Showing 27001 words to 30000 words out of 259716 words
zaune ba dan motar da d’an duhu,sai da ta d’an sunkuya ta shiga ta zauna ta
mayar da k’ofar ta rufe tukunna ta d’an zabura ta d’ago ta kalleshi sa
kamokon kamshinsa wanda ta ji ya k’aru sosai a cikin hancinta da kuma alamun mutum da ta ji a zaune a gefen ta.
Suna had’a ido ya yi mata gwalo yana mai jin kamshin da take yi yana shirin zautar da shi da kyar k’asa k’asa ta yadda ya tabbatar ita kad’ai c
e za ta ji yace’’an guje min kuma anzo an taddani,a clear reminder to you wifey’destiny will forever bring us together,har abada muna manne da juna InshaaAllah’.’’
Shiruu Manubiya ta yi dan ita ta ma kasa magana,sam tunaninta bai sa ta tuna da hannunsh
i ba sai da suka yi ido biyu da shi ta kalli hannun tukunna ta tuna ba fa zai iya tuk’in ba.
Ahankali ta d’ago ta d’an kalleshi kafin tace’’Ina wuni’’
Da kyar ya iya cewa lafiya idanunsa a kanta yana mamakin mai ya same ta haka da ta k’ara wannan azabb
’en kyan cikin k’ank’ani lokaci a gefe guda kuma na zuciyarsa yana jin takaicin kasancewar drivern da ke gaba da ke a
cikin motar dan ya san shima tabbas ya shak’i wannan sumamman k’amshin da take ta zubawa,addu’ar sa d’aya kar yazo gaisheta yace zai juyo
ya k’are mata kallo dan arayuwarsa bayason abunda zai sa ake kalle masa ita balle yanzu da shi kansa yake jin numfashin sa yana shirin d’aukewa…..yana cikin wannan tunanin yaji ta cewa drivern’’ina wuni’’
Cikin girmamawa da yin k’asa da kai drivern ya gai
sheta ba tare da ya juyo ba daganan ya kunna motar bayan Yash ya fad’amasa Ina suka nufa,suka d’au hanya…..
Dukda drivern ne ya kamata ya gaidasu amman sai Yash ya ji dad’in yadda Manu da Muhsin suka girmama dattijon mutumin dan ko Muhsin ma bayan sun g
aisa sai da ya gaida drivern shima,hakan ya nuna sun san girman d’an Adam da farin gemu unlike su Yasmeen.
A k’ofar shagon wata shaharariysr mai d’inki suka yi parking kafin drivern ya kashe motar ya fita haka ma Muhsin,bai yi gigin bud’e musu ba dan ba
i san ko za su tattauna ba kafin su fito dan haka ya koma gefe ya ja ya tsaya haka shima Muhsin.
A hankali cikin wata murya kamar ta wanda ba ya son yin magana yace’’mu je ko?’’
Jin jina kai ta yi tukunna ta sa hannu da niyyar bud’ewa amma sai ta gag
ara,ta juyo da niyyar yin magana ta ga ya bud’e side d’insa ya fita ya zagayaya.Da kansa ya bud’e mata dan ko da drivern ya matso ma d’aga masa hannu kawai ya yi ya tsaidashi.
Ahankali duk tanajin kunya da nauyi sun lullub’eta haka ta sa k’afa ta fito,sai
da ta gama fitowa tukunna ya rufe marfin motar ya ja mata mayafinta daya d’an zame yana shirin sauk’a da ga kanta tukunna suka nufi k’atoton shagon suka bar driver cikin tsananin mamakin yau Oga ya zama driver!amma har ga Allah ya ji dad’i kuma sun matuk’
ar burgesa,hatta Muhsin ma da yake Yaro sai da suka burgesa,bai bisu har ciki ba ya tsaya a wajen driver suka shiga hirar su.
Suna shiga wajen taga ashe har ya bayar da kaya wajen kala ashirin majorments d’inta kawai ake buk’ata…dan haka suka shiga wan
i d’aki matar ta aunata aunin kwakwaf dan ba abunda ba ta gwada ba saboda wai za’ayi d’inkin nikkah wanda zai yi fitting ragowar ma duk ana so su yi fittng tunda a lefe ya ce mata za’a saka so kayan dole su fito rasss!!!hakanan ta yi ta janta da hira dan m
atar professional tailor ce
mai kirki kanta a waye shiyasa kamar za ta goya ta.
Manu ta ji dad’in yadda Yash ya yi respecting decision d’inta dan tunda ta ji matar tace ‘’iyaka d’inkin nikkah,ragowar kuma na lefe” to ta san ya yarda shi da y’an gidans
u babu wani event d’in da za su yi kenan.
Ba bu maganar deposite dan Yash complete ya juyewa matar kud’in d’inkunan kaff a account,har suka fito suka shiga mota suka fara tafiya kan Manubiya bai daina juyawa ba…sai da aka tura kud’in tukunna ta ji amma
wallahi ba dan haka ba to da ba za ta yarda a yi wannan uban b’arnar kud’in a iyaka d’inkuna ba….
Ba gida suka koma ba wajen jewelries da shoe and bag d’in da za ta yi amfani dashi sukaje
suka sissiya,daganan
suka biya mudassir,ya riga ya sayi koma
i amma akwai d’akin dama da ya ware akan itace za ta zab’a da kanta sai kuma deco da kayan kitchen da yake da bukatar ta k’ara choices d’inta akan waenda ya sissiya,shiyasa ya kaita ya ce ta tayashi zab’e dan ya kasa..
Siyayya sosai kuwa suka yi dan har s
ai da ta fara tunanin maybe ko harda iyayenshi zai chanjawa kayan kyale kyale da kitchen saboda bikin dan uban kayan da suka d’iba wasu aka yi order abun ba ‘a cewa komai.
Tabbas ta yi mamaki matuk’a
amman da ta tuna yawan estates d’in shi da business
d’in da yake yi sai
taga kud’in da suka bata tsoro waenda suka kashe a iyaka yau kad’ai ba komai bane a wajensa.Ta san Yash yana sonta kuma ta san so gaskiya ne amma yadda taga yake rawar k’afa da waensu abubuwan duk akanta wasu lokutan har tsoro da mama
ki takeyi…duk wani kud’i! dukiya!class! ajjiyewa yakeyi a gefe
ya sauk’ar da kanshi k’asa sannan ya kawar ya goge the fact that ‘she and him sam class d’insu ba d’aya bane’.! Yadda yake treating d’in ta a gaban kowa da koina kamar wata queen tabbas hakan
yana bata alajabi,gashi dai ya san itan ma tana sonshi
ballantana tace ko campaign yake yi….Tabbas ta yarda ta amince she’s fortunate infact she’s morethan fortunate…….
Sai chan dare tukunna suka d’auki hanyar gida bayan ya loda na lodawa ya kira w
ani driver d’insa ya yi assigning an tafi kai kayan da za a kai gidan amarya…ta gaji lik’is dan haka ta na gishingid’ewa bacci ya kwasheta.
Ahankali ya d’an tab’o Muhsin wanda suke ta hira da drivern dan har sun saba sosai kamar wasu sa’anni,sai da ya juy
o tukunna Yash ya d’aura yatsarshi akan bakin sa alamun su yi shiru kar su tasheta,jinjina kai Muhsin yayi ya juya yana murmushi bai gama sanin meye so ba amman yana jin dad’in yadda ya Yash ya damu da Addar su,shima drivern ya gani kuma ya fahimci mai Yas
h yake nufi shiyasa ya yi shiruu ya bada himma a tuk’in da yake yi.
A hankali kamar mai shirin d’aukar cracked egg haka Yash ya d’auki wata suite d’insa dake a cikin jakar kujerar driver ta baya ya d’an matsa kusa da ita kad’an ya lullub’a mata dan ya l
ura ba ta son sanyin.
Manu bata da nauyin bacci
shiyasa yana rufa mata ta farka amma ba ta bud’e idanunta ba…ta ji dad’i a ranta,duba da yadda yanzun suka gama fad’a kuma yayi fushi da ita amma kalli yadda yake kula da ita,ba ta son yin fad’a da shi a
mma ta lura idan ba hakan ta yi masa ba to ba zai hak’ura ba ba zai bar maganar ba!. Saboda Allah ta ya dan su Baba sun aura masa ita sai kuma kawai aga sun kwashe kaya su koma gidan da ya ce ya basu,a ganinta hakan ba dacewa bane ba,ta san sun zama family
amman kuma idan suka yi haka ai sun sake da yawa,idan ma zai basu gida gaskiya ba yanzu ba besides ta san ma Baba ba zai tab’a yarda ba…
Tana wannan tunanin ta ji an yi
parking an kashe motar,ta na ji Muhsin ya yi musu sai da safe da godiya ya jidi l
aidojin gabansh ya fita dan haka ta yi saurin bud’e idanunta dan
ta lura ba shi da niyyar tashinta,dai dai nan drivern ma ya fita kenan..da sauri tace’’mun gode sai da safe daga haka ta fara kokawa da shegiyar handle d’in da ta rasa dalilinta na k’in bud’u
wa a koda yaushe idan ta ja.
Murmushi ya yi kafin yace’’kar mu rabu muna fad’a mana,ai tunda kin nuna bakyaso ba zan sake yin maganar ba,amma ki yi tunani akai pls’’
Jin jina kai kawai tayi ta ci gaba da k’ok’arin bud’ewa
Murmushi ya yi yace’’ba f
a za a bud’e k’ofar nan ba sai kin yi min murmushi.’’
Jin tayi shiru yasanya cikin wata kalar kasalalliyar murya ya ce’’kin san Allah zan yi miki cakulkuli’’
Sai da ta zabura sosai kamar ya riga ya yi mata cakulkulin tukunna ta juyo kamar za ta fashe d
a kuka tace’’dan Allah ka yi hak’uri,dare fa ya yi ka bud’e min’’
Ganin yadda ta fara fita a haiyyacintane ya sanya ya fahimci kad’aicewar nasu ne ba ta so,dan haka tashi d’aya ya sa hannu ta gaba ya bud’e mata sannsn ya bud’e tashi k’ofar ya fice da n
iyyar za gaya wa domin ya bud’e mata amman tuni ta yi wuff ta fice dai dai shikuma ya zagayo,tashi d’aya ya ji ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kamar wadda ta yi
y’ar tsere,murmushi kawai ya yi yana mamakin yadda daga sun zauna a mota iya su biyu du
k ta bi ta gigice a ranshi yace’’Yarinya za ki yi bayani ne’’.
Duk taurin kanta kuwa sai da ta yi masa murmushin nan tukunna ya kyaleta.
Da shi da ita da driver suka yi jidon ragowar siyayyar da ya yi mata har soro ya ajjiye mata
yana sake mamakin
gidan tukunna ya bata wata jaka mai d’an karen kyau yace”invitation ne a ciki ta bawa su Baba zai turo mata na waya ma sai ta tuttura shi kam ba wanda bai riga ya turama a cikin friends d’insa ba”
Karb’a ta yi tana mamakin zumud’i irin na Yash kafin yayi
mata sallama
suka rabu yana jin kamar ya d’auke ta su koma.
Tabbas inda ace irin wata d’aya d’in nan aka saka aurensa da Manubiya tou da sai ya bai san ya zai yi ba kafin ta zo….wata kalar zazzafar k’aunace ta ke d’awainiya da shi the more yana getting
to know her the more k’aunar ta take sake dagargaza mishi lisaafi! tunani! da zuciya…..
Sai da ta zo shiga kuma tukunna ta fara fara kame kame,ba k’aramin dad’i ta ji ba da bata ga Baba a d’akin ba,amma dukda haka sai da ta d’anji nauyi dan kasa had’a
Ido ta yi da inna illa kawai sai
taje ta durk’usa ta gaida ita daganan ta cewa Jidda ta zo ta tayata d’aukar kaya dan Muhsin yana shigowa ya fad’a toilet.
Ahanya take tambayar Jidda ko su Baba sun yi fad’an daren da ta yi amman sai ta ji jiddan tace
mata a’a besides ai ba ta yi dare sosai ba.
Sai a sannan ta sake,su ka kwashi kayan suka kai ciki.
Sai da Jidda ta je ta kira Siyama tukunna hankalinta ya kwanta,tare suka ware ledojin da komai,ita Manubiya sai da suka ware ma tukunna ta ga gift d’in M
uhsin(agogo mai tsananin kyau na maza)da wayar da ya saka mata ba tare da saninta ba
iPhone mai kyau k’irar wadda ake yayi,shiyasa a take ta kirasa domin ta yi masa godiya har ga Allah gaba d’aya Yash ya sa ta fara jin wani iri dan gaskiya ita dai hidima
r ta yi yawa..tana fara masa godiya kuwa ya chanza topic d’in dan dama yace mata ta daina yi masa godiya ba ya so!ba k’aramin dariya ya bata ba da ta ji yace’’ta je aiki,ta na da report’’
da farko ta d’auka da wasa yake yi sai da taga ya dage tukunna ta t
abbatar da gaske yake yi.
Aikuwa sai da ta yi da gaske tace’’ga skul da za su koma soon dan ba’a ba su wani hutu mai tsayi ba ga kuma hidimar biki dan Allah ya yi hak’uri ya bari ta tura masa kawai’’
tukunna da kyar ta samu ta shawo kansa ta lallab’asa y
a d’aga mata k’afa amman da cewa ya yi sai ta je.
Daga nan ta ji ya yi shiruu kamar mai tunanin wani abun dan haka ta shiga tambayar sa menene,sai da k’irjin ta ya buga da ta ji yace‘’Abbakar ya tab’a cewa yana son ki ne??’’
Sai da ya sake cewa’’umm???
’’
Tukunna da iyaka gaskiyarta tace’’A’a”
Numfashi ya fesar kafin yace’’can I ask you a favor???”
Ahankali ta samu da kyar tace’’sure!anything’’saboda yadda ta ji tashi d’aya muryarshi ta chanja sannan ranshi ya b’aci.
Cikin katse mata tunani ta
ji
yace’’ko gaisawa ba na so ki sake yi da shi”
Sai da ya sake cewa”am I asking for too much?”tukunna ahankali tace”A’a”sai kuma tace”ba ma ya yi min magana fa,ya daina kulani”cikin tarar numfashinta yace”saboda kishi ne ai yasa ya daina yi miki magan
a saboda ya ji an fara maganar aurenmu yanzu kuma ya ga za’a koma skul shine ya je ya karb’i transfer,yanzunnan Najeeb yake gayamin ya samu transfer,bakiga kalar wahala da kud’in da ya kashe ba amman haka ya bi a gaggauce ya yi transfer”
Shiruuu Manubiy
a ta yi tana jin wani takaicin Abbakar yana taso mata a tunaninta da kuma ganinta sam alk’awari bai ce haka ba wato
ma gudun ta yake,a ranta tace”idan ma wani abun na yi mishi ai kamata ya yi ya neme ni da zancen mu sasanta bawai ya yi irin wannan abu hak
a ba’’ dan ita kwata kwata ba ta yarda da maganar Yash da ya ce “saboda kishi ne ya sanya shi ya yi transfer ba….”
Cikin son kawar da zancen Abbakar d’in Manubiya ta sako wata hirar dan ya b’ata mata rai ba kad’an ba,da
kyar kuwa ta samu mood d’in Yash
ya chanja har yake bata labarin “ai Najeeb ma ya samu wani zazzafan appointment zai bar skul d’in”,ta kuwa yi murna sosai dan ko ba komai sir Najeeb ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarta…..
Sai da Manu ta tabbatar Yash ya huce sosai tukunna suka yiwa jun
a sallama,kamar za su cinye juna don so haka nan su ka yi sallama ko wannen su cikin tsananin so da shauk’in d’an uwansa.
Tana gamawa su Siyama suka tisa ta a gaba da tsokana abun mamaki har da Muhsin,ita sai a lokacin ma ta fara data sanin yin wayar a
gaban su.
Sai da Baba ya zo ta nuna mishi komai ya sanya albarka bayan ya gama fad’an hidimar ta yi yawa tukunna suka b’are wayar aka jonata a chargi
Dan jidda tace”tayi maza ta kwashe important abubuwa ta cire layinta a tshohuwar wayar ta bata dan
ta ma riga ta zama tata……
Har k’ofar side d’in su Siyama suka rakata dan lokacin da ta zo tafiya dare yayi sosai,tukunna suka koma nasu d’akin..
Yashjub yana gama waya da Manu dai dai ya shiga bedroom d’inshi kenan kiran Daddy ya shigo wayarsa,yana
d’auka ya ji muryar Daddy yana cewa”ka zo parlour na,Hajiya Maama na son magana da kai”
Yadda Yashjub ya ji murya Daddy dama sai da gabansa ya yanke ya fad’i shiyasa ko wanka ya gagara yi tashi d’aya ya juya ya nufi side d’in Daddyn yana jin yadda k’ir
jinsa ya ke bugawa akai akai.
A zaune ya same ta ita da Daddy da Ummi da mom da Abhi.
Sai da ya gaishesu one by one suka amsa tukunna ya nemi guri ya zauna.
Yana zama Hajiya Mama ta yi gyaran murya tukunna cikin lallashi tace”Yash! da ni da iyayenka g
asunan mun yanke shawarar za’a d’aga bikinka za’a k’ara wata uku a kai sakamokon matsalar gocewar k’ashi da ka samu kar ka yi gaggawa ka bi komai a hankali a je a samu a duba ka sosai dan a gaskiya ban gama yarda da gyaran da suka yi maka a nan ba,ka yi ha
k’uri ka bari a d’aga bikin,lafiyar ka ta fi komai ka warke garau tukunna sai a yi komai cikin nutsuwa da kwanciyan hankali ka ji d’an albarka”
Hajiya Mama ta k’arashe maganar cikin tsananin lallami.
Tunda ta fara magana idanun Yash suka cicciko da haw
aye.
Kamar wani d’an Yaro haka ya d’aga kai ya kalli Abhi da Daddy Irin ‘ku sa baki mana’ d’innan,ajiyar zuciya Abhi ya sauk’e kafin yace‘’Yash it’s for your own good in banda kai da abunka ina kai ina yin aure a haka saboda Allah fa,tunda har mukazo aka
yi tambaya aka yi komai aka baka yarinyar nan a ganina dan an k’ara wata uku ba komai bane kamar yau ne,ka yi hak’uri ka bi Junior da mom d’inku ku je a duba maka hannun sosai ka warke garau! In yaso sai ayi auren I promise you zan tsaya maka ka auri Manub
iya under any circumstances,Ina nan har 3 months da ni da Hajiya Mama inshaaAllah sai an yi auren an kai maka amaryarka tukunna za mu koma.
Cikin bashi assurance Daddy da Hajiya Mama ma suka mishi alk’awarin duk rintsi inshaaAllah zasu tsaya masa ya auri
Manu haka ma su Ummi.
Zuwa yanzu Yash har wani dishi dishi yake gani tsabar tsaka mai wuyar da ya shiga manya sun sakashi a tsakiya suna so a d’aga for his own good sannan sun yi masa alk’awarin tsaya masa duk rintsi a yi auren,on the
other hand kuma gani
yakeyi kamar idan aka d’aga wani abun ka iya faruwa infact kwata kwata baya k’aunar abunda zai janyo a d’aga auren nan.
Ahankali Hajiya Mama tace’’ka yi hak’uri ka kwantar da hankalinka ka samu lafiya tukunna fiancé d’inka tananan tana jiranka babu ind
a za ta je kana dawowa za’ayi auren ka ji ko?”
Cikin son jin amsar da za ta fito
daga bakinsa Abhi yace”kai muke jira Yash,a matsayinmu na iyayenka ga abunda muka ga