Showing 75001 words to 78000 words out of 259716 words

Chapter 26 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

56

zai tab’a yarda ya aureta ba har abada hatta su Yasira ta san sai bak’in jinin ta ya shafesu watak’il ma ya tartara kayansa ya tafi ya koma uk ya zauna a chan shikenan ba za a sake ganinsa ba

har abada.Shiyasa ta fara k’ok’arin fahimtar da Kausar d’in cikin lallami.

Ganin hakan ya sanya Kausar ta wuceta da sauri tana wani Irin kuka ta d’auki wayar ta da makullin mota ta fice da gudu gudun ma kar Mommyn ta yi yunk’urin tsaida ita,a ranta ta ga

ka yanke decision ‘wallahi sai ta bar gidan a yau!.’

Dai dai nan ne kuma Munirat ta zabgawa Yusra mari suna shirin rufar mata suka ga Kausar ta sauk’o da mugun gudu tana kuka Mommy ma wadda ta biyo ta tana kiran sunanta tana hawaye sharr kamar an kunna

famfo.

Da sauri Yassira ta k’arasa bakin main door ta tsaya dan taga nan Kausar d’in ta nufa,durk’ushewa Kausar ta yi a daidai gaban Yasira tace”Yasira dan girman Allah ki matsa in fita,idan na ci gaba da zama a cikin gidan nan mutuwa zan yi ba zan tab’

a iya zama a gida d’aya da Yash da Manubiya suna tare ni kuma ina kallonsu a gefe,yanzu haka ma baki san ya nake ji ba,na san suna chan tare!duk da haka na yi k’ok’ari na danne kai na amman naga Mommy so take yi sai na mutu tukunna za ta kyaleni”….muryart

a ce ta sark’e sakamokon numfashinta da ya d’auke dan haka ta kasa ci gaba da magana ta shiga kokawar janyo numfashinnata .

A hankali Yassira ta durk’usa a wajen k’asa k’asa tace”Kausar kar ki yi disgracing kanki,kalli

yadda su Ummi suke kallon….”

Cikin tsananin fushi tace

“Disgrace my foot!su kalla mana!ina ruwana so kike in yi pretending bayan kowa idan ya ganni ya san Ina cikin tashin hankali kuma na kasa kuma kun kasa yi min maganin matsalata?…akwai disgrace da rashin gatan da ya fi wanda n

ake a ciki??”

Ahankali Yasira ta janyota ta shiga lallashinta.

Kamar Kausar d’in zata mutu tace “Ina ta k’ok’arin ganin na yi picking pieces of myself nayi staying strong amman shine

kuma duk da haka wai Mommy

saboda ba ita ta haifeni ba

ta zo ta

na ce min wai Manubiya za ta dawo nan!

Wanne irin rashin adalci ne wannan?.Ba ku ma da shirin korarta kwana kusa kenan sannan ta ya zan iya zama ta dawo nan Ina kallonsu tare a waje d’aya a d’aki d’aya da Yash!?”

Ganin yadda su Yahanasu suka zuba musu

ido ne yasa Yasira tace”calm down mana Kausar,ki zo mu je….”

Fincikewa Kausar d’in ta yi cikin tsananin fushi

tace “Stop telling me to calm down!tun yaushe kuke cemin in yi calming down in yi shiru za ku san abunyi amman har yau shiru???inda ace ke ce k

o su Yusra na san da tuni Mommy ta uzzurawa Baba larai an yi an wuce wajen…….”

Da sauri Mommy da Baba larai suka k’arasa inda take k’asa k’asa suka shiga yi mata magana amman inaa kamar zuga Kausar ake yi gashi sai d’aga murya take yi tana ta yi musu b’a

ramb’atama.

Takaici ne ya rufe Yassira

ga Munirat Ummi da Yahanasu sun tsura musu ido,shiyasa ba ta san lokacin da tace “Useless munafukai kawai!kun wani tsaya kun tsurawa mutane ido”

Yahanasu ta ji zafin zagin amman sai ta danne ta saki dariya kaf

in tace”Ku fa kuka ce kar mu yi bacci yau,ko ba kune kukace kar wadda ta bar parlourn nan tsakanin mu nida Munirat ba!”

Cikin fushi Yassira ta k’arasa inda take ta tsaya a daff da ita

tace” Yahanasu ki kiyayeni!

Wallahi ki kiyayeni!.

Mara Imani mar

a tausayi kawai!na tabbatar misery d’in Kausar ne yasanya ki farin ciki da dariya haka,muguwa azzaluma!”

Murmushi Yahanasu ta yi kafin tace”Sam ba abunda ya saka ni dariya ba kennan,farin cikin ganin yadda kuka fara tonawa kanku asiri ne yasanya ni dari

ya Yassira ramin k’arya ai dama k’urarre ne!”

Cikin fushi Yasmeen ta matso ta ce “I have said enough Yaha”kafin tace “Da ke da Ummi da Munirat ku wuce ku bawa mutane waje.

Tun zagin da Yasira ta yi musu dama Munirat tazo k’arshen wuya,Ummi kuwa ji ta

yi da ta sani da tuni ta yi sama abunta…cikin b’acin rai Munirat ta ce”Saboda kar mu ji more of your dirty secret ko?wai ni Yasmeen wa kuka haifa a cikin mu ne?,ni ko Yahanasu ko Ummi?dan naga yadda kuke yi mana magana kamar irin kun samu ya’yan cikin ku

d’innan”

Ta fad’i hakan tana matsowa daff da su.

Yassira a k’ufule take

shiyasa tashi d’aya ta rufe Munirat da wani irin mahaukacin duka,kamar

jira Yasmeen take itama ta sa hannu dama ta tsani Yarinyar,

haka Yusra itama dama a wuya take.Hatta Ya’

isha da Yadira shiga sukayi sukai mata rubdugu.

Yahanasu da Ummi ne suka fara k’ok’arin kwatar Munirat,without thinking twice su Yasmeen suka fincikosu dama haushin Yahanasu suke ji shiyasa suka fi rufar mata suka fi laftarta,itama Ummi sai da suka kai m

ata duka a Kai suka kaita k’asa.

Dai dai nan Daddy ya fara sauk’owa k’asan sakamokon hayaniyar da ya jiyo.Wata mahaukaciyar tsawa ya daka musu wadda ta sa suka d’an tsaya sai da suka d’ago suka had’a idanu da shi tukunna suka ja da baya suna huciii,har

Mommy wadda ta matso kwatar Yahanasu.

Duk yadda Ummi ta so kasa daurewa ta yi,ba ta san lokacin da hawaye suka fara sintiri akan kumatunta ba…..wajen Ummin Daddy ya fara zuwa ya d’an shafa inda ya ga Yassira ta kai mata duka akai,wajen har ya d’an yi

jaaa.

Tashi d’aya idanuwansa suka yi jajir ya juya ga Yassira

tana shirin yin magana ya rufeta da duka,hatta Yasmeen da Yusra saida suka karb’i

rabon su amman sun samu sun zille dan Yassira ya rik’e,ita ta fi

fusatashi.dan dama Ummi ba ta dad’e da

gama faiyyace masa abunda suka aikata a gidan Yash da gidansu Manubiya ba…tashi d’aya daga jin zancenta ya fahimci ashe k’arya suka shirga masa d’azun da suka dawo,dama yana jin haushin su akan hakan yanzu kuma ya ga wannan shirme da aika aikar da suka yi

shiyasa ya fusata ba kad’an ba.MANNUBIYA

(Book 2)

Page 21

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Abunda bai tab’a yi ba kenan’dukan y’ayansa’.Shi da kansa yana jin zafin dukan nasu da yake yi a halin y

anzu amman kuma ya zama dole a taka musu burki dan tabbas abun na su ya zarce misali.

Waya Mommy ta karb’a a hannun Yadira wadda ta b’uya a bayanta,tashi d’aya Mommy ta danna kiran Yassir,dan sun gagara kwatar Yassira a hannun Daddy.Yana d’auka tace”dan

Allah Yassir ka yi maza ka zo yanzunna.”

Sai da kyar tukunna daidai

Yassir d’in yana shigowa cikin parlourn

Ummi ta samu ta janye Daddy

yana huci….babu abunda ya fi d’aga masa hankali kamar Yahanasu da ya gani a kwance dan ko numfashi ma yaga kama

r ba ta yi…idan sun daki Munirat saboda Allah

Yahanasu da Ummi ai ba sa’anninsu baneba.!

Cikin kuka Mommy ta matso tace”a kanta ka dakar min y’ay’ana mata ba maza ba??

yanzu kai a ganinka ya dace ace ka yi musu wannan dukan??dan ni a ganina ko

Yad

ira ta wuce duka ballantana Yassira!Yassira fa

ka daka!ka bud’e idanunka da kyau ka gani”

Cikin rashin jin dad’i

Ummi tace “Tabbas Mommy kin tabbata wadda ba ta san abunda ya kamata ba,dan an

daki Yassira?kalli Yahanasu fa ko motsi ba ta yi,kalli

goshin Munirat duk jini,sannan ni kaina Yaran nan ba su kyaleni ba amman shine……”

Cikin tsananin b’acin rai

Mommy ta yi kan Ummi kamar za ta daketa ne tace”Saddik’a!

zan miki first and last warning!daga yau duk wani abunda ya shafe ni!ni ko y’ay’ana ka

rki sake shiga!babu ruwanki da mu ba ruwanki da rayuwar mu ba ruwanki da damuwar mu!,ban san wanne Irin naci maita jaraba da shishshigi Allah ya yi miki ba…duk inda ake case d’in da bai shafeki ba a cikin gidan nan to sai an ganki a wajen.

Har ga Allah ki

n takurani ko tari ki ka jiyo na yi sai kin zo wanne irin jaraba ne wannan??”

Sakar baki kawai Ummi ta yi tana kallon ta…Baba larai kuwa ji ta yi kamar ta rufe Mommy da duka,dan yanzu kam ta san Mommyn ta riga ta gama nunawa Ummi wacece ita tsirararta.

Ummi tana shirin yin magana Daddy yace mata”wuce ki tafi

sama ki jirani a d’akina”

Har za ta yi musu sai kuma kawai ta juya ta wuce saman zuciyarta fall cike da mamakin Mommy,tashi d’aya itama Munirat ta mik’e ta nufi saman tana mamakin yadda ko kall

on inda take Yassir bai yi ba amman ya nufi Kausar ya je ya durk’usa a inda take yana ta faman lallashinta kmr shima zai fashe da kuka.Sai da Ummi ta biya da Munirat d’akinta ta bata paracetamol ta goge mata ciwon da ta ji da spirit ta saka mata plasta tuk

unna ta nufi chan sama ta shige bedroom d’in Daddy ta zauna zaman jiransa kamar yadda ya ce.

Suna wucewa Daddy ya dakawa Yassir tsawa”Tashi a wajen ka kyaleta!bansan mai ya faru ba amman na san itace ummulabaisin abun nan da ya faru!

Cikin rashin ji

n dad’i

Yassir ya mik’e yace”Haba Daddy…”

Wata uwar tsawa Daddy ya kuma daka masa tare da cewa

“na ce ka kyaleta!ka zo ka tayani kai Yarinyar nan asibiti ko?”

Kamar Yassir zai fashe dan takaici,haka nan ya na ji yana gani ya baro Kausar ya zo ya durk

’usa ya kinkimi

Yahanasu suka fice tare da Daddy ko kallon Yassira wadda take durk’ushe a wajen Daddy bai kuma yi ba….

Ita ta ma rasa ta yi kuka ne ko ta yi ihu!ba ma ta san ta Ina za ta fara ba,yau ita ce Daddy ya daka haka anya ba mafarki takeyi ba ku

wa?me ya faru?me ya shiga jikin Daddyn nasu tashi d’aya yau haka……

Su Yassir suna fita

Baba larai ta matsa inda take

ta mik’ar da ita ta zaunar da ita ta shiga lallashinta,sai a lokacin ne ta samu ta fashe da wani irin kuka kamar za ta mutu tace”Nima f

a na ji ciwo

kalli goshina!sannan cheeks d’ina gaba d’aya ciwo suke yi min amman ki duba ki ga yadda aka tafi kai Yahanasu asibiti ni aka barni anan.”

Gaba d’ayansu kanta suka nufa banda Kausar wadda ta yi suman wucin gadi.

A hankali Mommy ma ta k’aras

a wajen Yassirar zuciyarta tana wani irin tafarfasa..ta san ta tsani Ummi tsana ba ta wasa ba ta tsani the sight of her ko labarinta bata son ji amman bata tab’a jin tsanarta

ta masifa kamar ta yau ba!..a kanta aka dakar mata y’ay’a!

Inaa ba zai yiu ba

da sake..a tunaninta Ummi k’aramin alhaki ce ashe abun ba haka yake ba dan gashi da idanunta ta gani kuma ta fahimci abunda ta yi ta ke kuma kan yi akanta sam ba ya aiki!..babu abunda ya fi bata takaici irin yadda Daddy yace “ta je ta jirasa a d’akinsa”

I

ta kuma ta yi masa biyayya ta wuce d’ingui d’ingui ta tafi.

A b’angaren Yassira kuwa ta riga ta gama kai wa wuya!Wallahi Daddy ya kunna wuta a cikin gidansa da hannunsa,dan wallahi sai dai in ya koreta a gidan amman da Manubiya da Munirat da Yahanasu da

Ummi sun shiga uku a hannunta…ita kanta tanajin tsoron abubuwan da zuciyarta take aiyyana mata ta aikata wa su Ummin!wallahi duk sai sun ci ubansu…..

Babu yadda Baba Larai bata so ta fahimtar mata da amfanin kissa da siyasa ba amman tashi d’aya tace”wall

ahi ita ta gama kissa da siyasa dan bata ga anfani da ribar yin hakan ba!saita nunawa ummi da Munirat nan fa gidan ubanta ne wallahi hatta Yahanasu sai ta gane kuranta,sai ta sake fahimtar cewa’ba ta fa da uwa!ba ta da gata!sun fi ta power a cikin gidan’.”

Cikin takaici Baba larai tace”Yasira wai ya Ina baki kina k’in karb’a ne?duk fa inda mata suke mata ne kuma dole kowacce da tata kalar power ku daina ganinsu kamar k’ananan alhaki za su baku mamaki!yanzu kalli abunda aka aikata muku duk a ta dalilinsu,k

uma ina mai tabbar muku muddin kuka ci gaba da wannan shirmen wallahi wallahi this is just the begining….dan haka daga yau tunda har ga abunda ya fara faruwa to indai zan baku shawar ku d’auka hatta Manubiya dan Allah inaso daga yau ku nemi zaman lafiya da

ita a gaban idanun su Daddy daganan sai mu san abunyi ta kark’ashin k’asa…”

Cikin katseta Ya’isha tace”Baba larai munfa gama siyasa,mu da gidan uban mu!?amman ki ce sai mun yi musu siyasa?sun shigo sun mak’ale ta k’arfi da yaji and still ace ba mu isa mu

fad’a a yi ba kenan?so kike a taka mu a maida mu gefe kenan?ko ya kike nufi?”

Cikin fushi Baba larai tace”wai ta ya zan yi muku bayani ne ku fahimceni?…ai ba su Ummi na ce ku yiwa siyasa ba!Daddy ne ba na so ya lura ko su fahimci kune masu takalo fad’a s

annan suma kuma su Ummin ba wai b’aro b’aro za ku yi musu ba dole a sakaya wani abun idan ba hakan aka yi ba wallahi ina mai tabbatar muku shi Daddyn naku sai ya maidaku gefe su Ummin kuma su taka ku,idan bai zab’a muku mazaje ko kuna so ko bakwa so ya yi

muku aure kun bar masa gida ba kenan!,kuna abu kamar wasu marasa lissafi!ki duba fa ki ga yadda muka gaya masa abunda ya faru a gidan su Manubiya d’azu da muka dawo amman ya ajjiye namu ya d’auki na Ummi saboda ita ta fi ki iya kissa!,dan ba ni da tantama

itace ta zuga sa saboda tunda ta dawo ta haye b’angarensa ban sake ganinta ba sai yanzu da ta ji hayaniya tukunna ta sauk’k’o.”

Cikin tarar numfashinta Yadira tace”tun da suka dawo take samanshi.”Da sauri Baba larai tace”kin ji ko?ai na sani dama tunda na

ji yana dukanki yana cewa”kina Babba amma ke ce mai janyo magana,ba za ki b’ata masa sunan family ba”na san cewa Ummi ta fad’a masa wani abun.

Dan Allah ku tsaya ku nutsu mu taru mu rufawa juna asiri,ina danne ku kuna biyewa dokin zuciya wallahi za ku kw

ashi kashinku a hannayen ku fa!kuma idan har hakan ta faru kar wadda ta kalle ni dan babu abunda zan iya yi infact yanzu ba kamar da baceba saboda a da da mutane masu sauk’in sha’ani muke dealing da sab’anin yanzu!ki duba fa ki ga Manubiya a yadda ta shigo

cikin gidannnan ta k’arfi da yaji,sannan ita kanta Ummin yanayin aurenta da Daddyn naku komai a lullub’e yake,dan haka ya zama dole ku yi accepting fact ku daina ganinsu as k’anananun alhaki mu had’a k’arfi da k’arfi da wayo da komai tukunna shine za mu c

i riba.Ya kamata ace mun dad’e da wuce wajen nan wallahi ku kuke dawo da mu baya,last time duk kun sauk’k’o kun yi yadda ya kamata ammman yanzu kun sake burkicewa dan Allah ku gyara.”

Shiruu duk suka yi kafin chan Mommy tace”Allah ya sa mu dace,sai kuma

ta kalli Yassira tace”Yasira,ba na son fad’a tsakanin ki da Yahanasu bana so ki yi mata komai…”

K’ura mata ido Yasira ta yi ba tare da tace komai ba,wanda hakan ya sa Mommy ta matso kusa da ita ta dafa ta tukunna tace”Kamar yadda Baba larai ta fad’a’Ummi

!Munirat!Mannubiya!Yahanasu duk kar ki bari hayaniya ta tashin hankali ta shiga tsakanin ki da su wanda har zai janyo idanun

Mahaifinku har ma Yash,ban ce dole sai kin yi zaman lafiya da su ba amman kar ki bari su Daddy su fahimci kuna masu jangolo rigim

ar,mu yi abunda Baba larai ta ce har zuwa lokacin da Allah zai k’addara rabuwar mu da su a samu su kama gabansu.…sannan yanzu the most important thing shine Daddy!,a yadda ya zuciya d’innan komai ka iya faruwa,dan haka inaso da ni da ku mu yi sauri mu gyar

a mu dawo da hankalinsa garemu idan ba haka ba akwai babbar matsala dan indai har baya bayanmu to komai ya d’auko hanayar lalacewa kenan.”

Jin jina kai Baba larai ta yi kafin ta ce”Yauwa ko ke fa!hakan ne ya kamata and InshaaAllah nan ba da jimawa ba Da

ddy zai dawo saiti na san abunda zan yi,amman fa ku ma sai kun taimaka!…”

daga nan ta ci gaba da yi musu lecture….

Shiruu kuwa duk suka yi suna sauraron ta….Yadira ce ta fara lura da yadda Kausar take nan sheme a bakin k’ofa dan haka ta kwala kiran Kausa

r d’in sai

kuma ta nufi inda take suma duk suka rufar mata…..yau ma sai da Yasmeen ta sha wahala tukunna da ikon Allah aka samu Kausar ta farfad’o.

Babu wanda ba ta bawa tausayi ba dan tana farfad’owa da sunan Yashjub ta fara sai kuma ta fashe da kuka.

Dan tun d’azu idan ta rufe idanunta Yash kawai take hangowa tare da Manubiya dan ko ta k’i Allah ta riga ta san by now kam suna manne da juna,wallahi wallahi inda ace za ta iya d’aga k’afafuwanta da sai ta nemi gidan ta je a yau idan ba ta kashe Manubiya b

a to ba sunanta Kausar ba.

Baba larai da Yasmeen ne suka d’auketa suka yi sama da ita dan jikinta in banda karkarwa ba abunda yake yi ta ma kasa tsayuwa…Mommy da cewa ta yi a kaita asibiti amman sai Yasmeen tace”ba komai stress ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login