Showing 99001 words to 102000 words out of 259716 words

Chapter 34 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

20

yayi magana

Ya’isha tace

‘’Wallahi Daddy bamuyi koma

i ba,dama tun da mukaje ta tare hanya ta hanamu wucewa sai da ya zo tukunna ta matsa.

Ina ga yanayin fuskar ta ya kalla dan tanata faman kumbure kumbure shine ya kira Yasira ya ce ta kwashemu mu tafi’’

Wani irin takaici ne ya lullub’e Yashjub wanda ya

sa ya ji kamar ya finciko Ya’isha daga kusa da Daddy ya feffella mata mari…ya godewa Allah da ba a kusa da shi take ba dan ya san yau da sai ya illatata!

Ganin Yaran suna neman haukatasa ne yasa ya koma ya zauna ya dafe kansa da ya fara sara masa.

Gyar

an murya Daddy ya yi kafin yace”Yashjub!!tun wanchan ranar a asibiti na fad’a maka kar ka bada k’ofar da matar ka za ta raina y’an uwanka!and again a washegarin ranar da ka yi aure ma sai da na rok’ek’a da kaina akan kar ka bada k’ofar da kawunan ku zai ra

bu a ta dalilinta amman naga that’s exactly what you are trying to do. Sam!ban ga dalilin da zai sanya dan ka yi aure ka tsame y’an uwanka a jikin ka ba ba zai yiu ba ba zan zauna in zuba ido zumuncin ku ya tarwatse ba saboda rashin tunanin ka da kuma gigi

n giyar soyayyar da ka kurb’a.”

Yashjub ji yayi kamar ya d’aura hannu aka yayi ta faman zunduma ihu…ta ya Daddy zai biyewa waennan Yaran ya hau kan maganganunsu ya zauna daram sannan ji fa tone d’insa sai kace na mace yana magana kamar ta mata

yanzu

wannan d’an k’ank’anin abun har ya kai a titsiyesa a gaban su haka…….

Muryar Daddy ce ta katsesa jin yana cewa”ina sauraron ka,

ka fad’amin exactly abunda ya faru.

Ku kuma”

yayi maganar referring to su Yassira yace”kar in ji bakin ku

har ya gama ma

gana.”

Wato dai a gaban Yaran nan za a yi masa haka!alk’alanci kenan Daddy zai yi musu shi da k’annen sa….

“Ina jin ka mana!”

Ya ji muryar Daddyn a d’an zafafe.

A hankali ya d’ago ya kalli Daddyn yace”Ba su kula ta ba.

Kaff cikin su saida na yi

magana tukunna Yadira ta gaida ita‘’

Da takaici Mommy tace

“Saboda ba su gaida matar ka ba shine ka koro su daga gidan ka??’’

Cikin son fahimtar da ita yace

‘’Mommy saboda sun rainani kuma sun ki su yi abunda nace a gabanta sun nuna min ban Isa b

a shiyasa na koro su

Baya ga haka Mommy taya za su je har gidan ta su k’i su kulata sannan kuma ni da kaina in ce su yi su k’i yi

Maatata ce fa!’’

Ai ko da ace ba za su gaida ita ba da ko ‘Hi’ ya kamata su ce mata…..”

Cikin tarar numfashin sa Ya’i

sha tace

‘’Daddy cewa ya yi duk sai mun gaida ita har Yasira da Kausar,kuma fa ita ma bata kula mu ba how yake expecting mu mu gaida ita?.”

Throw pillow Daddy ya jefawa Ya’isha cikin fad’a yace

“Ba na ce bana son jin bakin kowa ba?”

Da b’acin rai

sosai ya juya ga Yashjub ya ce

“Yashjub’’

Ahankali Yash ya kalle sa ya ce

‘’Na’am Daddy’’

Cikin bada umarni da fahimtar wa Daddy ya fara magana

‘’kamar yadda na fad’a d’azu

ba zan bari giyar soyayyar da ka sha ta lalatamin zumuncin dake a tsakan

in ku ba!ba zan bari wata mace ta shiga tsakanin ku ba dan bakasan yadda muka sha fama ni da mahaifiyar ka wajen ganin mun daidaita kanku ba!”

Ahankali Yash ya lumshe ido yana mamakin yadda su Daddy suka d’auki laifi gaba d’aya suka d’aura wa Manubiya…t

a yaya Manubiya za ta shiga tsakanin sa da su Yasira shi kuma ya yarda..

Dan mai ya sa tun farko idan irin haka ta faru a tsakanin su ba’a d’abbak’a abun sai yanzu da yayi aure?

Kuma shi rainin da suka yi masa a gabanta ne ma ya sake harzuk’a sa ya koro

su a

tunanin sa ya Isa da su.

Inda ace ci musu fuska ya so yi ai da a gaban Manubiyan zai fatattake su…Ita Manubiyan ma da suke ta cewa ‘za ta shiga tsakanin su’ bama ta san da case d’in korar sun da yayi ba.

Ahankali tunanin sa ya dawo cikin parlou

rn jin Daddy yana cewa “Inaso ka sanar da Manubiya idan kuma ba za ka iya ba ni zan sanar mata cewa

‘Ya’isha da Yusra za su gaida ita wannan dole ne!amma

tun daga kan Ya’isha har zuwa kan Yassir har Kausar ita ce zata gaida su tunda duk sun girme ta.’”

Da mugun sauri Yashjub ya d’ago sosai ya zubawa Daddy idanuwan sa.

“Kwarai kuwa”Daddy yace shima yana kallonsa kafin ya d’aura da cewa

“Ba wai nace dole in sun had’u sai ta gaida su ba,ruwanta ne idan taga dama ta kula su in bata ga dama ba karta kul

a su

amman kasancewarsu yayyu a gareta yasanya bazai yiu ace su su fara gaida ita ba.

Idan ta kula su ta gaida su su amsa

In kuma bata kula su ba

wannan alhakin yana a kanka

na ganin ka daidaita alak’ar dake a tsakaninta da su

kaine za ka nuna m

ata cewa yayun ta ne kuma ta dinga gaida su saboda a samu a zauna lafiya a raya zumunci.

Sai kuma magana ta biyu

‘Daga yau har gaban abada idan su Yasira za su je gidan ka a rana sau goma to baka da iko sannan baka Isa ka kore su ba!na san gidan ka ne

nasan kai ka siya ka zuba furnitures ka yi komai da kanka amman ni kuma nine uban ka!

dan haka in dai ni na haife ka,to Yassira,Yahanasu,Ya’isha,Yadira,Yasmeen,Yusra,Yassir kai har ma da Kausar za su je gidan ka a duk lokacin da suke so

In ma hutu suke

so su yi za su je su yi har sai sun gaji dan kansu tukunna su dawo amma kai dai baka da ikon koro su…in har kuma kace za ka yi taurin kai to zan sa ka had’omin spare key na kaff gidan naka in rabawa ko wanne a cikinsu….

Ban d’aura auren da zai tarwatsami

n kan ya’ya na ba wallahi.!”

Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ce

‘’a kiyaye” daga nan ya wuce sama.”

Shiruu Yashjub yayi ya ma kasa cewa komai

Har sai da Mommy tace

“Sai magana ta uku!Yadira ta had’a kayan ta tun d’azu

In kun zo tafiya ku w

uce da ita

za ta zauna a gidan naka for sometimes.”

Saida ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya ce

“To Mommy ba damuwa,amma jiya na gaya miki za mu tafi Cyprus..y not a bari sai mun dawo t….”

Cikin tarar numfashinsa tace

“Ka wuce da ita,idan k

un zo tafiya sai ka dawo da ita in kuka dawo sai ku koma tare da ita”

Ahankali yace”Mommy, jibi ne ai…”

Cikin fushi tace

“Ka san Allah Yashjub in ka gwada min taurin kai idan bance ku tafi honeymoon d’in tare da ita ba ka chanja min suna..”

Shiruu

ya yi kafin ahankali ya ce “Shikenan Mommy..ki yi hak’uri”kafin ya kalli Yadira ya ce “Ki d’auko jakar ta ki yanzu zamu wuce.Bari in yi wa Daddy sallama”

Ya fad’i hakan yana mai hayewa sama.

Murna a wajen Yadira ba a magana…tashi d’aya itama ta yi wuf

f ta haye ta je d’auko kayanta.

Ko da Yashjub ya je wajen Daddy basa hak’uri yayi sosai

tukunna dakyar ya samu ya d’an sauk’k’o bayan zazzafan warning d’in da Daddyn ya zuba masa akan “indai har yanaso su zauna lafiya da shi tou ya ja k’annen sa a j

iki…duk ranar da aka ce ya mutu shi ne Uba!…kar ya biyewa mace ta rabasu tun yanzu.”

“InshaaAllah”kawai Yashjub d’in ya ce daganan yayi masa sallama suka rabu lafiya

A ranshi yana mamakin yadda Daddyn yayi masa sannan yadda suka d’auki laifi kachokam

suka d’aura akan Manubiya wadda bata ji ba bata gani ba

It’s like kamar ma Daddyn har ya fara jin haushinta ne tun kafin a je koina kawai dai bai nuna masa bane but ya fahimta dan tunda har Daddy yace “har Kausar sai Manubiya ta gaida ita ai abun babu s

auk’i dan duk mutumin da Daddy zai yi favoring Kausar akan sa to yakamata ayi gaggawar gyara tsakanin su

Shiyasa kawai ya hak’ura yake ta basu hak’uri…ya san su iyaye ne fushin su garesa masifa ne sannan kuma yasan yanzu yana yin taurin kai ko ya yi wata

maganar to Manubiya zai sake janyowa bak’in jini a wajensu.

A d’akin Yahanasu Yadira ta samesu dan haka suka fara shirin tafiya.

Manubiya ce tace “tana so ta je ta yiwa su Mommy da Ummi sallama”dan haka Yadira da Munirat suka tafi rakata.

Suna f

ita Yahanasu tace

‘Ayi hak’uri Yash

ayita hak’uri…d’azu Ina kitchen naji mommy tana waya da su

Yassira suna ajjiyewa na ji ta kiraka dama tun daga nan na san akwai matsala aikuwa da suka tashi shigowa kusan dukkansu da kuka suka shigo

wai ka kore

su k’annenta kuma suna gidan yanzu haka.

Dama yadda na ji Mommy da su suna yiwa Daddy bayani shi kuma yana fad’a na san kawai ya riga ya hau shiyasa ban saka Baki ba.

Na yanzu ya faru sai a kiyaye gaba dan Allah Yash karka basu k’ofar da zaka janyowa ba

iwar Allah n nan bak’in jini a wajen Daddy…”

Ajiyar zuciya ya sauk’e daganan yace

“InshaaAllah’’

Ba a wani dad’e ba su Manubiya suka dawo

Sark’ar gold Ummi ta bata y’ar k’arama wadda ba za ta wuce 4OOK ba a cewarta ta ajjiye a tunanin ta za’ayi b

ud’ar kai ne sai ta bata tou kuma ashe su basa bud’ar kai…daga nan ta d’an yi mata nasiha.

Mommy kuwa sallama kawai sukayi daganna suka fito Manubiya tana mamakin yadda yanayin fuskarta ya chanja dan d’azu sam ba haka ta yi mata ba a gaban Yash.

Ya

sh yaji dad’in gift d’in Ummi matuk’a kuma bai ji dad’in rashin ganin gift daga wajen Mommy ba yana sane ko a lefe ma ba ta basa komai ba Mom da Hajiya mama sai Yahanasu ne kawai suka bada…dukda ya san yau d’in ranta a b’ace yake

amman ai dama Uwa tana t

anadan gift d’in amarya a irin wannan ranar ko da ace ta bayar da na lefe,ya san maybe za suce ai ya yi komai ya saka komai amman ai Ana bada gift ne saboda karramawa ba wai dan babu ba.

Har mota Yahansu da Munirat da Yassir suka rakasu da Yadira da akw

atunan ta biyu.

Sai da suka ga ficewarsu tukunna suka nufi main door,

signal kawai Yassir ya yi wa Munirat daga nan Yahanasu bata san inda sukayi ba ita dai ta ganta ta shiga parlourn ita kad’ai.

Kausar tana ganin ficewarsu ta windown d’akinta ta ko

ma ta kwanta ta fashe da wani irin kuka babu abunda yafi b’ata mata rai irin yadda yake wani rik’e mata jaka yake bud’e mata murfin mota.

Tana kwance tana ta faman kuka a haka ta ji an bud’e k’ofar d’akin an shigo.

Ta san Mommy ce dan haka tace ‘’I’m f

ine”

Murmushi Mommy tayi ta nemi guri ta zauna a kusa da ita kafin tace”Ki yi hak’uri Kausar

saura d’an k’an’kanin lokaci

nasan da ciwo amman ki k’ara hak’uri…

Ki duba kiga yanzu da ikon Allah Daddy ya fara karkatowa side d’inmu duk abunda muke so sh

i yakeyi.

Shima Yashjub d’in ki duba kiga ni ko b’acin raina ba ya son gani ai da ba haka yake ba.

Ki kwantar da hankalinki na yi miki alkawri indai kina da ni bazakiyi kuka ba…”

Ahankali ta tashi ta zauna tana kallon ta tace”thanks for everything Mom

my,but na ga suntafi da Yadira kenan ba ranar dawowarta nan gidan kwana kusa kenan?idan fa ba ta dawo ba babu ta yadda za ayi mu…”

Cikin katse mata magana

Mommy tace

“Kar ki damu zata dawo

komai a hankali a keyi

ki kwantar da hankalin ki kinji”

Ahankali Kausar ta jin jina Kai daganan ta matsa ta kwanta a jikin Mommy tana mai sauk’e wata nannnauyar ajiyar zuciya.

Mommy tana so ta fad’a mata zancen tafiyar su Yash honeymoon amma kuma bata san ta Ina za ta fara rarrashinta ba dan ita kanta tu

n jiya da ya gaya mata ta rasa Ina za ta sa kanta…she just hope Yadira ta yi abunda ta tura yi a gidan…inshaaAllah in dai har ta yi to ita Manubiyan ce da kanta za ta tarwatsa batun tafiyar tasu.

Suna fita Daddy ya sauk’e ajiyar zuciya dan shima yana ts

aye ta window yana kallonsu har suka fice….ya san he s a little bit hard akan Yashjub b

amman kuma idan bai yiwa tufkar hanci da wuri ba tou tabbas akwai matsala.. duba da yadda ya Yash ya kori k’annensa ranar da aka je d’auko amarya dukda ya san laifin s

u Yasira ne but a yadda shi da kansa ya rok’esa sannan ya ce su had’a kawunansu sam bai yi tunanin Yash zai sake korar su daga gidan sa ba,baya ga haka kalli yadda yake nan nan da Manubiya ya san zafin soyayya ya san ya mutum yake ji shiysa ya fahimci ind

ai har bai tashi ya tsaya a kan Yash ya yi masa wuta wuta ba to a yadda ya rikice a kan Yarinyar tsaf zai yi fatali da zumunci ya zab’i soyayya……MANNUBIYA

(Book 2)

Page 24

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Associat

ion.

Tunda su Manubiya suka kamo hanya babu wanda yace ‘k’ala’ a cikin motar…Abu d’aya ta lura da shi shine yanayin Yash gaba d’aya ya chanja kamar yana fushi.

Sam ba ta yi mamaki ko ta ji haushi akan tahowa da Yadira da suka yi ba,kawai dai ta saka a

ranta maybe hutu za ta yi musu ko kuma zaman d’aki ko kuma ma maybe za ta zauna a wajen su ne har abada tunda as far as she knows Yash shine Babba a gidansu kuma dole dama yadda yake da rufin asiri ya kamata ace yana ragewa Daddy waensu abubuwan.

Addu’ar

ta d’aya itace’Allah Ubangiji ya sa Yadira kar ta zame mata matsala’…dukda ta lura ko d’azu da suka zo ita da Yusra ne suka gaida ita sannan yanzu ma bataga alamun rashin kunya ko rashin mutunci a tartare da Yarinyar ba,sai dai kuma ta fahimci ba sa yi mat

a rashin mutuncinsu idan a gaban Yash ne but yanayin Yarinyar na yanzu ta ga kamar ba irinsu bace ita dan haka ta saka kyakkyawan zato a ranta ta yi ta addu’ar Allah Ubangiji

ya sa su zauna lafiya ita da Yadira…dan tabbas ta san tafiyar Yadira ba kwana k

usa bane idan ma za ta tafin d’in kenan!duba da yadda ta ganta da akwatunanta d’urma d’urma har guda biyu da jaka.Ta san ko tafiyar ma da za su yi honeymoon definitely sai dai su barta a gidan a turo wata babba ko mai aiki ta zauna da ita kafin su dawo….ta

nata wannan tunanin ta ga Yash ya d’auki hanyar gidansu,ba ta san lokacin da ta fara zuba murmushi ba wanda har sai da Yashjub d’in ya ji ya d’an juyo ya kalleta suna had’a ido ya d’aga mata gira d’aya kafin yayi wani d’an guntun murmushi ya maida hankalin

sa ga tuk’in da ya ke yi.

Tun lokacin da su su Ya Musbah suka bar gidan Manubiya yake k’unci!.

Gaba d’ayan su sun ji haushi kuma sun ji babu dad’i game da halin da suka je suka tarar da y’ar uwar tasu a ciki amman kuma

dama Ya Nafi’u ya san akwai a

bunda yake damun Ya Musbahn kwana biyun nan dan tun kafin su je gidan Manubiyan ya ke la’akari da shi ya lura damuwar tasa ta yau ma ta fi ta kullum….shiru kawai ya yi masa ya na mamakin yadda k’iri k’iri wai yau shine Ya Musbah yake b’oye wa damuwarsa da

n ya lura sam baya so ma ya fahimci yana da matsala.

Shiyasa yau kam ya na yin parking a k’ofar gidan ya cewa su Aisha “su shiga wajen inna, za su taho nan ba da jimawa ba da shi ya Musbah.

Sai da Ya Musbah ya bud’ewa Muhsin wanda suke zaune a gaban

tare da shi ya fita

tukunna ya juya ya kalli ya Nafi’u ba tare da ya rufo murfin motar ba yace

‘’Jiya ma ka tambayeni kuma amsa d’aya zan baka,’ba abunda yake damuna’saboda dagaske babu abunda yake damuna d’in‘’.

Cikin tarar numfashin sa ya Nafi’u ya

ce

‘’Ko kuma dai ba za ka gaya min ba saboda ka san ba zan tab’a goya maka baya ba ko?,

Haba Musbahu na fa san a kan Baraka ka shiga wannan damuwar.”kafin ya gyara zama ya fuskance sa tukunna ya d’aura da cewa”har wanne dad’i ku ka yi da Baraka da har za

i sanya kake missing d’inta har haka?.

Baraka fa Musbahu!”

Ya k’arashe maganar tasa cikin rashin jin dad’i.

Shiruuu Ya Musbah ya yi kafin yace”ba fa a kan Baraka na shiga damuwa ba!shin ba ka ga halin da muka tadda Manubiya sannan muka baro ta a ciki ba

ne?”

Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace“Jiya waye ya je wajen Baraka bayan sallar Magrib???”

Da sauri Ya Musbah ya d’ago ya kalle sa sai kuma cikin fushi yace “Bibiyata kake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login