Showing 159001 words to 162000 words out of 259716 words

Chapter 54 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

50

ya had’u dake

kuma na san kin san negligence ya kan kashe har aure ba wai iyaka soyayya ba….”

“Wannan itace gaskiyar maganar Ya’isha da Najeeb dan haka the choice is yours amma ni dai ina baki shawarar ki saurari Najeeb ki auresa saboda na san yana son ki tsakani da

Allah kuma Najeeb is a very good kind and nice person.”

Shiruu parlourn ya d’auka kafin Yash ya mik’e ya ce “Bari na baku guri…”daga haka ya wuce chan sama d’akinsa.

A hankali Najeeb ya mik’e ya k’arasa ya zauna a gefenta kan three seater da ta ke a

zaune yace”what more reason kike buk’ata Siyama na ci gaba da azabtar da zuciyata?na garu haka dan Allah ki ji k’aina….”

Shiruu ta yi ta kasa cewa komai kafin tace”zan yi tunani akai”

Wani sanyin farin ciki ne ya lullub’e Najeeb a hankali yace”sai a

n ja mini rai kenan yanzun ma..”

Murmushin da yaga ta d’an yi ne ya sa ya ji kamar an tsunduma sa a aljannah dan haka a fili ya ce”Alhamdulillah”

“Yanzu ko zuwa anjima idan na zo za ki fito ko???”

Dariya ta yi wannan karon ta d’aga masa kai alamun”e

h”sai kuma ta mik’e da sauri ta haye sama….dama chan tana son Najeeb she’s just waiting for someone da zai ba ta genuine reason d’in da za ta auresa dan ba shi kad’ai ba ita kanta ta garu..yanzu kuwa da ta ji komai ta fahimci komai InshaaAllah za ta rufe i

do ta goge babin Ya’isha daga rayuwarsu…

Ko da su Manubiya suka ji labarin a take suka goya mata baya d’ari bisa d’ari suna ta murna suka kira Aisha itama ta ji dad’in batun matuk’a….

Najeeb kuwa farin cikin da yake a ciki ya k’i b’oyuwa…Tana wucewa

ya kira Yash yace masa “zai tafi”

Yana sauk’owa ya kallesa yace”har kun gama?”

Jin jina kai ya yi kafin ya mik’e yace”Yash Ya’isha kar ta zamo silar…”

Dariya ya ga Yash d’in ya fara kafin yace”Najeeb if I were in your shoes da gudu zan bar sistern ka

fa in zab’i Manubiya,na san menene so!”

Sai kuma ya yi tapping shoulder d’insa ya ce”laifin Ya’isha ne,na dad’e da fahimtar hakan,kar ka da mu!”

Ganin still Najeeb d’in bai sake ba yasa cikin zolaya yace”Allah ya sa nan da next week mu je mu yi gaisu

war iyaye”

Da sauri Najeeb ya ce”Ameen”

Dariya Yash ya yi yace”an zo

wajen da za ka yi magana kenan…..”

“You are welcome”

Daga haka suka fad’a zancen case d’in estate d’insa…akwai haske sosai dan ana ta samun ci gaba,soon inshaaAllah suna ganin za a k

amo culprit d’in….

Ba su san waye ya gaya wa su Yasira sun koma gidan ba sai kawai ganinsu suka yi har da babbar jaka…Yasira da Yusra da Yadira,dan Yasmeen ma cewa ta yi ba za ta bi su ba wannan karon,tace ita babu ruwanta saboda zuwa yanzu da ta za

una ta yi lissafi ta fahimci tabbas idan ba su daina biyewa Baba larai ba sai ta goge musu duk wani ilimin addini da suke da shi,she can’t believe wai Yassira tana wani ce mata”ai da ma Baba larai ta duba ta gani Manubiya za ta taho da masifu ita za ta ga

bayan Mommy tou kuwa gashi alama sun fara nunawa dan haka dole su tashi su tsaya…dama ai duk abunda Baba larai ta fad’a sai ya zama gaskiya”.

Bayan ba su san sakawa da suka yi a ransu ne ya sanya Allah ya barsu da halin su shiyasa suke ta ganin masifun su

na zuwar musu kamar yadda sukai zato,idan ba haka ba wacece Baba larai da za a ce duk abunda ta fad’a sai ya tabbata???…

Shiyasa Yasira tana gama zaiyyane mata tace”ita dai babu ruwanta,ba za ta hanasu ba dan ta san ba za su hanu ba idan kuma ta fad’a ta

san za ta samu matsala da Mommy amma kar su sake sakota a cikin zancensu….”

Shiyasa Yasirar ta kad’o kan Yadira da Yusra suka taho bayan Baba larai ta cika musu jakankuna da kayan barbad’e barbad’e dan tunda suka je asibiti aka ce an sallamesu ta fara h

arhad’awa.

Ba iyaka su Manubiya ba hatta Yash ya fahimci kissa ce da k’arya su Yasira suka zo da ita wannan karon…dan yadda suka yi suka chanja gaba d’aya tashi d’aya abun dole ya baka mamaki…hatta Yasira da murmushi ta gaida Manubiya ta shiga tambayar

ta ya jiki kamar za ta goyata har da zama a kusa da ita,tukunna tace”Mommy ce ta ce su zo

su tayata gyare gyare.”

Shi dai Yash ba don kar ya ce su tafi abun ya zama case ba da tuni ya sallame su dan gaba d’aya haka kurum hankalinsa bai kwanta da su ba.

Ya san watak’il idan gwaggo ta zo za su tafi shiyasa yace bara ya je ya d’aukota amma ko alamun gezau bai gani ba shiyasa kawai ya fita yana jimami.

Suma shiruu suka yi su Yasira tun suna magana da suka ga su Siyama da Manubiyan sun k’i sake wa sai ka

wai suka d’aga k’afa suma suka yi shiru.

Suna a haka suna jimami Ya Nafi’u ya kira su Jidda yace”mutum biyu su fito a bar mutum d’aya a gidan za su wuce gida su fara tartara kaya an sallami Baba..

Siyama aka bar mata,Jidda da Muhsin kuma suka tafi dan

idan zai yiu a yau suke so su tashi daga gadon k’aya su koma sabon gidansu dake a gandun albasa wanda Yashjub ya basu.Ba su yi ma tunanin za a sallami Baban yau ba da tuni sun yi parking d’in.

Ita Aisha Mama Anty Umma da Inna ne suka tartare komai kafi

n dare sun kammala komai ya Nafi’u da Muhsin kuma su sakayi ta zirga zirgar kai kaya a motarsa da motar kai kaya.

Sai da suka gama kammala kai komai gidan tukunna suka d’auko Baba daga asibiti suka nufi tsohon gidan nasu dan su je su yiwa su Uncle sall

ama saboda Baba dagewa ya yi yace”shi fa sai ya yi musu sallama.”

Suna zuwa Baba da Ya Nafi’u suka nufi wajen su Uncle d’in Inna da su Mama kuma suka nufi wajen matayensu.…yunwa Jidda ta ke ji dan ba ta tsaya taci abinci sosai ba,shiyasa ta je kitchen ta

d’aura ruwan zafi da niyyar ta je ta siyo milo da madara ta sha tea…

Sai da gabanta ya yanke ya fad’i sakamokon k’amshin turaren da hancinta ya fara jiyo mata,a take a ranta tace “nooo..it can’t be,ta ya ma zai shigo nan.”daga haka ta mik’e bayan ta gama

saita murhun ta juya za ta fita ta ga mutum a tsaye kyam!…..

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”tace a fili kafin ta d’an d’ago wayarta ta d’an haska dan ta samu ta tabbatarwa kanta da shi d’in ne…

Suna had’a ido ta fashe da kuka tace”dan girman Allah

ka fita Ya Al’ameen kar ka janyo mana masifa”

Ahankali ya yi taku d’aya ya matso gareta muryarsa har tana d’an karkarwa yace”D’azu na ji Mama tana gaya wa Ammi cewa za ku tashi…”

Cikin sharar hawaye tace”eh,mun ma tashi..dan Allah ka fita…”

A han

kali yace”Jidda ni da ke fa?ba za ma ki tsaya ki ji uzuri na ba?tun safe nake ta faman zirya Ina lek’en gidan nan Jidda duk dan saboda ke amma kora ta ma kike yi?”

Bai jira jin amsarta ba yace”a lokacin da na tafi,wallahi wallahi tun a kwana biyu da na ki

rawo wayarki na ji ba kya picking na had’o kayana na biyo jirgi na sauk’a a garin Abuja,inaga cousin d’ina da muka tafi tare da shi ne ya kirawo su Ammi yace musu na taho dan flight d’ina yana shirin boardn zuwa Kano Mahaifina ya kira ni yace idan na zo sa

i ya tsine mini tunda bani da hankali. Kalar fad’an da ya shiga yi min a wannan lokacin ni kaina na san akwai abunda Ammi ta gaya masa mai muni shiyasa ya yi fushi sosai ya ji haushi dan ko fad’a bai cika yi mini ba.A wannan lokacin babu yadda ban yi da sh

i ba amma ya k’i saurarona yace in juya in koma. Tun daga ranar ya daina kulani ya yi fushi da ni yace kuma wallahi idan ya ji labarin na zo Nigeria ba tare da na gama abunda ya tura ni ba sai ya bani mamaki yace kuma ko waya na yi miki bai yafe ba. Sai da

na dawo tukunna a cikin maganarsa na fahimci Ammi ce ta ce masa saboda ke na rubuta letter na bar course d’in da ya tura ni in yi saboda kince ‘Baba zai aurar da ke a Yusuf idan ban dawo an yi auren da ni ba’.

Jidda Course d’in duk yawansa na san ba z

ai kai wata hud’u ba shiyasa na hak’ura na yi masa biyayya akan idan na dawo sai a yi komai amma ko a wannan lokacin sai da na saka mai gadin mu ya sa mini ido gudun kar Ina chan Ina shirya ta yadda zan shayo kan iyayena ke kuma a aura miki Yusuf.”

Shir

uu ya yi kafin ya d’aura da cewa”wannan shine abunda ya faru Jidda shiysa kika ji ni shiru na san waye mahaifina yana son duk abunda nake so kuma zai tsaya mini a kai amma muddin na yi masa taurin kai na san tsaf za a samu matsala kuma na san halinsa da bi

n diddigi yadda yace”kar in kiraki wallahi da ace na kiraki sai ya sani ni na san waye shi”” na san kuma ya yi hakan ne saboda ya ga zan yi masa biyayya ko akasin hakan.

Cikin sake yin taku d’aya zuwa gareta yace”I love you!always and forever ba zan iya h

ak’ura dake ba Jidda gara ma tun wuri ki yi saurin karb’ar uzuri na ki yafe mini mu fara nemawa kan mu mafita!”

Shiruu ta yi a ranta ta ji matuk’ar sanyi da dad’i da ta ji ba banzatar da ita ya yi ba,a fili kuma sai tace”Ya Al’ameen ni kam na dad’e da h

ak’ura da kai,ka duba fa ka ga Mahaifinka ma ba so yake yi ba tunda shi ne yace kar ka ki…”

Cikin tarar nufashinta yace”noo Jidda wallahi ba da ke ya ke fushin ba da ni yake yi kuma na saboda ya ji batun aurenku da Yusuf ya taso da zai yi wani abun …a ran

ar da zan tafi a airport na yi masa bayanin komai na ce masa Ammi ba ta so,shi da kansa a wannan lokacin ya tabbatar mini da cewa”inshaaAllah ina dawowa za a yi auren mu kuma kafin ma in dawo za a yi tambaya batun Ammi kuma kar in damu ya san yadda zai yi

da ita ba matsala inshaaAllah,but for now in yi k’ok’ari in yi concentrating a kan abunda na je yi saboda it’s very important for our business”

Shiysa da ya ji na shallake sa na bar ma makarantar ya ji haushi ya yi mini haka,amma wallahi ko yanzu Mahaifin

a a shirye yake ya d’aura mana aure ko a yau!ita ma Ammi ta amince this time for real saboda halin da na shiga ta tsorata ta yi nadama ta gaskiya ba kamar wanchan lokacin ba da ni kaina ban san linke ni ta yi a baibai ba”

Babu wani ragowar reason d’in d

a Jidda za ta d’aura laifi a kan Al’ameen saidai ta san su Baba ba za su tab’a fahimtarsa kamar yadda ita ta fahimce sa ba,shiyasa kawai ta d’an ja da baya cikin sharar kwallah tace”ka yi hak’uri Ya Al’ameen mu yi hak’uri kawai”

Ta fad’i hakan tana mai fa

shewa da kuka.

Da sauri ya sake matsowa yana mai cewa “noo Jidda kar ma ki fara cewa mu yi hak’uri wallahi ba zan iya ba”

Ganin sa daff da ita ya sa ta yi sauri ta sake ja baya ita shaf ta ma manta da murhu da ruwan zafin da ta d’aura,shi kuma abunda ya

hango kenan dan haka ya yi saurin ruk’ota zuwa jikinsa ganin za ta afka kan murhun yace”careful!wuta a bayanki”

Salatin Ya Yusuf wanda ya hakse su tarr da wayarsa da kuma”Jidda”d’in da Baba yace ne ya fargar da su.

Da wani irin sauri ta ture Al’ameen shi

ma da mugun sauri ya cikata ya matsa ya shiga ambaton”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”

a cikin zuciyarsa

Juyawa kawai Baba ya yi ransa a mugun b’ace ya fice daga gidan yayin da Yusuf ya yi kansu zuciyarsa tana wani kalar mahaukacin tafasa..kamar wani

mahaukaci sabon kamu haka ya koma yana zuwa ya rarumi wani k’atoton iccen ya makawa Al’ameen a kai da mugun sauri wanda hakan ya yi sanadiyyar fad’uwarsa a wajen gefen kansa ya shiga zub da jini.

Wata razananniyar k’ara Jidda ta buga ta yunk’ura da niyyar

yin kan Al’ameen d’in dake nan kwance kamar gawa amma tashi d’aya itama Yusuf ya d’auketa da wani irin gigitaccen mari ya shak’o ta da dukkannin k’arfinsa ya buga ta jikin bango,dai dai nan su Anty Umma waenda k’arar Jidda ta Isar musu suka afko cikin ki

tchen d’in,da gudu anty Umma ta k’arasa ta shiga k’ok’arin kwatar Jidda wadda zuwa yanzu idanuwanta suka fara lullumshewa kafin duhu ya maye gurbin ganinta jikinta ya saki a take ta sume a wajen……

A hankali take bud’e idanunta da suka yi mata rauni..d

ishi dishi ta ke gani kafin ta fara gani da kyau kad’an kad’an..ba ta gama tantance a inda take ba…cikin fushi ta ji Baba wanda ta ga ya juya mata baya suna magana shi da Inna yana cewa”saboda su Uncle sun yi mini abu sai in d’aura karan tsana a kan Yusuf

in rufe idanunwa na in k’i in bi bayan gaskiya?fad’a da su Uncle mu ka yi ba da Yusuf ba kuma suna d’in inshaaAllah wata rana za mu shirya amma ki daina saka Yusuf a cikin fad’an mu,ke ko irin karar da ya yi mana ma ba kya gani?wanne d’a ne kika tab’a gani

ana fad’a da mahaifinsa amma ya rufe idanuwansa ya bi bayan k’anin mahaifinnasa da ake fad’an da shi? ki duba ki ga yadda ya dinga bin bayan mu a gaban Baba Habu har kusan marin sa fa ya yi suka samu sab’ani duk a ta dalilin mu amma duk da haka ke Yusuf

bai kwanta miki ba?…….a da gaskiya na sa a raina ba za ta auri Yusuf ba amma kuma abunda idanuwa suka gane mini yau ya sanya naga dole fa in yi abunda na ga ya kamata a matsayina na ubanta ko so kike mu zuba mata ido Al’ameen d’in ya gama lalatata?ba ri ki

ji abunda ba ki sani ba hatta makaranta wasu lokutan shi yake kai ta ya d’auko ta Yusuf ya dad’e da gaya mini hakan,ido kawai na zuba mata dama ina jiran ranar da zan kamata tana kulasa ashe abun nasu ma ya zarce misali!…”

Cikin kuka inna tace”yanzu z

argin Jidda kake yi ba tare da ka tsaya ka ji bayanin ta ba??”

Cikin tarar numfashinta yace”tabbas!tabbas zargin ta nake yi..idan kuma za ki iya gaya mini uban me ta ke yi a ruk’umk’ume a jikinsa a kitchen cikin dare inda ba a tab’a tunanin ganin Al’ameen

d’in ba to Ina sauraronki…”

Cikin d’an b’acin rai Inna tace”wallahi zan iya dafa Al’k’urani akan akasi aka samu,Haba Baba Jidda fa?ashe da ma ba ka yi mata sanin da za ka iya shaidarta idan irin haka ta taso ba?sannan kalli fa abunda Yusuf d’in ya yiwa

Yarinyarnan har ta kaisa ga sumar da ita amma shine za ka d’auke ta ka aura masa ita? A ganinka hakan dai dai ne?

Sannan idan kace Yusuf a bayan mu yake ka ji ka gani ya zama mijinta me za ka ce a kan baba habu surikinta,wanda hatta yau da ya san tashi z

a ka yi a kusa da su kuma saboda su bai tsaya kun yi rabuwar arzik’i ba?”

Cikin tsananin fushi Baba yace”na riga fa na gama magana!babu wani abunda ya Isa ya sakani in chanja ra’ayina,na tabbata inda ace Musbahu ne ya ganta a yadda Yusuf ya gansu ita da

Al’ameen da shima abunda zai aikata a gareta kenan tunda hakan ne dai dai…to shi Musbahu ya gudu ya yaye kansa da kansa dan hakan idan Yusuf ya hukunta Jidda a matsayinsa na yayanta hakan bai zama laifi ba….”

Cikin kuka inna tace”ta ya sumar da Jidda y

a zama ba laifi ba?”

Da mugun k’arfi Baba yace”Aminatu!!!!!”

Cikin fushi ya d’aura da cewa”ba na son jayayya ki barni in ji da abubuwan da suke damuwa…ba na so in sake fuskantar tirjiya daga gareki,ina umartar ki da ki yi mini biyayya a yi auren nan a go

be a kaita d’akinta idan ba haka ba wallahi wallahi wallahi za mu samu gagarumin sab’ani da ni da ke!”

Yana gama fad’in haka ya juya ya fice…

A hankali Jidda ta mayar da idanunta ta rufe…tana jinta kamar ba a duniyar ba…tunda take ba ta tab’a jin Baba

ya d’agawa Inna murya ba sai yau duk a ta dalilin ta…ta na son Al’ameen sannan ta san idan ta auri Yusuf tabbas bak’in ciki ne ajalinta amma kuma inshaaAllah ko alamun tashin hankali ko kuma yunk’urin kare kanta ba za ta yi ba…ta fahimci inna ta yarda da i

ta ta yi trusting d’inta Manu ma ta san za ta yarda da ita Baba kuma za ta barsa ya aurar ta a Yusuf d’in indai hakan zai sa ya huce,inda rabon wanke kanta wata rana shima zai fahimci ba wani abun suke yi da Al’ameen ba….za ta yi masa biyayya inshaaAllah d

an tunda ta fara tirjiya a Yusuf ta nuna Al’Ameen take so babu abunda relationship d’inta da Al’Ameen d’in yake ta janyowa Ahalinta sai masifa………..

Siyama ba ta so kwana a gidan Manu ba amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login