Showing 24001 words to 27000 words out of 259716 words

Chapter 9 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

34

Mommy ta nuna tashin hankalinta har ta kai ta gagara sauk’owa a yi breakfast da ita hakan ba kad’an ba ya sosa masa rai dan ya san daga ita har su Yasmeen da suka k’i zama duk saboda

Hajiya maman ne,amma zai ci ubansu in ya samu lokacin

su dan uwa ba ta fi uwa ba.

Faram faram kamar su Ummi da Hajiya Mama za su cinye juna haka aka shiga gaisawa ana murnar had’uwa har ma

da Sameeha dan Itanma suna waya suna chatting da Ummin,kamar yadda suka yiwa Ummi haka suka yi wa Munirat Itama ta ji

dad’i kuwa

matuk’a dan atleast ta san ba duka aka taru aka zama d’aya ba kuma yanzu ta tabbatar Ummin ta za ta d’an rage zafi tunda ga oga kwata kwata ta gani da idanunta ba wai a waya ba

ta na sonta kuma tana ji da ita.

Su kad’ai sai Daddy da Abhi

ne aka yi break fast d’in yau dan ko Ya’isha ma k’in zama ta yi tace za ta makara depending project d’inta na masters da take yi.

Tana fita Hajiya Mama ta kalli Daddy tace ‘’Saboda shegiya!

da kai da matarka kun janyo wa y’ay’anku karatu a Nigeria’’

Kallon Ummi tayi sai kuma ta kalli Daddy kafin ta ci gaba da cewa’’ai ni ban san irin power da wannan shegiyar Yarinyar take da ita a cikin gidan nan ba ,Saddik’a saboda fa ni da Daddy mun ce ‘idan kausar ta fita k’asar waje karatu za ta sake lalacewa a

barta ta yi

karatu anan gida Nigeria’shine

ita uwar Yaran tace’tunda Kausar ba ta fita waje ba to babu wanda zai sake yin karatu a waje’.Duk dan kar ran y’ar gwal d’in ya b’aci!akan

ranta ya b’aci gara na ya’yan ta ya b’aci kuma shima Imam din ya zuba

mata ido ya k’i tab’uka komai akai shiyasa ka kaf cikinsu Yassira ce kawai ta zo ta yi karatunta

Itanma dan ta riga Kausar d’in farawa ne da wata d’aya shiyasa aka barta ta kammala Oxford sai Yash da Yassir da Yahanasu tunda su sun riga ta yi’’

Hajiya

Mama ta faiyyace hakan cikin d’an b’acin rai.

Shiruu Ummi ta yi ta rasa abin cewa dan haka kawai sai ta sunkuyar da kanta.

Cikin b’acin rai still Hajiya Mama tace ‘’Kuma ai gaskiya aka fad’a tun kafin fa ta tafi makarantar k’asar wajen ta yi ciki ta

haihu d’an ba rai,lokacin tana gama secondary school.

Me kike tunanin zai faru inda an barta ta je wata k’asar..?’’

Ahankali Abhi yace’’Maaamaaa’’

Ya d’an jaaa maganar.

Sai a lokacin Hajiya Mama ta lura da yadda gaba d’aya ita kanta Ummin she’s not

comfortable da zancen dan haka ta yi shiruu kawai tana mai sake tabbatar da innocence d’in Ummin a ranta tace’’tabbas ban ga ta zama ba dan matar nan ba ta san komai ba

sannan ba ta san wacece mommy ba,ya kamata a yi wani abun tun kafin ta cutar ta ita

that is

idan ta kasa cireta a gidan kenan…’’

Shiruu dining d’in ya yi ba ka jin k’arar komai sai cokula sai

kuma albarkar da Hajiya Mama taketa sakawa Ummi dan ta ji dad’in girkin da ta tarar Ummin ta yi da kanta kuma ya yi mata dad’i sosai.

Ummi

kuwa baki har kunne dan ba kad’an ba take jin dad’in addu’o’in da Hajiya Mama take ta zuba mata.

Sosai Daddy ya ji dad’in yadda Ummi da Hajiya Mama suka fahimci juna suke shiri da kuma yadda Ummin take girmama Hajiya Mama

shiyasa ya yanke shawarar zai s

ake tuntub’ar ta maybe zuwa yanzu ya san ta huce..shi dai ba zai bata hak’uri ba no matter what dukda zuwa yanzu shi kansa ya san ya garu!Ummi ba yaji ta yi ba tana cikin gidan shi amman fushin ta gareshi ya fara illata shi matuk’a…..

Ganinta a tsaki

yar manya yasa gaba d’aya ta ke ta jinta unconfortable shiyasa ta yi sauri ta kammala daga haka ta mik’e tace musu’’ta k’oshi’’ta yi musu sai anjima kafin ta

nufi sama.

Clashing suka yi da Yassir wanda yake sauk’owa k’asan sanye da suite har da briefi

case ya yi masifar yin kyau kana ganinsa kasan office zai tafi.

Sarai ya lura da ita amman sai ya d’auke kai kawai ya wuce wanda hakan kuwa ba k’aramin gigita Munirat yayi ba

dan ba ta yi tunanin zai iya yi mata haka ba..tun jiya take jiran kiranshi bai

kira ta ba sannan yanzu kalli abunda ya yi mata duk dan shekaran jiya ya ce ‘’su had’u a gidan Abokinsa’’ta k’i yarda ta yi fushi tace ‘’ita ya ma daina yi mata irin maganar nan bata so’’dga haka ta kashe wayar to ashe shima ya d’au zafi da gaske tunda ga

shi ya d’auke mata d’iff…anya kuwa ba za ta sauk’ar da kai tun wuri ba su shirya ta nuni masa komai ba komai ba dan tana jin tsoro kar ta je ta taro match d’in da ba za ta iya ba dan wllahi ba za ta iya rayuwa babu Yassir ba….

Ya yi mamakin ganin Hajiy

a Mama dan haka ya yi saurin k’arasawa suka gaisa ba yabo ba fallasa kafin ya tambayesu Junior,ya kuwa ji dad’i kwarai da ya ji Junior ya zo,bai wani damu ba da aka ce mishi Na’ima ba za ta zo ba dan bai damu da Yarinyar ba

muguwar gidahumace

kamar ba

a uk aka haifeta ta girma ba ga shegiyar rowa sannan tun ranar da ta fito mishi a mutum ta gaya mishi Yash take so ko chatting d’in kirki ba sa yi

shi manta wa ma yakeyi da ita in ba a family group ya ga ta yi magana ba.

Kad’an ya d’an chakali abinch

in kafin ya mik’e ya yi musu sallama yace ‘’bara ya je office’’kai kana ganin Daddy ka san yana cikin tsananin farin ciki sai murmushi yake ta zubawa sakamokon ganin Yassir da ya yi a shirye caff!zai tafi office kuma da wurwuri haka,a ranshi ya godewa Alla

h ya shiga addu’a Allah ya sa fad’an da aka yiwa Yassir ya shige sa kenan Allah ya sa ya shiryu kenan har abada’’. Kasa hak’ura Daddy ya yi sai da ya mik’e har bakin k’ofa ya je ya shafa kan sa ya yi masa addu’o’i tare da fatan nasara tukunna ya koma ya za

una yana ta zuba murmushi.

Tunda Yassir yake a rayuwar sa bai tab’a jin guilty conscious irin na yau ba,ya san saboda ya ga zai je aiki ne ya sa yaketa wannan murnar alhalin a asalin gaskiya shi ba aiki ne zai kaisa ba..wani Abokin sa ne ya had’a sa da wa

ta yarinya yarinyar ta had’u matuk’a mahaifinsu ya rasu kuma itace babba shine take neman aiki,shiyasa aka had’ata da shi shi kuma yace su had’u yau yaga ko za su daidaita……

‘’Tunanin mai kake yi??’’muryar Daddy ta katse masa tunani,murmushi kawai ya yi

bayan ya kallesa daga haka ya yi waving d’insu ya sa kai ya fice.

Dukda uwar suite d’in da ya ci kuwa yana fara magana Yarinyar ta fahimci inda ya dosa ta kuma

fahimci ba aiki ake son ba ta ba dan haka ta mik’e tsulum ta fice ta bar sa cikin tsananin

mamakin ta,dan ko irin sallamar nan ba ta yi masa ba hakanan ta mik’e ba um ba um um ta fice ta bar masa office d’insa…..ko minti uku bai k’ara ba shima ya fice daga company d’in ransa a mugun b’ace yana mmakin yadda sam ya daina cin galaba a kan y’an mat

a anyhow kamar wanda aka yiwa asiri,duk wani abu mai kyau na gidan Daddy Yashjub ya d’auke harma da farin jinin y’an mata……

Ko da ya dawo gida direct side d’in Yash ya nufa wajen Junior aikuwa kafin awa d’aya ya ware war suka ta hira abunsu

dan kusan

Junior shine best friend d’in Yassir,halin su kusan d’aya ne dan indai aka zo batun mata to kowannen su sai a hankali sai dai unlike Yassir shi Junior ya san class d’insa sannan shi he’s very hardworking yanzu haka Doctor ne shi looking forward into becom

ing a consultant.

Junior ya yi mamaki da ya ce mishi ‘’ya zo su je su gaida antynsu matar Yashjub but sai ya ji Yassir yace ‘’shi bai ma tab’a ganinta ba’’amma kuma

Junior d’in da ya tuna waye Yashjub sai ya ga hakan a wajenshi ba komai bane dan haka y

a kawar da zancen su ka fad’a wata hirar.

….

Mommy tana shiga cikin d’akinta ta fashe da wani irin kuka mai hawaye wiwi kamar wata yarinya,ta kasa tsaye ta kasa zaune sai faman safa da marwa take yi tana hawaye

tunda ta shigo cikin d’akin.A haka Baaba L

arai ta turo k’ofar d’akin ta shigo dan d’azu tana parlourn Kausar wadda itama damuwa ta sauk’ar wa da zazzab’i ta fara jiyo

Hajiya Mama da Mommy shiyasa ta bari sai da suka wuce tukunna ta biyo ta ga halin da y’ar uwartata take a ciki.Da mugun sauri ta r

ufe k’ofar ta k’arasa kusa da ita ta rik’eta tace’’subhanallah Mommy….’’

Ingijetan da Mommy ta yi ne yasanya ta kasa ci gaba da magana,cikin tsananin fushi Mommy ta fara magana tana hawaye tana cewa’’kar ki soma tab’ani,ki bar ni kawai in mutu Larai tun

da kin kasa min maganin matsalata,abu d’aya tak zuwa biyu amma ya gagareki which makes me think anya ma kuwa kina min aikin nan tsakani da Allah?.In ba ki ci in ba ki sha in baki sutura da wajen zama amma ace wai ki kasa mi……’’

Yadda Mommy ta ga Baaba Lar

ai ta kafeta da manyan idanunwanta da suka yi jazir suka cicciko da kwallah ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana dan haka kawai sai ta juya mata baya ta sake rushewa da wani irin kuka.

Baaba Larai ta so yin fushi da Mommy itama ta so mayar mata da mar

tani daga nan in yaso su yi kacha kacha amman kuma sai ta kasa,saboda ta san zafin failure d’in da suke ta fuskanta ne ya tunzura ta ga aikata hakan,dan ko ita kanta daurewa kawai takeyi amman abun ya fara bata tsoro kuma ta fara gajiya,ba wai iyaka kai ku

d’in Yash da suka kasa hanawa ba hatta su Hajiya Mama sai da suka so su hana su zuwa amma kalli tsulum kawai sai ganin su sukayi…..

Tana cikin wannan tunanin Mommy ta juyo tana kallonta tana goge hawayenta kafin ahankali cikin sheshshek’a tace’’yi hak’u

ri dan Allah’’sai kuma ta sake rushewa da kuka.

Wani irin tausayin Mommy ne ya lullub’e Baaba Larai tashi guda..tun suna yara ita kanta ta san abunda yake saka Mommy kuka ba k’arami bane,shiyasa yanzun da ta ga tana kuka ta sake tausaya mata ta tausaya

musu ta kuma yi wa kanta alk’awarin inshaaAllah ba za su kwashi kashin su a hannun ba….

Ahankali ta sa hannu ta janyota jikinta ta yi hugging nata ta shiga bubbuga bayanta alamun rarrashi.

Kamar zuga Mommy ake haka ta shiga rera kuka kamar jira takeyi,

cikin kukan ta fara magana tana cewa’’Larai na gaji,kuma na sad’akar,dan na san tunda har aka kai kud’i aka saka rana kuma matar nan ta riga ta zo to kamar an yi auren Yash ne an gama…shikenan mun yi failling we fail flat on our faces Larai!.

Sannan ga z

uwan matar nan bana son ta a cikin gidana mutuwa zan yi Larai bana son ganinsu a cikin gidana zuciyata za ta buga ban san da wanne zan ji ba Larai abun ya yi yawa duka ta ko’ina ban san wanne zan tare ba…..’’

Ganin yadda take magana out of pain ne ya sa

nya Baaba Larai ta zaro ta da ga jikinta cikin sigar lallashi tace’’ban san mai zan ce miki ki sake yarda da ni wannan karon ba amma inaso ki yarda da ni ki yi putting trust d’inki in me inshaaAllah ba zan sake baki kunya ba,ni na san mai zan yi wannan kar

on ba za mu yi failing ba inshaaAllah ba za ayi auren ba not in 9days time not forever!

Sannan itama Hajiya Mama inshaaAllah sai sun koma inda suka fito da yardar Allah dan ba zan zuba miki ido in barki a hakaba ba zan iya ba y’ar uwata sannan ba zan zub

a ido ina gani ake ci miki kashi a cikin gidan ki ba!sanann ga shi daga zuwanta na lura so take ta yi wa mutane handsfree a gaban idon kowa’’…

Gyara sosai Manubiya take sha dan a cikin cikin kwana d’aya da aka yi mata sau biyu safe da rana kawai har t

a fara chanzawa in banda kamshi ba abunda yake tashi daga jikinta,fatarta har ta fara sumul sumul da yellow ta na d’aukar ido.

Yanzun ma na uku aka yi aka gama dan Mama ta ce ba su da lokaci dan haka a dinga yi

akai akai tunda ba su fara da wuri ba,ana

gama gyaran jikin ta fad’a wanka tana fitowa kuma ta sake zama a kan kujerar tsugunno ba dan ta so ba sai yadda taga Mama ta dage akan sai fa ta sake zama a cewarta ‘’d’azu tana sane da ita ba ta zauna sosai ba ta fake da cin abinci’’,dariya duk suka yi h

ar Manubiya wadda take Allah Allah ta yi ta shirya dan ta san anytime from now zai iya zuwa saboda ce mata yayi da yamma,already Jidda ta tambaya mata su Baba sun bata go ahead amma sun ce ta tafi da d’an rakiya shiyasa tun d’azu ta cewa Muhsin ya shirya.

Sai da ta kusan sakawa Mama kuka tukunna ta yarda ta ce shikenan ta tashi tana ta yi mata tsiya tana ce mata’’raguwa’’daga haka ta yi musu sllama ta tafi dan tana so ta je itama ta d’an huta.

Manubiya ta na tashi ta nufi wardrobe ta zaro kayan da za

ta zata saka tukunna ta zauna ta shiga shiri…mai gyaran jikin tana gama shirin tafiya dai dai ita itama ta gama shirin ta kenan,kiran Yashjub ya shigo wayarta.

Dama wayar tana hannunta yau kam babu wani maganar jan aji dan ita kanta kawai gani ta yi ta d’

auka ta kara a kunnenta…..shiruuu ta ji ya yi da farko kafin chan ta ji yace‘’Ina k’ofar gida.’’

Da kyar ta iya cewa ‘’tam’’daga haka ta kashe ta k’arasa wajen inna ta d’an durk’usa ta gaya mata daga nan ta mik’e ta d’auki mayafi me kyau da girma da kau

ri sosai ta d’aura akan doguwar riga y’ar kantin dake a jikinta.

Har za ta fita sai kuma ta dawo ta k’ara turare har da d’an lipstick pink ta d’an goga sannan ta gyara zaman hular ta,ta na juyawa suka had’a ido da inna dan haka gaba d’aya duk sai kunya

ta rufeta,da sauri ta juya da niyyar cewa Jidda Ina Muhsin yayi amma sai suka had’a ido da shi ya d’ago labule,dan haka ta yi gaba bayan ta ce musu ‘’sai sun dawo‘’suka fita ita da Muhsin da mai gyaran jiki….

Suna fita ta yi mata sallama

ta wuce ita

kuma ita da Muhsin suka tsaya kallon dalleliyar motar da ke fake a gaban su.MANNUBIYA

(Book 2)

Page 10

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Suna fita ta yi mata sallama

ta wuce ita kuma ita da Mu

hsin suka tsaya kallon dalleliyar motar da ke fake a gaban su.Dukda ba ta riga ta ga na ciki ba dan motar tinted glass gareta amma tashi d’aya jikinta ya bata shine.

A b’angaren Yash kuwa tunda ya zo ya yi parking a k’ofar gidan yake sake k’arewa gidan

kallo yana sak’e sak’e a ranshi…tun ranar farko da suka zo shi da Najeeb yake tunanin ta yadda zai siya musu gida su yarda su karb’a dan ya san tabbas da wuya su amince da hakan,amman zai gwada ya gani saboda har ga Allah daga arean har gidan basu kwanta m

ishi ba,a take tashi d’aya tausayinta da k’imarta suka lullub’e shi

a ranshi yace’’yanzu a nan ta girma ta yi wayo amma kalli yadda abun duniya da kwad’ayi sam ba su rufe mata ido ba.’’

Yana wannan tunanin ya ganta sun fito su uku,sun yi wa d’ayar mata

r sallama ta wuce ita kuma sun tsaya itada

Muhsin.

Murmushi ya yi kafin ya d’ago wayarsa ya shiga kiranta so yake ya ga yadda za ta yi shiyasa ya k’i fitowa balle ma taga inda yake,tana d’auka kamar d’azu yace’’ki shigo mana’’kawai.

Shiruu ta d’an yi

sai da ta ji yace’’Come in pls’’tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta kashe wayar suka nufi motar ita da Muhsin.

Su na zuwa ta bud’ewa Muhsin gidan gaba,sai da ya shige ya zauna ta rufe masa tukunna ta nufi baya ta sa hannu a kan handle d’in.

Dariy

a sosai ce ta ke tasowa Yash wanda yake zaune a gidan baya,dama ya san hakan za ta yi tun lokacin da ya ga sun fito ita da Muhsin he just can’t wait ya ga reaction d’inta idan ta shigo gidan baya suka yi ido biyu da shi,yana wannan tunanin yaga ta d’aura

hannunta a kan handle d’in dan haka ya yi saurin matsawa ya bud’e mata tun kafin ta murd’a.

Ta d’an yi mamakin ganin yadda k’ofar ta bud’u tun kafin ta murd’a amma sai ta yi tunanin maybe Yash d’in ne ya bud’e mata ta gaba inda yake zaune.

K’amshin m

ayatacccen turarenshi da sanyin ac ne suka fara yi mata sallama,har ga Allah sam ba ta lura da shi a ciki a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login