Showing 156001 words to 159000 words out of 244674 words

Chapter 53 - LAYLERH MALEEK COMPLETE

ta yafa ajiki

nta, wanda ya tsaya daga wuyanta zuwa cinyoyinta, kasancewar kuma d’an kwalin kayannata babbane yasa ta d’aurashi akanta irin d’aurin nan da ake parking d’insa a tsakiyar kai, sosai kuwa d’aurin ya sake fito da kyaun da tayi, wani cool parfume me dad’in k’

amshi ta fesa, batare kuma da ta sake kallon madubi ba ta zura wasu new designer half cover shoe ak’afanta kai tsaye ta fice daga cikin d’akin.

Direct sashin Oum Ayush ta nufa koda ta k’arasa part d’in Oum Ayush d’in kuwa ta samu harta kammala had’a abin

cin da zasu kai asibitin, yayinda Fou’ad kuwa tuni ma ya koma asibitin.

Ganin Laylerh’n ne kuma yasa Oum Ayush d’auko mayafinta, domin dama itama already ta shirya don komawa asibitin.

D’aya daga cikin basket d’in da food flask d’in abincin ke ciki Layle

rh’n ta d’auka, yayinda Oum Ayush kuma ta d’auki sauran.

Kusan atare suka fito daga cikin sashin na Oum Ayush d’in tana me tambayanta.

“Ya ciwon kannata?.

‿

“Da sauk’i.

‿

Ta bawa Oum Ayush d’in amsa adaidai lokacin da suka iso bakin motar Oum Ayush d’in.

Kamar dae yanda suka tafi d’azu haka yanzun ma Oum Ayush da kanta tayi driving.

Tunda suka d’auki hanyar asibitin kuwa Laylerh keta faman sak’awa da kuncewa, yayinda acikin zuciyarta take fata da kuma burin idan taje ta samu Maleek d’in ya farfad’o, domi

n kuwa tasan akasin hakan zai k’ara sata acikin wani sabuwar fargaba da kuma fad’uwar gaba.

Isowarsu cikin asibitin kuwa yayi daidai da isowar Alhaji Farouk da kuma Ilayansa wato Hajiya Buzuwa da kuma Munnira wanda take matsayin amarya, duk da kuwa cewar

asibiti suka zo amma fuskarnan tata ayalwace take da meckup yayinda kuma kallo d’aya kawae zakayi mata ka fahimci cewa, cike take da yauk’i.

Kasancewar kuma motarsu ce agaba yasa sam basu lura da ta su Laylerh’n ba, suna gama daidaita parking kuwa suka fi

to direct suka nufi cikin asibitin.

Su kuwa su Laylerh sam basu ma lura dasu ba, domin saida su Munnira’n suka wuce kafun su Laylerh suka fito daga cikin motar ita da Oum Ayush.

Hannayensu d’auke da basket suka nufi sashin da aka kwantar da Maleek d’in.

Daf da zasu haura steps d’in da zai sadasu da d’akin Maleek d’inne kuma bisa tsautsayi Laylerh tayi missing d’aya daga cikin steps d’in take kuwa tatafi su ta fad’i k’asa.

Wanda hakan yayi sanadiyar zubewar gaba d’aya kayan dake hannunta, fad’uwan da tay

inne kuma yasa ta saki wani irin k’ara, saboda ta d’an bugu kad’an ahannunta.

Adaidai lokacin kuwa zuciyar da bugawanta ke tafiya slowly tayi wani irin harbawa, har saida gangar jikin mamallakin zuciyar nan ta samu motsawa.

*(Bani da enough charge sh

iyasa na muku wannan kud’an rage lokaci kafun gobe Idan Allah Ya kaimu.

Shin me kuke tunani akan Maleek? Idan Alhaji Farouk yaji matsala da kuma lalurarsa zai bashi auren yarsa? koma me Insha Allah Zakujishi a page d’in gobe.)*

*9:10 pm*

2/19/21, 9:36

PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*

fatymasardauna

*Not editing*

*Chapter 54*

K’ara da kuma ganin fad’uwar da Laylerh’n tayi ne yasa Oum Ayush da ta wuce gaba tayi saurin juyowa tare da d’an dawowa baya.

Hannunta tasa ta kamo

hannun Laylerh’n wanda ta d’an yunk’ura ta tashi tsaye.

“Subahanallah sannu Allah Yasa bakiji ciwo ba?.

‿

Oum Ayush ta tambaya tana me mik’ar da Laylerh’n tsaye.

Fuska ta b’ata tare da marairaice idanunta wanda tuni suka ciko da hawaye, d’aya hannunta da

ta fad’i akai ta rik’e, wanda asanadin hakan yasa hannun nata ya d’an kuje har da jini, ganin jinin da tayi ne kuma yasa ta langwab’ar da fuska, ashagwab’e tace.

“Nabuge Oum Ayush hannuna zafi yakemin.

‿

Kallon hannun nata Oum Ayush tayi, ai kuwa gashi k

ujewan har ya d’an fara fitar da jini, kasancewarta farar fata ne kuma yasa take wajen yayi jajur dashi.

“Ya Ilahi tabbas kinji ciwo gashi harma da jini, sannu ko bari nak’ira ko da nurse ce ta d’an miki treating wajen.

‿

Oum Ayush ta fad’i hakan cikin ku

lawa tare da d’an soma rarraba idanunta a sonta wai ko zataga nurses d’in hospital d’in.

Cikin sa’a kuwa saiga wata nurse ta fito daga cikin wani d’aki.

Da sauri Oum Ayush d’in ta k’arasa ta k’ira nurse d’in, cikin kulawa kuwa nurse d’in tazo wanda tun k

afun ma Oum Ayush ta gama yi mata bayanin kujewan da Laylerh’n tayi, har idanunta sun sauk’a akai, saboda yanda Laylerh keta faman yayarfa hannun harda kuwa acikin idanunta, wanda kuma bawai k’wallan na zafin ciwon bane kawae, tsantsar sakalcine kawae yake

damunta.

Hannun Laylerh’n nurse d’in ta kamo, kana cikin kulawa tace.

“Ayyah Sorry baby girl muje ko na d’anyi miki treating wajen, yana miki zafi sosai ne?

‿

Sake shagwab’e fuskarta tayi, musamman ma da taji nurse d’in tace zatayi mata treating wajen,

tasan dole acikin biyu sai anyi d’aya, dole ne ma sai sun wanke mata wajen, takuma san cewa ba k’aramin zafi zataji ba.

D’an k’aramin bakinta ta turo gaba cikin d’ari d’ari da kuma tsoro tace.

“Bayamin zafi sosai, nasan ma da kansa zai warke basai an wan

ke ba.

‿

Idanu nurse d’in ta d’an zaro cikin d’an mamaki tace.

“Abarki ahaka kenan kije ciwon yata miki zafi, tun yana k’arami har ya dawo babba?.

‿

Kai ta sunkuyar k’asa tare da soma mamul mamul da bakinta.

“Please nurse karki biye mata kuje ki wanke ma

ta, idan angama treating wajen sai kizo ki sameni ad’akin da aka kwantar da Maleek d’in, mun gode sosae nurse.

‿

Oum Ayush ta fad’i hakan tana me tattare kayayyakin abincin da Laylerh’n ta watsar, kuma cikin ikon Allah Ba abunda ya zube acikinsu.

Jin ab

unda Oum Ayush d’in ta fad’ane yasa nurse d’in kama hannun Laylerh wanda tuni hawaye har sun wanke mata fuska, suka nufi wani sashi na daban.

Oum Ayush kuwa kaitsaye d’akin da aka kwantar da Maleek d’in ta nufa.

Hak’ik’a bugawan da zuciyarsa tayi da k’

arfi shiya haifar masa da motsawan gangan jikinsa, cikin abunda baiwuce 12minute ba kuwa numfashinsa ya dawo, wanda kuma hakan shi ya sake daidaitawa wajen taimakawa bugun zuciyartasa ya zama tana tafiya adaidai yanda ya kamata.

Ahankali yakejin kansa na

wani irin juyawa, tamkar wanda ake wainasa.

Wannan dalilin yasa shi soma motsa y’an yatsun hannunsa da kuma na k’afarsa, Take kuma ahankali ya soma bud’e idanunsa wanda suka d’an k’ank’ance kad’an.

Sauk’e ganinsa yayi asaman d’akin da yake ganin rufins

a dishi dishi, yayinda yakejin kansa na wani irin sarawa.

Ahankali ya maida idanun nasa ya lumshe, domin koda ya bud’esu bai fahimci a ina yake ba, saboda dishi dishi yake gani.

Sannu ahankali abubuwan da suka faru dashi na accident d’in suka shiga dawow

a cikin kansa filla filla, har saida komai da ya faru ya gama dawowa cikin tunaninsa kafun ya sake bud’e idanunsa akaro na biyu, cikin sa’a kuwa ko kad’an wannan karon idanunnasa basu nuna masa dishi dishin ba, rass yake gani bawani yana ko gizo.

Wata iri

n nunmfashin da ya fusgane kuma yasa gaba d’aya hankalin su Abbou Jaheed ya dawo kansa, ganin idanunsa a bud’e ne yasa su Abbou Jaheed d’in saurin k’arasawa inda yake kwance.

“Maleek! Maleek!! ka farfad’o ka bud’e idanunka Alhamdulillah!!!

‿

Abbou Jaheed

ya fad’a cikin yanayi na d’an rud’ewa da kuma farinciki.

Kamar amafarki kuwa haka yaji muryar Abbou’n nasa hakanne kuma yasashi d’an juyowa ya kalli inda Abbou Jaheed da kuma Abbou Khareem ke tsaye.

Idanu ya d’an k’ura musu na y’an wasu sakanni kafun

ahankali ya d’an soma yunk’urin tashi.

Da sauri Abbou Jaheed yasa hannayensa duka biyu ya soma k’ok’arin d’ago Maleek d’in fuskarsa d’auke da matsanancin farinciki.

Maleek kuwa dake k’ok’arin tashi idanunsa ya rumtse da k’arfi sakamakon wani azababben za

fin da yaji acikin mararsa, wanda har saida yasa ya kasa hak’uri saida yasa teeth ya datse lips d’insa.

Ganin hakanne kuwa yasa Abbou Jaheed cike da matsanancin tausayin sa yace.

“Sannu ko Maleek, bari ak’ira Dr. yazo ya dubaka.

‿

Aikuwa ko rufe baki Abb

ou Jaheed d’in baiyiba Dr.Mouhammad ya turo k’ofar d’akin ya shigo, bayansa kuwa su Alhaji Farouk ne.

Ganin Maleek d’in azaunene yasa Dr.Mouhammad had’iye sallaman da yake k’ok’arin yi cikin hanzari ya k’araso jikin gadon, hannunsa d’aya yasa ya dafa kafa

d’an Maleek d’in fuskarsa d’auke da yalwataccen murmushi yace.

“Alhamdulillah naji dad’i matuk’a dana ga ka farfad’o har kuma kana iya zama, yanzu Ina da inane keyi maka ciwo?.

‿

Dr.Mouhammad d’in ya k’are maganan yana me d’an tattab’a jikin Maleek d’in.

Idanunsa dake alumshe ya bud’e cikin yanayin kasala da kuma rashin kuzarin daya samu kansa aciki yayiwa Dr. Mouhammad d’in nuni da kansa da kuma mararsa.

D’an Jim Dr. Mouhammad d’in yayi tare da sauk’e ajiyar zuciya, cikin yanayin tausayawa yace.

“Don’t

worrie zasu daina ciwo Insha Allah, burinmu mu dama shine ka samu dawowa hayyacinka, akwai magungunan da zan baka dakasha komai zai zama normal da Yardar Allah, bari naje na kawosu.

‿

Cikin sauri Dr. Mouhammad ya juya ya fice daga cikin d’akin, matsawarsa

daga kusa da Maleek d’inne kuma yabawa su Alhaji Farouk wanda suke gaisawa dasu Abbou Jaheed daman sauk’e idanunsu akansa, ciki kuwa harda Munnira da ganinsa haka babu riga yasa ta k’ara tabbatarwa da kanta cewar ashe ma duk yanda take ganin had’uwarsa ya

wuce haka.

Take kuwa taji wani irin abu na musamman akansa, har saida taji kaman taje ta fad’a jikinsa ahaka.

Kyawawan red lips d’insa masu shining ta kalla, wanda kuma bisa dole kallonsu yasa ta had’iyi wani yawu, idanunta ta d’an lumshe cikin k’asa da

murya ta yanda ba maijinta acikinsu tace.

“Wow hot and handsome guy, gaskiya wannan man d’in komai nasa is so special, tayaya ma zan fara imagine duniyar da zaikaini idan munyi aure?.

‿

Wani murmushine ya sub’uce mata, sakamakon imani da tayi cewa, irin s

ane suke shid’ar da mace, su sata manta kowa da komai.

Sake bud’e idanunta tayi tare da soma yawo da idanun nata akansa, Lallai dan mahaifiyarta ta gargad’etane kafun su taho, amma bayan haka da babu abunda zai hana ta zuwa tayi hugging d’insa, koda kuwa

sau d’aya ne tanaso taji ni’imar jikinsa wanda aka horasa da Gym, duk da cewar jikinnasa bawai ko ina bane yake amurd’e damatsan hannayensa ne kawae, sai kuma lafiyayyun six packs d’in dake kwance akan cikinsa.

K’arasawa jikin gadon Alhaji Farouk yayi,

cikin yanayin tausayawa kuwa yayiwa Maleek d’in ya jiki.

Kansa kawai ya jinjina alaman da sauk’i tare da maida idanunsa ya lumshe, domin kuwa tun farfad’owarsa baiyi magana da kowa ba, komai kallonsa kawae yake da ido.

Koda Buzuwa ma ta yi masa ya jiki

da kuma Allah Ya tsare na gaba, ita d’inma dakai ya amsa mata.

Munnira kuwa tsayawa tayi tana kallonsa baki da hanci takasa yi masa koda ya jikinne ma, abu d’aya kawae tun sauk’e idanunta akansa taketa imagine shine wae ita Allah ya bawa wannan daman na z

amowa matar, d’aya daga cikin mazan da irinsu basu da yawa aduniya, lallai Allah Ya had’a ta da babban rabo.

Shikuwa Maleek sam baimasan da wata wai Munnira awajen ba, domin kuwa ko gefen da take idanunsa basu kalla ba, hasali shi yama manta da ita dama k

amanninta gaba d’aya.

Fitan Dr.Mouhammad kuwa bai wuce da mintuna 10 ba sai gashi ya shigo, yayinda Oum Ayush ke biye dashi, wanda hannunta ke d’auke da basket d’in abinci.

Shigowarsu ne kuma yasa su Buzuwa suka dawo da kallonsu ga Oum Ayush d’in, ciki

kuwa harda Maleek.

Oum Ayush kuwa ganin Maleek d’in ya farfad’o da kuma arba da surukan su da tayi ne yasa murmushi da fari’a suka bayyana akan fuskarta, cikin kulawa tayi musu sannu da zuwa, fuska ba yabo ba fallasa Buzuwa ta amsa, tare da soma yiwa Oum

Ayush d’in kallon k’urulla musamman da ta sauk’e idanunta akan lace d’in dake jikin Oum Ayush d’in wanda ak’alla kud’insa yakai 100k, irin dai lace d’innan ne wanda matan shugaban k’asa ko kuma manyan k’usoshin gwammanati ke sawa.

“Lallai akwai kud’i awa

nnan family’n.

‿

Buzuwan ta fad’a acikin ranta, tare da soma hasashen yanda zata samu daman k’ulla alak’a da Oum Ayush d’in duk dama bataji matar ta kwanta mata arai ba, amma zata daure su k’ulla alak’a kodan fahimtar da tayi cewa, Oum Ayush d’in y’ar fash

ion ce sannan kuma akwai naira da had’uwa.

Oum Ayush kuwa bama takan Buzuwan take ba, basket d’in dake hannunta ta ajiye, tare da k’arasawa wajen Maleek d’in fuskarta d’auke da murmushi tace.

“Masha Allah Maleek lafiya tasamu kenan, Allah Abun godiya ya

jikinnaka?.

‿

Murmushin daya d’an bayyana secret dimple d’insa yayi, tare da lumshe idanunsa, akasalance ya jinjina mata kai alaman “Da sauk’i.

‿

Acikin zuciyarsa kuwa sunan Layleh ya k’ira, tare kuma da tambayan kansa cewar Ina take, wani irin azalzala ya

keji acikin zuciyarsa, ita kawae yakeson ya fara gani ayanzun, yunwa da k’ishin ruwanta yakeji, tabbas yasan kuma rashin ganinta awajen shi ya k’ara haifar masa da kasala, yayinda sam ajikinsa bayajin komai waidan yayi tunanin Laylerh’n kasancewarta matar

wani, domin yasan hakan k’addararsa ne, duk da cewar kuma yasan tunaninta haramunne agaresa, amma baya tunanin akwai wani second na cikin rayuwarsa dazai wuce batare da tunanin Laylerh’n ba.

Wata allura da Dr. Mouhammad ya tsikara masa akan jijiyan hannun

sa ne, ya sashi d’an bud’e idanunsa.

Kallonsa Dr. Mouhammad yayi kana anutse yace.

“Ya kamata kasawa cikinka abinci koda tea ne ka samu kasha, idan yaso bayan kaci abinci sai kasha way’annan magungunan Dan sune zasu taimaka k’warai wajen rage maka ciwo

n da kakeji amararka da kuma kanka, please ka daure kashasu saboda pain relievers ne masu kyau.

‿



Kamar ko yaushe kansa kawai ya jinjinawa Dr. Mouhamad d’in, tare kuma da maida idanunsa ya rufe.

Dr.Mouhammad kuwa juyawa yayi ya fice daga cikin d’akin.

H

akan kuwa shi

Ya bawa Munnira daman matsowa kusa da Maleek d’in, cikin yauk’i da kuma siranta murya had’i dason jawo hankalinsa gareta tace.

“I’am sorry Dear ya jikin naka?

‿

Bak’uwar muryar da yaji akusa dashi ne yasashi d’an bud’e idanunsa tare da sauk

’e ganinsa akanta.

Kallo d’aya kawae yayi mata ya watsar, acikin zuciyarsa yace.

“Tsinken sigari ta sake biyoni Yah Allah Kanesantani da wannan babyn roban, because I hate her.

‿



Ita kuwa Munnira ganin baice da ita komai bane yasa tasake matsawa kusa

dashi, tare da soma yin magana k’asa k’asa.

Oum Ayush dake kallon yarinyar da wai itace zata auri Maleek d’in ajiyar zuciya ta sauk’e tare da d’auke kanta, itakam bata d’auka irin zab’in da Abbou Jaheed yayiwa Maleek d’in kenan ba.

Sam yarinyar bata ma

ta ba, because daga ganinta bata da kunya, irin fand’ararrun y’an matan nanne marassa kamun kai.

Food flask d’in da ta shigo dashi ta jawo tare da d’aukan plate ta soma k’ok’arin zubawa Maleek d’in abinci aciki.

K’aran turomin k’ofar d’akin da akayine

yasa gaba d’aya duk suka maida idanunsu ga jikin k’ofar.

Ciki kuwa harda Maleek da hakanan turo k’ofar d’akin da akayi yasa zuciyarsa soma bugawa da k’arfi.

Kyawawan fararen k’afafunta wanda suke sanye cikin half cover shoe ta fara sakowa cikin d’akin, k

afun daga bisani sauran gangar jikinta suka shigo, hannunta na damane ke rik’e dana hagu, wanda kuma shine ke d’auke da ciwon da akayi treating d’insa, akasa masa magani da kuma auduga, bisa umarnin wannan nurse d’ince kuma yasa tasaka y’ar yatsarta ta dan

ne audugan kada ya fad’i, domin kasancewar ciwon nata bawani babba bane yasa ba’a saka fulasta an suturceshi ba.

Tabbas shigowarta cikin d’akin ya haifar da bugawar zuciyar wasu, saidai kuma amma bugawa ne ma banbanta.

Yayinda bugawar zuciyar Maleek t

a zama ta musamman dana sauran.

Ahankali ta d’ago idanunta daga kallon ciwon nata da take, tare da d’ago gaba d’aya kanta, wanda hakan yasa cikin yanayin bazata ta sauk’e ganinta akansa.

Kyawawan idanunta dake d’auke da danshin hawaye ta zaro waje, cik

e da alamun mamakin ganinsa da tayi azaune.

Lokaci guda kuwa taji wani irin sanyi na ratsa cikin tafin k’afanta har izuwa duka gangar jikinta.

Wani abu me kama da matsanancin farinciki ne ya lullub’e duk zuciyarta, wanda har hakan yasa idanunta sake cik

a tab da k’walla.

Sam ba zata iya jurewa kallon da sukeyi juna ba, domin kuwa kallone dake shigar da sak’onni kala kala wa gangar jikinsu.

Haka zalika kallone dake rura watar abunda ke cin zuciyarta.

Tabbas tayi imani cewa da ace daga ita saishi ne ad’a

kin to tabbas da babu abunda zai hana bataje ta fad’a jikinsa ba.

Kanta ta sunkuyar k’asa tare kuma da kasa koda motsa k’afartane, asanyaye ta had’e y’an yatsunta tare da soma jujjuyasu.

Shima akaron farko kenan daya janye idanunsa daga gareta, domin k

uwa ad’an kallon sakannin da ya mata shi kad’ai yasan me yaji, inama da ace yau ita d’in takasance matarsa, tabbas da ajikinta zai kasance domin hakan ba k’aramin cire masa radad’i zaiyi ba.

Bayansa ya jingina da jikin bango had’e da lumshe kasalallun id

anunsa.

Munnira dake gefensa kuwa wani irin bugawa zuciyarta keyi asakamakon ganin Laylerh’n da tayi, tabbas bazata manta fuskar Laylerh’n ba domin ta tab’a ganinta sau d’aya, saidai kuma amma alokacin Laylerh’n bata kai haka girma ba.

K’warae ganin La

ylerh’n ya tayar mata da hankali, tare da jin wani irin matsanancin kishin Laylerh’n da Allah Yayiwa baiwar kyau da kuma kyawun halitta, wanda asanadin hakanne kuma yasa duk taji ta muzanta, saita ji cewar ita ba komai bace a had’uwa.

Ae kuwa baga Munnira

kad’ai ba harga Buzuwa ganin da tayiwa Laylerh yasa taji gabanta ya fad’i, domin kuwa ko za’a had’a sama da k’asa akwai tazara da kuma banbanci me masifar yawa atsakanin Laylerh’n da kuma y’arta Munnira, nesa ba kusa ba Laylerh tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login