Showing 150001 words to 153000 words out of 259716 words

Chapter 51 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

92

mata a haka,cikin son sake ganin reaction d’inta yace”tun lokacin da ya kira ni ya fara magana gaba d’aya hankalina ya karkarta ne a kan watak’ilan Khadija ma tana raye.”

A take ya ga idanuwanta sun

fara ciccikowa da hawaye kamar za ta yi kuka…da kyar bakinta yana wani irin karkarwa ta samu tace”Noo Daddy it can’t be,idan shi ya rayu ita ba zai yiu ta yi rai ba,ko ka manta yadda ita d’in da hannunka fa ka c….”

Yadda taga idanuwansa sun yi jaaa a tak

e ne ya sa ta had’iye maganarta ta sunkuyar da kanta,kafin da kyar ta sake d’agowa tace”amma ban sani ba sai dai mu fara bincikenta,watak’il itanma she made it out alive..saboda ka san dama na gaya maka wajen yadda ya koma ba mu iya detecting ko da biro ba

ballantana gawa komai ya kone k’urmus ruwa kawai muka yayyafa aka yi musu salla a haka…..”

Wuff kawai ta ga ya juya ya fita zuciyarsa ta na wani irin tafarfasa dan ya san tabbas idan ya ci gaba da zama to zai iya aikata abun ban mamaki ga Mommy…Mommy t

a yi masa abubuwa daban daban tun daga kan yadda ta tilasta masa aurenta har kawo yanzu kullum a cikin b’acin ranta ya ke,amma bai tab’a tunanin za ta iya aikata haka ba,sannan gashi still k’ok’arin b’oyewa amma ya san ta yadda zai kamata dumu dumu yadda z

ai k’ulleta da jijiyoyin jikinta ya tona mata aisiri kowa ya ganta…hacking wayarta kawai zai yi ta yadda ko typing take yi sai ya gani.A nan ne kawai zai ji komai da take yi ya ga komai ya kamata dumu dumu ya tabbatar da zarginsa a kanta.

He really can’t

believe this!he can’t believe Mommy ta saka shi ya kashe Khadijah da hannunsa ba tare da laifin ta ba,dan kamar yadda ita ma Mommy ta fad’a idan mallan lawal ya samu ya yi making out alive ita Khadijah ba ta Isa ta fita da rai ba.

Tabbas kisan kai it’s

too easy for Mommy…shi kansa yana jin tsoron abunda zai yi mata Wallahi.

Kasancewar Yassir a napep ya taho ya sanya sai yanzu ya samu ya shigo cikin gidan…..

Yana zuwa a fusace ya haye sama ya nufi d’akin Kausar,zuciyarsa tana wani irin tafa

rfasa.

Kausar ta na wani irin kuka haka nan ta shiga d’akin ta ta fad’a kan gado…..ta yi kuka a wannan rana kamar ranta zai fita kafin ta mik’e ta fad’a toilet ta shiga wanke fuskarta a ranta kuwa ta gama aiyyanawa “wallahi

daga yau ita ma ta kanta

za ta yi farin cikin ta kawai za ta duba!kowa ya yi ya kansa….inshaaAllah sai ta mallaki Yashjub ko ta halin yaya ne,daga nan za ta nunawa Mommy wacece Kausar,sai ta san ta yi betraying d’inta wallahi daga kanta ko d’an aiki ba za ta sake betraying ba.”

Tana wannan lissafin ta fito daga toilet d’in…a d’akin ta tarar da Yasira,cikin rashin kwarin jiki Yassirar ta mik’e ta k’arasa ta ruko hannunta kafin tace “ta zo ne akan ta yi mata gargad’in ta bi Yassir a hankali kar ta bari ya fahimci wani abun gudun k

ar yaje ya yi mata kwab’a.Dan yadda ya yi mata d’azu a asibiti ita kanta ta d’an tsorata gaskiya”da “to” kawai ta bi ta daganan Yasirar ta juya ta fita dan ta fahimci kamar Kausar d’in ta na buk’atar space.

Tana fita Kausar d’in ta girgiza kai a ranta tac

e’’kwab’a kuma ta nawa?bayan abunda ya aikata,’’wannan shine karo na biyu da ya so ya kashe Yashjub kuma ta lura Mommy ma ta fahimci wani abun amma ta ga kamar k’ok’ari ma take yi ta b’oye…

A hankali tana jin kanta yana wani irin mahaukacin sarawa

ta

nemi guri ta kwanta.

Lumshe idanuwanta tayi

atake hawaye suka shiga sintiri a kan farar fuskarta

Wannan wacce irin rana ce ta risketa?…ga ciki tana d’auke da shi,ga Mommy wadda ta juya mata baya ga kuma Yassir wanda take zargi da wannan

shirmen a k

aro na biyu

sannan bata Isa ta tunkare sa da maganar ba dan ba ta so ya

fahimci wani abun

Sannan ga rayuwar Yashjub dake a cikin hatsari ga Manubiya ga shi Yashjub d’in ma kansa har yanzu ta kasa samun sa!,ta Ina za ta fara ne?dan abubuwan sun yi mata

yawa.

K’arar bud’e k’ofar d’akin nata ta ji da mugun k’arfi dan haka ta tashi a d’an rikice duk da kuwa da ma ta riga ta san waye ne.

A tsaye a bakin k’ofar ta gansa yana huci kafin ya juya ya rufe k’ofar ya murza key tukuna ya nufota gadan gadan…

Du

k tsaurin idon Kausar sai da ta tsorata dan haka tun kafin ya k’araso ta mik’e tsaye tana mai gyara doguwar rigar jikinta ta hau inda inda cikin in’ina tace’’Yassir I’m sick dan Allah ka bar….’’

Mahaukacin marin da ya d’auke ta da shi ne ya sanya ta gagar

a k’arasa maganar tata,sai da numfashinta ya d’auke na y’an seconds tsabar tsananin shock d’in da ta shiga,a rikice ta d’ago fuskarta da ta yi jajir ga shatin y’an yatsunsa sun fito rad’o rad’o a fuskar tata tace ‘’Yassir ni ka mara??’’

Cikin karsashi yac

e‘’appetizer ne wannan kar ki damu,if you like ki bari in yi miki tambaya ki yi mini k’arya…’’

Ya fad’i hakan yana mai kunce belt d’in wandon sa.

Cikin fushi tace “dukana za ka yi?baka da hankali ne?duk abubuwan da ka yi basu ishe ka ba???’’

Dakatawa

ya yi daga nad’e k’asan belt d’in da ya ke yi around his fingers kafin ya d’ago jajayen idanuwansa ya zuba su akanta tukunna yace ‘’abubuwan da na yi?me da me na yi kenan?’’

Ya fad’i hakan cikin matsowa daff da ita yana mai tsare ta da dara daram idanuwan

sa da suka yi jajir hatta fuskarsa ta yi jaaa tsabar bala’i.

Ahankali ta d’an ja da baya dan a mugun tsorace take dashi

Sai da ta d’an kauda kanta gefe tukunna ta yi k’asa da murya tace’’ Wallahi zan tona maka asiri,in har ka tab’a lafiya ta sai kowa

ya san kai ne ka tura y’an fashi estate d’in Yashjub yau’’

Cak!haka ya k’ame,kafin ya juyo da fuskarta cikin karsashi yace ‘’Kausar ni za ki yiwa sharri da borin kunya saboda kinga na kama ki dumu dumu?’’

Ganin yadda jikinsa ya yi sanyi kuma ta ga ta

d’an samu galaba a kansa ne yasanya ta fincike fuskar ta tace’’ba iya wannan ba ma Wallahi har tayar motar sa da ka cire kwanakin baya sai na fad’a kowa ya ji ,tun da dama son da nake yi maka ne yasanya nake rufa maka asiri amma in har zaka iya d’aga hann

u ka mareni to na san ka daina sona dan haka nima ban ga amfanin ci gaba da son ka Ina bin bayan ka ba ,’’

Ta fad’i hakan tana mai rushewa da wani uban kuka wanda yayi tsananin tasiri akan Yassir.

Ganin kamar so take ta bugi cikinsa sannan kamar wayo t

ake so ta yi masa ne yasanya ya dake yace’’ke!Kausar bana son hauka da shirme da sharri…idan ba so kike in yi miki more than abunda na yi niyyar yi ba to kawai ki bani amsoshina da na zo k’arba mu yi ta ta k’are,”

‘’How dare you!ta ya ma zaki k’ala mini s

harri wai ni Ina so in kashe Yashjub! baki da hankali ne?kuma wa kike tunanin za ki gayawa wannan maganar ya yarda?bari ki ji ko Mommy idan kika gayawa wallahi ba za ta tab’a yarda da ke ba,za ki sha mamaki idan ta juya miki baya har abada ,dan babu uwar

da za ta yarda wata tazo ta ce mata d’anta yanaso ya kashe d’anta!’’.

Goge hawaye Kausar ta yi ta d’ago ta fuskance sa tukunna tace’’Yassir cewa na yi ‘zan fad’awa kowa kaine ka cire tayar mota sannan zan fad’awa kowa kaine ka saka bomb a estate d’in Ya

shjub’.A kaff cikin maganata ka ji ta inda nace ‘kana so ka kashe Yashjub’?’’.

Cikin fushi hargagi da hargowa yace’’Kausar zan illataki fa! ni za ki yiwa wasa da tunani?ai indai aka ji kince na cire taya to an san kashe sa nake son yi kenan!’’

Tsit!hak

a muryarsa ta tsaya chak!yana mai recalculating what he just said yanzun a cikin kwakwalwar sa’’

Kafin ya yi cilli da belt d’in hannunsa tukunna ya d’aga hannu kamar zai damk’i wuyanta kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai ya tsaya chak!! kafin ya juya

mata baya yana wani irin huci kamar mayuncin zaki….

Wata bahaguwar ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e kafin ta d’an matsa garesa tace’’ Bari kaji abunda baka sani ba! Ko da ace Mommy bata tab’a shiga aji ba,wallahi ba zan yi kaffara ba itama ta d’an fahimc

i wani abun,sakamokon yadda ka dinga k’ok’arin tonawa kan ka asiri tun a crime scene d’in,har sign na dinga yi maka da ido amma sam ka kasa fahimta

Shiyasa ka ga hankalina ya tashi raina ya b’aci,ga kuma rashin lafiyar da take damuna,’’

Ahankali ta sake

taku d’aya ta kamo hannunsa ba tare da ta zagaya gaban sa ba ta ci gaba da cewa’’ranar a d’akinka na gaya maka we re on this together,Yassir tunda har na iya danne zuciyata na had’a ka da Munirat inaso ka san na d’auki mission d’innan da mahimmanci,duk da

na san cewa kashe Yashjub ba ya cikin tsarinmu amma idan har ka gaya mini dalilinka zan goya maka baya,kai ko da ace ba za

ma ka gaya mini dalilin naka ba Yassir zan goya maka baya I love you I want to see u win akan komai kai kuma a ko da yaushe zargina

kake yi ban san ta ya zan nuna maka ina sonka ka yarda da ni da gaske ba, da ace na san taimakon ka da muka yi da ni da Mommy zai janyo mini haka daga gareka da ban yi ba tunda na lura tun lokacin da na d’an ja baya da kai saboda mu samu a fasa aurenmu a

k’ara maka share har gobe baka yarda da ni ba Yassir’’

Ta k’arashe maganar tana mai durk’ushewa a wajen ta fashe da kuka.

Ahankali Yassir ya sauk’e ajiyar zuciya tashi d’aya ya fara ganin rashin kyautarwar sa,how can he not trust Kausar?despite irin go

gayyar da take yi wajen ganin ta taimaka masa,shi sai yanzu ma kwakwalwar sa ta d’au charji amma kwanaki da d’azu gaba d’aya duk kishi ya rufe masa ido,tabbas everything is fair in love and war!’they are at war’ dan haka komai is fair kamar yadda ta fad’a

dan ta had’asa da Munirat saboda su samu su yi achieving abunda suke so bai kamata ya dasa ayar tambaya a kanta ba wanda hakan ne farkon zargin nata da ya fara,tunda in komai ya yi daidai ya tafi yadda suke so ai sune da win.

Ahankali ya juyo yana jin t

sananin tausayi da k’aunarta suna ratsa sa ya ce ‘’stand up’’

A ranshi yana mai cewa “inshaaAllah zai yi k’ok’ari ya goge tunanin’watak’il Kausar tana son Yashjub’ daga cikin zuciyar sa.But for last time akwai abunda yake son confirming ta yadda zai yarda

da ita d’ari bisa d’ari.

Ganin ta k’i tashi ne ya sanya shi ya durk’usa ya kamota ya d’ago da ita tashi d’aya ya sakata a jikinsa yana mai bubbuga bayanta alamun rarrashi,sun jima a haka sai da ya ji ta yi shiru tukunna yace “Kausar one last question….na

ga kina kuka sannan na ga hankalinki ya tashi kuma muna shiga da kika ga Yashjub da Manubiya kika juya za ki fita which means you can’t take it ba zaki iya ganin su a haka ba kenan!,inaso ki faiyyace mini dalilin reaction d’inki ta yadda komai zai tafi no

rmal a tsakani na da ke.”

Da d’an fushi sakamokon tuno mata da abunda ya fi komai d’aga mata hankali da yayi tace “Yassir bani da lafiya amai nake ji shiyasa na yi deciding in tafi”

Kallon ta ya yi kafin yace’’amai kuma?….wanne irin rashin lafiya kike

yi da zai baiyyana kishi da b’acin rai a kan fuskar ki?ko dai ba zaki iya tolerating ganinsu…’’

Turesa ta yi da dukkannin ragowar k’arfin da take ji tukunna ta juya a fusace ta nufi toilet…bin ta shima ya yi dan bai gama da ita ba yet.

Tana d’auko pt

s d’in ta juya za ta fita suka yi kicib’is da shi,kallon sa ta yi ta kamo hannunsa ta damk’a masa still tana kallon cikin idanunsa tace

“Bani da lafiya!”

Had’e girar sama da k’asa ya yi

kafin ya d’ago abunda ya ji ta saka masa a cikin hannunsa,sai

da ya kai hannun nasa saitin fuskarsa kafin ya

janye idanunsa

a cikin nata

ya mayar kan tsinken.

Da mamaki k’arara kwance a kan fuskarsa yace

“What!!”

Sai kuma ya kalleta yace

“How?”

Cikin fushi tace

“Kut!!!tambaya ta ma kakeyi

‘How??’.“

Tsabar takaici kasa ma cigaba da tsayuwa tayi dan haka ta bangaje sa ta wuce.

Lumshe idanunsa yayi ya furzar da iska kafin ya bud’e ya juya da sauri ya bi bayanta.

Har ta kusan kaiwa bakin k’ofar d’akinta dan haka ya bi bayanta da d’an gudu ya cafkota

ya juyo da ita.

Takaicine ya sanya ta fashewa da wani sabon kuka gwanin ban tausayi.

Tashi d’aya jikin Yassir ya sake yin sanyi,bai ma san lokacin da ya janyota ya sake rungume ta ba,yana mai jin tausayi da k’aunar.

Cikin muryar lallashi

yace “Haba

Kausar,sai kace wata k’aramar Yarinya?

kar ki damu kanki mana just like last time wannan d’in ma za mu san yadda za mu yi da shi,plss ki daina kukan nan.”

Cikin kuka tace”Yassir ka cuceni!

Shikenan ni na zama sarauniyar zubar da ciki kenan???

kaf g

idan nan

a kaff cikin y’an uwan ka mata

ko missing period babu wadda ta tab’a yi amman ni k’iri k’iri ka maidani karuwar k’arfi da yaji

saboda ni ba y’ar uwarka baceba ko?

Idan nace ‘A’a’ kuma

ka dasa ayar tambaya a kaina.”

Kamar zai yi kuka

yace

“Not at all Kausar,kawai dama I was thinking ne”

shiruu ya yi

sai kuma yace

“Shikenan

I trust you now na fahimci komai komai ya wuce,na yi trusting d’inki daga yau inshaaAllah”

Turesa ta sake yi

tana kuka kamar ranta zai fita

da kyar

ta iya cewa Yassir

what were you thinking before a kaina?”

Sake ruk’ota yayi

cikin sigar lallashi yace

“Na fad’a miki ki manta kawai”

A karo na uku ta sake turesa itama tukunna tace

“You have to tell me

me kake tunani a kaina da! Ba ya ga t

unanin ka na bana sonka ba na kishin ka?what is it?”

Runtse idanunsa yayi ya d’an sunkuyar da kansa

tukunna ya d’ago ya furzar da iska ya bud’e idanuwan nasa sannan yace

“Okay fine!

Da Ina tunanin kamar kina son Yashjub ne.”

Da k’arfi tace



What,sai kuma ta sake fashewa da kuka

kafin ta sa hannu ta kamo sa sai da suka isa k’ofar d’akin ta murza key ta bud’e tukunna tace

“Get out Yassir!

Tunda dak’ik’in tunaninka

da kishi sun rufe maka ido

ba na jin akwai abunda zan gaya maka kuma ka

yarda da ni.Think what ever you want to think ban damu ba tunda duk bayanin da na yi maka ranar a d’akinka ba ka yarda ba

htta sirrin da Mommy ta gaya mana wanda ba kowa ake so ya ji ba duk sai da na gaya maka..amma shine still ba m yarda da ni ba??

sh

ikenan!!

Ba komai.”

Ahankali yace “Kausar”

Cikin fushi tace

“trust is a very important thing Yassir taya ma za ka yi wannan tunanin a kaina?.

Baka san yadda ka yi hurting d’ina ba yau!

Just get out of my room”

Matsowa ya yi da sauri yai hugg

ing d’inta yasa k’afa ya tura k’ofar ya rufe.

Ba yadda ba ta yi da shi ba

amman sam ta kasa kwatar kanta,dan haka ta fashe da wani sabon kuka.

Lallashinta ya shiga yi a chan k’asan zuciyarsa kuma yana daya sanin zarginta da yayi…

Sai da ya ji ta

d’anyi shiru

tukunna ya cikata ya ce”na yi laifi

For the first time gashi na yi accepting na yarda na yi miki laifi,ki yi hak’uri

InshaaAllah ba zan sake ba

sannan daga yau ba zan sake dasa ayar tambaya a kanki game da komai ba I promise!

Duk abu

nda kika yi I’m going to trust you ko menene.

Pls Kausar forgive me”

Ya fad’i hakan ya na k’ok’arin durk’usawa.

Da sauri ta rikesa ta d’an girgiza masa kai…sake yunk’urawa yayi zai durk’usa dan haka tace

“Ya wuce ba komai”

Ahankali yace “thanks l

ove..sosai sosai”

Sai kuma ya d’an kalli flat tummy d’inta yace”mu zauna sai mu yi magana ko?”

Jinjina kai kawai ta yi

daga haka ta wucesa ta isa

bakin gadonta ta zauna

Tana zama shima ya zauna

Ba tare da b’ata lokaci ba yace

“Yaushe kike so

mu je asibitin??”

Sai da ta d’an d’auki lokaci tukunna tace”ba zan je asibiti ba,idan cikin ya kai wata biyar sai in fara zuwa awo

InshaaAllah”

Da sauri yace “Kausar pls

kar mu yi haka da ke mana!

Wacce irin magana ce wannan??”

Girgiza kai ta

yi kafin tace

“Yassir ba zan iya yin wani abortion d’in ba fa,ai ka ji dai da kunnenka abunda Doctor yace mana the last time ko?…ko kana so mahaifata ta lalace tun kafin na fara tara iyali??

Besides

ai ni na sha gaya maka dama a ko da yaushe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login