Showing 177001 words to 180000 words out of 259716 words
nuni da ta karb’i k’addararta hannu bibbiyu,Allah ya na sane da ita shi zai sake bata wani.
Da kyar ta samu ta iya bud’e idanuwanta da suka yi mata nauyi,tukunna da taimakon S
iyama da na Hajiya Mama aka samu ta tashi ta zauna still hawaye sun k’i su daina sintiri a kan fuskarta.
Ya jiki suka yi mata ta gaida Inna daga haka ta shiga kallonsu
One by one idanuwanta suna masu begen son ganin fuskar Yashjub ta samu su ta ga halin
da yake ciki su koka tare su rarrashi juna tare,amma sai ta ga babu shi babu mai kama da shi…
Siyama ta tambaya Siyaman tace mata”ita ma yanzu suka shigo,ba ta gansa ba”
Dan haka ta juya ta fara laluben wayarta still hawaye suna sintiri a kan fuskarta s
un k’i tsayawa ko na second d’aya.
Kallonsu Hajiya Mama wadda ta gama cewa Najeeb ya je ya Kira Doctor ta yi,tace”me kike so Manu?”
Ta yi mata tambayar cike da tausayawa don yadda take hawaye jikinta har yana karkarwa dole ta baka tausayi!
A hankali I
nna ta matso ta ruk’o hannunta da niyyar yi rarrashinta aikuwa kamar jira take yi tashi d’aya ta fashe da wani irin kuka ta fad’a jikin Inna ta k’ank’ameta.
Duk dauriyar Hajiya Mama sai da ta yi hawaye….duk kalar kunya da kawaici irin na Manubiya kalli
yadda take kuka a gabansu ita da Inna ai kuwa tab’uwa ta yi tab’uwa,kuma ta sake tabbatarwa ba ita ta zubar da cikin da kanta ba zubar mata aka yi,tabbas Mommy ta zalinci baiwar Allah nan amma ba ta Isa ta ci b’agas ba wallahi……wani irin tausayin baiwar Al
lahn ne ya lullub’eta a haka ma ba ta ji abunda Likita ya ce ba, tashi d’aya ta shiga addu’a Allah ya sa kar maganar sa ta tabbata Allah ya sa Manubiya za ta haihu shiyasa ma ba ta gaya wa ko su Inna ba kuma za ta cewa su Ummi suma su b’oye gudun ma kar ba
ki ya yi yawa a zancen ya tabbata,inshaaAllah Manubiya sai ta haihu,babu abunda ya samu mahaifarta.
Kuka sosai Manubiya take yi kamar ranta zai fita dan zuwa yanzu ta kasa b’oye kawaicin ta,shigowar Najeeb da Likita ne ya tsagaita hak’urin da su Hajiya
Mama suke ta bata suka d’an matsa gefe domin ya yi aikinsa.
A karon farko ya tabbatar musu jininta yayi mugun hawa,sannan she needs more rest dan haka bari ya yi mata allurar bacci.
Cikin kuka tace”ya fara jira Ya Yash ya zo tukunna sai ya yi mata,tana
son ganinsa.”
Kallonsu Likitan ya yi zai yi magana Najeeb yace”ka barta tukunna bari in kira sa.”
With full confidence ya shiga gwada numbobin Yashjub amma duka hud’un da ya ke amfani da su a kashe!
Gashi kowa ya tsura masa ido yana jira…shi abun ma ma
maki ya basa Anya kuwa Yashjub ne ya aikata haka?Manubiya ba lafiya tana asibiti ba ya wajen sannan ya kashe gaba d’aya wayoyinsa!something is wrong,definitely…
A hankali ya d’ago ya kallesu cikin in ina yace”wayoyinsa ba sa tafiya bari in je gidansa in
duba”
Shiruuu Manubiya ta yi hawayen idanunta suka k’afe ta shiga wani irin rikitaccen yanayi,dama ta san Ya Yash sai ya shiga tashin hankali amma ba ta yi tunanin zai yi abandoning d’inta ba ko wanne Hali yake a ciki ta yi tunanin zai taushi zuciyar s
a ya zo gareta!,to ko dai bai san ta yi b’ari ba? Inaa ya sani ta san he’ll be the first person da su Hajiya Mama za su kira.
Tana wannan tunanin Likita ya kamo hannunta ta cikin cannula ya juye mata ruwan allurar bacci wanda tun kafin ya gama zarewa ba
cci ya yi awon gaba da ita.
Ba ta dad’e da yin baccin ba Daddy ya zo dan haka bayan sun gaisa da su Inna suka fita shi da Hajiya Mama.
A garden d’in da ke cikin asibitin suka nemi guri suka zauna.
Cikin fahimtarwa ba tare da b’oye b’oye ba Hajiya Ma
ma tace”Manubiya ta yi b’ari,kuma Likita ya tabbatar mana magani ta yi ta sha watak’ila ma ba lallai ta haihu ba.na san ka shiga ka ga halin da Yarinyar nan take ciki kuma ka san ko da wasa ba ita ta yi yunk’urin zubar da cikin nan ba,dan haka inaso ka gay
a mini me lissafinka ya baka a halin da ake ciki yanzu?.”
Shiruu ya yi ya fi minti ashirin duk su biyun suka yi shiru babu mai cewa komai kafin ya d’ago ya kalli Hajiya Mama yace”ina riba ga su Yasira idan sun zubar mata da ciki?”
Lumshe idanuwanta
ta yi ta bud’e tace”mashaaAllah Imam,na gode Allah da soyayyar y’ay’anka ta daina rufe maka idanu daga ganin gaskiya.
Ina so ka san cewa su Yasira ba su da riba dan sun zubar da cikin Manu amma Khadijah fa?”
A mugun zuciye ya mik’e yana wani irin huci t
ashi d’aya idanuwansa suka kad’a suka yi jazir cikin fushi yace”now everything makes sense”
Ya fad’i hakan yana mai mik’ewa had’i da shirin barin wajen….da sauri Hajiya Mama ta mik’e itama ta ruk’o sa,cikin hikima tace”Imam idan ba ka iya kama b’arawo ba
fa shi sai ya kama ka.Yanzu ka gaya mini hujja d’aya da zaka nuna ka kamasu da laifi?babu!
Kuma idan ka yi haka ka sake dulmiyar da y’ay’anka mata ka saka a halaka mazan kuma har abada ba za su tab’a yafe maka ba,ka ga ta raba ka da su kenan har abada
.”
Cikin rashin fahimta yace”Hajiya Mama ni ne Uba ni zan fad’a a ji da ni da ke duk mun san ita ce do we really need to prove anything to them?”
Girgiza kai ta yi kafin tace”dad’ina da kai kenan idan zuciyarka ta motsa Imam ba ka ji ba ka gani!
Walla
hi d’azu da na fahimci abunda Khadija ta saka yaran nan suka yi sai da na yi hawaye,Imam su Yasira y’ay’anka ne jininka ne kai ya kamata ka tashi ka tsaya ka gyara tarbiyyar su da lissafinsu da aka lalata,yanzu idan ka kori uwarsu kana tunanin za su rabu d
a ita ne?
Za ka sha mamaki idan suka kwashe kayansu suka yi maka yaji suka koma gabanta gaba d’aya tunda bakinsu d’aya kalli fa abunda ta tura su suka aikata meye kake tunanin ba za su iya yi mata ba?kaga da ga nan sai abunda Hali ya yi hakanan za ta lala
ta maka zuri’a Allah kad’ai ya san abunda Hali zai yi.Su kuma mazan ba za su tab’a yafe maka ba cewa za su yi ka kori uwarsu saboda kawai ba ka sonta.
Abunda ya kamata mu yi yanzu shine mu nutsu mu karance su sai mu san abun yi saboda wallahi Imam akwai a
bubuwa da dama da bamu sani a kan Khadijah ba kuma idan muka ce za mu yanke hukunci cikin fushi tou kuwa za mu kwafsa dan indai har Khadija za ta iya kashe d’an cikin Yash to akwai wasu abubuwa da yawa game da ita wanda mu ba mu sani ba.
Sannan yanzu ida
n aka yi hayaniya ta tafi ba za mu tab’a sani ba sannan yaranka bamu samu mun gyara abunda ta b’ata ba wanda na tabbata Wallahi ko gidan miji ba su Isa su iya zama da wannan mugun halin ba…daga karshe su yi muguwar rayuwa!Imam yaran nan amana ne Ubangiji y
a baka kuma zai tambayeka ranar gobe k’iyama fa!…ka nutsu ka yi abunda nace sai ka ga an dace”
A hankali ya koma ya zauna ya dafe kansa da hannu bibbiyu,kafin ya d’ago ya kalli Hajiya Mama yace”Mamaa ba zan iya ci gaba da zama a inuwa d’aya da matar na
n ba,ta yi mini abubuwa da dama ta cuce ni da yawa,Hatta lamarin Khadija ba ni da tantama itace wallahi….”
Tiryan tiryan ya zaiyyano mata yadda mallan lawal ya kirasa da yadda ya mutu kafin ya samu ganinsa,sannan ya ce”ya yi hacking wayarta but yana ga k
amar ta gane dan ta ma chanja layi ta kashe wanchan,kenan definitely ba ta da gaskiya.”
Waje Hajiya Mama ta nema itama ta zauna ta kamo hannun Imam wanda zuwa yanzu yake kuka kamar k’aramin Yaro,cikin tsananin rashin jin dad’i tace”ka yi hak’uri Imam,da
ni da mahaifinka mu muka tilasta maka aurenta,ka yi hak’uri ka yafe mana mun had’aka da…..”
Da sauri yace”ba laifinku bane Mama,na san ba ku yi tunanin za ta zama haka ba ai,saboda da ba hakan take ba,na san tana da masifar kishi amma sam ban yi tunani
n zata zamo haka ba.”
Ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauk’e kafin tace”kaga ire iren abunda na ke gaya maka ko?kaga lamarin Khadija ma har da sa hannunta sannan recent mutuwar lawal ma muna zargin itace..Ni tunda na ga abunda ta aikata a Yash na san ta yi
abubuwa da dama waenda bamu sani ba shiysa ka ji na ce maka mu bi komai a sannu mu bincike ta kafin mu san abunyi idan ba haka ba ba za mu ci ribar al’amarin ba…..”
Sun jima sosai a wajen da kyar Hajiya Mama ta yi convincing Daddy ya hak’ura suka tsaya
r akan za su saka ido a kan Mommy kuma su san yadda suka yi suka nunawa su Yasira abunda suke yi is wrong su dawo da su hanya….
Ba dan Hajiya Mama ce ta rok’esa ba wallahi da ba zai k’ara kwana d’aya da Mommy a cikin gidansa ba kuma sai ya wulak’antata ya
k’ask’antar da ita dukda ya san ba shi da tsayayyiyar hujja da zai nuna ya ce ita ta yiwa Khadija sharri sannan ita ta yi sanadiyyar zubewar cikin Manu amma ya san itace kuma shi kawai he can’t tolerate her anymore a cikin gidansa ya tsaneta! sai dai kuma
abunda Hajiya Mama ta fad’a gaskiya ne shiyasa da kyar ya aminta ya kuma zab’i su biyo mata ta yadda ta bi da su ta hakan ne za su yi nasara a kanta…idan ya koreta yanzu bai rabata da su Yasira ba ai aikin banza kenan kuma ya barta da gatan ta.Shi kuma so
yake yi ta wulak’anta ta shiga masifar da sai ta zab’i mutuwa akan rayuwa sai ya rabata da duk wani kwanciyar hankali da jin dad’i kamar yadda ta yi masa.
A take a lokacin ya warware ragowar igiyar aurensa d’aya da ta yi saura a kanta,dama kwanaki tun
farko da ta hana auren Yassir da Kausar ta taso masa da maganar Khadija ya sake ta ba tare da ya fad’a mata ba gudun ma kar ta tada masa hankali, ya bari a kan sai ta fita daga idda tukunna zai sallameta,tausayinta ya ji ta kuma ci darajar y’ay’anta shiya
sa kawai ya mayar da ita a wannan lokacin yanzu kuwa ya riga ya rufe ya gama babu sauran aure a tsakanin su shi da ita kuma sai ya zo korarta tukunna zai sanar mata ya dad’e ma da sakin ta.!…
Awa biyu su Inna suka yi suka tafi ita da Muhsin suka bar S
iyama,suna tafiya Yahanasu ta zo,itama tsoro da tsananin tashin hankali sun rufar mata dan ita kam tana tsaka mai wuya ne a wannan al’amarin saboda itama Ummi tana gama gaya mata lissafinta da zarginta akan Mommy ya dira.
Ita ta zauna a wajen Manu ita d
a Hajiya Mama da Siyama,dan ita Hajiya Mama ma tace”a asibitin za ta kwana da Manubiya”
A chan gida kuwa zuwan Kausar biyu side d’in Yash amma a rufe,gashi duk wayoyinsa a kashe,dan haka ta gayawa Yassir shi kuma yace”kar ta damu…gasunan zuwa idan s
uka zo dole zai bud’e daga nan sai su san abun yi.
After 3 hours
Su Mommy ne suka fara dawowa sai
Ummi da ga baya Daddy…babu kalar bugun da ba a yiwa Yashjub ba amma ya k’i bud’ewa.Najeeb ma ya zo shi da Yahanasu dan zuwa yanzu Manubiya ta farka k
amar yadda ta yi bacci da sunansa a bakinta tana farkawa da sunan sa ta fara.
Daddy ne ya je ya nemo spare key da kyar ya samo ya zo ya bud’e k’ofar suka shiga amma wani abun takaicin iyaka waiting parlour da corridor kawai suka tarar dan ya rufe k’ofar s
higa da ma duk wasu k’ofofi.
Zuwa yanzu sun fara tsorata shiyasa Daddy ya ware murya ya shiga kwala masa kira….
Tun a bugun farko Yash ya ji su duk kuma abunda suke yi yana jinsu kuma ya saka a ransa ba zai kula kowa ba he needs some time alone….
Sun
fi minti ashirin a wajen Daddy da Najeeb har ma da Yassir da Junior waenda suka zagaya ta baya saitin d’akin sa suna ta faman kwala masa kira!
Jin muryar Daddy har ta dashe yana kiransa yana haki da nishi su Najeeb kuma suna cewa bari kawai a nemo masu
b’alle k’ofa ne ya sa kawai ya mik’e ba don ya so ya nufi k’asan.
Ta cikin glass door d’in suka hangosa ya taho dan haka hankalinsu ya d’an kwanta,yana zuwa ya d’auki key d’in a jikin k’atoton frame d’in da ya mak’ala ya saka ya murza ya bud’e musu ya
koma cikin parlourn ya nemi guri ya zauna,dan bibbiyu yake gani wani Irin mahaukacin jiri yake yi.
Jiki a salub’e hakanan suka shigo suka nemi guri suka zazzauna.
Kasa magana duk suka yi kowa ya yi shiru suna mamakin yadda ya rame tashi d’aya fuskarsa
ta yi jazir ya yi wujuga wujuga.
Yahanasu ce tace”Yash bawa fa baya wuce k’addararsa,duk abunda kaga bai zama naka ba it wasn’t yours to begin with!Allahn da ya baka ya karba shi zai mayar maka da mafi alkhairi,don’t torture yourself ka rungumi k’addara m
ana!you have to stay strong Yash ita ma Manubiya tana da buk’atarka a gareka za ta samu support da kwarin guiwa if you are this weak ta ina zaka fara bata support ka kwantar mata da hankali??”
Ga mamakinsu kawai sai suka ga hawaye ya shiga sintiri a kan
fuskarsa babu k’akk’autawa abunda dayawansu ba su tab’a gani ba dan haka suka shiga al’ajabi Mommy kuwa kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha ita da Baba larai,cikin jan hanci da share fuskarsa da tafin hannunsa ya juya ya kalli Daddy yace”Daddy I want to be
alone!dan Allah.”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e shi kad’ai ya san me yake ji ji yake yi kamar ya yi super ya damk’i wuyan Mommy har sai ya ga ta daina numfashi.Cikin jinjina kai yace”okay Yash,but kar ka sake kulle k’ofofin ka.”ya d’an yi tapping kafad’ar
sa tukunna ya mik’e yace”kowa ya fito”ba tare da ya yarda ya kalli direction d’in Mommy ba,daga haka ya sa kai ya fice.
Haka nan duk suka fita one by one aka bar Yashjub Najeeb sai Yahanasu,Yusra da Yadira tun kafin a je koina har sun fara dana sanin
abunda suka aikata dan basu yi tunannin d’an uwan nasu zai shiga wannan halin ba,a tunaninsu kawai zai sake ta ne ta tafi shikenan a wuce gurin ba su yi tunanin zai tsaya yana turturing kansa har haka ba su sai yanzu ma kwakwalwarsu ta yi lissafin tabbas
fa zai shiga damuwa da tashin hankali dan a yadda yake son Manubiya dole ya shiga masifa idan aka ce ta yi betraying d’insa…..also! they are not supposed to feel sorry for her amma yadda suka ganta a asibitin a kwance rai a hannun Allah ga ciki ya zube hak
a nan sai ta basu tausayi,shiyasa gaba d’aya suka shiga wani yanayi har sai da su Mommy suka lura.Ya’isha kam ko a jikinta daddana wayarta take yi tana bawa Yassira wadda take office update dan ita da Yasmeen ne kawai babu a wajen sun tafi aiki.Tana gama t
ura mata ta ja ta tsaya jiran fitowar Najeeb su kuma suka wuce.
Suna gama fita Najeeb ya k’arasa ya murza key ya dawo ya zauna a kusa da shi,cikin tattausan lafazi yace”Yash akwai wata matsalar ta daban ne?”
Ya yi masa tambayar yana mai kafe sa da ido,
d’agowa shima Yashjub d’in ya yi ya zuba masa shanyayyun rinannun idanunsa kafin yace”Najeeb tunda nake a rayuwata ban tab’a kwallafa rai a abu kamar Manubiya da Babyn da na rasa a yau ba,a ganinka hakan bai Isa ya jefa ni a damuwa ba?”
Numfashi Najeeb
ya sauk’e kafin yace”sorry for your lost Yash,Allah ya sa mai ceto ne ya baka masu albarka.”
Sau kuma ya sake fesar da numfashi kafin yace
“Yashjub baka tab’a b’oye mini komai ba sai yau dan tabbas na san bayaga b’arin da Manu ta yi akwai wani abun da ya
ke damunka,if not Yashjub d’in da na sani ba zai bar Manubiya a asibiti ita kad’ai a wannan lokaci da tafi buk’atar sa ba.”
Runtse idanuwa Yashjub ya yi ba tare da ya bud’e ba yace”Najeeb ka je kawai,kaina ya na ciwo ina da buk’atar kasancewa ni d’aya!”
Cikin d’an b’acin rai Yahansu tace”Yash amma ka bani mamaki matuk’a!dan inda ace wani ne ya gaya mini cewa ka hau ka zauna akan abunda Doctor ya gaya maka wallahi ba zan yarda ba.”
Da sauri ya mik’e tsaye yace”Yaha plssss.Not now!”
Ya fad’i hakan cik
in d’an b’acin rai.
Itama cikin b’acin rai tace”yanzu zamu yi Yash!yanzu za mu yi saboda yanzu nake so in tabbatar kaine kuwa ko ko dai wani ne mai kama da kai ya zo mana dan Yash d’in da na sani ba zai yarda da k’azafin da Likita ya yi ba.”
Cikin rash
in fahimta Najeeb yace”Yahanasu me kike cewa?me kike nufi kun bar ni a duhu.”
Sai da ta gama zabgawa Yash harara dan ji take yi kamar ta rufesa da duka,tukunna ta juya ga Najeeb tace”Nima d’azu Ummi take gaya mini,Doctor d’in cewa ya yi maganin zubar da c
iki ta yi ta sha har cikin ya zube.”
Da sauri Yash ya lumshe idanuwansa ya koma ya zauna dab’asss