Showing 240001 words to 243000 words out of 259716 words

Chapter 81 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

64

gunki dan haka gwaggo Suwaiba ta ja ta ta kaita kan kujerar da ta taso ta zaunar da ita ta rungumeta tana wani irin kuka kira take”Mannubiya ki yi kuka,da

n Allah ki yi kukan nan ko kya rage zugi da zafin zuciya……..”

Dai dai nan Baraka ta shigo d’akin d’ankwalinta rik’e a hannu,haka kurum d’azu suka ga ta fita a rikice yanzu kuma gata ta dawo a hargitse!!!!

Ba ta ita suke ba shiyasa babu wanda ya ko sake k

allonta ma har ta Isa ta je ta bintik’e Manubiya daga jikin Gwaggo Suwaiba ta mik’ar da ita cikin tsananin tashin hankali tace”Manu ya ake ciki?”

Girgiza kai Manubiya ta yi cikin rauni ta durk’ushe a wajen tana k’ok’arin janyo kuka amma sam ya k’i zuwa!

Sake mik’ar da ita Baraka ta yi tace”ta mutu kenan yanzu shikenan??”

Cikin fara jin haushinta gwaggo Suwaiba tace”ta rasu zaki ce Baraka ba wai ta mutu ba kuma addu’a za ki yi mata ba hauka ba!”

D’amara Baraka ta yi da d’ankwalin Hannunta tace”ki gaya

mini tsakaninki da Allah

A tsakankanin jiya da muka rabu da ku zuwa yau shin ta bi ta kan k’ofar band’akinta ta wuce bi ma’ana ta shiga b’andakin ta kafin ta mutu!???”

Cikin k’unci Ya Musbah yace”Baraka bar nan!!”

Kan sa ta nufa tana zuwa ta tsaya

a gabansa tace”Amsa d’aya za ku bani sai in tafi!!

Shin kafin Inna ta mutu ta bi ta kan k’ofar band’akinta? ‘eh’ ko ‘A’a’?

Dan Allah ku bani amsa in san makomata saboda idan ba ta wuce ta shiga band’akinta ba akwai matsala fa!!wallahi akwai matsala!!!!”.

Sai kuma ta nufi Inna tana zuwa ta fara k’ok’arin ruk’ota tana cewa “Allah yau sai kin tashi kin fad’a mini kin bi ta kai ko baki bi ba,ki tashi idan ba ki

bi ba to ki bi yanzu a gabn idanuna in gani…..”

Dai dai na Ya Musbah ya k’araso ya juyo da ita y

a d’auketa da wani rikitaccen mari.

Kuka ta fashe da shi tace”ba ta haukace ba ta mutu ni kuma na haukace!!!saboda Allah in banda mugunta irin nata ta ya zata kwanta ta mutu ba tare da ta bi ta kan abunda na zuba mata ba?

salon ta jaza mini bala’i!!!!” s

ai kuma ta fincike ribbom d’in kanta ta hau barbaza gashin kanta ta fara tsalle tana dira tana cewa”ai ku barshi ba sai kun fad’a mini komai ba ma,yadda na fara ji a jikin nan nawa na san ba ta bi ba ni kuma asirina ya dawo kaina,Innalillahi wa inna ilaihi

rrajiun mun tafi ba zamu dawo ba,da ni da Inna mun tafi inda ba a dawo wa!! ita ta tafi garin matattu ni kuma na tafi garin mahaukata daga ni har ita ba zamu tab’a dawowa ba!!

Bokan yace mini asirin baya karyewa ba a tab’a iya k’aryawa…”

Daga haka ta ju

ya ta kinkimi takalmin da ta gani a k’ofar band’akin ta rungume ta fice da wani irin mahaukacin

gudu tana kurma uban ihu!!!…

Iyaka maganganunta sun isa su faiyyace musu komai!!!shiyasa kawai duk suka bita da ido kowa yana Allah wadai!!!.

Halin da su

ke a ciki bai sanya kowa ya sake bi ta kan Baraka ba..tana wucewa suka ci gaba da koke kokensu.

Kafin awa d’aya gidan ya cika taff har da matan su Uncle da Mama kowa ya hallara har Najeeb da Siyama su Jidda ma sun ce suna airport.

A nan parlourn Ba

ba mai k’ofa ta baya Gwaggo Suwaiba da Mama suka yiwa Inna wanka amma da ikon Allah ana gama yi mata wankan Gwaggo Suwaiba ta hana a yi mata sutura har kawo yanzu kawai dai sun rufa mata zani sunata yi mata addu’a ita kuma ta k’ura mata idanu tana ta kall

onta.

…….

Najeeb da Manubiya sun kira Yash amma bai d’aga ba kuma bai biyo kiran ba shiyasa Najeeb yace bari ya je gidan ya dubosa.

Tun cikin dare Yash ya kasa barci sakamokon mummunan mawuyacin halin da ya dinga ganin Mommy da Ya’isha a ciki a mafark

i…shiyasa ya kasa hak’ura duk da yadda Mommy ta ja masa kunne kar ya je inda suke! k’arfe bakwai ta na yi ya fita ya nufi gidan saboda ko rufe idanunsa ya yi kamar Irin a cikin gobara haka yake ganinsu shiysa ma ya yi tunanin ko gobara ce ta kama a gidan g

ashi duk d’insu babu mai d’aukar wayarsa.

Yasira,da! ta yi fushi tace Wallahi Hatta office d’in ma ta daina zuwa amma sai Mommy da Y’aisha suka yi mata magana jiya da daddare suka ce “ta je ai bazasu zuba masa ido su kyalesa hakanan ba kuma idan ba ta

je ba tsaf zai iya d’aura Ummi a kan komai tunda Yash bai gama resumin aiki ba”…dan haka ta shirya saboda dama yau ta san da zuwan manya manyan bak’i.

Tare suka fita ita da Yusra wadda zata ga invigilator d’inta a yau,ta sauk’e Yusran ita kuma ta wuce

office……

Sosai yau Mommy take jinta a sama ta dad’e bata samu soundsleep kamar na jiya ba saboda ta riga ta san yau zata ji labarin mutuwar Manubiya….:

Tun a jiyan da suka gama magana da Ya’isha ta yi musu sai da safe ta shige d’aki har suka gama bre

akfast su Yasira suka fice sam Mommy ba ta ji motsinta ba dan haka ta lek’a d’akin da yake mallakinta..

Da wani irin mahaukacin gudu ta k’arasa cikin d’akin sakamokon hango Ya’isha da ta yi wanwarr a k’asa a yashe…..

Tana zuwa ta d’agota ta d’aurata a ka

n cinyarta ta shiga kiran sunanta amma ko gezau!!

Duddubata ta hau yi amma sam ba ta ga alamun rai a tartare da Ya’ishan ba ga idanunta sun k’afe suna kallon sama wanda hakan ya sanya tashi d’aya Mommyn ta fashe da wani irin kuka ta rungumeta da k’arfi a

jikinta cikin kuka ta shiga cewa “I’m so sorry Ya’isha Innalillahi wa Innailaihirrajiun….”

Sai kuma ta mik’e zumbur ta fita waje

Sai da tabbatar ta kulle ko’ina sannan babu kowa tukunna ta koma ta d’auko makullin mota da Hijabi ta zo ta bud’e boot d’in

motar gudun kar a kamata dan motarta babu tint.

Tana wani irin kuka ta je ta kinkimo Ya’isha da kyar ta sakata a booth hakanan tana ji tana gani ta rufe y’ar tata a booth a ranta tana k’iyasta yadda zata yi da su Yashjub muddin ta samu Ya’isha ta farfad

’o dan wannan duk laifinsu ne!!! tunda uwarsa ta shigo rayuwar Daddy har yau ba ta samu kwanciyar hankali ba,gashi yanzu saboda shi da Manubiya ta zo wannan flat house d’in d’an mitsitsi ta zauna sannan kalli a booth ta saka y’arta yo

Idan bata ga bayan s

u Manu ba ma ai ba ta cika sunanta Khadija ba wallahi…..

Sannan ad’uarta d’aya Allah dai ya sa ba aikin bane ya lalace Allah ya sa dai abun ya kama Manu dan tabbas jiya Ya’isha tace mata bata yi mistake ba to amma kuma mai ya faru!!!?me yasa abun ya tab’a

mata y’a!!!!?

Hakanan tana ta sak’e sak’e hankalinta a masifar tashe ta je ta zuge gate d’in tana wani irin kuka…tana gama zugewa ta koma ta fitar da motar ta fito ta mayar da gate d’in ta rufe ta koma ta ja motar ta nufi gidan tsohon jiya ta san shi kad

’ai ne zai iya farfad’o mata da Ya’isha………

Sosai tun d’azu Yashjub wanda sam ba ta lura da shi ba ya ke tsaye yana kallonta yana mamakin yadda take kuka sannan yadda ta zuge gate da kanta ta fita da asussubah haka abun mamaki ne tabbas.

Sai da ta I

sa k’ofar gidan tsohon tukunna ta tuna ba ma d’auko wayarta ba balle ta kirasa ya bud’e mata dan haka kawai ta fito ta Isa bakin k’ofar gidan nasa ta hau bugu.

Ba ta wani dad’e tana bugawa ba tsohon ya zo ya bud’e mata k’ofar dan dama da ga shi sai

dab

bobi ne a gidan

A rikice ta afka ta tura k’ofar ta rufe cikin tsananin tashin hankali tana ganin dishi dishi tace masa”Mun wayi gari

babu Ya’isha,ka taimaka mini ka san yadda ka yi y’ata ta dawo

Ina son y’ata ita kad’ai ce ba ta tab’a yi mini jayayya

ba wallahi!

sannan in har su Yasira suka ganta haka sun san ni ce sun san me ya faru tunda a gabnsu aka fara maganar jiya na san wallahi ba za su tab’a yafe mini ba!!! dan girman Allah ka yi wani abun….”

“Biyo ni”

Kawai yace daga haka ya nufi cikin

gidan….

Wajen Birin jiya suka je kamar jiyan suna zuwa birin ya matsa musu shi kuma tsohon ya saka hannu ya d’aga dutsen tun kafin ya d’auko babyn robar ya kwab’e fuska ya ce “too ikon Allah mai ya faru kenan?”

Da sauri Mommy ta matso tace”ya akayi?

mai ya faru?

Ba dai aikin ne ya lalace gaba d’aya ba ko??

Ta yi masa tambayar a gigice

Girgiza kai yayi ya sa Hannu ya d’auko Babyn robar tukunna yace”gaskiya kunyi kuskure amma bansan ta Ina ba!sai dai kuma yadda y’ar tsanar ta yi bak’i hakan yana

nuni da aiki ya ci ya kama,kuskuren ne ban fahimci ta ina kuka yi ba

Saboda tunda har ya shafi Ya’isha tou tabbas akwai wani abu da kuka yi ba daidai ba.”

Sai kuma ya kalleta yace”ke fa??lafiya kike jin ki dai ko??”

Jinjina masa Kai ta yi da farko sai

kuma tace”idanuwana dai suna ta yi mini dishi dishi tun d’azu!!!!”

Jin jina kai ya yi ya sauk’e ajiyar zuciya yace”idanunki ne kenan zasu tab’u,sai kuma ya mayar da gabaki d’aya hankalinsa gareta yace”idan kinaso za a iya karyawa amma in aka karya ba l

alle a sake yi mata ya kamata ba sannan babu tabbacin Ya’isha za ta tashi sai dai mu gwada sa’ar mu!”

Kuka ta fashe dashi tace”kamar ya zaka ce mini Ya’isha ba za ta tashi ba!!idan fa Yarinyar nan ba ta tashi ba wallahi na san duk su Yasira sai sun fahi

mci komai kuma ba za su tab’a yafe mini ba k’arshentamasu tona mini asiri…”

Cikin tarar numfashin yace”ai

dama sai da na gaya miki aikin yana buk’atar taka tsantsan yanada hatsari….”

Cikin yi mata nuni da babyn robar yace”dan ci kam aiki ya ci…amma kuma

halin da Ya’isha ta shiga yana nuni da aiki ya riga ya fara tab’arb’arewa kenan…..kuma zamu iya warwaresa….ta you Ya’isha ta tashi ta you kuma ta tafi kenan amma tabbas Manubiya za ta tashi ita wannan a rubuce yake…..”

Cikin tarar numfashinsa tace”to mu

bari mana sai an kaita sai mu warware a tare!”

Girgiza Kai yayi yace”sam ba haka abun yake ba..kuma ni yanzu mintuna uku ne ma

suka ragemini zaki ga y’ar tsanar nan ta kama da wuta (idan har ta kama da wuta to baza a iya warware wa ba)saboda abun ya fita

daga hannuna,daga nan!!

dan haka ki yanke hukunci da wurwuri kin riga kin lalata komai da ke da y’ar ki aiki ba ya hannuna kuma….”

Shiruu ta yi kafin tace”idanuwan nawa da na fara ganin dishi dishi a haka zan dauwwama?”

Shiruu ya d’anyi kafin yace”

akwai taimakon da zan baki,inshaaAllah za a dace”

Cikin sake jeho masa wata tambayar tace”tashin Ya’isha k’ila wak’ala ne ko?”

Jinjina kai ya yi yace”Bari ki ji ba zan b’oye miki ba Ya’isha ba ma na jin tanada rai dan haka ba zan iya yin komai a kai ba s

aboda kun damalmala komai ne,gashi kuma bamusan ma ta ina matsalar take…ga dai aiki ya yi yana ci…to shafarta da abun ya yi ne matsalar shiyasa abun zai fi k’arfina!”

A hankali Mommy ta lumshe idanuwanta hawaye suka zubo cikin d’acin zuciya tace”ka ba

r shi kar ka karya!!!”

Ta ji tsananin zafin mutuwar Ya’isha tabbas amma da ta tuna abunda ya ke faruwa da Manubiya a halin yanzu sai ta d’an ji sanyi ko banza ta san kwalliya ta biya kud’in sabulu!!!!….

Ba ta dad’e da gama rufe bakinta ba Babyn robar t

a kama da wuta tana jin tsohon yana cewa “yanzu shi kansa kam bai san ranar da numfashin Manu zai dawo mata ba aiki ba a hannunsa yake ba sun riga sun damalmala komai!!”

Itadai Mommy ta ji sanyi a ranta tunda ba a warware ba ta san duk bala’i ko nan da

shekara nawa ne Manubiya ba ta Isa ta fito ba!.

Da shi da ita suka yanke shawarar gara su binne Ya’isha maganar ta tsaya a iyaka su biyu dan idan wani ya sani tofa a kwai matsala

Inyaso

Mommyn sai ta ce ta aike ta k’auye kafin su san abun yi,shi ku

ma inshaaAllah zai rufewa duk wani wanda zai d’aga mata hankali wajen tambayar ‘Ina Ya’isha’ Baki.

Hakanan suka je wani k’ungurmi daji ya hak’a rami yana shirin d’auko Ya’isha ya sakata a ramin aka kirasa.

Kiran mai matuk’ar mahimmanci ne dan haka yace

ta yi masa hak’uri dole

zai tafi ta k’arasa sakata ta rufe ramin ta koma gida,hakanan ya wuce ya barta a wajen jikinsa yana karkarwa dan babban mutum ne ya kirasa ya san a k’allan a lalace yau sai ya samu sama da miliyan biyu…..

Tsoro da fargabar daji

n gata tare da gawa ne suka sanya Mommy saka Ya’isha cikin ramin anyhow,ko gama rufewa ma ba ta yi ba hakanan ta yi sauri tabar wajen jikinta ya na karkarwa tana kuka.

Bata wani jima da komawa gidan ba su Yasira suka dawo…

Jikinsu daga ita har Yusra du

k a sanyaye suka gaisa tana mai bin Mommyn da wani irin kallo daga ita har Yusran kafin chan ta d’an yi waige waige tace mata “Ina Ya’isha?” hakanan

Mommy ta had’e fuska tace musu”ta turata k’auye!tunda sun hana a tsayar da numfashi ta turata k’auye zata

yo musu mai sauk’i…”

Shiruu Yasira ta yi kawai Tana kallonta…sam ba ta son ta zargi Mommy amma kuma considering abunda ya faru ta ji ta gani a jiya ya sanya hankalinta ya kasa kwanciya hundred percent da Momyn tun lokacin da ta ji labarin rasuwar Inna…

Ta jima tana tunani kafin tace mata”I hope bakiyi komai ba Mommy”

cikin alhini ta d’aura da cewa”Mahaifiyar Manubiya ta rasu yau!,ki shirye mu je,mu yi musu gaisuwa.”

Daga haka ta mik’e da niyyar kimtsawa ta fito su tafi.

Shiruu ta ga Mommyn ta yi ta sh

iga mugun shock kafin kawai ta ga ta mik’e tsaye.

K’iri k’iri ta hau bori tace musu

“ba zata je ba suma kuma ta hanasu zuwa tace ai suma su Manubiyan jiya ba su zo mata gaisuwar Larai ba!”

Da mugun mamaki Yasirar ta bi ta da kallo har ta shige cikin be

droom d’inta ta banko k’ofar…

Tana shiga ta sak’ala key k’irjinta yana dukan uku uku,ta durk’ushe a nan bakin k’ofar…

kar dai maman manubiya ce ta rasu ba manubiya ba…Gidan babu wuta bata jona wayarta ba babu charji shiyasa bata samu ta yi confirming

ba dama tun d’azu…inna lillahi wa inna ilaihirrajiun kenan yanzu duk wani effort da sacrifices d’inta sun tafi a banza kenan?

Kaii inaa ba zai yiu ba,inshaaAllah ma ba haka bane ba inshaaAllah Manubiya da mahaifiyarta tata ne suka mutu tare…amma kuma inda

Manubiya ta rasu ai da Yasira zata gaya mata…..

Wani Irin bugawa k’irjinta ya shiga yi gashi zuwa yanzu dishi dishi sosai take gani ga wani irin juyawa da kanta yakeyi dan haka ta mik’e da kyar ta k’arasa kan gadonta ta kwanta ta lumshe Idanuwanta tana j

in kamar ta saka hannu a cikin k’irjinta ta kwak’ulo zuciyarta ta jefar tsabar azabar da ta ke yi mata………

Bata da wani ragowar hope d’in da ya wuce tirsasawa zuciyarta’ta tsaya ta d’an jira zuwa anjima zata ji labarin mutuwar Manubiyan itama’.

Saboda she

can’t even begin to imagine Manubiya ba zata mutu ba!effort da sacrifice d’inta sun tafi a banza!.

Tabbas Yasira ta tsorata kuma ta shiga al’ajabi da lamarin Mommy ko bayan shigar Mommyn d’aki har Yusra ta wuce d’aki ita tana nan a zaune ta ma kasa m

otsi kafin da kyar ta zaro waya ta Kira Manu ta yi mata gaisuwa tace “zasu zo inshaaAllah”

Daganan ta kashe wayar ta yi shiruuu…chan ta zaro wayar ta ta danna kiran Ya’isha!

Ta san Ya’isha tanada taurin kai amma zata gwada lallab’ata a samu ta hak’ura da

aikin da Mommy ta turata yi kawai ta dawo,ba wai son Manubiya take yi ba amma Mommy ta wuce gona da iri tun kafin ta kai kanta ga halaka ya kamata a dawo da ita saiti,Wanne Irin bala’i ne har ka tashi mutum gari ya gari dan kawai ya je ya yo maka asiri ya

dawo!har mai ya yi zafi haka…….

Layin Ya’isha yana shiga ga mamakinta kawai sai ta jiyo k’arar wayartata a d’akin da Ya’ishan ta kwana dan haka ta mik’e ta shige….ko da ta je d’akin ta duba ga wayarta har da charger da su AirPod d’inta da watch duk ba ta

d’auki ko d’aya ba sannan kayanta ciff suka ba ta d’iba ba daga gani tun jiya ba ma ta tab’a ba…dan haka kawai ta juya ta fita ta je ta shiga buga d’akin Mommy…

ta fi mintuna ashirin a wajen har Yusra itama ta fito ta jona ta tukunna aka samu Mommy ta bu

d’e,yadda suka ganta dagaje dagaje sannan idanunta duk kwantsa sai da abun ya basu tsoro ya basu mamaki dan haka Yasira ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi amma dukda haka sai cewa ta yi”Mommy ki gaya mini tsakaninki da Allah Ina Ya’isha saboda na duba d’akin

ta Hatta wayarta ba ta d’auka ba!!”

Shiruu ta yi dan ita sai yanzu nema kwakwalwarta ta bata duk waennnan abubuwan…..da kyar ta nemo mafita tace musu”da k’aramar wayata ta tafi saboda hanya, kaya kuma ta d’auki dogayen rigguna biyu. Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login