Showing 42001 words to 45000 words out of 259716 words

Chapter 15 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

57

kam tun lokacin da Baba ya fara magana ta fara kuka.

Sosai kukan nata da nasihar Baba suka taru suka kashewa Yash jik

i,shiyasa ya gagara d’agowa yana jin kamar shima ya fashe da kukan.

Sai da aka kiran sallar isha tukunna Baba ya sallameta shi kuma suka wuce masallaci shi da Yash.

Tana shiga d’akin nasu Aisha ta dafe kai tace”shikenan an dawo mana da aiki sabo”

Murm

ushi su inna da Siyama suka yi daga haka suka ci gaba da had’a jakar takeaway d’in da za a raba gobe inshaaAllah a wajen d’aurin aure.

Kamar d’azu yanzun ma

Aisha ce ta yi ta aikin lallashi,especially ma da ta tab’a jikin Manu d’in ta ji zafi rad’au,na

n take hankalinta ya sake tashi……

Da kyar kuwa Manubiya ta samu ta yi sallah dan tashi d’aya zazzab’i da ciwon kai suka yi mata rufdugu,shiyasa Aisha ta ja ta zuwa d’akin su yaMusbah ta bata magani ta sha tukunna tace “ta kwanta anan”dan d’akin nasu ya ci

ka da makwaftan da suka lek’o taya su aiki.

Ba ta dad’e da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita dan har da maganin bacci Aisha ta had’a mata da shi ai kuwa kasancewarta a gajiye kwana biyu ya sanya nan da nan baccin ya d’auke ta.

Ko da Yash ya kira

Aisha ce ta d’auka,yana ji Aishar tace ta yi bacci ya ce “Alhamdulillah”dama aikin lallashi ya so ya yi kafin ya wuce but tunda har an lallab’ata ta yi bacci shikenan dan haka ya yi wa Aisha sallama da godiya daga haka ya kashe wayar ya wuce bayan yayi s

allama da su Baba da kaka mallan………

Washegari.

A d’akin ya Musbah Aisha Manubiya da khairat suka kwana dan tunda Manu ta kwanta sai kiran sallar asubah ne ya farkar da ita,Aisha bata so ta tasheta shiyasa ta cewa su ya Nafi’u su tafi da shi da su Muh

sin da ya Musbah yau d’akin su is occupied

Tana farka wa ta hango Aisha a kan daddum tana nafila,dan haka itama ta mik’e ta fad’a toilet ta kama ruwa ta yi alwallah ta d’auraye bakinta da iyaka makilin d’in da yake available ta fito tana jin yadda jik

inta yake yi mata ciwo dan ba ta saba kwana da manyan kaya ba.

Har ta fito Aisha ba ta Ida ba…darduma itama ta nema ta shimfid’a a gefen Aisha itama ta tada ik’ama domin gabatar da nafila….ta na idarwa aka kira asslatu dan haka ta mik’e ta gabatar da sa

llar asubah….

Sai da suka kammala Azkar tukunna suka gaisa ita da Aisha, ta bata wayar ta..miscalls d’in Yash ta gani na jiya kafin Aisha ta d’auka sai wanda ya kirata around sha biyu na dare da kuma yanzu da asubah.

Sai da ta fara cire wayar a silent tu

kunna ta kira sa…ringing uku ta yi ta kashe dan ta san ko ta bari ya kai k’arshe ba d’auka zai yi ba.

Ko gama haske wayar ba ta yi ba ya biyo kiran,sai da ta d’an d’auki lokaci dai dai wayar tana shirin tsinkewa tukunna ta amsa. Murmushi ya yi kafin yace”

sai an ja min aji tukunna za’a d’auka?kar ki damu gobe by this time na san babu maganar jan aji ko kunya a tsakanin mu dan tuni zan yi fata fata da su.”

Da sauri cikin san kawar da zancen tace”Ina wuni”

Ta fad’i hakan a ranta tana mamakin Yash,a da kam

ar ba ya magana amma ta lura tun lokacin da aurensu ya matso ya zama mai surutu,ko wacce Irin magana in ta zo bakinsa juye mata yake yi,gaba d’aya ya daina jin kunyar ta.”

Ta na cikin wannan tunanin ta ji yace”lafiya Alhamdulillah,matar Yash in the next 5

hours!7 minutes!37seconds inshaaAllah.”

A take ta ji gabanta ya yanke ya fad’i,tana son Yash amman ta rasa dalilin wannan fargaba da tsoron da suka lullub’eta tun shekran jiya suka k’i barinta,tun shekaran jiya hankalinta yake a tashe….

A hankali ta j

i yace”baby!kin yi shiruu,ko ba a yau zan cire kunyar b…”

Cikin katseshi ta ce”na’aam!”

Sai kuma tace”inna tana kirana,bari inje?”

Dariya sosai ya yi dan ya fahimci zillewa take son yi,kylaleta kawai ya yi ba dan wayonta ba….cikin sanyin murya yace”ki g

aida ita….”

Ahankali tace “sai anjima”

Yana wani irin blushing yace”Allah ya kaimu”

Daga haka Manubiya ta yi saurin kashe wayar ta d’aura a kan k’irjinta tana haki akai akai,dariyar da Aisha ta kwashe da ita ne ya dawo da hankalinta cikin d’akin sam ita

ta ma manta da Aisha a d’akin wallahi….

Sosai Aisha take dariya kafin ta mik’e tsaye ta je ta ta tofawa y’arta da take ta bacci add’ua tukunna ta juyo ta kalli Manubiya cike da zolaya tace”Yarinya ba ki ga komai,ba ki ji komai ba.”

Tana gama fad’in haka

ta sa kai ta fice abinta

Da sauri Manubiya ta cusa kanta a cikin cinyoyinta tana mai jin kunya!fargaba da wani irin yanayin da ba ta tab’a tsintar kanta a ciki ba.

Har Yash ya kashe wayar ya ajjiye a gefe bai daina blushing ba,ya jima a zaune yanata

tunane tunane da zumud’i kafin ya mik’e ya fad’a bathroom.

A side d’in Yashjub da ga shi sai Abokansa biyu da suka zo jiya..…gidan kamar ba biki ake yi ba!bakowa,dan side d’in su Mommy ma ba kowa hatta y’ay’an uncle d’inta ma ba su zo ba sakamokon fad’

an da suka yi da ita kacha kacha recently.Yayar Munirat ma ta so zuwa amman sai ta had’u da laulayi mai tsanani shiyasa ta hak’ura akan bayan bikin in ta samu sai ta zo ta ga amarya ta yi Allah ya sanya alkhairi.

K’arfe 7:25am Yashjub ya fito daga wanka

k’arfe 8:00dai dai ya shirya tsaf ya kafa hula ya d’auki makullin mota da wayoyinsa ya zuba a aljihu rik’e da babbar rigarsa ya nufi k’asa sai tashin k’amshi yake yi.

A zaune ya tarar da Abokansa suna breakfast akan dining table ko wanka ma ba su yi ba,t

sadadden agogon da ke d’aure a tsintsiyar hannunsa ya kalla kafin yace”ku yi sauri fa kar ku sa mu makara.”

Dariya d’ayan yayi kafin yace”ango ka sha k’amshi”

“Bai sha ba tukun!wai Yash da gaske yanzu kake so mu tafi?8:00fa yanzun,ba sai 11:00 ne d’a

urin auren ba?”cewar d’ayan

Cikin takunsa ya k’araso ya zo ya chake musu yace”na san 11:00 ne mana amman ai ya kamata mu tafi da wuri pls ku taso in ba haka ba Wallahi zan yi gaba in barku”

Dariya suka yi suka fara tsokanarshi da’mai zumud’i’suna yi su

na k’ak’arin fahimtar da shi akan ya d’an jira amma inaa!sam Yash ya k’i hak’ura,hakanan suna ji suna gani ya azalzalesu suka yi wanka suka shirya8:30am suka fice daga sid’e d’insa,suka je suka gaida Daddy ya yi masa addu’a ya sa masa albarka haka ma Mommy

da Ummi…daga haka suka fice daga gidan shi kam ko breakfast d’in ma bai yi ba.

Tun k’arfe 8:00am unguwar su Manubiya ta san yau akwai gagarumin d’aurin aure sakamokon motocin polisawa da sojoji da suka fara yi musu sallama,kafin 10:00am kuwa taff layin

ya cika da jama’a,duk saurin Yash sai 10:00 am d’in tukunna shima ya samu ya k’arasa unguwar dan suna fita suka had’u da Najeeb da electrician d’in da zai yi wani wiring a gidan dan haka suka d’unguma gaba d’ayansu,da farko Yash so ya yi ya yace musu ‘su

su je su tsaya a kan electrician d’in!shi kuma ya wuce’,sai kuma ya ga idan ya yi haka kamar yayi rashin kara ne ga kuma su Najeeb d’in da suke ta cewa “wallahi idan ya je tun yanzu dariya za’a yi masa,”shiyasa kawai ya hak’ura ya bi su ba dan ya so ba.

10:30am dai dai Daddy da Abhi suka k’araso da tawagar manyan mutane Abokanansu,ba iyaka layin ba hatta titi sai da ya cika da manya manyan motoci na alfarma…….

11:00am dai dai dubban mutane suka shaida d’aurin auren Yashjub Iman kura

Da amaryarsa

Manu

biya Musa akan sadaki naira dubu d’ari uku lakadan ba ajalan ba.MANNUBIYA

(Book 2)

Page 15

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Mai kwalliyar da Aisha ta d’auko tana gama pinning mayafin Manubiya a jik

in d’ankwalin ta suka ji loudspeaker ana sanar da d’aurin auren Yashjub Imam Kura da Manubiya Musa wanda aka gama d’aurawa yanzun akan sadaki dubu d’ari uku lakadan ba ajalan ba…sai kuma hayaniyar maza ta fara tashi…..

Kuka ta fashe dashi ta zube anan k

an katifar,yayinda su Aisha kuma suka shiga jero hamdala,matan da suke shigowa cikin gidan yanzun kuma suka shiga rangad’a gud’a…..nan da nan a cikin mintunan da ba su kai ashirin ba d’akin nasu har ma da gidan gaba d’aya ya cika taff da jama’a ba masaka t

sinke masu hoto da amarya na yi masu Allah sanya alkhairi da hayaniya suna yi,…..itakam Manubiya gaba d’aya fuskarta ta kumbura kwalliyar ma har ta fara d’an gogewa.

Suna cikin haka gwaggo suwaiba ta kira waya,da inna suka fara gaisawa ta yi mata Allah ya

sanya alkhairi sannan ta sake bata hak’urin rashin zuwanta (dan k’iri k’iri jatau ya hanata zuwa)tukunna ta nemi magana ta Manu…..fad’a da nasiha ta yi mata sannan ta sanya mata albarka daga haka suka yi sallama.

Duk yadda Manu ta so daurewa sam sai ta k

asa dan haka ta saki hawayen da take ta rik’ewa,tana yi tana sheshshek’a da jan hanci…..su kansu su Aisha zuwa yanzu jikinsu ya fara yin sanyi

dan sai yanzu suka sake tabbatarwa da cewa “Manubiya tafiya za ta yi ta barsu”ga kuma fargaba da sanyin jiki

n da kan lullub’e kowa kama daga kan Amarya zuwa kam y’an uwanta

tashi d’aya duk sai ya lullub’esu gaba d’ayansu.

Jidda ce ta fara fashewa da kuka ganin haka yasa itama Siyama ta saki nata kukan da take ta k’ok’arin dannewa,murmushi kawai inna da mama su

ka yi suka ci gaba da harhad’a abubuwan da sukeyi ba tare da sun yi yunk’urin lallashinsu ba dan sun san muddin suka doshi inda suke tau tabbas suma kukan za su yi. Especially ma Mama wadda hankalinta yake a matuk’ar tashe sannan kanta ya d’aure katamau tu

n lokacin da ta ji an ambaci ‘imam kura’ ta san maybe coincidence ne amman dukda haka sai da ta shiga cikin tsananin fargaba.

Dakyar Aisha ta daure ta k’arasa inda Manubiyan take da niyyar lallashinta amman tana zuwa itama kawai sai ta fara hawaye.

D

ai dai nan anty umma ta shigo tana cewa”Siyama ku zo ku tayani fara zuba abinci kuna mimmik’awa jama’a ga mutane chan suna ta shigowa har a b’angaren su Uncle,sannan ku kira su Musbahu a samu a fitar da takeaway d’innan kafin jama’a su watse…...”

Salati t

a saka ganin yadda suke shirin mayar da d’akin kamar na zaman makoki,k’arasa shigowa cikin d’akin ta yi ta ajjiye k’atuwar kular hannunta tukunna ta k’arasa inda suke suka shiga lallashin Manu ita da ragowar matan da ke cikin d’akin.

Da kyar aka samu su

ka yi shiru kuwa tukunna ahankali cikin mutuwar jiki Aishar tace “Bari inje mu fara mik’a abincin”

Mik’e wa su Jidda suka yi suma suka bi bayan Aisha……

Duk wannan girkin da hayaniyar d’aurin auren da ake ta yi babu wanda ya lek’a ya taya su inna girki sa

i anty umma sannan kaff gidan ya Yusuf ne kawai ya lek’a wajen d’aurin auren sai kaka mallan wanda ya daddannawa Baba Habu zagi da ya so ya hanashi zuwa….sune ba sa kula Baba kuma fa ya bisu ya basu hak’uri ya fi sau nawa, shekaran jiya ya bi su ya basu in

vitation amman sunce”wai sau d’aya ya gaiyyacesu sannan bai sako su a cikin al’amarin sosai ba,sannan lokacin da aka kawo kud’i a gaban sa Nafi’u ya so yiwa Baba Habu rashin kunya amman bai ce komai ba sai da ga baya ya biyosa zai basa hak’uri tsabar ya ra

ina musu wayo.”

Shiyasa yanzun ma ba su je ba kuma ba su turo matayensu hidimar mata ba,kaka mallan ma sun so su hanasa zuwa amman ya k’i hanuwa dan shi tun

sassafe ma ya shirya ya sanya farar shaddarsa ta sallah ya nufi masallaci bayan ya yiwa baba habu

kaca kaca…da shi kuwa aka dinga tarar bak’i…..babu wanda ya lura da su ba wanda ya san da su amman haka suka dinga faman shishshigi a wajen da shi da Yusuf!shi Yusuf connection yake nema Kaka mallan kuwa maula tuk’uru ya dinga yi a wajen dan ko marok’in wa

jen bai kai ya shi a iya maula da tara abun duniya a wannan rana ba.

Ba wanda ya fi tsanar sa a kaff wajen kamar Yassir dan ji yake yi kmr ya d’auke shi yaje ya jefa a rami kowa ya huta,ya tsani tsohon nan haka kurum bai mishi ba tun farkon had’uwar su. Y

a tsani layin…gaba d’aya kunyar Abokansa guda biyu

da suka zo d’aurin auren tare yake yi,shiyasa fa dama shi bai gaiyyaci kowa ba! waennan d’inma dan Yashjub d’in ya sansu ne shiyasa ya gaiyyacesu da kansa su kuma suka zo,tun da suka shigo layin suke ta

jero masa tambayoyi “me ya kawo Yashjub nan?

a nan kuma matar tashi take?”waye waye…..

Tou kuma yanzu ga kakan ta

wanda idanunsa suka rufe har Yashjub d’in ya je ya cewa” ya bashi kud’in da za a rabawa almajirai anjima ayi musu sauk’a” ……

Anan cik

in gida kuwa

Su anty amarya suna nan a d’aki har yanzu ba wanda ya lek’o ko murna ko taya aiki,sun so su d’an lek’a su yi murna amma sai mazajensu suka sake hanasu,hatta su Salaha rufe su a d’aki maman su tayi hakanan Yaran suka hak’ura ba dan sun so

ba….sai dai kuma ko minti talatin ba ta yi da rufe k’ofar ba aka zo aka fara bubbuga mata tana bud’ewa ta ga mak’oftan da take shiri da su ne suka shigo wunin biki hakanan suka shige suka zazzauna mata,kafin minti d’aya parlourn nata ya cika har ma da na

su Baba Habu suma duk sai da aka shiga, ba yadda suka iya dan duk wanda ya fi shiri da su a neighbors idan ya zo wajen su ya ke zuwa ya zauna bayan ya je ya ga amarya….

Su siyama ma haka suka dinga kai abincin suna ajjiyewa da fara’a a fuskokinsu kamar b

a su san me ma suka yi ba,shiyasa gaba d’aya kunya ta kama su ga shi dai ko Allah sanya alkhairi ba su je sunyi ba amman wunin biki ya kankama a parlourn su.

…..

Anan waje kuwa sun sha hotuna abunsu…haka aka yi komai aka kammala da ikon Allah cikin kwan

ciyar hankali da tsananin farin ciki. Sai da su Daddy suka wuce Abokan Yash ma duk suka wuwwuce dan bai cewa kowa zai shiga ya ga amarya ba saboda tsabar kishi, tukunna shi da Najeeb suka k’arasa wajen ya Musbah wanda suke tsaye da shi da ya Nafi’u suka

mik’a musu hannu suka yi musabaha suka yiwa juna Allah ya sanya alkhairi kafin Najeeb yace”Am,muna so za mu ga amaryar

za a d’an yi

hoto,sannan za mu gaida su inna”

Ahankali ya Musbah wanda gaba d’aya yake jinsa upsidedown ya jinjina musu kai kafin y

ace”Bara in sanar da su

Innar”

Daga haka ya wuce ciki….

Su Siyama suna gamawa,suka yi sauri suka shiga wanka dan Aisha su take jira suje su kwashi kaya su kai gidan amrya,suna fitowa suka shiga shiri da hanzari…ba komai a fuskokinsu sai Vaseline anko

n

su da suka yi na atamfa shi

suka saka dan har Aisha

Itama shi ta saka da mama,

A shape aka yi wa Siyama Jidda kuma riga da skirt

Atamfar kalar light blue ne da white shiyasa ta karb’i jikinsu ta sake fito da ainihin kyawun hasken fatar su…Tsayin

su kusan d’aya ne sai dai Jidda ta d’an fi Siyama jiki kad’an.

White vail Siyama ta rufa ta yi d’aurin ta mai kyau,Yayinda Jidda ta rufa blue vail itanma sosai d’aurin ta ya yi kyau.

Suna fitowa daga side d’in su Siyama suka had’u da ya Musbah…sak’on Ya

shjub ya gaya musu saboda d’akin su innar ya cika taff shiyasa bai samu ya iya shiga ba,yana gama gaya musu sak’on ya juya ya koma d’akin shi ko waje wajen Nafi’un ma bai koma ba dan kansa wani kalar azababban ciwo yake masa..ba daban bai yarda da tsubb’ac

e taubb’ace ba to da babu abunda zai sa ya k’i yarda da cewa ‘Baraka tsafi ta yi masa!’idan fa ya rufe ido har ganinta yakeyi sannan ji yake kamar ya je ya d’auko ta kawai ya dawo da ita,bai tab’a missing mutum kamar yadda yake missing Baraka ba

sannan a

iyaka kwana biyu kawai ya ji soyayyarta da k’aunarta sun dawo mishi sun zauna daram sun mamaye koina sab’anin kwanankin baya da ya tsani ya ji ko da sunanta ne. Dama tun sati biyu bayan da ya sake ta ya fara jin hakan amman abun bai yi worst kamar yanzu b

a.

A shagub’e ya d’an gwada tuntub’ar Nafi’u ba wai direct ba,amsar da Nafi’un ya basa yasanya ya fahimci tabbas indai har ya dawo da Baraka to Abotarsu za ta iya tarwatsewa,shi kuwa a yadda yake jin Nafi’u yanzu ya ma fi k’arfin Aboki a wajen sa sai da

i d’an uwa shiyasa sam ba ya son abunda zai shiga tsakanin su…..to Nafi’u ma ya nuna baya so ballantana kuma inna

wadda akayiwa abun!

Shiyasa gaba d’aya yake a burkice bai ma san ta ina zai fara kallon family d’inshi yace musu ‘zai dawo da Baraka’ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login