Showing 222001 words to 225000 words out of 259716 words
take so sai da ta yi mata aiki a Kai ta
samu!!
A b’oye suke yin abun kuma daga ita sai waenda ta yi trusting shiyasa abun bai baza gari ba.
Amma ta ce mini abu d’aya ne har yau ta kasa yiwa kanta aiki a kai shi ne mijin aure dan ko da ta koma wajen bokan ya koya mata duba da ta duba ranar aure
nta ta ga ‘babu!’ hakan bai sa ta yi giving up ba hakanan har gobe take neman mijin aure ido a rufe amma babu shi babu alamarsa.
Ragowar k’awayenta da k’annen k’annen k’awayenta duk sun yi aure kuma ba laifi sun rik’e mata sirrinta ba su fad’awa kowa ba,M
utuwar wannan boka itace ta tona mata asiri dan da ya kusa mutuwa sai ya raba sunanta ma clients d’insa to ta hakane da wata mata ta zo wajenta ta sa ta yiwa d’an kishiyarta asiri ya yi ta rashin lafiya d’aga k’arshe Yaron har ya zo ya rasu..shine fa da bi
ncike ya yi bincike aka ganota aka ce za a k’onata a k’auyen ai mayya ce tunda gashi da ma gata babu miji kuma zan iya ce miki kaff k’auyen mu har yau ba ayi mai kyan larai ba shiysa su kuwa suka ce mata mayya.
Ina gama jin labarinta ko wasi wasi ban ts
aya yi ba na amince da tayinta muka fara aiki babu dare ba rana a kan Khadija da Imam.
Ba a yi sati d’aya ba kusan gaba d’aya hankalin Imam ya dawo kaina yaddda yake treating Khadija nima haka yake treating d’ina sai dai kuma ni kaina na san soyayyar Amar
yarsa ta daban ce duba da yadda ba ya kishi na kamar yadda yake kishinta dan haka muka sake zage damtse aiki ba dare ba rana ga kuma kissa da muka bawa mahimmanci,dan ko
wani abun aka yi sai dai in shige d’aki in yi kuka in goge daga ni sai larai ba ma ta
b’a bari wani ya ji ko ya gani…
Haka kurum kwata kwata sai na kasa d’aukar ciki.
Hankalina bai gama tashi ba sai da Imam ya kwashe dukiyar sa gaba d’aya ya damk’awa d’an cikin anaryarsa !!!
dama chan ba so nake yi Yaron ya zo duniya ba saboda Larai ta
ce mini tabbas Namiji za ta haifa…dan haka Ina jin wannan batun na jajirce na dinga yiwa Larai kuka har sai da ta taya ni muka kashe Yaron tun yana ciki saboda ita Larai ta ce za ta yi komai amman banda kisan Kai dan shi ya rabota daga garinsu ya kusan to
na mata asiri bayaga haka ita har ga Allah ba ta son yin kisa..to kukan da na dinga yi mata da kuma zancen raba dukiya da ta ji ne ya sanya ta biye mini a wanchan lokacin.
Tun daga nan muka k’ara k’aimi akan asirin da muke yiwa Khadija akan ta bar gidan
Imam,mu bata ta ci ta sha mu zuba mata a ruwan wanka amma sam abu ya k’i yin tasiri a kanta kwata kwata ba ta ma da shirin tafiya,abun yana kama ta ba wai ba ya kama ta kwata kwata ba kawai dai ba ya yin tasiri a kanta.
A kwana a tashi a haka har muka
samu ciki a tare ni da ita…
Tunda muka samu ciikin Larai take aiki Akan ni in haifi Namiji ita kuma ta haihu babu rai kamar yadda ta yi na farko…cikin yana yin watanni biyar Larai ta fahimci Tabbas fa Khadija sai ta haihu kuma Namiji za ta haifa sannan Y
aron mai tsananin albarka ne dukkannin abunda ya saka a gaba sai ya cimma kuma attajiri ne mai masifar kud’i sa’a da nasara ta ko wanne angle na rayuwarsa!.
Sai da na suma a tsaye dan hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba saboda a ranar ne na lab’e musu na
ji Imam d’in yana sake damk’awa cikin jikin Khadija dukiyar sa kamar yadda ya yi a na farko ita kuma tace ba zai you ba shine yace mata to a cikin mu ni da ita duk wadda ta haifi Namiji ita za a bawa shiyasa na nufi wajenta a hargitse dan na San idan muka
yi kunnen doki tsaff Imam zai yi son kai.
Shiyasa na nufi wajen larai direct mu samu mu tattauna ita kuma ina shiga
shine ta tare ni da wannan zancen….
Da kyar sai da Larai ta yayyafa mini ruwa tukunna na dawo haiyyaci na da kyar.
Ganin Ina shirin
had’iyar zuciya in mutu ne ya sanya tace mini Y not mu musanya Yaran ni in karb’i mai albarkar..tashi d’aya tun kafin ta k’arasa na k’i amincewa na ce kawai a cigaba da aiki a kansa ta yadda ba zai yi albarka ba kuma ya yi rayuwa mara dad’i mara nasara ya
mutu wulak’antacciyar mutuwa,tunda mun riga mun san sai fa ya zo duniya.
Wani babban tashin hankalin saida na yi scanning na tabbatar ni mace zan haifa saboda ban tab’a kawowa zan haifi mace ba duba da yadda muka dinga aiki a akan in haifi Namiji.
A
wannan lokacin ma Baba larai ce ta sake bani shawara kamar farko a kan mu musanya Yaran idan bayan mun haihu an bayar da dukiyar idan ma kashe Yaron za mu yi sai mu yi tunda dai Yaro yana a hannunmu ai tsaf za mu iya yin kome muka ga dama sab’anin yanzu da
yake a ciki.
Tashi d’aya na amince dan na gamsu kuma na fahimta…tun a lokacin muka san yadda muka yi muka siye likitan da muke zuwa asibitin wajensa ta hanyar yarda da shi da Baba Larai ta yi bayan ya fad’i mana hakan kawai yake da buk’ata daga garemu.
A ranar da na fara labour muka bata magani itama muka tayar mata da labour ta hanyar ba ta kwayar da ya bamu a ruwa ta sha ba tare da ta sani ba.
Tana shiga d’akin haihuwa gudun kar ta fahimci wani abun aka shak’a mata anesthesia aka yi mata cs
Kusan
a tare muka haihu
Ita aka fito mata da Yashjub ni kuma na haifoki Likitan da nurse d’in da Baba larai suka yi sauri suka sauya aka fitar da ke a matsayin Y’ar da ta haifa ni kuma bayan y’an mintuna aka fitar da Yashjub aka ce na haihu.
Daddy ya bada ra
bin dukiya kamar yadda ya yi alk’awari amma fa ba ni da burin mallakar wannan dukiya kamar yadda nake da burin kashe Yashjub saboda kwata kwata ko fuskarsa ba na son kalla gashi aka tilasta mini hakanan Ina ji Ina gani na dinga shayar da shi.
Kwatsam!!in
a ta shirye shiryen yadda za a yi in raba shi da duniya ba tare da kowa ya zargemu ba sai ga ciki a jikina cikin y’an biyu mai wahalar laulayi.
Tun cikin yana da watanni hud’u Baba Larai ta fara mafarkai marasa dad’i game da Yaron da zan haifa..Tabbas mun
fahimci Namiji ne kam wannan karon ammafa Yaron kwata kwata bashi da albarka ga kuma mutuwa da zai yi wulak’antacciya idan har bai yi arzik’i ba!!! sannan duk abunda ya soma to ba zai yi albarka ba…hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba dan sai da jini na y
a hau na kwanta a asibiti sau bakwai saboda wannan duba da Baba larai ta yi ta gano mini bala’i..sai da muka nutsu muka yi lissafi Sosai muka bincika tukunna muka gano Ashe asirin da muka yiwa Yashjub tun kafin ya zo duniya ne ya fad’a a kan Yassir tunda a
sirin an yi sa ne a d’an Khadija matar Imam kuma kinga nima sunana Khadija sannan ko bayan da muka fahimci abun bai kama Yashjub ba bamu damu mu yi wani abun a kai ba dan kwata kwata ba mu kawo cewa zai fad’a kan Yassir ba bayaga haka babu ma ta yadda za a
yi mu karya abun saboda ba zamu iya nemosaba dan a babban ruwa mai tafiya muka jefa dan haka kinga la shakkah ba ma ya cikin Nigeria ya bi ruwa.
Babu abunda ba mu yi ba babu abunda bamu gwada ba amma idan muka yi aikin muka gwada in banda wasu sabbin m
asifu a kan na da babu abunda muke gani a tauraron Yassir amma ita d’ayar Yarinyar lafiya lau dan zuwa wannan lokacin mun fahimci twins ne.
Kamar kullum a wannan lokacin ma Baba larai ce ta kawo shawarar’mai zai hana mu yi hak’uri mu taushi zuciyoyinmu
mu raini Yashjub tunda shi zai yi albarka in ya so idan ya girma ya gama tara abunda ya tara sai mu San yadda muka yi muka d’aura Yassir a kan dukiyar sa shi kuma mu kashesa komai ya dawo hannun mu in ya so sai Yassir ya kula da komai tunda ba Yassir d’in
ne ya fara tara wa ba ta san komai zai tafi cikin sauk’i abun zai yi albarka dan shi Yassir d’in abunda ya fara ne dakansa ba zai yi albarka ba.inshaaAllah komai zai yi kyau.
Sannan idan hakan ta faru babu batun wulak’antacciyar mutuwa a Yassir tunda a y
adda ta gani sai idan ya rasa komai ya rasa kowa tukunna wannan al’amarin
zai faru da shi.
Ko kad’an ban yi mata jayayya ba dan nima plan d’in ya yi mini d’arr bisa d’ari.
Dan haka muka tashi muka tsaya tsayin daka na danne zuciyata na ja Yashjub a ji
kina na kula da shi duk dan saboda y’ay’ana sai dai kuma tun lokacin da Yashjub ya kai shekaru 5 a duniya na fahimci kamar ma ya tsane ni!sam ba ya son magana ma da ni ba ya son shiga jikina baya jan y’an uwansa a jiki…
Gashi duk ciki mahaifinku ya fi son
shi
Daga k’arshe ma Hajiya mama ta d’aukesa gaba d’aya ya koma wajenta…na so ya dawo a wannan lokacin amman a banza dan yadda Hajiya mama ta ga na d’aga hankalina na san shiyasa ita kuma ta ce ba zai dawo ba.
Yashjub tun yana zuwa mana
hutu sau 2 a
shekara daga baya ya koma sau d’aya ko
bayan shekaru biyu daga k’arshe ma ya daina sai dai Daddy da su Yassir su je ni kuma a lokacin mun yi kacha kacha da su Hajiya mama tace idan ta ganni a inda take sai ta yi mini abunda ban tab’a tsammani ba.
Tun
Yashjub yana shekaru 17 na so ya fara saka su Yassir d’in a jikinsa da suka girma suka yi wayo nan ma na yi masa maganar ya fara saka shi a business d’insa amma ya k’i na zo nace to ya bashi jari nan ma ya k’i gashi a lokacin na fahimci son kan da Daddy ya
kuma yi a share na company d’insa shima
gashi shi Yashjub d’in ba ma ya nan ballantana in san yadda zan yi in yaudare sa ya ja d’an uwansa shi kuma asiri bai cika tasiri a kan sa ba kamar Khadija
Hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba da na ji kishin kis
hin d’in Na’ima ta ce wa Yassir Yashjub take so dan dukda cewa na san mun cire masa son mata da sha’awar su a rai amman kuma na san in dai har Na’ima ta gayawa su Daddy tana son shi tofa dole ya aureta kuma yau da gobe sai Allah na san duk abunda muka yi
dole wata rana Na’ima ta iya samun ciki…Shiyasa muka k’arawa abun namu k’aimi gaba d’aya ya kuma tsanar mata sannan muka fara aiki a kan ya dawo a yi ayi ya d’aura Yassir da Yassira a kan komai na dukiyar sa mu samu mu kashe sa dan na yiwa kaina alk’awar
in jinin khadija bai Isa ya rayu ya ji dad’i har ya yi aure ba,saboda yadda Yashjub da mahaifiyar sa suka d’aga mini hankali he don’t deserve to live
That is my revenge….
Kwatsam!! Sai kuma tauraruwar mace ta fara b’ullowa wadda Baba larai tace ita z
a ta kawo
k’arshena muddin muka bari aka yi auren….
Yo dama ai ko ina hauka Yash bai Isa ya yi aure ya haihu ya ji dadi sannan Yaro ya shigo cikin gadon sa ba….ga kuma maganar matar ma ta zo har da su kawo k’arshena shiyasa na tsani kuma bata son Manubiy
a kamar mutuwa ta!
Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta kalli Yahanasu tace”yanzu na san kin fahimci dalilina na aikata duk wani abunda na aikata kuma inda ace ba na sonki ko ban d’auke ki a matsayin jinina ba Yahanasu da ba zan tab’a zama in faiyyace
miki komai in bud’e miki cikina kamar haka ba!!
Na san na yi laifi na san na yi kuskure amma Daddynku shine ummulaba’isin komai da na fara aikatawa sannan da tafiya ta yi tafiya na san kin fahimci saboda Yassir da kuma ku na aikata ragowar abubuwan da na
aikata.
Sannan Manubiya had’ari ce ga rayuwata shiyasa ya zame mini dole in….”
Cikin tarar numfashinta Yahansun tana wani irin kuka kamar ranta zai fita tace”Mommy babu ruwan Mannubiya da duk wani abu da ya sameki da kuma yake shirin samunki Ubangiji
ne ya fara nuna miki k’arshenki!!…”
Wani irin abu ne ya rik’e mata zuciya da mak’ogaro dan haka ta yi shiru numfashinta ya tsaya da kyar ta samu ya dawo ai kuwa tashi d’aya ta mik’e ta kamo hannun Mommy ta fara janta sai da suka isa bak’in k’ofa tukunna t
a bud’e ta had’e hannuwanta waje guda tace”dan girman Allah ki fita,ki fita kafin ki sa zuciyata ta buga!!!!”
Tabbas Mommy ta fahimci tarkon ta ya kama kurciya Yahansu ba za ta iya yin komai ba kamar yadda take ik’irari kuma yadda ta bud’e mata cikinta
ta fad’a mata sirrin ta ta san hakan ma sake k’ulle Yahansun ta yi da jijiyoyin jikinta dan haka ba za ta iya yin komai ba.
Shiyasa kawai ta shafa fuskarta a hankali ta d’an goge mata hawayenta daga haka ta sa Kai ta fice hankalinta a d’an kwance dan tun
d’azu da Yahansu tace’ guilty conscious zai addabeta idan ta fad’i abubuwan da ta aikata aka hukuntata’
Ya sanya ta fahimci all she needs to do shine ta sake nunawa Yahanasu itan fa itace mahaifiyarta kuma tana sonta daga nan ta san za ta yi silencing d’i
nta shiyasa ta bud’e mata cikinta saboda tana so ta ga ta yarda da ita kuma ta d’auke ta y’a.
Kafin ta gama fita daga shock ta dawo dai dai ita kuma InshaaAllah kafin nan da lokaci k’ank’ani za ta san yadda zata da su Daddy za ra san yadda zata yi
dist
roying d’insu gaba d’aya ta kawo k’arshen su kar ma su sake bata ciwon kai
Mommy tana fita da sauri Yahanasu ta mayar da k’ofar ta rufe k’irjinta yana dukan tara tara dan bayaga haushi da takaici har ga Allah zuwa yanzu kam tsoron Mommy take ji Any
a kuwa Mommy tana da zuciya a cikin k’irjinta??ita da Baba Larai anya kuwa za su ga Annabi?ashe dama akwai mutane irinsu har yanzu a duniya?
A da ita tana jin haushin Mommy saboda abubuwan da ta yiyyi ashe ba ta ji duka ba ba ta san duka ba!!!!
“Innalill
ahi wa inna ilaihirrajiun”
Ta shiga ambato a cikin zuciyarta kanta yana wani irin sarawa…tabbas kamar yadda Mommy ta yi zato a yadda ta zauna ta bud’ewa Yahansu cikinta hakan ya sanya Yahanasun ta d’an ji d’arr sannan kuma ta yarda Mommy ta d’auke ta a m
atsayin y’a!!
Ba wai ta yafe mata abubuwan da ta yiyyi ba kawai dai hakan ya sanya ta sake fad’awa cikin duniyar tsoron tona mata asiri saboda ta san guilty conscious ba zai bartaba no matter what uwa uwace gara kawai ta barta Ubangiji ya nuna mata iyakar
ta…
Ba za ta sake da ita ba ba kuma za ta kula ta babu ruwan kowa da kowa kamar da dan tabbas Mommy ba uwar da zaka sake ka yi mu’amala da ita baceba,she is everything Bad!…..
Sai da Baba larai ta yi sati d’aya tukunna Mommy ta basu izini suka fara n
emanta sai dai kuma babu kalar kiran da ba su yi mata ba amma wayarta ba ta shiga kuma sun kira k’auyensu ance bata je ba dan haka hankalinsu ya tashi matuk’a.
A b’angaren Kausar da Yassir kuwa ko da yayi mata maganar aurenta da Yashjub nuna masa ta y
i itama ba ta so kuma ta yi abunda ta yi ne saboda ta yi tunanin Yash d’in zai fara bata wani abun daga cikin dukiyar sa ko ya ba ta gida ya ce ta zauna a inda za ta je d’in…amma ita sam ba ta yi tunanin su Daddy za su yi musu aure ba.Dan haka ya taimaka y
a taya ta nemo Yash ya sauwwak’e mata ita kam aurensa ba ya cikin plan d’insu.
Sai da Yassir ya nuna mata b’acin ransa na k’in tuntunb’arsa da ta yi kafin ta yi abun ita kuma ta basa hak’uri tare da alk’awarin ba za ta k’ara ba tukunna ya yi mata alk’awar
in nemo Yash a duk inda yake ko ta message ne a samu ya sake ta…Hakanan suka rabu daga shi har ita babu wanda ya san ba aure ma tsakanin Kausar da Yashjub d’in.
Bayan kwana biyu ta san yadda ta yi ta bincika wayarsa ta d’auki number mutanen nan masu evide
nce ta b’oye numberta ta tura musu message tace”su turawa Yashjub da duk wasu mutanen da suke neman wanda ya yi aika aika a Estate d’in Yashjub za ta basu ko nawa ne.”
Saboda ita har ga Allah Yassir ya ishe ta kuma ta san idan ba kama sa aka yi aka kash
esa ba to tabbas ba zai barta ta sakata ta wala ba.
Abuja su Manubiya suka fara zuwa kafin su