Showing 210001 words to 213000 words out of 259716 words

Chapter 71 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

65

Yash ba t

a san ba xa at iya ba….amma Kausar kam!wani kalar zafin kishinta ne yake azalzalar zuciyar ta ji take yi kamar ta je ta sameta ta shak’eta!.

Sun jima a haka kafin ta ji yace”na san da maganar binciken da kuke yi ke da Yaha a kan case d’in estate d’ina

…na gode sosai Allah a saka muku da alkhairi na ji dad’i matuk’a da na ji batun kuma na yi farin ciki amma daga yau ku dakatar da komai ku daina.”

Ya k’arashe maganar muryarsa tana kakkatsewa kamar zai fashe da wani kukan.

A hankali ta d’ago ta kallesa

tace”meyasa?”

“Saboda na riga na san waye”

Ya bata amsar hawaye suna masu saukk’o masa kafin ya zaro wayarsa ya shiga chat d’in ya kunna mata ya mik’a mata ta karb’a ya sa hannu biyu ya dafe kansa yana mai zubar da hawaye….da d’an sauk’i da ya kasance

ba Mahifiyarsa Mommy bace behind ita,amma fa dukda haka masifa da tashin hankalin da ya shiga da ya fahimci Yassir ne babu sauk’i.

Tabbas dama Manubiya tunda akace insider ne Yassir ta zarga amma dukda haka itama sai da ta shiga shock ba na wasa ba.

Kasa ma magana Mannubiya ta yi gaba d’aya tausayin Yashjub ya rufe ta tun bama da ya fara magana cikin d’acin zuciya abun tausayi ba!”amma ni kad’ai ne mai irin d’an uwan nan ko?babu wani d’an uwa da na tab’a jin labarin ya aikata hakan ga d’an uwansa uw

a d’aya uba d’aya!!babu shi.

Ji nake kamar zuciyata za ta fashe!!shiyasa fa case d’in farko na k’i yin bincike saboda inyi avoiding wannan pain d’in!!!

It hurts it sucks ace naka ne yake son ganin bayanka!

me na yiwa Yassir haka!ya za a yi ya tsaneni to

this extent???me ya yi zafi har haka?.”

A hankali Manu ta rungumesa itama tana hawaye ta shiga shafa bayansa alamun rarrashi.

Suna zaune a haka wayarsa ta d’au k’ara!!

Sai da aka kira sau uku tukunna ya zaro wayar Da kyar! ya iya karanta sunan Ummi t

sabar masifar da yake ciki,a hankali ya amsa ya kara a kunnensa yace”Hello Ummi”

Cikin hargitsi da b’acin rai ya ji Ummin tana cewa

“Yashjub kana Ina?ka zo yanzunnan,Daddynku yanzu suka gama d’aura maka aure da Kausar.”

Kashe wayar kawai ya yi ya ajjiye

a gefe ya runtse idanunsa da mugun k’arfi yana jin kansa kamar ba a jikinsa ba!

Yana cikin wannan yanayin ya ji k’arar fad’uwa…

A mugun rikice ya bud’e ido yana kallon Manubiya da ke yashe a k’asa kan kafet.

Sai da numfashinsa ya d’auke da kyar ya da

wo jikinsa ya d’au wani mahaukacin karkarwa.

Tabbas ya san abunda aka fad’a ta ji dan wayar tasa tana da murya sosai!!shiyasa tashi d’aya wani sabon tsanar Kausar ya lullub’esa…haka kurum Yarinya ta bi ta d’aga musu hankali babu gaira babu dalili!!!!

bai

san lokacin da ya shiga tsinewa Kausar albarka ba!.

Da hanzari ya rufarwa Manubiya…sai da ya k’ura mata ido sosai ya lura Ashe ba suma ta yi ba tsabar tashin hankali ne ya sanya ta yanke jiki ta fad’i.

Shafa fuskarta ya yi a hankali ya mik’ar da ita

ya rungume ya ce”kar ki bari hakan ya d’aga miki hankali dan Allah saboda Abu ne wanda ba zan tab’a aminta da shi ba”

Daga haka ya sa hannu ya d’auki wayarsa da kyar ya nemo number Kausar a wani group na y’an gidan nasu ya tura mata message daga garesa m

ai d’auke da saki guda biyu kwarara!

Ta watsapp da ta sms duk ya tura mata da niyyar gobe da safe zai ce ya mayar da ita sannan atake ya sake sakinta,shikenan!!!

Ya san idan ya yi uku lokaci guda tsaff za a mayar da shi d’aya.

Lokacin da Yashjub ya

yi sakin su Kausar suna zaune ita da su Yasira suna zab’ar gado a wayartata messge d’in ya shigo,ta sama duk suka gani amma ba sosai ba dan kad’an suka gani…cikin tsananin tashin hankali Yasira ta amshe wayar ta bud’e gaba d’aya dan Kausar ta kasa bud’ewa…

da kyar ta lek’a suka karanta a tare su duka tashi d’aya ta zube a kan gadon ta fashe da wani irin kuka.

Salati duk sukayi Yasira ta mik’e ta k’arasa ta nunawa su Mommy da suka mik’e tsaye a tare sakamokon salatin da suka ga suna yi da kuma kukan Kaus

ar da rikicewar da suka ga sunyi.

Suna gama karantawa Mommy ta kalli Ya’isha da Yasira tace su biyo ta kafin ta kalli Baba larai tace”bari mu je mu dawo,incase idan Daddy ya tambaya ina ina kice na sha magani na kwanta Idan kuma sun ji an fita sun tambaya

kuce su Yasira ne suka tafi siyowa Kausar magani…”

Tana gama fad’in haka suka saka sa kai suka fice su uku ragowar kuma suka ci gaba da lallashin Kausar.

Ya’isha ce ta biya side d’inta ta d’auko musu hijabai dan Mommy ba ta da kuzarin wannan,daganan t

a taho da makullin motarta ta mik’awa Yasira…daga haka suka sauk’a k’asan.

Dama Yasira ta san gidan Yashjub suka nufa aikuwa tana kunna motar Mommy tace mata”gidan Yashjub za mu je.”MANNUBIYA

(Book 2)

Page 39

Na

Hum

ayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Lokacin da su Mommy suka isa gidan,su Yashjub suna chan sama d’akinsa shi yana wanka Manubiya kuma tana zaune a kan sofa ta fara jiyo k’arar door bell!.

Kusan minti biyu suna a tsaya ba’a zo an bud’e ba,

dan haka suka fara danna masa call ta wayar Mommy.

Wanka yake yi alokacin shiyasa Manu ta d’auko Hijab d’inta ta sauk’o.

Sai da ta lek’a ta y’ar b’ular jikin k’ofar tukunna ta sa Hannu ta bud’e k’irjinta yana wani irin bugu dan tana ganinsu Hankalinta ya

tashi zuciyar ta ta shiga tsitstsinkewa.

Har k’asa ta durk’usa tace”Mommy Ina wuni”

Ba tare da ta kalleta ba ta wuce kawai ta nufi sama tana mai cewa”Ya’isha duba mini k’asan ko yana nan in baya nan ki hawo mu duba sama”.

Tana gani Ya’isha ta k’ara

ci dube dubenta ta zo ta haye saman suka barta nan bak’in k’ofar a durk’ushe dan tun d’azu ta kasa tashi.

Da kyar ta samu ta mik’e ta tura k’ofar ta mayar ta rufe daga haka ta shige d’akin bak’i na nan k’asan tana shiga ta fashe da wani irin kuka….A yadda

ta ga Mommy ta zo a zuciyen nan it’s either ta saka Yashjub ya mayar da Kausar ko kuma ta sa itama a sake ta.!

Ya fito kenan d’aure da towel kawai ya ga sun shigo su duka ukun.

“Subahanallah” ya ambata daga haka ya juya ya koma cikin closet d’in da sa

uri hankalinsa a tashe ransa a mugun b’ace….ita kanta Mommy yana da tabbacin ba ta tab’a ganinsa a haka ba da girmansa ballantana su Yasira

sannan yadda ya ganta a gidansa a cikin bedroom d’insa haka ya san ba alkhairi ne ya kawo ta ba amma fa yau sai d

ai duk abunda zai faru ya faru dan shima a high yake

Yana wannan tunanin ya zura jallabiya bai zare towel d’in ba ya fito fuskarsa a mugun murtuke kamar bai tab’a dariya ba.

Idanuwansa waenda har yanzu kalarsu bai daidaita ba ya zubawa su Yasira kafin

yace”ku fita ku bani guri!!!”

“Ba inda za su fita su je!!

Ai idan za a yi tsinuwa ana buk’atar wasu a wajen saboda su bayar da sheda!!!”

Zuwa yanzu jikin Yashjub ya fara karkarwa…ya zubawa Mommy idanu kawai ya gagara cewa komai kafin ya yi taku biy

ar zuwa shidda ya k’arasa ya tsaya a daff da ita har tana jin hucin numfashinsa yace”Mommy saboda na saki Kausar shine za ki tsine mini????”

Ta d’an tsorata dan yanayinsa na yanzun yanayine na wanda yake cikin tsananin b’acin rai capable of anything san

nan taga kamar furucin nata bai yi wani tasiri a kan sa ba,amma sai ta dake cikin sake son cin nasara a kansa tace”kwarai ma kuwa Yashjub!na rantse da girman Allah Wallahi Tallahi billahilazim idan har baka mayar da Kausar ba a yanzu a take sai na tsine ma

ka ka bi duniya!!!

Tun muna daga mu sai kai tun kafin duniya ta ji su Daddy su ji ka mayar da Kausar matsayinta na matar ka idan ba haka ba sai na yi maka Allah ya Isa nonona da ka sha!”.

A hankali Yasira wadda jikinta ya yi sanyi ta fara tsorata dan s

am ba ta kawo abun da suka zo yi kenan ba,ta matso jiki ba kwari tace”Mommy kar ki yi haka,a nemo wata mafita amma banda wannan.”

Wani irin kallo Yashjub ya yi mata kamar zai yi magana sai kuma ya kauda kai yace”Mommy ni da kaina na tab’a kama Kausar da

Yassir a side d’inmu shiru kawai na yi muku ban fad’a ba!ta ya kike so

In yi zaman aure da dadiron k’anina?

Kausar ta haramta a gareni dan Allah ki ma janye wannan maganar saboda anzo in da ba zan tab’a yin abunda kike so ba.”

Jin jina kai ta yi kafi

n tace”ko da ace zan tsine maka ko?”

Cikin d’an d’aga murya yace”Mommy are you not listening to me?

Kama ta fa na yi red handed ita da Yassir on bed,ta ya zan rayu da ita??”

“Allah na tuba kana Ina Yaya yake rabuwa da mace k’ani ya aura?!ai ba wai anc

e haramun bane kawai dai ana barin Halak ne dan kunya.Dan haka dan ka ga Kausar da Yassir wannan tsakanin su ne su da Ubangijin su,kai kuma kai ne wanda duniya ta sani a matsayin mijinta dan haka wannan duk bai shafeka ba!!!!”

Mommy ta fad’i hakan tana hu

ci.

Cikin d’aurewar kai haushi bak’in ciki da tsananin mamaki yace”bai shafe ni ba idan Kausar ta kwanta da k’anina???

bai shafeniba dan ta kasance karuwa??Mommy wacce irin uwa ce ke!?da kike k’ok’arin ignoring duk waennan facts d’in saboda kawai ki fa

rantawa Kausar.”

A hankali yana kallonta yace”anya Mommy kin san ciwo na kuwa??kin san zafi na kuwa?wannan rashin adalci haka har ina?ko dai inada wata uwar daban ba ke ba??!!!”

A rikice ta d’ago tashi d’aya ta d’aukesa da wani gigitaccen Mari sai kuma

ta fashe da kuka…

Cikin kukan tace”Wata tara ciff ka d’auka a cikin cikina,bayan dogon laulayi mai wahalarwa haka na kawo ka duniya bayan na sha tsananin wahalar nak’uda! na shayar da kai na tsawon shekaru biyu,kashinka fitsari tumbid’i duk ni mai wankew

a mai gyarawa,sai da ka yi watanni shidda a duniya tukunna ka fara baccin dare wanda a ta dalilin hakan ne ya janyomini na kamu da ciwon hawan jini tsabar rashin samun ishashshen bacci. Idan baka da lafiya in kwana a zaune in wuni a zaune cikin damuwa har

sai naga ka warke!k’iriniyar k’uruciyarka babu kalar wadda ban gani ba babu wadda ban sha ba amma yau ni ce nake gaya maka abu kana yi mini musu Ina fad’a kana fad’a Yashjub har ta kaimu ga kana iya kallon cikin tsabar idanuna kana cewa ‘ba ni na haifeka b

a!!’

Ka san yadda maganar nan ta sanya ni na ji kuwa?

Auren Kausar fa a k’arshe duk kai na ke k’ok’arin yiwa gata amma ka kasa fahimtata!”

Ta k’arashe maganar tata cikin fashewa da wani Irin kuka.”

Duk shiruu suka yi kafin su Yasira su fara rarrashin

ta..ganin yadda shima ya yi shiru kamar maganganunta sun yi tasiri akansa ne ya sanya ta goge hawayenta tace”tunda ka ce ban yi maka adalci ba ka saurara ka kasa kunne ka ji ga adalci nan zan yi maka…

It’s either ka sake Manubiya itama,ko kuma ka dawo da

Kausar!

A cikin biyun nan ka zab’i d’aya ka aiwatar na baka mintuna biyu kawai kacal idan ba ka yi ko d’aya ba mintuna biyun nan suka cika Yashjub Allah ya Isa ban yafe maka ba!”

Runtse idanuwa Yashjub ya yi da mugun k’arfi a take wasu hawaye suka zubo

masa.

Ba tare da ya bud’e idanunsa ba ya ce mata”ki yi hak’uri!!na dawo da Kausar.”

Cikin tarar numfashinsa tace”na gode!kuma inaso ka sani Muddin ka sake sakinta b’acin ran da za ka fuskanta sai ya fi na yau wallahi!!!”

Sannan gobe inshaaAllah za ta

tare,ba ma buk’atar ka yi sabon gida ballanta ka tafka rashin adalci a nan za ta zauna d’akin ta kusa da na Manubiya idan na ga kamun ludayinka daga nan zan yi deciding idan ware gida za a yi,ko kuma Babba za ku chanja wanda ya fi wannan….”

Tana gama f

ad’in haka ta juya ta fice su Yasira ma suka mara mata baya..Yasira jiki ba lakka Ya’isha kam abun ba k’aramin dad’i ya yi mata ba.”

Har suka fita bai bud’e idanunsa ba yana nan a yadda yake…..har Manu ta hawo saman bayan ta ga fitar su ta je ta rufe k’

ofa,yana nan bai motsa ba.

Yanayin yadda ta gansa kad’ai ta san ba lafiya ba.

Ta dai san ba sakinta ya yi ba dan da tuni su Ya’isha sun nemota a gidan sun yi mata tujara..amma in ba da kyar ba tanada tabbacin Mommy ta saka shi ya maido da Kausar ne.

A

hankali cikin tsananin k’arfin hali ta k’arasa ta kamo hannayensa duka biyu ta ja shi…

Bai yi mata musu ba ya bita suka zauna a kan sofa ta yi hugging d’inshi a hankali cikin son kwantar masa da hankali tace”all will be fine,wata rana sai dai labari..ka

kwantar da hankalinka…”

Cikin tarar numfashinta yace”Mommy ta saka na mayar da Kausar,cewa tayi idan ban mayar da ita ba za ta tsine min.”

Tunda ya fara magana Manubiya ta fara hawaye..he can feel yadda jikinta yake vibrating k’irjinta yake bugawa shiy

asa tashi d’aya wani matsanancin tausayinsu ya lullub’esa.

Manubiya ji take yi kamar za ta mutu..kishi tashin hankali da komai ma duk sun lullub’eta amma kuma ba za ta biyewa son kan ta ta je ta kai Mijin da take masifar kishi da so wuta ba!

Indai har

tana son Yashjub da gaske to za ta so su rayu har a Aljannah a tare ba wai ta bashi kwarin guiwar da zai tafi wuta ba,dan haka ta tattaro duk wata jarumta da k’ok’arinta da juriya ta fara magana”Ya Yash duk abunda ka ga Allah ya tsara hakan shine mafi alkh

airi,ni kam na hak’ura babu komai zan zauna da kishiyar,dan Allah kar ka sake yin jayayyya da su Mommy ba zan so ka tafi wuta ba….”

Wani irin kuka ne ya taho mata wanda ya katse mata maganar tata ,dama tunda ta fara maganar muryarta ta shiga rawa tana kak

katsewa.

K’ank’ameta Yashjub ya yi k’irjinsa yana wani irin mahaukacin gudu.

Sun jima a haka kafin yace”ki fara had’a kayanki”

Da farko ba ta fahimci inda zancen nasa ya dosa ba sai daga baya,dan haka tace”Ya Yash we can’t just pack up and leave..ko b

a komai Kausar matar ka ce akwai hakki…”

Cikin tsananin b’acin rai ya zuba mata jajayen idanunsa yace”idan kika sake cewa Kausar mata ta ce za ki ga b’acin rai na”.

Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa wanda hakan ya sanya ya ruk’o hannunta duka biyu

yace”Mannubiya we deserve to be happy!

Annabi Muhammad sallahu alaihiwasallam da kansa a lokacin da aka nuna ba a sonshi Hijara ya yi daga Mecca ya koma Madina!.

Ki duba fa kiga Yassir is after my life..Mommy tana so ta had’a ni dole in yi zaman aure

da dadiron brother d’ina sannan sisters d’ina suma bangama yarda masoya na bane ba.

Ki gaya mini abu guda d’aya reason kwaya d’aya tak da zai sanya in ci gaba da zama a cikin mutanen nan,sun nuna ba sa so na ba sa sonki so kike yi mu cika gaba da zama a h

aka har sai bak’in ciki ya kashe mu???”

“Cikin kuka sosai kamar ranta zai fita tace”Rayuwarmu a nan take,bani da dream d’in zuwa k’asar wasu in yi rayuwa..a nan muka had’u da kai ba ni da burin da ya wuce in rayu a nan in tsufa a nan..”

A hankali ya yi c

upping face d’inta a cikin palm d’insa duka biyu yace”Mannubiya idan akwai lokacin da nake buk’atar support d’inki to yau ne dan Allah dan Annabi kar ki yi mini turjiya.

Ba na buk’atar musu ko wani sabon Abu negative, na cika dayawa! level na tolerance d’

ina ya kai k’arshe….please ko me nace kawai ki ce mini ‘to’dan Allah”

Ya fad’i hakan hawaye suna masu zubo masa.

Wani irin kuka ta sake fashewa da shi ta rungumesa ta na mai jinjina kanta alamun ‘to’.

……..

Najeeb Yashjub ya kira yace msa “dan Allah y

a zo yana da buk’atar ganinsa”.Daga nan ya fara nema musu flight d’in Abuja kafin ya yi musu arrangin barin k’asar gaba d’aya.



Komai na company d’insa na nan Nigeria ya d’aura Najeeb d’in a kai yace masa”zai yi tafiya na tsawon wani lokacin ya rik’e

masa amana.”

Najeeb bai yi niyyar yi masa maganar ba dan kunya da tausayinsa yake ji amma kuma sai ya ga bai kamata ya b’oye masa cewa ya sani ba, dan haka cikin tsananin jin tausayin Abokin nasa ya dafa kafad’arsa yace”ba a kan ka aka fara ba!komai ya

yi zafi maganin sa Allah.”

D’an k’ura masa Ido Yash ya yi kafin ya d’auke kai ya fesar da iska yace”kai ma sun tura maka kenan!”

Jinjina kai Najeeb ya yi yace”a tare suka tura mana!

Na san ba za ka so ka zamo wanda zai fallasa a kashe Yassir ba shiy

asa na yi shiru ban yi maka maganar ba kawai! haka suma masu bincike ban ce musu mun gano komai ba amma dai na ari bakinka na ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login