Showing 54001 words to 57000 words out of 259716 words
yi kamar ta koma cikin motar dan ta tsani
yaran dama tun kafin ta gansu,sam ba ta k’aunar Manubiya da duk wani ahalinta….
Ba yadda ta iya haka ta tsaya dan ga Najeeb ya tunkarosu ta san shima gaida ita zai yi if not wallahi da
tuni ta koma cikin motar.
Aisha ce ta fara gaida Baba Larai kafin su Siyama.
“Alhamdulillah”kawai tace daga haka ta d’auke kai Yasira kuma ta yi sauri ta kara waya a kunneta ta matsa gefe gudun kar ma su yi gigin kulata.
Still Aisha ce ta ce wa su Ya
dira “sannunku”
Kamar ba su ji ta ba haka suka yi mata.
Still Aishan ce ta kuma cewa Baba larai”ya taro?Allah ya sanya alkhairi”
Sai da ta juyo ta kalleta kafin tace“Ameen”daga haka ta zubawa Jidda da Siyama jajayen idanuwanta.
Ita Jidda har ga Allah t
soro matar ta bata,ga kuma Al’ameen da shege Yassir da suka kunno ta,ga shi taga ana amsa musu dakyar su Yusra kam ko kallo ma ba su ishesu ba.Shiyasa kawai sai ta juya ta ce “Siyama,ku taho mu wuce ciki”
Kamar dama jira Yusra take,sai cewa tayi”Atleast a
i kya tsaya ki yi kyakkyawar gaisuwa da y’an uwan wanda kike k’ok’arin shigewa cikin gidan nasa”
Ta fad’i hakan tana murmushin
da mutum zai kasa gane rashn iya magana ne koko dai rainin hankali ne.
Cike da mamaki Najeeb yace “Yusra!Languagee!”
Ya d’a
n ja k’arshen yana mai d’age gira sannan yad’an motse baki.
Juya ido kawai ta yi ta kalli sama dan haushinsa dama gaba d’ayansu suke ji.
Ganin abunda ta yi ne yasa kawai ya d’auke kansa ya kalli Baba larai yace”Ina wuni
Baba ya hidima?
Murmushin yak’e
ta yi
kafin tace”Alhamdulillah
Ya gajiyarku?”
“Mun gode Allah”yace
kafin ya juya ya kalli Yassira wadda ta gama wayar k’aryar ta zo tana gaida shi,da kulawa ya amsa mata daga haka ya juya ya nufi cikin gidan yana mamakin yadda Yadira da Yusra suka
yi masa..wato ko kallo ma bai ishe su ba!tabbas
Yara sun girma kam….
Sir Najeeb yana shiga motar Ummi ta k’araso.
Already su Siyama ko gama gaisawa basu bari sir Najeeb ya yi da su Yassira ba suka matsa da niyyar shiga ciki….Yahanasu ta fito da fara
a ta tarbe su kamar za ta goyasu,wanda hakan ba k’aramin sake tunzura su Baba larai ya yi ba…ita Baba larai
Babban tashin hankalinta ma shine
ta yaya za ta aiwatar da mission d’inta
da waennan jama’un a cikin gidan?..
Lissafin da takeyi kenan suka
ga gate ya zuge motar Ummi ta danno kai.
Cikin b’acin rai Yassira tace
“Innalillahi!
Tabbas matar nan ta ci a bata sarauniyar y’an naci,
Mace ace ba zuciya kwata kwata,a taho a barki amman sai da kika zo?ko wa ma ya yi mata kwatance oho?!”
“Ba zai
wuce angon da kika kira yace ‘mu jira mu taho da y’an d’aukar amarya’ba,kinga
ita da ta fiki ai gashi yayi mata tashi d’aya!”
Yusra ta bata amsa tana mai
wucewa ciki
ranta a mugun b’ace…ta so su Jidda sun biyeta yau da sun ji maganganu wallahi!ta
san
ba class d’inta bane su
sannan ta san idan ta yi hakan zatayi acting childish amman
wallahi sai dai a kirata da jinjirar k’auye!ba ta damu ba. Dan tun da ta d’aura idanunta a kansu ta ji ta yi loosing temper da duk wani hankalinta tashi d’aya.
T
unda take a rayuwarta bata tab’a jin tsana irin wadda take yi musu ba…gashi ta san dole ta dinga ganinsu tunda sun riga sun had’a y’ar uwarsu da yayanta,watak’il ma a haifo
musu mai kama dasu
Innalillahi
wallahi za ta iya mutuwa!ya zama dole a san ta
yi da Manubiya dan ba ta da guri da muhalli a rayuwar d’an uwanta! ashe dama akan wannan y’ar talakawan ya Yash ya d’agawa kowa hankali kenan!dan ganin da ta yiwa su Jidda ya nuna mata cewa Manubiya talakan tukuff ce,shegu talakawan
banza!babu abunda ya f
i sake b’ata mata rai kamar ankon atamfar 4500 d’in da suka yi a bikin d’an uwanta!kamar Yash ace wai an yi ankon 4500 a bikin sa wannan lalacewa haka har ina?…..
Kamar zata fashe haka ta afka parlourn,ko bi ta kan masu goge goge bata yi ba ta wuce sama
Wucewa su Yassira suma suka yi suka nufi cikin parlourn
dan haka da sauri Yahanasu tace”mu je ciki muma,idan muka je kowa sai ta kama floor a samu a sassaka turaren wuta ya ratsa ko Ina dan ba lokaci.”
Ko ishashshiyar gaisuwa da introduction Yahanasu
bata bari Ummi da Munirat sunyi da su Siyama ba,haka nan ta azalzalesu suka shige ciki.
Aisha ta d’an fahimci wani abun,ga kuma yadda y’an uwan Yashjub d’in suka rabu gida biyu da masu hankali da jahilai,shiyasa suna shiga itama ta cewa Siyama ta tsaya i
ta da Munirat da Jidda su saka turare a k’asan su yi ta
gyaygyarawa.
Ita da Ummi kuma suka yi sama da masu gado,
Yahanasu kuma ta yi chan sama turakar mai gida…inda
d’aki d’aya ne tak a floor d’in sai tafkeken roof top open terrace.Saman farko kuma
d’akuna biyu ne da parlour d’aya,sai wani parlour mai kamar d’aki wanda Yash ya zuba kayan gym a ciki dan haka suka tattara kayayyakin gym d’in Najeeb ya kira wasu a cikin masu gyara gidan suka kwasa aka kai d’akin Yashjub dan akwai wani guri a cikin g
lass inda za a iya zuba kayan su kuma suka fara kafa gadon su a nan Najeeb yana cewa “idan Yashjub ya zo Aisha zai nuna”
Itama tace
“Shi za ta ce ya chanza masa tsarin gida!”
Hakanan suna raha suka shiga had’a gidan.
A tunanin su Aisha sun yi zab’
en gado mai kyau da tsada amman sai da suka b’ige da d’an jin kunyar
gadon nasu da suka ga kayan gidan,dan hatta d’akin chan k’asa guda daya na bak’i
Turkish ne a ciki wanda a k’alla sai an zuba miliyan shida tukunna za a sayi gadon.
Kaff gidan Turki
sh ne,Main parlourn k’asa ne kawai
royal white da royal blue,colour din mai masifar kyau,shima kuma saboda ansan Turkish zai yiwa parlourn kad’an kasancewarsa
tafkeken gaske shiyasa aka zuba royal complete set d’urma d’urman gaske mai tafe da set d’in
dining table da madubin sa da komai.
Kitchen d’inta ma royal blue ne da white,wanda had’uwa girma da tsaruwar kitchen d’in
yasanya Siyama da Munirat suka tsaya suna ta zancen kitchen d’in da k’auyanci suna yiwa kansu dariya
Dan tashi d’aya tasu ta zo
daya gashi har sun saba……
Gidan ya had’u k’arshen had’uwa,ko ina wajen deco
da saka tv an yi decorating
da wani had’add’en painting
jikinshi kmr marbles,kuma duk
iri d’aya grey da white kalar marbles d’in gidan mai masifar kyau,Pop da chandelier k
am ba a magana ga toilets da closets suma abun kallo,gida dai ya had’u iya had’uwa
wani abun ma sai wanda ya gani
….
Shiyasa su Siyama suka dinga jinjina izza da kud’urar ubangiji dan tabbas idan ba Allah ba to babu wanda zai yi haka,wai nan ne gidan
Manubiya!
Allah mai girma da iko!.
Murna da farin ciki kam sunyi mata bila adadin dan ta samu duniya sai dai ta tashi ta nemi lahira,sannan ta samu miji mai
tsananin sonta da k’aunarta,ga hutu Allah ya bata matsalar d’aya ce ‘dangin miji’amman baya ga
wannan
Manubiya kam ta samu komai…a ce a d’aukota daga gidansu tashi d’aya a kawota wannan gidan haka
mara makusa ko d’aya!
dan tun daga waje!gate!har compound d’in gidan wanda ya ji interlocking concrete da grass carpet da garden
a haka ma basu za
gaya baya sunga swimming pool ba
sam babu makusa.
Duk iya kushewar mutum sai dai ya hak’ura in ya shigo wannan gida na Manubiya da Yashjub.
…….
…D’akin bak’i Jidda ta bud’e ta shiga,ita sam ba ta yi tunanin akwai mutum bama sai da ta yi
ido biyu das
u Yasmeen tukunna tashi d’aya tace”Sorry
daga haka ta juya.
Tsaki Ya’isha tayi,dai dai
Jidda ta kama handle d’in k’ofar ta bud’e da niyyar fita ita kuma Yasmeen tace
“Nikam ace wai mutane ko darajar privacy basu saniba
saboda Allah kamar wasu
d
abbobi!”Daga haka suma suka nufo k’ofar da niyyar fita da kuma bi ta kan Jiddan idan ba ta ba su hanya da wuri ba.
Duk ba su lura da Najeeb a bakin k’ofar ba sai da Ya’isha ta zo zata wuce tukunna suka yi ido biyu da shi.
Kallon ta yayi sosai kafin ya
maida dubansa ga Jidda yace
“Anata nemanki!ki je sama wajensu Ummi za ki taya su da wani abun”
Jin jina kai kawai ta iya yi dan ita kam ta gama shiga shock bayan b’acin rai da kuma mamaki…su da suke a matsayin surukan juna amma kalli yadda suke musu
msgana kmr masu shirin shiga filin dambe!.A tunaninta wayayyun mutane masu kud’i da illimi kamar su ba za su yi wannan tumasancin ba.
Shi kansa Sir Najeeb tunanin da yake yi kenan….ya san Ya’isha ba ta da kunya kuma tana da tsiwa amman sam bai yi expec
ting haka daga garesu gaba d’aya ba.Ya ma rasa me zai ce shine matsalarsu ko yana damunsu!shin kishi ne!ko haushi!ko bak’in ciki!ko rashin sanin ya kamata?.
Shiyasa Jidda tana wucewa
shima ya juya zai wuce ko second look bai yi tunanin sake yi musu ba.
Ahankali ya ji Ya’isha tace “Ya
Najeeb!”
Kamar ba zai juyo ba sai
kuma ya juya yace”Naam
Ya’isha!”
Wuceshi Yasmeen ta zo ta yi ta bar musu space shi da Ya’ishan.
Ganin ta yi shiru tak’i yin magana kuma sai wani irin kallo take yi masa ne ya sa
yace “Inada abubuwan yi fa Ya’isha akwai matsala ne??”
Ya yi mata tambayar yana d’an juyawa yana kallon masu aiki dake a cikin parlourn dan har sun kusan kammalawa.
Ba k’aramin b’aci kuwa ranta ya sake yi ba shiyasa itama ta fito bakin k’ofar ta tsaya
daff da shi sannan tace”A ganinka bai kamata mu yi magana anan ba ko?shiyasa kake k’ok’arin zille wa gudun kar ta ganmu tare??”
Dama ya san sai tayi maganar Siyama shi kuwa har ga Allah bai shiryawa maganar yanzu ba dan ya san tsaf zai iya breaking up
da ita right away shi kuma ba ya so yayi breaking up da ita ba a right manner ba….
Sai da ta sake cewa”Bakace komaiba”tukunna ya juyo yace
“Tou me kike so in ce miki??
Ya’isha Meyene problem d’in ku da mutanen nan?daga ke har su Yasmeen har ga Allah
I’m very disappointed in you guys!Kuma na tabbatar kin san me zai faru idan Yash yaji haukar da kukeyi ko?
Dama ashe kishi tsakanin matar wa da siblings d’inshi
Is real?dan ni dai ban tab’a gani ba sai a kanku to be honest
sannan kishin naku ma is way
too local,haba mana!.
Ki gayawa su Yasmeen
kar su sake wani shirme kema kuma ki nutsu
Amarya za a kawo idan ba haka ba wallahi zan fad’a ma Yash.”
Yana gama fad’in haka ya fara k’ok’arin juyawa sakamokon hango Munirat da Siyama dayayi sun tunkaros
u da kaskon turaren wuta…..ya san
abunda yakeyi is so selfish amman Yaisha ita ta janyo komai in da ace tana bashi time d’inta da maybe a lokacin da ya ga Siyama months ago da ba lalle ya saka hope d’in samunta ba,zai iya lallashin zuciyarshi ya hak’ura
da ita
duk da ya san zai sha wahala.
Amman Ya’isha ita ta banzatar da shi shi kuma ya kamu ya fad’a yayi dakon soyayyar Siyama for almost 4 months,sannan yanzu da ya sake ganinta a yadda yakeji wallahi ko goya sa Ya’isha takeyi ba za ta samu gurbi a zuc
iyar sa ba dan Siyama ta mamaye ko Ina shiyasa shi kansa ya ke d’an jin tausayin Ya’ishan dan har ga
Allah ba ta da matsayin da zata hana sa zama selfish bata da matsayin da zata sa yak’i rabuwa da ita kuma bata da matsayin da zata hanasa bin zab’in zuci
yarsa……
Ba k’aramin mamaki ya shiga ba da yaji Ya’ishan ta ruk’o hannunshi dan haka ya juyo a mugun firgice
Ita kanta su Siyaman ta hango
shiyasa ta yin hakan,hannun
ya kalla kafin ya d’ago ranshi a mugun b’ace yana shirin fara magana yaga fuska
rta shab’e shab’e da hawaye.
Da mamaki yace”Ke!lafiyarki kuwa?”
Cikin kuka tace”na san saboda sister d’inta kake ta wahalar da ni haba Ya Najeeb
taya kake tunanin ba zan ji
haushinsu in kuma tsanesu gaba d’aya ba?kalli fa yadda ka ganni a situation
d’in da ka ganni amman sam baka damu ba instead treatning d’ina ma kake yi akan zaka gaya wa Yash mun tab’a dangin matar sa.Shekara nawa muna tare
tashi d’aya ka juyamin baya ya kake so inyi?shin ba ka tsoron hakki?idan ka yaudareni fa Allah ba zai barka
ba.
A tunanina a matsayin k’anwa nake a wajen ka bayan masoyiya,ta yaya za ka min haka tashi d’aya sannan kuma kace ni da y’an uwana ba zamu ji haushin sa ba?”
Tausayinta ne ya d’an kama shi ganin yadda take kuka wiwi…tabbas ya kamata ya rabu da Ya’is
ha as soon a possible ya kamata ya yi setting nata free tun kafin a samu more damage….”
Yana cikin wannan tunanin ya ji kansa ya wani irin sarawa sakamokon rungumar da ta yi masa.
Cikin kuka tace
“Allah ban shirya barwa kowa kai ba”.
Bai tsaya wata
wata ba ya zarota da dukkan k’arfinsa cikin fushi yace”ba ki da hankali ne?wanne irin shirme ne wannan?..”
Ya fad’i hakan yana juyawa ya ga ko Siyama ta gansu,bai ga kowa ba amman tabbas ya san ta gansu….ji ya yi kamar ya rufe Ya’isha da duka!ko hannunsh
i bata tab’a rik’ewa ba sai yau kuma yau d’in ma har da runguma tsabar iskanci.
Ganin in ya ci gaba da tsayuwa a gaban ta zai iya mammaketa ne ya sa kawai ya juya da sauri,ko a parlourn bai yarda ya ci gaba da zama ba tashi d’aya ya fice ya na fita ya nu
fi motar sa ya shige ya zauna ya kunna ac.Bashi da tantama Siyama ta gansu tabbas shiyasa ta yi sauri ta gudu,shikenan ya san tun kafin
aje ko Ina har ta fara yi masa kallon d’an iska kuma mayaudari.
Suna shiga kitchen Siyama ta cika hannun Munirat
tukunna ta dafe k’irjinta ta na mamakin
zafin kishin Najeeb da taji,yau ne fa kawai suka d’an samu momment amman kalli yadda zuciyarta take tafarfasa na ganin shi da wata da tayi.
Dariya Munirat ta yi kafin tace”Tab!amman ba ki riga kin shiga universit
y ba ko?kina ina couple suke kissing juna in public!dan kinga d’an wannan shine duk kika koma haka sai kace wadda taga wani abu serious….”
Cikin katseta
Siyama tace”couple?Mijinta ne?”
“Nop,amman saurayinta ne
kuma shi zata aura na ji Mommyn
su tana fada rannan
kmr sun kai almost 7 years tare
tun tana secondary school…but gaskiya ni kaina ta bani mamaki saboda ban tab’a ganin wani d’an gidan da bad behavior haka ba
Apart from Kausar da Yassir,ban yi tunanin suna irin haka ba suma shi kan
sa Najeeb d’in he looks decent..anyways sha su ta shafa!.
Kina gayamin Manubiya a buk take?maybe ma mun taba haduwa fa”
Sai yanzu Munirat ta lura da yadda sam hankalin Siyama baya a kanta.
Dan haka ta d’an yi snapping fingers d’inta tace”Hey!”
F
irgigit Siyama tayi
dakyar ta d’an daidaita b’acin ranta tukunna ta kalleta tace”Yassir! wanda suka kawo mu shi da Ya Najeeb ko?,dama daga ganinshi wanann d’an iska ne”sai kuma ta yi sauri tace”Au sorry brother dinki ne ko?”
Shiruuu Munirat tayi daga
jin zancen Yassir…zuwa yanzu ta gama tsara yadda za ta yi su shirya dan tana mugun son Yassir gaskiya…..
“Munirat kin yi shiru”
Muryar Siyama ta katse mata tunani.
Numfashi Munirat ta fesar kafin tace”A’a ba brother d’ina bane,mu bar maganarsa kawa
i”
“Ok”Siyama ta ce kafin ta d’aura da cewa dama na ga kamar he is intrested in my sister shiyasa na ke so in d’an yi confirming halinsa kafin komai.
Dasauri Munirat tace”Really?
wanann farar ko?”
“Yeah” kawai Siyama tace
daga haka ta chanja top
ic d’in
ba tare da ta tsaya ta lura da fuska da kuma reaction din Muniran ba..
A parlour Su Baba larai suka zauna Yassira kuma ta wuce sama wajen Yahanasu,ba abunda ya basu mamaki ya kuma basu takaici kamar yadda su Aisha suka rarrabu
it’s like su
n fahimci wani abun kuma sun lura Yahanasu ce ta nace ayi hakan…….
Tana zaune akan couch d’in
private balcony na d’akin tana tunani ta ji an bud’e k’ofa dan haka ta mik’e da sauri
ta shigo cikin dakin.
Ido biyu sukayi da Yassira dan haka tace “As
he kece”
“Are u expecting someone else
besides me?kema kika shigo ballantana ni?,a tunani na da lissafina na fiki iko da d’akin nan da gidan nan ma gaba daya” Yassira ta fad’i hakan tana mai k’arewa d’akin kallo.
Numfashi Yahanasu ta fesar kafin t
a matsa kusa da ita ta tsaya tukunna tace”Finally kin fito da real face d’inki kenan ko?
hakan yafi ai dan kin san ni I hate pretends,and FYI da ni da ke duk iko d’aya muke dashi da d’akin nan
u are just living in delusion!”
Shiruuu Yassira ta d’an y
i kafin
ta matsa kusa da ita itama
tace’me nene problem d’in ki?
me kikeso kiyi proving?