Showing 198001 words to 201000 words out of 244674 words

Chapter 67 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

zai biyo baya ba, tanasa rai da kuma fatan cewa Alkhairi ne Insha Allah.

Mik’ewa tsaye tayi cikin kuma yanayin sakin

fuska ta juya ta fice daga cikin falon.

Nan tabar su Abbou Khareem na tattaunawa, ita kuwa kaitsaye sashinta ta wuce tare da soma kimtsa kanta, saboda sam batason b’ata lokaci awajen d’auko Laylerh’n.

Acan gidan Aunty Zee kuwa, tunda suka dawo daga

makaranta.

Laylerh ta shiga d’aki ta kwanta, wani irin yanayi takejin kanta aciki na musamman, tun kuma k’iran wayarta da akayi takejin hakan, Yayinda kuma takejin wani sashi na zuciyarta yayi mata nauyi.

Lumsassun idanunta dake bayyana gaskiyar abun

da ke cikin zuciyarta ta bud’e ahankali, tare dasa hannunta ta d’auko wayarta dake ajiye asaman bedside drawer, touching screen d’in wayar nata tayi, Kamar kuma yanda ta saba, always shine a mind d’inta, kome takeyi tunaninsa baya iya barin cikin zuciyarta

, hotonsa guda d’aya rak dake cikin wayar ta zubawa ido bata ko k’yaftawa.

Hak’ik’a zata iya rantsuwa cewar bata tab’a ganin wani me kya’un Yah Maleek d’innata ba, komai nasa dabanne, more expecially beautiful eyes d’insa da basu cika girma ba, har sai

idan shi d’inne ya waresu, ba komae ke d’aukan hankali atattare dasu ba kuwa face yanayin tsarin cikinsu, dake d’auke da black brown eye balls, sai kuma zara zaran lashes masu matuk’ar kyau da burgewa.

Ahankali ta shiga yawo da idanunta akan hoton nas

a, har dai ta kuma sauk’e ganinta akan lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa, wanda ya zauna sosai, ya kuma k’arawa fuskartasa kyau, Tabbas ko bashi da kyau, tayi imani cewa da wannan beard d’innasa kad’ai zai iya narkar da zuciya.

Asanyaye wani iri

n tattausan murmushi ya Bayyana akan fuskarta, murmushin da ita kanta batasan tayi sa ba, saidai kuma abu d’aya kawai ta yarda dashi, wanda akansa ko tantama baza tayi ba, shine shape d’in jajayen lips d’insa da nata iri d’aya ne, domin kuwa kamar yanda l

abb’an bakinta suke jajaye, haka shima nasa suke.

Still wani murmushin ta sakeyi, saidai kuma awannan karon harta hak’waranta saida suka bayyana.

Daidai lokacin kuwa Aleeya da tun d’azu ke tsaye abakin k’ofar shigowa d’akin tace.

“Har abada Lay

lerh, banajin akwai watarana da zata zo da zaisa, ki gaji da kallon hoton wannan balaraben yayan naki.

‿



Sauk’ar muryar Aleeya acikin kunnuwanta kuwa, shiya saka tayi saurin kifa wayar ta ta, tare da tashi zaune, anutse cikin kuma son kawae da maganan

Aleeya’n ta soma gyara wuyar rigar dake jikinta.

Aleeya kuwa murmushi tayi, batare kuma da ta k’arasa shigowa cikin d’akin ba tace.

“Oum Ayush tazo.

‿

Da sauri ta d’ago kai ta kalli Aleeya’n, cikin yanayin mamaki da kuma jin dad’i tace.

“Daga

ske kike? Please Aleeya banason wasa.

‿



Ayanzu kam Aleeya dariya tayi, saidai kuma kafun ma ta bawa Laylerh’n amsa, tuni harta Sauk’o daga kan gadon, cikin hanzari ta rab’a ta bayan Aleeya’n ta wuce.

Agarin sauri kuwa har k’afarta na hard’ewa, haka

ta k’araso cikin falon, ganin kuma Oum Ayush d’ince da gaske, yasa fari’ar fuskarta fad’ad’a ashagwab’e taje ta fad’a jikinta.

Oum Ayush kuwa murmushin jin dad’i tayi tare da sake rungume Laylerh’n, cike da kulawa tace.

“Nayi kewarki sosai Laylerh,

ya exam d’in fatan kun gama lafiya.

‿



Kai Laylerh’n ta jinjina mata, cikin kuma yanayinta na shagwab’a tace.

“Alhamdulillah exam yayi dad’i, nima nayi kewarku sosai Ina Abbou Khareem dina!

‿



Again murmushi Oum Ayush tayi, tare da cewa.

“Duk s

una lafiya, sune ma suka aikoni natafi dake, sunce hutunnaki ya isa haka, zaki bini mutafi ko?

‿



Kanta ta jinjina alaman “Eh.

‿

Domin Allah Yasani tayi matuk’ar kewar gidannasu, musamman Yah M.Jay d’inta, saboda har yanzu batasan cewar yayi tafiya zuwa U

SA ba.

K’arasowar Aunty Zee cikin falonne kuma yasa, hirar Laylerh da Oum Ayush d’in katsewa.

Bayan kuma Oum Ayush din Tasha drinks din dake gabanta ne ta shiga korawa Aunty Zee duk abunda ke faruwa, da kuma maganar tafiya da Laylerh da tazo yi.

Hakika Aunty Zee din taji babu dadi, domin abune da tasani cewar zatayi kewar Laylerh’n, amma kuma to ya ta iya.

Aleeya takira tare da bata umarnin taya Laylerh’n kimtsa kayanta, koda Aleeya taji cewa Laylerh’n tafiya zatayi, bataji dadi ba sam, musam

man ayanzu da take matuk’ar jin dad’in zama da Laylerh’n, akwai sabo me kyau sosae atsakaninsu.

Haka dai ta taya Laylerh’n duk suka had’e kayanta waje d’aya.

Koda suka tashi tafiya kuwa har bakin mota Aunty Zee da Aleeya suka rakasu, Yayinda Aunty Ze

e d’in tabawa Laylerh kyautuka masu yawa. Aleeya kuwa cewa tayi

‿

Insha Allah Zatana kawowa Laylerh’n ziyara.

‿

Da haka dai suka rabu cike da kewar juna.

Ko acikin Mota kuwa gaba d’aya Laylerh farincikinta ya kasa b’oyuwa, burinta ayanzu kuwa bai wuce

taga Yah M.Jay d’innata ba, saboda wani irin kewarsa takeji.

Oum Ayush dake driving ita kanta ta lura da hakan saidai batace komai ba.

Ahaka har suka iso bakin makeken estate d’innasu.

Horn d’aya kawae maigadi ya wangale musu makeken gate d’in, Oum

Ayush kuwa cike da k’warewa ta tura hancin motar nata ciki.

Kamar dai yanda ta saba ababban parking space d’in dake cikin gidan ta faka motar nata, bayan kuma ta gama daidaita parking d’in, Kusan atare suka fito daga cikin motar.

D’aya daga cikin

ma’aikatan da suke bawa flowers ruwa ne yazo ya d’auki jakar Laylerh’n, tare da nufar cikin gidan da shi.

Itakuwa Laylerh bayan Oum Ayush tabi, saidai kuma bai wuce taku hud’u tayi ba, ahankali ta juyar da kanta, tare da sauk’e idanunta akan part d’in

da ada yakasance nasu ita da Najeeb.

Wani irin abu mai kama da fad’uwar gaba da taji ya daki zuciyarta ne, yasa tayi saurin janye idanunta had’e da sunkuyar da kanta k’asa.

Daidai lokacin kuwa suka iso sashin Oum Ayush d’in.

Suna shiga ciki kuw

a Oum Ayush tace mata.

“taje tayi wanka, sannan kuma idan ta fito daga wankan taje Abbou Jaheed na k’iranta.

‿

Da “to.

‿

Kawae ta amsa, tare dajan trolleybag dinta kaitsaye ta wuce d’aya daga cikin 3bedrooms d’in dake cikin falon Oum Ayush d’in.

Tan

a shiga cikin d’akin kuwa ta soma rage kayan dake jikinta, tare da d’aukan wani towel marar nauyi ta d’aura ajikinta.

Cikin yanayin da takeyin komanta na nutsuwa, ta wuce toilet.

Wanka tayi sannan ta d’auro alwalan sallan la’asar.

Koda ta fito awan

kan, zip d’in trolleybag d’inta ta zuge, tare da zaro wata doguwar riga mai yanayin Kimono ta sanya ajikinta.

Zama tayi akan gado tare da d’auko wayarta, saidai kuma tunawa da tayi cewar Abbou Jaheed na k’iranta ne yasa tayi saurin mik’ewa tsaye.

Ru

bber hijab da kuma slipper mai kalan rigarta tasa, ahanzarce ta nufi sashin Abbou Jaheed d’in.

Saidai kuma tun fitowarta compound d’in gidan, ta ajiye idanunta akan sashin Maleek d’in, wanda aduk cikin gidan shine tsarinsa ya fita daban, had’uwarsa na m

usamman ne.

Bata kuma d’auke idanunta akan part d’in nasa ba kuwa, har saida taga ta iso, sashin Abbou Jaheed.

Ahankali

Ta tura k’ofar falon ta shiga bakinta d’auke da sallama.

Abbou Jaheed dake zaune akan lallausan Turkish sofa, yana me shan

fruit salad ne ya amsa mata, fuskarsa d’auke da murmushi’n Jin dad’in ganinta.

Ita d’inma murmushine kwance akan fuskarta, cikin kuma yanayi na d’an hanzari ta k’arasa shigowa cikin falon, anan gefen Abbou Jaheed d’in ta zauna, tare da gaishe sa.

Fu

ska asake ya amsa mata, tare da tambayarta Exam.

Da “Alhamdulillah!!

‿

Kawae ta amsa masa.

Shikuwa Abbou Jaheed ganin murmushi kwance akan fuskartane yasashi sake Jin wani irin dad’i acikin ransa, saboda yana matuk’ar son ganinta acikin farinciki.

Glass bowl na fruit salad d’in dake gabansa ya turo mata, tare dayi mata alama akan tasha.

Sam musu ba al’adarta bane, shiyasa bata iya ce masa a’a ba, duk da kuwa cewar bata jin yunwa amma haka ta daure tayi 3spoons na fruitsalad d’in.

Abbou Jahee

d kuwa gyara zamansa yayi, tare da tank’washe k’afafunsa, saboda maganar da yakeso suyi yau d’in ta banbanta dana kullum.

“Laylerh!!

‿

Ya k’ira sunanta cikin sanyi da kuma tausasa murya.

Amon muryarsa da taji ne kuma yasa ta d’ago kanta ahankali t

a kalleshi.

Lokaci d’aya kuma taji zuciyarta tayi rauni sosai, wanda kuma har saida hakan ya kasa b’uya.

Abbou Jaheed kuwa ayau so yakeyi yayiwa Laylerh’n magana, bawai amatsayin y’ar k’aninsa ba kawai, so yake yayi mata magana amatsayin y’ar daya ha

ifa ta cikinsa.

Saboda hakane ma ya d’anyi gyaran murya, cikin kuma yanayin da yasan cewa zata fahimce sa yace.

“Ayau zan miki magana amatsayina na Uba mahaifi, bawai mai rik’onki kawai ba, Ina kuma fatan zaki fahimce ni, Kamar dai yanda yake a add

inance idan aka saki mace yin Iddah ya hau kanta, har saidai idan yakasance Mijin daya aureta bai tab’a kusantarta ba, To fa wannannne Iddah bai hau kanta ba, Kamar dai ke, duk da cewar ada munyi tunanin cewa akwai Iddah akanki, saida Oum Ayush ta fayyace

mana komai kafun muka fahimci cewar Iddah bai hau kanki ba, Tabbas ako da yaushe Allah Yakan jarrabtar bawa da k’addarori kala kala, wasu masu wuyar d’auka da kuma jurewa, saidai kuma hakan bawai yana nufin cewa Allah Ba yason bawannasa bane, bansan me y

asa k’addara ke wasa da rayuwarku ba Laylerh, amma inaji ajikina cewar Insha Allah Watarana zaku samu farinciki....

‿

D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, tare da sakin wata irin nannuayar ajiyar zuciya, wanda hakan ya faru ne kuma saboda tuna d’ansa Ma

leek da yayi.

K’warae yana matuk’ar jin tausayin Maleek d’in wanda tun tasowarsa ba abunda ya sani sai dai neman cimma muradin rayuwa.

Shiru gaba d’aya falon ya d’auka, almost 5mn kafun ya iya tattaro kwarin guiwarsa.

Cikin kuma hikima irin tasu ta m

anya yace.

“Ada ina wani tunani akanki na daban, wanda batare dana tambayi shawarki ba har na yanke hukunci, inda na yanke cewar zan turaki syprus kije kiyi karatunki acan, saidai kuma kamar yanda Oum Ayush ta fad’a lallai ne ya kamata aji daga gareki

, ya kamata kuma abaki zab’i, wannan rayuwarki ce Laylerh, ayau akuma karon farko na baki zab’i, domin y’ancin kine, duk da bansaniba ko akwai wanda zuciyarki keso, saboda haka zab’i biyu kike dashi ayanzu, ko tafiyarki k’asar Syprus ko kuma baki daman sak

e kawo wani Mijin da zuciyarki keso, matuk’ar kina ga auren shine abu mafi sauki agareki, ba kuma zan tsauwala miki ba agame da hakan!!!

‿

Hannunta tasa ahankali ta share gumin daya keto mata, lokaci d’aya kuma taji zuciyarta na wani irin bugawa tamkar z

ata faso k’irjinta ta fito.

Tabbas ita kanta batasan cewar tana da wannan raunin ba sai ayau.

Idanununta da suka ciko da k’walla ta rumtse, tare da soma murza y’an y’atsun hannunta.

Shin tayaya zata iya zab’an wata rayuwa?

Tayaya ma zata so n

esanta kanta?

Ko kad’an batajin zata iya, domin aikata hakan tamkar cutar da kanta ne, yaya zatayi da Rauninsa dake damu da kuma sake cika zuciyarta akullum?

Wace macece zata karb’esa saboda Allah?

Koda sau d’aya tana son ganinta atare dashi.

Tabba

s ayau zata fad’i duk wani abunda ke cikin zuciyarta, duk da kasancewar maganganun nata suna da nauyi sosai, amma Lallai ayau bazata iya dakatar da zuciyarta da akullum taje azabtuwa ba.

Zafafan hawayene suka sauk’a akan fuskarta, cikin kuma muryarta d

ake matsanancin rawa tace.....

“Yah Maleek Idan natafi wazai kula dashi? Kullum bayacin abinci, sannan koda yaushe haka yake tafiyar da rayuwarsa, babu farinciki acikinta, nakuma yi imani cewa har I yanzu baya cikin farinciki, saboda acikin zuciyata n

akejin duk wani ciwo da kuma damuwarsa, waye zai basa farinciki? Koda sau daya ne kawai Abbou Jaheed inason ganin Yah M.Jay acikin farinciki, saboda haka na zab’i zama dashi fiye da kowa da komai, na sadaukar da duk wani farinciki na agaresa, bandamu Akan

kowacce irin lalurarsa ba, abunda dai kawai nasani shine zan zauna dashi ahaka, zan rayu dashi, zan kuma jure duk wata damuwarsa, sannan kuma nayi imani cewa kowacce irin K’addara mai kyau ko akasinta Allah Shiya tsara mana!!!

‿

*21/3/2021*

3/23/21, 9

:14 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Not editing*

*Chapter 71*

Idanu Abbou Jaheed ya zuba mata, Yayinda fuskarsa ke bayyana zalla da kuma tarin mamakin daya samu kansa aciki, sam koda wasa bai tab’a tunanin ce

wa akwai watarana da Laylerh’n zata zo gareshi da irin wannan maganan ba.

Wani irin raunin kuma daya lullub’e zuciyarsa ne yasa, take hawaye suka cika idanunsa.

Sam kwata kwata ma bayajin hakan zaiyiwu, tayaya zai d’auki Laylerh ya bawa Maleek dake

d’auke da lalura? tayaya zai jefa rayuwar yarinya marainiya acikin k’addarar d’ansa?

Kansa ya d’an soma girgizawa, tare kuma da danne abunda ke cinsa acikin zuciyarsa, cikin wata irin muryar da takasa b’oye rauninsa yace.

“Hakan bazai yiwu ba Layl

erh, abunda kike fad’a ayanzu wani abune da yake karkatacce, na kuma san ba komaine ke d’ibanki ba, illa k’uruciya da kuma raunin zuciya, tayaya kike son sa kanki acikin k’addarar Maleek? k’addarar da ta zame masa tamkar tabo acikin rayuwarsa, tayaya kike

son tursasa zuciyarki akan auren Namijin da likitoti suka tabbatar da cewar bazai haihu ba, meyasa Laylerh? Meyasa kikeson kasancewa ahaka? Meyasa kikeson takurawa rayuwarki? Kada kice zaki rungumi k’addarar da bata zamo dolenki ba, domin kuwa ko ba komai

ke MACE ce, dole kina da hope anan gaba, saboda haka zaifi kyau kitsarawa kanki rayuwar da zata zama cikinta akwai d’orewar farinciki...

‿

“Babu wani farinciki aduk wata rayuwar da babu sadaukarwa, sannan babu ingantacciyar farinciki ga wanda yasan kans

a, matuk’ar har kullum zaiga d’an uwansa acikin damuwa, sai yaushe ne wanda yake cikin k’unci zaibar k’unci? Sai yaushe ne K’addarar sa zata yaye? Yaushe zai samu farinciki kamar yanda mafi yawan cin mutane ke samu? Wacece zata zauna dashi, ta sakashi murm

ushi, sannan kuma ta cire masa k’uncinsa? Wacece zata zauna dashi batare da ta cutar dashi ba? Saboda k’addarar da ta samesa kawai nefa, yasa aka janye maganar aurensa, bayan kuma kowa yasan cewa ba akansa aka fara halittar wannan k’addarar ba, sam banaso

Abbou Jaheed, banason watarana Yah M.Jay yaji ajikinsa cewar shid’in mai yankakken farinciki ne, ba kuma nason ya fara Jin cewar shi mai nakas

a ne, bana fatan wannan ranan, ranan da zaiji tamkar bashi da kowa, Tabbas bana fatan zuwanta, akullum akuma koda

yaushe zanso ganin k’arfafawarsa, babu wanda yasan me yakeji, akoda yaushe shi kad’ai yake shanye duk wata damuwarsa, koda kuwa damuwar tasa takai girman da zata iya tar watsa zuciya!!!

‿

Idanunta dake tsiyayar da hawaye ta bud’e, wanda suka rikid’e suk

a zama jajur.

Gaba d’aya jikinta kuwa b’ari yake, wanda kuma hakan yasamo asaline saboda yanda wani irin azababben kuka me sauti keson k’wace mata.

A karon farko na gaba d’aya rayuwarta, da taji bazata tab’a iya b’oye abunda ke cikin zuciyarta ba, hasa

lima ganin Abbou Jaheed d’in take tamkar mahaifinta Abbou Mahmoud ne zaune agabanta.

Ahankali ta d’an matso kusa da Abbou Jaheed d’in, hannayensa duka biyu ta rik’o, cikin wani irin matsanancin kukan daya k’wace mata ta shiga girgiza masa kai, murya Am

atuk’ar raunane tace.

“Dan Allah Abbou! Zan rayu dashi dakowacce irin k’addara koda kuwa tafi wanda ta sameshi ayanzu muni, zan zauna dashi koda ace shid’in Majanuni ne, lokuta da yawa danshi kawai nakeyin rayuwa, tun Ina k’arama shine yake kokarin zam

e min Garkuwa, ga kowanni d’an Adam jinin mahaifansa ne ke gudana acikin jikinsa, amma ni acikin jikina jinin Yah Maleek ne, shine komai nawa, shine wanda bayason yaga nayi kuka, shine kuma mutum na farko da yake fara bani abinci akowacce rana, shine wanda

yake sanin kowacce irin damuwa ta, ba kuma zan tab’a mantawa da hakan ba har abada, domin abayan kowani bugun zuciya da numfashinsa al’amura nane, shine wanda ya fara koyamin yanda zanyi rayuwa, komai nasani aduniyar nan ta dalilinsa ne, tun Ina da shekar

u 2 har izuwa 12 shi kawai

nasani acikin rayuwata, har iyanzu ma shid’in kawai nasani....

‿

Wani irin kuka maitsanin sauti daya ci k’arfinta ne kuma yasa ta kasa k’arasa maganganun nata, kanta ta kifa da jikin kujera ta shiga rera wani irin kukan, dake b

ayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarta.

Sannan kuma kukane dake nuna tsananin Rauninta akan Maleek, kukan da yayi matuk’ar tab’a zuciyar Abbou Jaheed.

Wanda har saida yayi sanadiyar hawayen dake kwance acikin idanunsa, suka gangaro kan fuskarsa.

Domin shikansa yayi imani acikin kalaman da Laylerh’n ta fad’a sam babu k’arya, ko waye zai sota bayan soyayyar da Maleek ya nuna mata ne, kasancewar abune da ke abayyane, duk wani wanda yasan su acan baya, to tabbas zai shaida cewar Maleek yamafi son Lay

lerh’n akan kansa.

Lallai ayau ya yarda cewa su duka biyun suna rayuwa ne akan abunda ko wannensu yake so, Muradi fata da kuma burinsu duk iri d’ayane, Laylerh ce fatan Maleek haka ma, Laylerh’n Maleek ne fatan ta.

Kuma Tabbas ita kad’aice macen da za

ta iya zama da Maleek d’in koda kuwa munin k’addararsa ta zarce misali, hak’ik’a ayanzu kam bashi da bakin dakatar da faruwar komai, domin ya riga ya fahimci abunda Allah Yayi ikonsa akai babu wanda ya isa hanawa.

Duk da cewar kuwa Auren Maleek d’in zai z

ama tamkar k’alubale ne agareta, Duk da cewar kuma ba shine mahaifinta ba, amma bazae tab’a so ace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login