Showing 1 words to 3000 words out of 259716 words

Chapter 1 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

2

Bismillahirrahmanirrahim

MANNUBIYA

(Book 2)

Page 01

Na

Humayrah Bulama

Daga k’ungiyar Mikiya Writers Association.

Sai da aka fara kiraye kirayen assalatu tukunna da taimakon shed’an Yassir ya samu wani bacci mai

d’an karen dad’i ya kwashesa.

Ba dan ya saka alarm d’in 7:30 ba da ba zai ga fitar Yashjub d’in da ya shiryawa gani ba.

Alarm d’in yana fara k’ara ya farka dan bashi da wani nauyin bacci dama, da sauri ya d’auki wayar sa ya kalla ya kashe alarm d’in k

afin ya ajjiye ta tukunna ya fad’a toilet…fitsari ya fara yi kafin yayi brush sannan ya fito ya k’arasa jikin windown d’akin ya tsaya.

Sai da ya yi kusan 2 minute a tsaye tukunna Yashjub ya fito..tabbas Yassir ya ji babu dadi a lokacin da yaga Yashjub y

a kira driver ya basa makullin motar yace ya tuk’asa su je,da alamun aiki ne a gabanshi birjik dan suna shiga yaga ya baza takardu da computer ya duk’ufa aiki a nan doguwar kujerar bayan inda ya shiga ya zauna.

D’aga kafad’a Yassir yayi ya d’an tab’e ba

ki a ransa yace’’Atleast ka samu Abokin mutuwa’’

Sai da ya ga fitar su tukunna ya koma cikin d’akin ya d’auki airpod d’in sa ya mak’ala a kunne ya kunna kid’a a wayarshi.Wani d’an labule ya d’aga ata gefe guda chan kusurwar d’akin

kayan motsa jikinsa su

ka baiyyana

tsaki yayi a ranshi yace

‘’Wajen motsa jiki sai kace d’akin b’era!i can’t wait ayi ayi a gama min ginin chan in tartara in koma gidana nima,

I feel suffocated in here!’’.

Daga haka ya fara motsa jikin nasa

ya d’an jima dan a k’alla yayi

30 minutes yana abu d’aya tukunna ya fad’a toilet don ya samu ya watsa ruwa

ko wacce b’ular gashi dake a jikinshi tana mai tsatstsafo da zufa.A band’akin ma sai da ya kwashe sama da mintuna ashirin tukunna ya fito ya shiga goge goge da shafe shafe da

feshe feshe,tukunna ya d’auki wasu had’ad’d’u kuma tsadaddun suite masu masifar kyau ya sanyawa jikinsa.

Tsaff ya shirya ya fito tas da shi,ya kuwa yi kyau,longsleeve d’in sa ce kawai fara amma hatta takalminsa da belt da links duk komai bak’ak’e ne.

A

gaban madubi ya tsaya yana taje sumar sa wacce takenan tsaf da ita sannan a cike taff bak’ak’irin babu alamar sank’o

ga wani had’ad’den gyaran fuska da ya sha wanda ya tafi

da tsararren sajen sa da gashin baki had’i da d’an tudun gemunshi,kana ganin su

mar tasa kaga ta asalin Bahaushe

amman tsabar kud’i da gyaran da take sha yasanya har wani shek’i sumar takeyi mai tsananin kyau da d’aukar hankali.

Kallon kansa yayi a gaban madubi ya sake,tabbas ya san yana da kyau!son kowa k’in wadda ta rasa, a yad

da yake da kyan nan Wallahi mace ko da kud’in ta sai da rabon ta,amman wai dukda haka kalli yadda Kausar take gara sa itama wachchar shegiyar Munirat d’in sai wani kakkaucewa takeyi ta k’i ta bada had’in kai ayi a wuce gurin!wallahi ba dan ya kwallafa rai

a kanta ba da tuni ya watsar da lamarin ta….

Yana cikin wannan tunanin ya fara jiyo hayaniya a nan saman,bai gama fahimtar su waye ba ya jiyo muryar Yasmeen tana kuka tana cewa’’Mommy!

Ya Yash ne sukayi accident shine doctor d’in ya kirani,wai

yanzu

n nan aka kai masa su.’’

Wani kalar murmushi Yassir ya saki daga jin zancen Yasmeen,a take wani farin ciki mara misaltuwa ya lullub’e sa,sai da yayi da gaske tukunna dakyar ya samu ya kawar da farin cikin daya baiyyana akan kyakkyawar fuskarshi ya fita

a gigice….

Yana fitowa ya tarar da su gaba d’aya kowa ka kalla hankalin sa a tashe yake har su Ummi…….already Daddy ya riga ya tafi office shida Yasira,dan haka suka tura musu message kawai daganan gaba d’ayansu suka d’unguma asibitin da Yasmeen ta gaya

musu,dan a yadda hankalinsu yake a tashe

babu wanda zai yarda a tafi a barshi,

Baba Larai ce kawai ta tsaya a cewar Mommy in wani ya dawo sai ta je.

Sai da suka kusan Isa asibitin ma tukunna su Yasmeen suka lura babu Kausar,kowa hankalinshi ba a jik

inshi yake ba shiyasa ba su neme ta ba.

A b’angaren Kausar d’in kuwa

duk wannan ife ifen da akayi aka gama ba ta sani ba,har suka fita

Jiya through ko rintsawa bata yi ba shiyasa daff da asuba da taga ciwon kai yana shirin halaka ta ta sha maganin b

acci mai tsananin k’arfi.

Suna shiga Asibitin dai dai lokacin likitan ya fito kenan daga inda aka shiga da drivern domin taimakon gaggawa.

Gaba d’ayansu rufar masa sukayi

Yasmeen kuwa bata ma tsaya bi takansa ba ta fad’a cikin d’akin da taga ya fit

o.

Girgiza kai likitan yayi fuska cike da alhini yace’’i’m sorry!

we couldn’t save him!’’

Diff numfashi kowa ya d’auke

suka ma kasa cewa komai

Wani mahaukacin bugawa zuciyar ta tayi jin likitan yana ci gaba da cewa ‘’amma Yashjub is fine!da i

kon Allah

da taimakon seat belt

sannan kuma kasancewarshi a seat d’in baya…ya samu iyaka

gocewar k’ashi a hannunshi na hagu.Amman motar da suka daka itama gaba d’aya mutanen ciki duk sun rasu

Haka shima driver d’insa ya rasu sakamokon buguwar da y

ayi

da kuma glass d’in da ya chakesa a ciki,we tried our possible best amman we couldn’t save him.’’

Ahankali Yassir wanda ya fara ganin dishi dishi ya matsa kusa da likitan ya dafa kafad’arshi ya ce ‘’Doctor Yashjub Is fine am man s h i ko??’’

Ya

yi masa tambayar a rarrabe.

Jinjina kai likitan ya yi kafin ya d’aura da cewa’’yana wanchan d’akin anan muka ajjiye sa dan ya samu ya huta an gama gyara hannun nasa da duk wani abunda ya kamata ayi masa.’’

‘’Alhamdulillah gada d’ayansu suka furta cik

in tsananin jin dad’i banda Yassir wanda wata kalar zufa ta shiga tsatstsafowa masa kafin a hankali wani hawaye ya biyo ta idonshi guda d’aya,da sauri ya sunkuyar da kansa k’asa ya sa hannu ya goge ya fara murmushi mai kamar dariya kafin a fili yace ‘’Al

hamdulillah!’’

sai kuma ya d’ago ya kalli likitan tukunna yace’’can we see him??’’

‘’Yes,sure!’’likitan ya ce kafin ya kira wata nurse yace ‘’ta nuna musu inda Yashjub yake’’.

daganan ya juya ya koma wajen Yasmeen zuciyarsa taff

cike da mamakin

yadda gaba d’ayansu suka nuna halin ko Inkula game da rasuwar drivern Yashjub

Yana shiga ya tarar da Yasmeen ta na waya,da alama da familyn drivern take waya.

Tana gamawa ta kallesa tace

‘’Sir!wallahi na tsorata sosai,ashe ma ba abunda ya samu Yash



Alhamdulillah

bara inje in ganshi.’’

Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace’’am sir….family d’in deceased din suna hanya dan na ji yadda hankalinsu ya tashi a wayar nasan anytime from now za mu iya ganinsu anan’’.

Daga haka ta wuce ta fita.

A d

’akin da Yashjub yake suka tarar da Daddy da Yassira

dan office d’insu yafi kusa da asibitin shiyasa suka riga su zuwa,suna shiga Yahanasu ta tafi da gudu ta fad’a jikin Yash ta fashe da wani Irin kuka.

Tun d’azu sai yanzu ya samu

murmushi ya d’an su

b’uce masa,ahankali ya d’an yi tapping bayanta alamun lallashi,

Cikin kuka ta d’ago ta shiga

duddubashi tana kallon hannun a hankali tace ‘’Allah ya ci gaba da kare ka a duk inda kake’’

Murmushi yayi yace

‘’Ameen,Allah ya kare mu gaba d’aya’’

Da

ga haka ya d’aga kai ya fara bin su da kallo d’aya bayan d’aya.

Duk matsowa suka yi suka yanyamesa suka shiga yi mishi sannu.

Yayi mamakin rashin ganin Kausar amman kawai sai ya basar a d’ayan b’angare na zuciyar sa kuma yana mai sake tabbatar da zargi

nshi akanta.

Kowa waje ya samu ya zauna aka shiga jimami kafin Daddy ya kalli Yahanasu yace’’sun gama duba drivern??’’

Shiruu tayi sai daga baya tukunna ahankali ta girgiza Kai tace’’ya rasu’’

‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’

Yashjub da Da

ddy suka shiga maimaitawa.

Daga haka d’akin ya yi shiruuu.

Dan rasuwar drivern ta girgiza Yashjub ba kad’an ba.Kasa zama suka yi shi da Daddy sai da suka je suka gansa a lokacin har nurses d’in sun rufesa an toshe kumnuwa da hanci,duk dauriyar Yash sai

da yayi hawaye yayi masa addu’a tukunna suka koma d’akin da Yash d’in yake bayan sun ce in iyalin sa sunzo ayi musu magana.

Ko da suka koma d’akin ma

haka aka ci gaba da zaman jigum,kafin Yahanasu da Ummi suka ci gaba da jajanta al’amarin.

gyaran m

urya Daddy yayi kafin

Yace

‘’Tsautsayi irin haka daman yakan faru a irin wannan lokutan na shiga sabon fagen rayuwa’’

Duk nutsuwa sukayi suna sauraron sa yayinda shi kuma

ya ci gaba da ce wa’’ Na so

dama yau in gaya muku

amman tunda gamu duk

anan

Alhamdulillah.InshaaAllah

nan da sati biyu in komai ya tafi daidai ba wata matsala

Za’a d’aura auren Yashjub!

Hajiya Mama ma ta riga ta sani anytime from now in ta gaya wa su Abhi za ku iya ganinsu whar da su

Imam.

Khadija ke da Saddik’a i

n akwai walima da taron da kuke buk’ata za kuyi sai ku yi min magana in samu in sallameku da wuri.’’

Daddy yana dasa aya cikin

tsananin murna

Munirat tace’’Allah ya sanya alkhairi’’

Ta fad’i hakan fuskarta d’auke da faffad’an murmushi.

Sai kuma

tayi shiru da sauri ganin babu wanda yace komai sai ita sannan tsabar yadda da fad’a cikin murna yasanya gaba d’aya muryarta ta cika d’akin.

A b’angaren su Yassira kuwa tun daga kan Mommy har izuwa kan Yadira babu wanda bai shiga tashin hankalin a cik

in su ba,sun san da maganar ba wai basu sani ba amman kuma fad’a musu d’in da Daddy ya yi a yanzu ya sanya

suka sake tabbatar da dahir d’in maganar shiyasa tashin hankalin da suke a ciki ya sake hauhawa.

Murmushi Ummi tayi tace’’

MashaaAllah Yashjub,n

a yi matuk’ar farin ciki….dukda bamu da ishashshen lokaci

amman inshaaAllah

za mu zage dantse ayi hidima sosai.Na ji dad’i kwarai

Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya yasa matarka ce har abada har a gidan aljannah’’

Murmushi yayi a hankali

yace

‘’Ameen Ummi,nagode.’’

Kafin ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zubasu a kan Mommy

daidai ita ma shi take kallo tana nazartar fara’ar da yake ta zubawa.

Diriricewa tayi dan haka sai tahau kame kame

kafin tace’’ni na ma rasa bakin

magana’’

Shiru Daddy Ummi Munirat da Yashjub sukayi suna tsammanin su ji ta d’aura da wani abun amman sai suka ji tayi shiru

dan haka duk sai aka zuba mata ido.

So take tayi magana amman sam ta kasa tama rasa me za ta ce shiyasa kawai sai tahau wasa da bak

in mayafinta kamar wata yarinya.

Girgiza kai kawai Daddy yayi ahankali yace

‘’Hmm’’

Cikin son kawar da situation d’in Ummi tace‘’I know this isn’t the right time

amman yakamata ko zuwa anjima in ka d’an huta sai mu

fara maganar had’a lefe

d

an nasan maza ba ku iya zab’ar test d’in da mu mata mukeso ba.

Kayi mana magana sai in taya Momin ka tunda bamu da isheshshen lokaci.’’

Murmushi Yashjub yayi kafin finally ya d’auke idanuwanshi akan Mommy ya mayar kan Ummi tukunna yace’’am..actually Um

mi

Yahanasu ce za ta had’a

na ma tambayeta already…’’

Cikin katse shi Yasmeen tace’’ oooh,wato Yahanasu ta riga ta san maganar auren naka ahead of us,ko Yaha??’’

Ta k’arashe maganar tata tana mai kallon Yahanasu da alamun tambaya.

Wani kallo Ya

sh ya d’ago ya watsa mata wanda yasa ta kawar da kanta gefe

Yahanasu tana shirin yin magana Ya’isha ta sake cewa

‘’Yaha ba ki amsa tambayar Yasmeen ba’’

Sai kuma ta kalli Yash tace‘’I mean no disrespect bu

a ganina

you have like 6 classic sister

s

then y choose Yahanasu wadda batasan komai ba?

No offense

but duk mun san bata da wayewar mu bata son shiga mutane ita haka nature d’in ta yake.

Wannan shine biki na farko da za a yi a family d’in nan so I think bai kamata mu bawa kanmu kunya ta

ko wacce hanya ba,sam bai kamata a bar Yaha ta je ta ta had’o abun da bai kamata ba salon ta ja mana jin kunya tunda na san itama yarinyar definitely y’ar manya ce.

Anyways I’m already hurt by the fact that’sai da ka fara gaya mata har kuka fara had’a l

efe tukunna mu muka sani’

therefore I can’t stay here

bara kawai in wuce tun kafin in je in fad’i wata maganar da za ace na yi rashin kunya!!’’

Shiruu kawai Yashjub yayi ya zubawa Ya’isha ido…ranar da Najeeb ya fito mishi a mutum yace’’Ya’isha bat

ada kunya kullum rashin kunyarta k’aruwa takeyi’’

dukda yasan tsiwa nature d’in ta ne amma sai da ya ji haushin Najeeb.

Yau kam tabbas ya tabbatar

he can’t believe yadda take magana da kuma attitude d’in ta sam ba respect.

Muryar Ummi ce ta katse mi

shi tunani jin cikin kwantar da murya tana cewa’’Ya’isha waya ce miki ta san maganar kafin ki sani?ai cewa yayi ita yakeso ta had’a kawai bai riga yace ya bata ba,besides ko ta sani ma ai itace Babba kuma naga kmr yafi shak’uwa da ita’’.

Cikin katseta Y

a’ishan ta d’aga mata hannu tace’’Ummi Plss’’sannan ta juya ta kalli Yashjub tace’’Allah ya sanya alkhairi

Allah ya baku zaman lafiya

Allah ya baka lafiya’’

Daga haka ta juya ta fita fuuu

kamar zata tashi sama

Tsayawa kawai Yashjub yayi yana ka

llon inda ta bi ta fita a ransa ya raya’’wato dai yanzu ita bata tsoro ko shakkar kowa’’

Yassir dama neman hanyar fecewa yake yi,dan haka da sauri ya samu ya juya shima ya fice hankalinsa a mugun tashe.

Ajiyar zuciya Yasmeen ta sauk’e kafin itama t

a mik’e tace’’nima bara inbi bayan Ya’isha mu tafi tare.’’

Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace’’Ummi plss next time kar ki sake cewa wani wai Yash ya fi shak’uwa da Yahanasu or something like that!saboda

ba haka family d’in nan yake ba,babu banbanci

a tsakanin sibling d’in gidan Daddy we re all one and the same

Iyakar fad’an hakan ma da kikayi ya soosa min rai’’

Ahankali ta kalli Yashjub sannan tace’’i hope u can imagine yadda zan ji idan aka yi treating d’ina haka and less important.

Allah ya k

’ara sauk’i

Allah ya sanya alkhairi’’

Tana gama fad’in haka ta juya ta fita.

Dafe kai Ummi ta yi tana danasanin kulasa Yasmeen da ta yi yau bayan ta yiwa kanta alk’awarin fita a harkar su har abada

Maybe kawai dan tana cikin farin ciki ne shiyasa ta

manta ta biye su

Har ga Allah taji dad’in maganar auren Yashjub,ta san ko wacece yarinyar to tabbbas tana da hankali da tarbiyya dan a yadda Yashjub yake ba zai d’auko musu ballagaza ba da izinin Allah, tun a bakin Daddy take jin labarin Yashjub

da k

uma ya dawo ya fara aiki dasu nan ta tabbatar tabbas Yash mutum ne asalin jajirtaccen me hankali wayo nutsuwa neman na kanshi me mutunci kamala da sanin ya kamata………….

…..ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin yace’’Yash!da gaske suke Yahanasu ta san magan

ar auren nan kafin su??’’

Lumshe ido yayi ya bud’e kafin yace’’Daddy plss mana….’’

Cikin d’an fushi Daddy yace ‘’tambayar ka nakeyi ka bani amsata kawai!’’

Ahankali Yashjub ya jinjina kai yace’’eh’’

Shiruuu Daddy yayi kafin chan ya kawar da kan

shi gefe kawai.

Ahankali Mommy ta matsa inda Yash d’in yake ta dafa kanshi tace’’Allah ya cigaba da kare ka a duk inda kake Allah ya baka sauk’i’’

Tana gama fad’in haka ta juya ta fice,hatta Yadira bata ci gaba da zama a d’akin ba dan Mommy tana fit

a suma duk suka bi bayanta suka fice.

Yassira ce kawai ta tsaya sai Ummi da Munirat da Daddy da Yahanasu.

Ahankali

Yassira ta matso kusa da su tace’’Ya Yash,aure zaka yi,new member zaka kawo mana! tayaya kake tunanin za ta yi respecting d’in mu as y

our sisters idan kai da kanka ka nuna mata akwai banbanci a tsakaninmu?.

Atleast in mu mata baka gaya mana ba ya kamata ka gayawa Yassir tunda shima Namiji ne kmr kai ya kamata ka fara jan shi a jikin ka.

Mata in-laws d’in gida in aka auro su su suke tar

watsa kan family musamman in suka ga akwai hanya mafi sauk’i da za su bi

Nasan za ka ce wannan k’aramin abu ne amma mu a wajen mu and yadda yanayin rayuwa yake sam wannan ba k’aramin abu baneba.

Kamata yayi in aka fara auratayya mu had’e kawununamu mu yi

sticking together kar mu bawa kowa damar shiga tsakaninmu

amman a yadda ka fara nuna wa tun yanzu Yahanasu ce favorite d’in ka ita ka fi so kaf cikimu

To fa idan matar taka ta zo Yahanasu kad’ai za ta ja a jikinta mu kuma ba za ta bamu muhimmanci ba

wanda hakan ba k’aramin issue zai janyo ba.

Dan Allah ka yi considering maganata in kuma na b’ata maka rai ka yi hak’uri amma

dan Allah ko ba komai ka yi k’ok’ari ka gyara tsakaninka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login