Showing 102001 words to 105000 words out of 259716 words
yi?”.
“Babu zancen bibiya a nan!
amsa kawai nakeso ka bani”.
K
amar Ya Musbah ba zai ce komai ba sai kuma ya kallesa yace
‘’Wajen mai sunan baba na je, ko ban Isa na je naga d’ana ba??”
Cikin katsesa sannan cikin tsananin fushi Ya Nafi’u yace
‘’ba za ka tsaya ka gaya min gaskiya ba? Yau nine na zama wanda za ka
yiwa wannan k’umbiya k’umbiyar???
Shikenan ka je ka yi ta yi,dama shawara ce zan baka amma tunda na ga bakaso fine!
In dai Baraka ce bismillah,ga ka ga ita amma inaso ka san cewa ba za ta tab’a chanza zani ba.”
Ya fad’i hakan yana mai k’ok’arin zare mak
ullin motar ya fita.
A hankali Ya Musbah ya ce
‘’d’an tsaya Nafi’u.”
Shiruu Ya Naif’un ya yi kamar ba zai kula sa ba sai kuma ya juya yana kallon sa tare da basa dukkan nin attenbtion d’insa.
Ahankali Ya Musbah ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“I
na son ta,har yanzu’’
Wani irin kululun takaicin Baraka da tsantsar tausayin Ya Musbah ne suka lullub’e Ya Nafi’u a lokaci guda.Da kyar ya had’iye abunda ya ji ya tokare masa mak’oshi yana shirin yin magana ya ji Ya Musbah ya ci gaba da cewa
“Har gobe
inason Baraka,har abada!.Kai Abokina ne kana fahimta ta akan komai dan Allah ka fahimceni ka bani goyon baya akan wannan ma.
Itama ta shiryu ta ce min za ta gyara halayyarta sannan tana so ta zo ta bawa su Inna hak’uri kuma tace za ta rik’e Muhsin.
Har
yanzu ba ta riga ta fita a idda ba shiyasa da ni da ita muke so a had’u a gyara abun nan kafin ta fita idda kaga ba sai an yi sabon d’aurin aure ba.
Wannan shine abunda yaketa damu na, na rasa wa zan gayawa kuma ni a ganina Baraka za ta zauna lafiya da n
i da kowa ma tunda yanzu Ina aiki kuma Inada rufin asiri.”
Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace
‘’Musbahu duk matar da ba ta zauna ta ci talaucinka ba to bata yi deserving arzik’inka da kai kanka ba.
Musbahu Baraka bata da kirki ta raina ka ta rai
na iyayenka…..”
Shiruuu ya Nafi’un ya d’anyi ya tsagaita da magana ya dafe kansa saboda ciwon da ya ji ya fara yi masa a sakamokon b’acin rai da takaicin Ya Musbah da Baraka.
Ya d’an jima bai ce komai ba kafin ya cika kan nasa tukunna ya kalli Ya Musbah
ya ci gaba da cewa”shikenan, tunda ka nace…sai ka je ka samu Inna ka ce mata kanaso za ka dawo da Baraka.”
Da d’an zafi Ya Musbah yace
‘’Ya za ka ce in je in samu Innaa?bayan abunda Baraka ta yi mata taya kake expecting in je ince mata zan dawo da ita
?ai wannan aikin ka ne
Kai ka san ta inda za ka b’ullowa al’amarin Kai ne za ka taimaka mini shiyasa na ke gaya maka,saboda ka taimakeni‘’
Shiruu kawai Ya Nafi’u ya yi yana nazartar sa…bayaso ya zargi Baraka amma kuma kana ganin Ya Musbah da zantukan
sa tashi d’aya zaka fahimci tabbas aikin asiri ne ba haka ta bar sa ba.
Ya taso masa da maganar Inna ne saboda yanaso ya tuno masa da abunda Baraka ta yi wa mahaifiyarsa ya ji zafin abun ya daina tunanin dawo da ita
amman it’s like kamar ma an yi delet
ing takaicin da wannan ranar ta k’unsa dan kwata kwata bai hango haushi ko takaicin Baraka a idanunsa ba
bayaga zazzafar soyayyarta da tausayinta dayake hangowa a tattare da shi.
“Ba laifinta bane itama,sharrin shaid’an ne amma ta yi mini alk’awarin b
a za ta sake ba har hak’uri tace za ta zo ta bayar,ka yarda da ni Nafi’u Baraka ta shiryu tun ba yau ba”
Ya sake jin muryar Ya Musbah.
Kallonsa ya yi da kyau kafin yace”Tun ba yau ba?kenan tun ba yau ba kuke waya kake zuwa???”
Bai basa damar cewa kom
ai ba yace”Am Musbahu…
ba zan baka goyon baya ba sannan ba zan hanaka ba.As far as I can remember na san kanada hankali da sanin abun da ya kamata dan haka ka yi
duk abunda ka ga dama.”
Yana gama fad’in haka ya bud’e k’ofar ya fice ya wuce cikin gida ya
bar Ya Musbah a nan zaune shi kad’ai.
Ya jima sosai a cikin motar tukunna ya zare makullin ya rufe motar shima ya nufi cikin gidan.
A zaune ya same shi suna raha wasa da dariya shi da su Inna,
yana shigowa Ya Nafi’u ya mik’e ya yi wa su Inna sallam
a suka wuce shi da iyalinsa…ko ba a fad’a ba tashi d’aya zaka fahimci Ya Nafi’u haushin Ya Musbah yakeji shiyasa dukkan su suka shiga al’ajabi dan abu ne wanda bai tab’a faruwa ba.
Suna fita Baba ya kalli Ya Musbah yace
“Tashi ka bi sa ku sasanta.”
Za
i yi magana yace
“Jeka”
Saboda dama shi tunda aka ce masa suna waje suna magana ya san akwai wani abun,yanzu kuma da ya ga hakan sai ya fahimci tabbas sab’ani suka samu…maybe ma shiyasa kwana biyu yake ta ganin Musbahun a cikin damuwa…
Ba su jima da
fita ba Baba ma ya mik’e ya fita bayan an tabbatar masa da cewa su Manubiya suna lafiya,daganan Muhsin yace “bara ya je d’akin su”Jidda kuma ta tafi raka Siyama…
Suna fita Siyama tace “ni kam ina ma ace Ammi za ta
hak’ura wallahi…kinga d’azu fa dakyar
ya iya jan motarsa ya shiga gida!,ko ba ki lura da shi a time d’in da muke shirin shigowa gida ba lokacin shima yana k’okarin shiga gida.
Kinga yadda ya rame kuwa a cikin kwana hud’u gask…..”
Kukan da Jidda ta fashe mata da shi ne yasanya Siyaman yin s
hiru,kafin da sauri tace “Innalillahi yi hak’uri Jidda mai ya yi zafi??”
Cikin kuka tace
‘’Siyama dan Allah ki daina min maganar Al‘Ameen dan Allah!kin san Ammin sa ba za ta tab’a amincewa ba ko ta amince ma su Ya Musbah suma yadda suka zuciya na san
ba za su bada goyon baya ba.
Ki daina yi min zancen sa ki taimaka min in samu in fitar da shi a raina dan Allah.”
Shiruu Siyama ta yi tana mai jin tausayinta yana sake rufeta…
rana d’aya tak ta d’an samu moment da Najeeb ta kuma fahimci k’udirin sa a
kanta amman ba k’aramin Namijin k’ok’ari take yi wajen dannawa calls d’in sa reject ba.
Shiyasa ta ke ganin k’ok’arin Jidda na hak’ura da Al’ameen bayan shekaru wajen hud’u da suka yi a tare kawai yanzu tashi d’aya an raba su,tabbas abun da ciwo.
Rarra
shin ta ta shiga yi tare da bata baki dakyar Jiddan ta d’an dawo dai dai dan a kwana biyun nan ita kad’ai tasan halin da take ciki..kwanakin baya ta ji haushi ta ji takaici amman kuma tun da ta gansa gaba d’aya sai ta ji ta yafe masa.
Kuma tabbas a yadda
ta ga ya yi ta san yana da uzuri sannan uzurin na sa mai k’arfi ne…she just wants to hear him out,forgive forget and be with him….
Tana wannan tunanin suka fara takawa towards wajen su Siyama kowa ta yi shiru da abunda yake damunta a haka suka k’arasa Siy
ama ta zaro makulli daga jakarta ta bud’e
Parlourn dan maman nata
bata nan ta tafi gidan suna.
Suna shiga ko gama zama ba su yi ba
Siyama tace
“Kina ganin mu kira Manu mu yi magana ko mu je gidanta bayan kwana biyu?”
Shiruu Jidda ta yi kafin
tace
“Sai dai zuwa anjima mu kirata dan kinsan tafiya za su yi tace jibi ne da asuba.
Amman zakice na gaya miki dangin mijin nan nata ne suka sakata kuka ba ruwan Ya Yash
kinga yadda jikin sa yayi sanyi
ai ba laifin sa bane.”
A hankali Siyama ta
nemi guri ta zauna sannan tace
“I hope so dan ba na so su fara samun matsala da shi.Allah dai ya sa ta gaya mana.”
Cike da assurance Jidda tace “za ta fad’a inshaaAllah..idan na bayar da shawara ne sai mu bata idan kuma munga ya fi k’arfin mu sai mu s
anar da su Innaa dan ba zai yiu mu zuba ido ba…kwata kwata fa yau ne ta yi 4 days a gidan.
Ahankali Siyama tace
“InshaaAllah ma k’aramin abu ne Allah ya sa ba wani babban issue bane ba.”
Ya Musbah yana fita daidai motar su Nafi’u tana tashi,sarai y
a san ya gan sa amman haka ya murza giya ya ja sukayi gaba.
Shiruu ya yi kawai ya fad’a duniyar tunani a hankali ya nema waje ya zauna akan d’an dakalin k’ofar gidan ya buga uban tagumi…Bai tab’a samun matsala da Nafi’u ba tunda yake sai a kan Baraka,shiy
asa ya ke jin tsoron tunkarar su Baba ma da maganar dan ya san suma akwai matsala
shi kuma a yadda yake jin Baraka in har aka hana sa ya maida ita to tabbas akwai matsala Babba.
Ya jima sosai yana tunani a wajen ya ga motar Yashjub ta yi parking a daidai
k’ofar gidan.Dama tunda suka nufo sa ya gane su dan haka ya d’an k’ura wa motar ido kafin ya mik’e tsaye bayan sun gama parking d’in.
Murmushi ya yi ganin yadda Manubiya ta fito har tana d’an tuntub’e shi kuma Yash d’in yana cewa ta yi a hankalin
yana mai zagaya wa da sauri inda take.
Yana gani Yadira ta bud’e k’ofa ta fito dan haka ya d’auke kai ya maida hankalin sa ga Yashjub yana mai ce masa “Ashe kuna tafe barka da zuwa mu shiga daga ciki mana”
murmushi Yashjub ya yi yana mai jin dad’in yadda
ya Musbah ya amshesa sam bai rik’e kukan da ya baro Manubiya tanayi a rai ba.
Cikin jin dad’i ya cewa ya Musbah “ya gajiyar ku”
“Alhamdulillah”yace kafin cikin yanayin sigar zolaya yace”Yashjub!a k’aida fa sai mace ta yi wata uku take zuwa ganin gida
daganan kuma ita da ta dawo sai ta haihu”
Wani kallo Manubiya ta yi masa kamar za ta yi kuka
sai kuma ta fara bubbuga k’afa tana cewa “dan Allah kar ka fad’a ya ji,Allah ba zai d’auka da wasa kake ba”
Da sauri ya tsare gida yace
“Au ke a naki tunan
in wasa ne?”
Sai kuma ya kalli Yash yace
“Dagaske Yash ba a zuwa sai bayan wata uku”
Jin jina kai Yashjub ya yi shima in a serious way yace
‘’ai ban sani ba,yanzu kam mun riga mun zo dama kuma shima saboda za mu yi tafiya ne shine muka zo yi muku sa
llama,amman daga wannan zuwan kam inaga sai in ta haihu d’in kenan’’
Kan Ya Musbah Manubiya ta yi ta na cewa”Allah bana so ka daina”
Ganin ta na shirin fara kuka ne yasa duk suka saka dariya wanda hakan ne ya sanya ta fahimci zolayar ce dan haka ta kom
a gefe ta chuno baki gaba.
Murmushi Ya Musbah ya yi yace”yi hkr mana”ya fad’i hakan kamar yana lallashin wata y’ar Yarinya.Yadda ya yi d’in ne ya sanya murmushi sub’uce mata ba tare da ta shirya ba.
Daganan ita da Yadira wadda ko kallo Ya Musbah bai ishe
ta ba balle ta gaida shi sukayi cikin gidan Ya Musbah da Yashjub kuma suka nufi masallaci…ba ya son case ko ta kawo masa raini a gaban mutane shiyasa kawai ya rabu da ita,yana addu’a a cikin ransa Allah ya sa in sun shiga ta gaida su Inna a d’ayan b’angare
na zuciyarsa kuma yana mamakin how Daddy failed to see how wrong and rude behavior d’insu Yadira yake.
A fanfon masallacin sukayi alwallah duk da masallacin yanada matuk’ar kyau amma yana alwallar yana aiyyana yadda zai sake gyara masallacin duk da insha
aAllah ya san su Baba sun kusan tashi dan ya gama siya masu gida amman yanaso kawai ya gyara masallacin saboda yana daga cikin tarihin rayuwarsa.
Ba su dad’e da shiga ba Baba ya shigo kusan a tare shi da su Baba Habu
Da mutuntawa Yashjub ya gaida su b
a yabo ba fallasa suka amsa shi daga haka suka koma gefe shi kuma da shi da Baba suka d’an gaisa sama sama suma dan ba su wani tsananta magana ba sakamokon a masallaci suke kuma Allah ya taimakesu babu Kaka mallan wanda kwana biyu yake fama da zazzab’i da
sai gaisuwar ta fi haka.Cikin nutsuwa aka gabatar da sallar Magrib d’in
Ko da aka idar bayan an gama gaishe gaishe.
Yashjub a masallacin ya zauna dan yana son ya yiwa Ya Musbah magana…..sam bai ji dad’in yadda Ya Musbah shima ya k’i amincewa da maganar
tashin nasu ba dan kamar yadda Manubiya tak’i yarda ya chanja musu gida hakanan shima yak’i amincewa amman dai ya ce zai sanar da su Innaa su saka masa albarka but ya san suma bazasu tab’a yarda ba.
Sun jima suna kai ruwa rana kafin daga baya Yashjub ya h
ak’ura kawai ya rabu da shi ba wai dan ya hak’ura ba sai dan ya basa time ne ya yi nazari kafin ya sake zuwa masa da zancen.
Sai da aka yi sallar isha tukunna Yashjub ya shiga ya gaida Inna.
Tsaraba ya so ya siya musu amman babu lokaci kuma ya lura kam
ar C I D aka turo Yadira dama shi kuma ba ya son case a halin yanzu,shiyasa sai da ya bari su Manubiya sun dawo daga wajen Aisha dai dai sun zo tafiya kenan tukunna ya damk’awa Muhsin kud’i yace da shi da Siyama da Jidda naira dubu hamsin hamsin
Ya so ya
basu wanda ya fi haka amman ya lura ba lalle su karb’a ba idan ya fi hakan
Dan dubu hamsin hamsin d’in ma sai da ya yi dagaske tukunna Muhsin ya k’arba musu…dan shi Yaron kud’in ma tsoro suka basa gashi saida Yashjub d’in ya ga su Jiddan sunyi gaba su d
a Manubiya tukunna ya basa.
Har mota suka rakasu kuwa Manubiya ta so ta shiga ta ga Mama amman sai Yashjub yace mata “ta bari taa ganta next time yanzu dare yayi,ya na so su yi sauri su je su had’a kayayyakin su saboda gobe siyayya za su yi na tafiya ji
bi kuma 6 za su bar k’asar…”
Ba dan ta so ba ta bari akan za ta kira ta ta yi mata sallama,cikin share kwallarta ta shiga motar ta zauna dan tunda aka zo tafiya ta k’ank’ame Inna da kyar ta cika ta su Jidda suka raka ta har mota suka wuce.
Su Jidda
sunso su yi maganar da suke son yi da Manu d’in su samu su tambayeta menene matsalar ta amman Yadira ta kafa ta tsare….da kyar aka ci sa’a ta gaida Inna, k’iri k’iri da aka zo yin alwallah ta k’i shiga toilet tace wa inna “idan suka k’arasa gida za ta yi”
Babu bak’ar magana babu rashin kunya amma yadda ta dinga wani d’ari d’ari tsaf kana gani ka san kyankyamin gidan take yi kuma kamar gadin Manubiya take yi tana nad’ar zance dan idanuwanta kyar a kan kowa…
A b’angaren Yadira kuwa,tsoron Yash ne kawai y
a hanata yiwa su Yasira videon d’akin…ashe daman a inda suka d’auki Manubiya ba nan ne asalin d’akin su ba,ashe dama Babanta gurgu ne??..
Shiyasa ta na zama ta zaro waya ta hau watsapp hatta kalar k’ofar band’akin su Manubiya da komai sai da ta zaiyyane
wa su Yasira a group…..
Washegari da sassafe Ya Musbah ya gagara gane kansa ko aiki ma ya kasa zuwa,ganin
yana neman mutuwa ne ya sa ya mik’e ya fad’a toilet ya yi wanka dama Muhsin ya dad’e ta tafiya makaranta.
Da kyar ya samu ya kimtsa dan kamar mu
ryar Baraka ya ke ji a duk wata kusurwa ta d’akin…a daddafe ya fito ya sakawa d’akin nasu key ya nufi
d’akin su Inna..ya san inna za ta ga kamar ya yi mata tsaurin ido amma kuma hakan shine kad’ai option d’insa…
A zaune ya sameta tana nad’e kayanta da
na Baba tana gyara musu wajen kayan dan Jidda ma bata nan ta tafi makaranta dan har sun koma, gaba d’aya tashi d’aya duk sai ya ji kunyar Innar ta rufe sa amman kuma ya kasa hana kansa abunda zuciyar sa ta ke so…….MANNUBIYA
(Book 2)
Page 25
Na
Humayrah Bulama
Ganin ya koma ya zauna ya yi shiru bayan sun gaisa ne ya sanya Inna ta ajjiye kayan dake hannunta ta mik’e ta k’arasa inda yake ta zauna.A hankali tace”Da!na ce ba zan yi maka magana ba nima,amma kuma na ga ab
un naka kullum k’aruwa yake yi.Jiya dai Baba ya ce mini yana tunanin matsala kuka samu kai da Nafi’u kwana biyu duba da yadda kukayi jiya kai da shi a gabanmu,sai dai kuma ni ina kokwanto.
Dan haka inaso Musbahu ya gaya mini meye ne yake damunsa kwana biy
un nan?ko ya fara b’oyewa Innar sa abu ne bata sani ba?”.
A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa kafin yace
‘’Inna kunyar ki nake ji shiyasa kika ga na kasa gaya miki,”
da sauri ta kamo fuskar sa da hannu biyu ta d’ago da shi kafin tace”kunya ta kuma M
usbahu?ni ce ma kenan silar damuwar taka?.Gaya mini kar ka d’auki lokaci, Ina sauraron ka, ka gayamin ko ma menene yanzunnan.’’
Ahankali ya Musbah ya kama hannayen nata duka biyu yana jin wani nauyin ta da kunyar ta
tukunna da kyar kamar wanda dama