Showing 105001 words to 108000 words out of 259716 words

Chapter 36 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

63

ch

an jira yakeyi a tambayesa yace

“Idan na ce inaso in dawo da Baraka inna za ki iya yafe mini?’’

Ya fad’i hakan kwayar idanun sa suna kallon k’asa.

Ahankali ta zame hannunta daga fuskar sa ta kawar da kanta gefe.

Da sauri yace

‘’ki yi hak’uri ins

haaAllah ba zan sake yin maganar ba‘’

Ahankali ba tare da ta kallesa ba tace

‘’Musbahu mai ka d’auke ni?”

Da sauri ya sake cewa

‘’Ki yi hak’uri Inna inshaaAllah ba zan sake yin maganar ba har abada,dan Allah ki yi hak’uri’’

Ya fad’i hakan yana m

ai k’ok’orin mik’ewa.

A hankali ta ruk’o hannunsa ta d’ago da fuskarta ta kalle sa kafin tace‘’Ba ka bani amsata ba!.

Mai ka d’auke ni?”

Ganin ya yi shiru ya sunkuyar da kansa k’asa ne ya sa tace”A tunanin ka idan uwar Mijin Jidda ko Manubiya ta bayar d

a gudunmawa wajen kashe musu aure murus zan ji dad’i?.

Sannan kana tunanin dama chan Ina farin ciki ne saboda ka hukunta Baraka a ta dalilina?

Bari kaji..Baraka ta yi mini k’ololuwar rashin mutunci amman a ko da yaushe idan na tuna da mai sunan baba na t

una cewa a ta dalilina iyayen sa suka rabu gaba d’aya sai in ji babu dad’i.

Dukda na ji dad’i kuma ka zame mini abun alfahari Musbahu saboda yadda ka nuna b’acin ranka a lokacin da aka wulak’anta ni,na ji dad’i!na ji dad’i matuk’a! kuma har gobe Ina sanya

maka albarka amma kuma idan ka ce za ka dawo da matar ka ba zan ji haushi ba dan Babban burina a yanzu shine in ga kai da k’annenka zaune lafiya a gidajenku..”

Hawayen farin ciki da k’aunar mahaifiyar tasa ne suka shiga sintiri a kan fuskarsa bai san l

okacin da ya rungumeta ba yace”Amman Innaa sai nake gani kmr ban kyauta miki ba…”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta saki murmushi ta d’ago ta kallesa tace

‘’ ka dawo da ita na san yanzu ta ku san fita daga idda ma ko?”

Ba ta jira jin amsar tasa ba ta

d’aura da cewa”ni kaina ba son zaman nan naka nake yi a d’aki gabjeje da kai ba.Ka dawo da ita ku koma gidan ku ku ci gaba da rayuwar ku Allah ya yi maka albarka.”

Tana gama fad’in haka ta mik’e ta fice daga d’akin ta nufi kitchen bayan ta d’auki mayafi

n ta.

Ya Musbah bai tashi a wajen ba sai da ya maida Baraka

Cikin tsananin jin dad’i ya mik’e ya fice…wajenta ya fara zuwa ya sanar mata ta yi masa iso cikin gidan su ya sanar da Mamanta aka kira kawunta a waya dake ba a garin yake ba shima aka sanar

masa…tukunna ya wuce aiki daga baya,suna ta murna shi da Baraka.

Sai dare tukunna Innaa ta samu Baba ta gaya masa yadda sukayi da Ya Musbah.

Dama ta san zai yi fad’a shiyasa ta bari sai dare..ai

kuwa ta sha fad’a dan rabon da Baba ya yi mata irin ha

ka har ta manta.

Jidda kanta ba ta ji dad’i ba

dan ita har ga Allah a tunanin ta Baraka ta tafi kenan..wacce iriyar zuciya ce da Inna haka?ta ya za ki bayar da goyon baya d’anki ya dawo da matar da ta yi miki wannaann kalar wulak’ancin….

Kuma ta san In

nar ta san Baba ba zai yarda ba shiyasa ta k’i tsayawa a yi shawara da shi ta yanke hukuncin ita kad’ai.

A b’angaren Baba kuwa….ya san idan har zama bai k’are ba to ko yankasu Baraka take yi a da! sai ta dawo.

Dan haka dama shi basa da m burin raba aur

enta da Musbahu murus rabuwa ta har abada kuma shi ba wai yanaso ta dawo baneba kawai dai a nasa b’angaren duk abunda Allah ya tsara tou zai yi maraba da shi…Kawai shi babban abun da ya b’ata masa rai shine yadda aka dawo da ita da wurwuri ba tare da ta ga

ma gane mutuncin iyayensa ba

dan yanzu ba ta horu ba ya tabbatar ko da gidan gyaran Hali aka kaita bai ci ace ta yi hankali a cikin wata uku da y’an kwanaki ba.

Saboda Allah tsabar rashin lissafi ace wai duk kalar tujarar da Baraka ta yi amman Musbah ya

maido da ita ko idda ba ta fita ba sai kace er gwal!.

Ba kalar fad’an da Baba bai yi ba,daga k’arshe ma kawai ya mik’e zai fita dan takaici yasa yake ji ba zai iya ci gaba da zama a cikin d’akin ba.

Yana Isa bakin k’ofa ya ci karo da Ya Musbah da mai

sunan baba.Bai gama k’are musu kallo ba ya ga Baraka a bayan su…da farko so ya yi kawai ya zagayeta ya wuce amman kuma sai ya koma ya nemi guri ya zauna..

To dai Allah kad’ai ya san kalar turare da rubutun da Baraka ta yi ta sha dan tashi d’aya zuciyar Ba

ba Inna da Jidda har ma da Muhsin wanda shigowarsa kenan daga d’akinsu ta yi sanyi.

Har k’asa da durk’usa ta bawa Inna hak’uri tana kuka tana cewa sharrrin shaid’an ne

haka shima ma Baba ta basa hak’uri.

Har Jidda sai da ta bawa hak’uri Akan abubuwan

da ta yiyyi.

Daganan d’akin ya d’auki shiru

kafin Baba ya kalli Ya Musbahu yace “ka riga ka maida ita ko?”

Jin jina kai ya yi alamun ‘eh’

ya na mai jin kunya da nauyin Baba.

Ajiyar zuciya Baba ya sauk’e kafin ya ce”Sai ku tare da wuri,

Allah y

a so naga gidan naka babu kowa a ciki”

Daga haka ya fara k’ok’arin fita.

Kamar Ya Musbah ba zai ce komai ba sai kuma ya d’an yi gyaran murya yace

“Wai da sai nan da sati biyu tukunna dan itama ta samu ta bayar da kayayyakinta gyara nima kuma akwai y’

an gyare gyaren da zan yi a gidan.”

Jin jina kai kawai Baba yayi daga haka ya mik’e ya ce “Allah ya yi albarka.”

Yana gama fad’in haka ya sa kai ya fice.

Sai chan dare tukunna Baraka ta tafi ta barsu da abubuwan mamaki…ko magana za ta yi da Inna sai

ta sunkuyar da kai k’asa

Hatta Jidda yadda take janta a jiki abun sai da ya basu matuk’ar mamaki

Gashi tace za su tare ne tare da Muhsin

Shi dai Muhsin ya bita da to ne amman har ga Allah in ya tuno halayenta sai ya ji baya son bin su,matar da ada kwa

ta kwata ko dariya ba ta yi masa bata jan sa a jiki yanzu kuwa tashi d’aya ta dawo kamar za ta goya sa dukda Yarone amma ya saka a ransa watakil dan ta ga Innaa ne kuma dan taga Gidan su ta zo shiyasa take ta faman lallab’asa ya san yana zuwa gidan ta zata

fara cin k’aniyar sa.

Dukda yadda yanzun yake jinta har cikin ransa amman still yana iya tuno halayen Baraka a gidan ta….

Jidda kuwa Allah Allah takeyi Baraka ta tafi ta samu ta kira Manubiya,dan kanta ya rabu biyu

It’s either

Fad’a akayi mata a g

ida da kuma yanayin duniya da ta gani ta gane gaskiya ta yi dana sani ta shiryu da gaske

Ko

kuma dai

Wani abun ne a cikin zuciyarta dan Barakar da ta sani ba zata nutsu irin haka a lokaci guda ba tare da kwakkwaran dalili ba……

Sai chan dare su

Manubiya suka isa Gida dan sai da suka biya suka ci abinci suka d’an zagaya suka fara rage siyayyar su tukunna suka nufi gida kowa a gajiye.Suna zuwa Yashjub ya cewa Yadira “ta zab’a d’aki”

Na nan saman opposite d’akin Manubiya ta nuna dan haka ya cewa

drivern gidan da ya tayasu hawowa da kayayyaki “ya saka mata kayan ta a ciki”.

Wanka kawai ta yi ko sallah ba ta nutsu ta yi ba ta d’auki abunda su Mommy suka bata ta fito.

A zaune ta sami Manubiya tana waya da Jidda tana bata labarin Baraka.

Kamar Ma

nubiya za ta had’iyi zuciya kuwa haka taji..ashe dama shiyasa ta ga yanata tunani for the past few weeks,d’azu kuma ita a tunanin ta ma ko kukan da ta yi ne ya b’ata masa mood d’in sa ya saka shi a damuwa ashe shi tunanin shegiya Baraka yakeyi.

Taya Ya Mu

sbah zai so Baraka ta dawo wanne irin abu ne haka!…a hankali ta lumshe idanuwanta ta bud’e kafin ta d’ago ta kalli Yadira tace “zauna mana”

Sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tace “zan kiranku Jidda”daga haka ta katse wayar,tana mai jin kanta yana wani ir

in juyawa tsabar takaicin Baraka da Ya Musbah.

Tsaki Yadira ta yi kafin tace

“Ai ko ba ki fad’a ba!”

Sai kuma ta zauna tace”duk fushin da mutum zai yi nan gani nan bari..zama daram babu inda zanje”

Ahankali Manubiya ta d’ago ta kalle ta har za ta

bata amsa sai kuma kawai ta mayar da kanta k’asa.

Ba tare da b’ata lokaci ba

kawai ta ga Yadira ta mik’e tafad’a toilet d’inta wuff!

A shirye da shirin ta na bacci tsaff ta ganta shiyasa abun ya bata mamaki ta shiga tunanin ‘to mai ta shige za ta yi…



A b’angaren Yadira kuwa ba kalar barbad’en da batayi ba a b’an d’akin dukda ta ji ba dad’i kuma tana ganin abun somehow amman hakanan ta rufe ido ta yi ta bankawa tana yi tana jin wani iri dan kusan kullum a makaranta ita da k’awayenta basu da aiki sai

zagin masu asiri da uwar da take koyawa yaranta asiri sai gata yau tsulum a cikin harkar dumu dumu…

Tunda ta shige Manubiya ta saki baki dan Yarinyar ta bata mamaki sosai

Ita ba ma wai batun zargi ko wani abun ba audacity d’in Yarinyar ne ya fi bata

concern.

Tashi d’aya kuma sai ta ji gabanta ya yanke ya fad’i tsigar jikinta tana tashi dan haka Yadiran tana fitowa ta mik’e tace

‘’Dakata Yadira’’.

Ko kallon ta Yadira bata yi ba haka ta juya ta kama hanyar fita…tsabar takaici Manubiya bata san lokac

in da ta matsa da sauri ta ruk’ota ba dan a ganinta wannan k’arshen rainin wayo kenan

Ta shigo ta gaya mata magana ta mik’e ta shige mata toilet kuma ta fito ko sallama ba ta yi mata ba zata fice

Shiyasa ta na ruk’ota ta juyo da ita cikin fushi tace



’akwai band’aki a k’asa na bak’i akwai a dakin ki akwai a corridor d’in saman nan sannan akwai a d’akin bak’in dake a k’asa,duk wani uzurin ki ki je ki yi a chan ko da wasa kar in sake ganin kin shige mini band’aki,bamuyi wannan sabon ni da ku ba as far as

I know da kuma yadda kuke nunawa ‘kun tsaneni!’.’’

Cikin fushi Yadira ta fincike hannunta sannan tace

‘’Eh lalle Manubiya kin auri mai kud’i, Allah sarki d’an Adam mai manta gobe, yanzu ke har kin manta yadda ke da uwarki da ubanki kuke sharing band’

aki shine yanzu har kike da bakin cemin wannan personal toilet d’inki ne…..”

Mahaukacin marin da Manubiya ta d’auke ta da shi ne yasa ta gagara ci gaba da magana dai dai nan ne kuma

Yashjub ya shigo cikin d’akin.

Da sauri ya k’arasa inda suke a tsaye

yana cewa lafiya??!Baby mai ya faru har kika mareta haka?..”

Ihun kukan da Yadira ta fasa ne yasa ya kasa cigaba da magana,da sauri ya juya ya kalleta ya shiga duddubata yana kallon yadda shatin y’an yatsun Manubiya suka fito rad’au a fuskar ta..cikin ki

d’ima da tashin hankalin ya shiga addu’a a cikin ransa’Allah ya sa kar Yadira ta gaya wa su Mommy an daketa’ dan idan akwai abunda Daddy ya tsana to shine ka tab’a masa Yaro”

Cikin d’an fushi ya juya ga Manubiya yace‘’ next time idan ta yi miki laifi u

report to me!kar ki sake marin ta.”

Daga haka ya ja hannun Yadira suka fice tanata uban kuka tana kiran sunan Mommy.

Suna fita Manubiya ta share zafafan hawayen da suka zubo mata ta durk’ushe a wajen….anya auren Yashjub ba mistake bane ba kuwa!

anya

zata tab’a samu farin ciki a cikin gidan nan, gashi tun ba a je ko ina ba ta fahimci kamar so yake ya hanata karatu!da farko yace mata ba ya son chud’anyar ta da maza yanzu kuma ya zo yace”ya riga ya yiwa Najeeb magana zai sanar da ex colleagues d’insa su

yi mata chuku chukun deferring zuwa nan da lokacin da za su dawo. Zai yi tunani kafin nan…”

Ta jima a tsugunne a wajen kafin ta mik’e ta fad’a toilet domin ta wanke fuskarta…

Tana shiga cikin band’akin lokaci guda ta ji duk duniya babu wanda ta tsana s

annan ba ta son kallon ko da fuskarsa ne kamar Yashjub

Ita tunani ma ta fara yi wanne dalilin ne ya sa ta aure shi in the first place dan ta nemi soyayyar da take yi masa tashi d’aya ta rasata….

Suna shiga d’aki Yadira ta juyo tana kuka tace

“Wall

ahi Ya Yash ban yi mata komai ba!”

Cikin katseta Yashjub yace”ban tambayeki ba!.Yadira kin bani mamaki…ashe haka kika zama haka kika koyi k’arya?Manubiya mahaukaciya ce da za ta dake ki ba tare da kin yi mata komai ba?dama zuwa kika yi ki kashe mini aure?

ashe bakya sona a matsayina na d’an uwan ki ni ban sani ba..”

Tashi d’aya ya fahimci yadda jikinta yayi sanyi k’alau dan haka ya sake tabbatarwa tabbas akwai abunda ta yiwa Manubiya….a tunanin sa su Mommy sun turota cid ne amman yanzu ya fahimci an tur

ota ne ta kashe masa aure!

mai yayi wa su Mommy ne da har suke son rabasa da Manubiya su had’a sa da Kausar dan ko shi Yarone tou ya kamata ace zuwa yanzu ya fahimci manufarsu kenan

Mai yayi musu da zafi haka mai yasa duk yadda yake k’ok’ari wajen gani

n ya shafe laifukan Mommy dole ita kuma sai ta san yadda ta yi ta nuna masa bafa ta son shi…..

Kasa ci gaba da tsayuwa a d’akin ya yi dan haka kawai ya juya ya fita zuciyar sa tanata faman tafarfasa.

Kitchen ya fara zuwa ya zauna a kan dining table d’in

ya yi shiruu kafin chan ya nufi fridge

ya d’auki ruwan sanyi ya b’alle murfin ya kafa a baki sai da ya shanye tukunna ya ajjiye robar yana mayar da numfashi….ya jima kafin ya fito ya nufi sama d’akin Manubiya.

Yana shiga daidai ita kuma tana fitowa d

aga band’aki…d’auke kai tayi ta turo baki gaba ta yi kamar bata gan sa ba.

Murmushi yayi ya k’arasa inda take anan gaban madubin ya rungomata ta baya.

Yadda Manubiya ta ji ita kanta saida abun ya bata mamaki dan ji ta yi kamar wani k’aton arne ne ya rung

umeta,saida ta yi da gaske tukunna ta lallashi zuciyarta da take azalzalarta akan ta hankad’e sa.

Ahankli ya d’an sunkuyar da kansa ya yi kissing wuyanta kafin yace “ki yi hak’uri Yadira Yarinya ce,um…”

ya fad’i hakan ya na sake rungumarta sosai izuwa ji

kinsa .

…Inaa she can’t take this anymore dan haka ta juya da sauri ta hankad’esa!ba dan Yashjub yana da k’arfinsa ba da sai ya zube a wajen.

K’ura mata ido ya yi sai kuma ahankali ya d’an matsa ya kamo hannunta yana kallon fuskarta da serious face yac

e “are u okay??”dan har wani jaa yaga idanuwanta da kan hancinta sunyi irin mutum yana cikin tsananin tashin hankali da b’acin ran nan.

Ba ta kulasa ba kuma yaga alamun bazata kula shin ba

dan haka ya sake matso ta a hankali da kyar kamar wanda yake jin

tsoro yace”mai ta ce miki?

Mayene ya faru dear tell me menene matsalar??”

Tashi d’aya ta fashe da wani irin gigitaccen kuka wanda ya gigita Yashjub yana shirin sake matsowa tace

“Kar ka tab’ani ka fita kawai banason ganin ka!”

Kamar zai fashe da kuka

yace

‘’baby ni d’in ne bakya son gani?ki yi hak’uri komai zai yi daidai yanzu sai kin d’anyi hak’uri da su am…”

Cikin katseshi sannan da k’arfi tace

“Ka fita nace!!”

Da k’arfi kamar ba mijin ta take yi wa magana ba.

Ahankali ya lumshe idanuwan sa

ya bud’e kafin yace “to mu je d’akina sai mu yi magana ko??..in bakya son zama da ita a kusa ne mu je sama d’akina ki kwashi kayanki ma gabad’aya daga nan sai ki koma chan da zama ko?”

Wani kuka ta sake rushewa da shi ta durk’ushe a wajen tace

“Dan A

llah ka fita bana son ganin ka!”

Wani irin bugawa zuciyar Yashjub ya yi dan kalamanta sun shige sa sosai…shiruu ya yi kafin kawai ya juya kamar mara lakka a jiki haka ya fice ya rufo mata k’ofar.

Sai da ya biya d’akin Yadira yace mata”Ko da wasa kar ta

kuskura ta je inda Manubiya take ko sun had’u daga nan har gobe bai yadda ta yi mata ko da kallon banza ba

Infact ta zauna a d’akin ta ma kar ta kuskura ta fita koina sai gobe ai taci abinci..”

Da “to” kawai ta amsa shi daga haka ya juya ya fita.

Ya

na fita Yadira ta yi wani murmushi dan da da farko ta d’an ji tausayin sa ta ji babu dad’i amman taba tuno hud’ubar su Mommy da Yasira sai ta ware.

A take ta d’auki hoton fuskarta Inda shatin hannun Manubiya ya fito,tun daga kan Daddy har zuwa kan Yusra b

abu wanda bata turawa ba tace”Manubiya ta mare ta daga zuwan ta yau!”

Daga nan kuma ta kira su Baba larai tace “ta zuba abunda aka bata successfullly.”

Yashjub yana fita Mannubiya ta sake sakin wani irin kuka kamar ranta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login