura akan fuskarsa.

Cikin dakiya da k’arfin hali kuwa yasoma k’ok’arin k’ak’alowa kans

a baccin dole.

Akuma daidai wannan lokacin itama ta lumshe Idanunta wanda suke cike da ruwan hawaye.

Ahankali ta juyar da kanta daga kallon Aleeya dake ta faman bacci, zuwa kan had’add’en agogon dake cikin d’akin.

12:45 am. Kenan amma har zuwa yan

zu bacci ya kasa d’aukarta, duk da cewar tanajinsa cike a idanunta, amma sam zuciyarta bata da nutsuwar yinsa.

Domin kuwa yau d’in ganin kanta takeyi acikin wata irin sabuwar rayuwa.

Pillown dake gefenta ta rungume, tare kuma da cusa kanta acikinsa.

Lallai ayau ta yarda cewa k’addara kan iya sauyawa in a few second, ba kuma lallaine sauyinta ya zamo mai sauk’i ba.

Haka zalika ba Lallai abunda kake hange da tunani ya zamanto shine akwae ba.

Tabbas ayau ta fahimci cewa akwae abubuwa da yawa da basu z

oba, sannan akwae kuma way’anda suka zo suka wuce, da har abada bazasu tab’a dawowa ba.

Sannan akullum akuma koda yaushe sanyawa kai k’warin guiwa, shi ke taimakawa izuwa Nasara.

Still sassanyar ajiyar zuciya ta sake sauk’ewa, akaro na biyu kuma ta l

umshe idanunta, Yayinda acikin ranta take fatan bacci ya d’auketa.

Ae kuwa Allah Ya duba zuciyarta, cikin mintuna k’alilan wani bacci mai nauyi ya d’auketa, saidai kuma acikin baccin nata akwai mafarkai da yawa mabanbanta.

*Washegari*

Alhamdulill

ah Yau tun tashinta takejin zuciyarta asanyaye, hakanne ma yasa ta taimakawa Aleeya suka shirya breakfast.

Ganin kuma yanda Laylerh’n ta d’an sakene yasa Aleeya jin dadi sosae haka ta dinga Jan Laylerh’n da hira.

Bayan anyi sallan azahar ne kuma Oum

Ayush tazo, ita da Teemah inda ta kawowa Laylerh’n sabon uniform da kuma kayan fiye ciye ciye.

Sosae Laylerh’n taji dad’in ganin Oum Ayush da kuma Teemah’n, musamman ma Teemah wanda tayi missing dinta sosae.

Anan cikin babban falon Aunty Zee suka zaun

a inda Teemah ta shiga koyawa Laylerh’n abubuwan da akayi a school d’in bayan bata nan.

Sosae kuwa ta fahimci abunda Teemah’n ke son fahimtar da ita.

Haka dae Teemah da Oum Ayush d’in suka zauna har saida dare yayi kafun suka tafi, Inda Oum Ayush da

kanta tamayar da Teemah’n gida, domin dama ita taje ta d’auko ta.

*8:46 pm*

*15/3/2021*

3/18/21, 9:36 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Not editing*

*Chapter 68*

7:00 am daidai haka k’ararrawar dake j

ikin babban agogon bangon dake cikin d’akin ya buga.

Daidai lokacin kuwa ta d’ago kanta ta kalli agogon, domin dama tun d’azu 7 d’in take jira ya cika, kasancewar k’arfe 8:00 am ne daidai zasu shiga exam d’innasu.

Shiyasa ma tunda tayi sallan asuba bat

a koma bacci ba, d’aukan takardun da Teemah ta kawo mata tayi ta soma karantawa.

Yayinda Aleeya ko keta sharar bacci, duk da cewar itama yau d’inne zasu fara exam a school d’insu, amma kuma saidai b’ata lokacin da tayi Daren jiya tana kallon film ne yasa

ko sallah’n asuba da k’yar ta iya tashi tayi.

Kallonta ta mayar ga Aleeya, kaman kuma zata tasheta saita fasa, ahankali ta mik’e tsaye, tare da zare hijab d’in dake jikinta, kaitsaye toilet d’in dake cikin d’akin ta nufa.

Koda ta k’arasa cikin toilet

d’in kayan dake jikinta ta cire tare da sanya shower cap akanta, kasancewar kuma yau d’in ana d’an yanayin zafi ne yasa ta k’arasawa gaban shower ta sakarwa kanta ruwa.

Bayan tagama wankanne kuma tayi brush, tare da d’aukan wani d’an k’aramin towel t

a shiga tsane ruwan dake jikinta.

Ahaka ta fito daga toilet d’in, still sake kallon Aleeya dake ta faman sharara bacci tayi, yanzun kam lokaci ya d’an tafi shiyasa bazata iya barin Aleeya’n ta cigaba da bacci ba.

Hannunta tasa tad’an tab’a Aleeya’n ha

kanne kuwa yasa Aleeya’n tashi zaune, cikin yanayin magagin bacci tace.

“Namakara ko?

‿

“Kindai kusa amma kuma ci gaba da baccinki daidai yake da makaranki.

‿

Laylerh’n ta bata amsa adaidai lokacin da take k’arasawa gaban mirror.

Body lotion na comp

any’n Nivea ta shafa ajikinta, sai kuma powder da wani brown lipsgloss da ta shafa akan jajayen labb’anta, iya kwalli kawae ta shafa acikin idanunta, daga haka kuwa bata sake goga komae akan fuskar nata ba, direct wajen drawer’n dake cikin d’akin ta nufa

, koda ta bud’e drawer’n sabon uniform d’in da Oum Ayush ta kawo mata ta ciro tare da sakawa ajikinta, sosai kuwa uniform d’in ya zauna ajikinta, sannan kuma ko kad’an bai bayyana wani shatin sura na jikinta ba, ya rufe ko ina d’inta, hatta hijab d’inma d

uk da cewar bashi da girma amma ya rufe guiwan hannayenta.

Wasu White socks d’inta masu tsayi ta saka, tare da wasu fararen takalma wayanda suke yanayi da sneakers shoe.

Sake d’ago kanta tayi ta kalli agogon dake cikin d’akin, wanda yake nuna 7:30 am d

aidai.

Face mask d’inta ta d’auka tare kuma da wasu fararen papers cikin sauri ta nufi hanyar fita daga cikin dakin, daidai lokacin kuwa Aleeya ta fito daga toilet jikinta d’auke da danshin ruwa.

Ganin da tayi kuma Laylerh’n ta shirya ne yasa itama ciki

n hanzari ta soma shirya kanta.

Laylerh kuwa tana fita daga cikin d’akin direct falo ta fito, inda ta samu Aunty Zee da Mijinta zaune akan dining table.

Aladabce ta gaishesu dukansu kuwa fuska d’auke da murmushi suka amsa mata, kana cikin kulawa Au

nty Zee tace.

“Yanzu nake da shirin zuwa k’iranku kuyi breakfast, domin naga har takwas d’in ma ta kusa baku fito ba, Ina Aleeya’n kuma ta tsaya?.

‿

“Tana shiryawa.

‿

Tafad’i hakan asanyaye, tare kuma da d’an sunkuyar da kanta k’asa.

Kai kawai Aunty

Zee tajinjina domin dama ita tasan halin Aleeya badai saib’i ba.

Kujera ta nunawa Laylerh’n had’e da cewa.

“Kizo kici abinci.

‿



“To.

‿

Kawae ta iya cewa duk da cewar kuwa bata wani jin yunwa sosai, saidai kuma amma sam batason cewa Aunty Zee d’in a’a

, musamman ma da tafahimci cewa Aunty Zee d’in da kuma Mijinta wanda Aleeya take k’ira da Yah Jameel suna da mutumci sosae.

K’arasowa dining area d’in tayi tare da zama akan kujeran da Aunty Zee d’in ke nuna mata.

Itakuwa Aunty Zee da kanta tayi servi

ng Laylerh’n.

Suna fara cin abincin kuwa Aleeya ta fito itama cikin shirinta.

Akujerar dake kusa dana Laylerh ta zauna, cikin sauri sauri ta soma cin abincin gudun kada tajawo musu latti, domin driver’n da zai kaisu makarantar saiya fara kai Laylerh kaf

un ita, kasancewar school d’in su Laylerh’n yafi kusa.

Kwata kwata kuwa ko mintuna 10 ba suyi sunacin abincin ba kuwa, kowaccensu ta ajiye spoon d’in dake hannunta.

Laylerh ce ta fara mik’ewa tsaye, domin kuwa taga time d’insu nata tafiya.

Ganin haka

nne kuma yasa Mijin Aunty Zee d’in sa hannunsa aciki aljihun rigar dake jikinsa, fararen 1k ya ciro tare da bawa kowaccensu d’aya, Laylerh kam bata saba hakan ba, shiyasa tak’i k’arb’a, amma kuma ganin yanda ya had’e fuska yasa ta k’arb’a tare dayi masa go

diya.

Aunty Zee kuwa addu’a da fatan samun nasara ta musu, Laylerh kuwa har takai bakin k’ofar fita daga falon, Jin da tayi kuma Aunty Zee d’in tak’ira sunanta ne yasata tsayawa tare da juyowa ta fuskanceta.

Murmushi Aunty Zee d’in ta sakar mata,

cikin kuma tsananin kulawa tace.

“Ina fata baki manta maganganun da Oum Ayush ta fad’a miki ba, sannan kome zakiyi kada ki tab’a mantawa da matsayin dakike kai ayanzu, kada ki kulawa kowa saidai idan yazama dolen dole, sannan ki k’ebe kanki waje d’aya, ba

nda yawan surutu, da zaran kunfito a exam kuma ki k’ira wayana zan turo driver ya d’aukeki, dan Allah Laylerh kikula da kanki sosae, kinga fita ma sam baikamaceki ba saidon kawae ya zamanto dole ne.

‿

Ahankali ta d’an jinjina kanta, cikin kuma son nunawa

Aunty Zee d’in cewa ta fahimci abunda suke son nusar da ita tace.

“Insha Allah Zankiyaye.

‿

“Allah Yasa.

‿

Aunty Zee d’in tafad’a.

Itakuwa Laylerh juyawa tayi ta fice daga cikin falon, Dan tuni Aleeya tayi waje.

Koda ta fito compound d’in gidan

kuwa direct inda motar da za’a kaisu makarantar ke fake ta nufa, tana zuwa kuwa ta bud’e murfin motar tashiga, akusa da Aleeya ta zauna.

Take driver’n kuwa yaja motar suka tafi.

Kamar yanda yake makarantar su Laylerh’nce afarko hakan yasa ita driver’

n ya fara sauk’ewa, saida suka ga shiganta cikin skull d’in kuwa kafun suka juya suka tafi.

Tana shigowa cikin school d’in nasu kuwa ta hango Teemah, hakanne yasa ta k’arasa wajen da Teemah’n ke zaune.

Teemah kuwa dake zaune ganin Laylerh’n ta nufot

a ne, yasa ta fad’a d’a murmushin dake kan fuskarta, take kuma duk wani tausayin Laylerh’n da takeji acikin zuciyarta ya bayyana kansa acikin k’wayoyin idanunta.

Tabbas Allah Yasani tana tausayin Laylerh’n sosai, ko adacan ma bare yanzu da k’addara ta fa

d’a mata.

Wasu irin hawaye da suka cika idanunta ne yasa ta wayance.

Cikin salon tsokana tace.

“Ke kuma ya haka kin b’oyemana kyawun fuskar taki da face mask, kodai har anfara tattalawa Mr.Soldier fuskar ne?

‿

Hararan wasa Laylerh’n ta watsa mat

a tare da cewa.

“Tayaya hakan zai faru bayan kinjima kina sonshi.

‿



Murmushi mai had’e da dariya Teemah tayi, tare da mik’ewa tsaye ta kamo hannun Laylerh’n, Idanunta ta d’an lumshe, cikin yanayi da kuma sigar da tasan Laylerh’n zata fahimceta tace.

“Tabbas ada nayi tunanin cewa abunda nakeji a kansa sone, but amma yanzu na tabbar da cewa ba sonsa nake ba, just kawae yana burgeni ne, kuma kin dai san Namiji irin Mr. Soldier babu macen da bazae burgeba, sannan kuma hak’ik’a nikam na yarda SO d’aya

ne, akuma duniyar nan gaba d’aya babu wacce zata soshi kamar yanda kike sonsa, sannan kuma ke kad’ai ce choice d’insa, saboda ke da shi d’in kun kasance MURADI d’aya ne, rabaku ayanzu daidai yake da raba mutum da rayuwa, infact ma ayanzu wanda yace zai ka

tse wannan burin zai iya mutuwa, ko dai kinason na mutu anan kusa ne?.

‿



Kai Laylerh’n ta girgiza mata, tare kuma da lumshe idanunta, wanda kuma hakanne ya bawa hawayen dake cikin idanunnata, daman gangarowa kan fuskarta.

Tabbas maganganun da Teemah’n

ta fad’a mata ayanzu, sunsa wani irin matsanancin soyayyar Maleek d’in ya sake motsa mata, hakanne kuma yasa ta kasa cewa komae.

Teemah kam tasan komai, da kuma irin raunin da zuciyar Laylerh’n ke dashi akan Maleek, shiyasa ma bataso sake jin wani abu

daga bakinta ba.

Ahankali ta kamo hannunta, batare kuma da tasake ce mata komae ba, kai tsaye suka nufi exam hall d’in, da acikinsa ne zasu gudanar da jarrabawar tasu, inda kowannensu yake d’auke da number’n kujerarsa.

Kasancewar kuma numbers d’insu

basa kamanceceniya da juna, wannan yasa koda suka shiga cikin exam hall d’in kowacce ta nufi mazauninta.

Suna zama kuwa aka soma raba musu questions papers.

Time na cika kuwa suka fara answer questions d’in.

Sosai kuwa abun yazowa Laylerh da sauk

’i, domin kusan rabin questions d’in takaranta amsansu ayau da asuba bayan tayi sallah, wannan yasa bata wani sha wahala ba.

Duk da cewar kuma 1hour and 30 minutes kad’ai aka basu sugama answering questions d’in, sai gashi kuma acikin 1hour kad’ae kusan

gaba d’aya students d’in sungama amsa questions d’in da zasu iya amsawa.

Ciki kuwa harda Laylerh da Teemah bayan sun gama ne kuma dukansu sukayi submit papers d’in suka fita.



Anan k’asan wata bishiya suka zauna ita da Teemah, tare da soma karatun

next paper’n da zasu shiga anan gaba wanda tsakaninsa da wancan papern kwata kwata 40minute ne.

Karatu sukayi sosae mintuna 40 na cika kuwa suka sake komawa exam.

Sosae wannan paper’n ya basu wahala kasancewar sa na Geography ne.

Amma kuma cikin ik

on Ubangiji sun samu sun rubutasa tare dasa ran cewa zasu samu marking mai yawa.

11:30 am daidai suka fito daga exam d’in nasu, kamar yanda Aunty Zee ta fad’a kuwa, suna fitowa Laylerh ta ciro wayarta dake kashe, kasancewar da zasu shiga exam d’in ka

she wayoyinsu sukayi kana suka bada ajiya, saboda doka ne ba’a shiga exam d’in da waya.

Kunna wayartata tayi tare dayin dialing Number’’n Aunty Zee.

Bugu biyu kuwa Aunty Zee d’in ta d’aga wayar.

Gaya mata kuma da Laylerh’n tayi cewar sun gama exam ne y

asa ta cewa gatanan zuwa, zata zo ta d’auketa, domin ayanzun tana kusa da makarantar su Laylerh’n.

Cikin abunda bai wuce 15minutes ba kuwa saiga Aunty Zee d’in tazo, har bakin Mota Teemah ta raka Laylerh’n, saida taga tafiyarsu kuma kafun ta koma cikin

makarantar dan a cewar ta zata shiga library’n makarantar tasu fad’an tab’a karatun exam d’in da zasuyi gobe, saboda goben ma two papers zasuyi.

B’angaren Laylerh’’n ma hakance takasance dan Koda suka koma gida karatu ta wuni yi, duk da yanda takejin

soyayyarsa nayi mata suka acikin zuciyarta amma haka ta daure, musamman ma da ayanzu ta gano cewa idan babu tunaninsa acikin mind d’inta to babu abunda zata iya.

Koda dare yayi kuwa bata wani iya samun bacci sosae ba, karatu tayi sosai, Yayinda kuma ke

warsa ke k’ara cika wani sashi na zuciyarta wanda har hakan yake sawa taji kamar tayi kuka.

Haka dai tayi ta abu d’aya har saida dare ya raba kafun ta iya samun bacci.

*Washegari*

Kamar dai yanda jiyan suka tafi school tare da Aleeya, haka ma yau,

still saida aka sauk’eta kafun aka wuce da Aleeya.

Balaifi kuma exam d’in nasu na yau ya d’anyi musu sauk’i.

Paper biyu sukayi saidai yau ba kaman jiya ba sai 12 dukansu sukabar makarantar.

Daga wannan ranan kuwa koda yaushe ya zamana Laylerh’n t

ana cikin karatu, duk da kuwa tanajin matsanancin kewarsa acikin rai da zuciyarta amma haka take daurewa, aduk lokacin da tayi imagine d’insa kuwa haka takejin kaman zata shid’e.

Yayinda akullum hot feeling d’in da takeji akansa ke sake k’aruwa

**** *

** ***

Tabbas adaidai irin wannan lokacin idan tace batajin dad’in zama agidan Aunty Zee tayi k’arya, domin suna bata kulawa maikyau, sannan kuma kullum sai tayi waya da Abbou Jaheed da kuma Oum Ayush, Yayinda Abbou Khareem ma ke k’ok’arin k’iranta.

Afannin mu’amala kuwa ita da Aleeya yanzu sun zama k’awaye sosae, aduk

lokacin da sukaje exam suka dawo sukan zauna su taya Aunty Zee aikace aikacen gida, hakan kuwa bak’aramin dad’i yakeyiwa Aunty Zee d’in ba, shi yasa ma yanzun bata shakkan saya musu

komai na k’yale k’yale idan ta gani.

Babban abun da yake bawa Aunty Zee d’in mamaki kuwa shine, yanda har abada, Laylerh’n bata tab’a gajiyawa da kallon wani hoton Maleek dake cikin wayarta, domin da yawan lokuta Laylerh’n takan zauna tayi shiru, idan ku

ma tana kallon hoton Maleek d’in abune mawuyaci kaga babu k’walla acikin idanunta, wannan abun kuwa shiyasa Aunty Zee take mamakin irin tsananin soyayyar da Laylerh’n keyiwa Maleek.

Kamar yanda ranar yau ta kasance Friday, wanda ayau d’inne kuma zasu k

ammala WAEC examination d’insu.

Hakan yasa duk d’aliban dake zana waec zuciyarsu ke cike da farinciki, ga masu shirin zana neco exam kuwa hankalinsu ya tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login